BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 1️⃣1

by @prettys01

> "Promise!! Promise!!." sai suka yi murmushi suna shiga wajen..............

2h suka yi a cikin wajen, sannan suka tashi, mota suka koma fuskokinsu ɗauke da farin ciki na daban, hanyar da suka biyo ta nan suka koma, bayan ya sun isa wajen da ya yi parking motarsa, suka mai da ma Mazan nan key ɗin su, sannan suka shiga motar Al-hussain, daga nan suka isa in da motar Merry yake, ta fita bayan sun yi sallama, ita ta nufi Company shi kuma ya nufa gida duk yana tunanin Marwa, dan yasan ta kira sa ya fi sau ba adadi, shi kuma baya zuwa irin wajen nan da wayarsa.

Ko da ya isa, masu aiki ne kawai, sai ya shiga part ɗinsu, wayarsa yana kan dressing mirrow, ya ɗauka, take ya ga missed calls masu yawa, 6 daga Al-hassan, sai 7 daga Marwa, zama ya yi sannan ya fara kiran Al-hassan.

"Lafiya lau, na fita ne na manta da wayar a gida." Ya faɗa yana shafa suman kansa, ta cikin wayar Al-hassan ya sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana cewa.

"Duk hankalina ya tashi wallahi, ka kula dan Allah, bana son kana fita ba tare da nasan in da ka tafi ba."

"Sorry My Tweeny."

"Shike nan, yau za ka wajen Marwa ne?."

"Eh amma sai anjima."

"Ok, Please ka dinga kula kaji." Sai ya ɗaga mai kai kaman yana ganinsa, daga haka ya katse kiran, take ya kira Marwa bugun zuciyarsa................

*****************

Abba aiki yake sosai, sai wajen zurh ya samu ya zauna a office, Marwa ya iska tana ta aikin da ya ɓata, zamansa ke da wiya, yaji ƙaran saƙo, da kamar ba zai duba ba sai ya duba, ganin SMS daga Yaya, yasa ya buɗe. 'Ga Number Najlah Rigima.' a ƙasan kuma numberta ne.

Take ya zaro ido yana sake duba saƙon, besan lokacin da ya daki desk ɗin dake gabansa yana cewa.

"Wow!! Wow!!! Wo......" da sauri ya haɗiye maganar yana kallon Marwa da ta zuba mai ido alaman tana neman ƙarin bayani.

"Lafiya kake wannan murnan?." sai ya yi murmushi sannan ya ce.

"Wani deal ne ya faɗo min, na jima ina jiransa ashe dai zan samu." Ya faɗa yana mazewa tare da fara latsa system keyboard yana rubutu NAJLAH da alaman heart a jiki.

Marwa kuwa baki ta taɓe ta ci gaba da abin da take yi, dan ya isa ta gama aikin amma Al-hussain be barta ta gaba ma saboda wayarsu da baya ƙare wa.

Da misalin 4:30pm, Abba da Marwa suka ɗauko Basma da Fauza, sannan suka nufa gida, tunda suke mota suke tambayar Abba farin cikin me yake yi sai ya girgiza kai kawai.

Suna isa gida suka iske masu aikin da suka sa a kawo sun iso, Abba dai ba bi ta su ba ya haura sama, Su kuma suka zauna suna kallon matan da suke a tsugunne cikin ladabi suna gaishe su.

Marwa ba ta da matsala akan su, dan haka chart take yi da Al-hussain, Basma kuwa ta gyara zama tana bin su da kallo.

"Ina son kowacce ta faɗa min sunanta." Ta faɗa tana kallon Fauza dake nufan part ɗin su dan sauya kaya.

Ba musu matan nan suka fara faɗin sunayensu a natse, Basma ta kalla lukutaye biyun da suke ciki ta ce musu.

"Suwaiba ke da Atine ku ɗan bamu waje." Ba musu suka tashi suka fita.

Saura Rakiya, wacce ta kasance siririya kamar one, sai dai tana da manyan idanuwa masu kyau, ta biyun kuma A'isha, gajera ce amma yana ɗan jiki, baƙa ce sosai, kuma ba ta da kyau a fuska sai a jiki, sai ta karshen, Basma na kallonta ta rintse ido sannan ta buɗe tana cewa.

"Kema yi ɗan bisu." ba musu yarinyar ta miƙe, ta fara tafiya a natse.

"Munafuka." Cewan Basma a natse tana bin ta da kallon ƙasa-ƙasa, dan kuwa yarinya ce budurwar, wacce ba za ta wuci sa'ar ta ba, Choculate ce amma tana da ƙyau, gaban dai babu komai amma baya kuwa, akwai su masu tudu da cika ido.

Sai Basma ta ce.

"Ke fara ke ce mai girki, daga Kitchen sai ɗakin kwanan ku, ke kuma baƙar ke za ki dinga jerawa a falon nan, sannan sanya hijabi har ƙasa wajeeb ne, zan sa a dinƙo muku Hijab da kayan aiki, sannna idan wani abu ya haɗaku da Abba, na ku bin umarni ne kawai, bance kowacce ta mai magana ba, ku zama kamar bebaye idan yana nan, bansan wasa da aiki, in mutum na son ya jima da mu, to tabbas ya bi doka ya zauna lafiya. Abu na ƙarshe kuma ba wai na baku aiki bane, sai na ga yanayin aikin naku, ku kasance masu tsafta da iya girki, ku shiga da kayanku wancan ɗakin, sauran bayanai kuma zan ƙara sa muku." Ta kai nan tana nuna musu ɓangaren su, godiya suka hau sosai sannan suka nufa in da ta nuna musu.

"Kin iya zaɓe, dan kuwa tun da na kallesu a biyun nan na fi ba da za ki zaɓa." sai ta kalla Marwa ta yi murmushi.

"Allah yasa karsu ba da matsala, dan a halitta sunyi, saura a aiki. Kema ina fatan sun miki?." ta yi tambayar tana mai da idanunta kan Fauza wacce ba ta jima da saukowa ba.

Kai ta ɗaga tana cewa.

"Zan sa ido akan tsaftarsu in ya yi shike nan."

"Ok, bara na sallame wa'incan tiƙa-tiƙan Mutanen." Da haka ta miƙa ta fita, Fauza kuma ta miƙe ta kunna t.v tana ɗaukan remote..........

Abba yana shiga room ɗinsa, sai ya murza ma ƙofar bedroom ɗinsa key, abin da be ta ɓa yi ba.

Zama ya yi gefan bed sannan ya ɗauki wayarsa ya yi copying number sannan ya shiga contact ya yi pesting number ya danna kira, yana fara ringing ya ji wani sanyi ya mamaye mai zuciya, ya lumshe ido, ya ɗauki pillow ya rungume tana ta murmushi dai, wayar ya katse sannan ya sake kira yana jero addu'a akan Allah yasa ta ɗauka, kiran har ya kusa katsewa sai aka yi picking.

Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya jinjina da gadon yana mai yin sallama cikin tausasa murya.

"Assalamu Alaikum warahmatullah." A natse kuma cikin shigar shaƙwaɓa wanda Abba ya ji tasirin har cikin zuciyarta ta amsa.

"Wassalamu alaikum warahmatullah." Sai ta yi shuru, shi kuma ya yi gyaran murya sannan ya kuma cewa.

"Ya jikin Najlahh?."

"Alhamdullah, wake magana dan ban gane muryan ba." Sai ya shafa suman kansa sannan ya ce.

"Abokin kine, a wajen General na samu number ta ki.".............

Ɓangaren Najlah kuwa, tana kwance ne take amsa wayar, jin abin da ya ce yasa ta zaro manyan idanunta ta ce.

"Laaa kaine?, Ya na ji muryanka ya ƙara zaƙi." Ta faɗa tana murmushi, shima murmushi ya yi.

"Kin iya zolaya wallahi, muryan tawa da yake kama da dukan durom shine akwai daɗi?."

"Hmm sosai yana da shi, fiye da yarda kake zato." sai ya yi dariya.

"To ya jikin an ce kunsha dambe, kuma har kin barshi a kwance."

"An faɗa maka Ni ta wasa ce? Ai kaɗan ma ya gani, sai ma na koma next week, zan je na fama ciwukan da suka fara warkewa."

"Kai Najlah, mugunta babu ƙyau, ya kamata ki dinga jin tausayi mana."

"Aboki kenan, sam banda tausayin azzalumai, kasan Allah saboda haka nake kallon fina-finan Korea da Chinese." Sai ya murmusa.

"India fa?."

"Ina kallo sosai shima, dan sun iya soyayya mai shiga rai."

Sai Abba ya gyara zama sannan ya ce.

"Kina soyayya kenan?." ya tambaya yana jin gabansa yana sauya duka.

"Soyayya, uhmmm ban fara ba saboda har yanzu ban samu wanda ya min ba." tana jin sautin da ya sauke.

"To wani irin saurayi kike so?." Sai ta yi dariya mai sanyi.

"Zan faɗa maka amma ba yau ba, amma me yasa ka nema numberta kuma ka kira?." Yana jin tambayar sai ya rintse idanunsa sannna ya buɗe.

"Ban iya ɓoye-ɓoye ba sam, tun a ranar da idanuna suka sauka a kanki na rasa natsuwa ta gaba ɗaya, hakan yasa washegari na kuma zuwa dan ganinki, cikin ikon Allah na samu damar da muka yi magana mai tsayi, sa'anan yau na kira General da ya haɗani da ke a waya...........bansan ya zan kira yanayin da nake ji ba, amma ina son na dinga ganinki a kusa da ni, kallonki na sanyi nishaɗi fiye da misali........sai dai Ni tsoho ne, nasan na yi miki tsufa." ya kai maganar cikin wani irin yanayi.

Najlah mamakin maganarsa ta yi duk da kuwa a iya firarsu ta fahimci yana sonta ne.

"Uhmmm matarka fa to?." ta tambaya tana lumshe ido.

"Matata ta jima da rasuwa, a ƙalla za ta kai shekara 8-9 haka, sannan ina da yara mata uku, kuma sun girma, a kodayaushe suna iya aure su barni, wallahi Najlah zan kula da ke kamar ƙwai, zan tarairayeki har zuwa mutuwata, ba zan miki dole ba, saboda nasan Ni ba sa'an aurenki bane."

"Uhmmm na ji, amma sai dai na baka haƙuri gaskiya, bazan iya aurenka ba, duk da kuwa bani da burin da ya wuci na auri babban mutum mai cikar kamala kamar dai kai.........sai dai har ga Allah ba zan iya aurenka ba." ta kai ƙarshen maganar cikin sanyi, shi kuma ya ji gaba ɗaya duniyar ta yi mai zafi.

"Me....meya.....meyasa to?." ya faɗa har bakinsa na rawa, sai da ta yi shuru na tsawon lokaci sannan ta ce.

"Ka ce za ka kula dani.........ka za tarairayeni..........sannan za ka ban farin ciki har ƙarshen rayuwarka, gaskiya idan dai shike nan to ba zan iya aurenka ba........." Da sauri ya katse ta.

"To me kike so kuma?."

" *RIGIMA* , bani da burin da ya wuci na aura mijin wata, shi yasa nake son auren Babban mutum, kaima na za ci tana raye ne, amma da ko magana ma ba zan yi da kai ba, yarda baka iya ɓoye-ɓoye ba, haka nima ban iya ba, hmmmmm ka yi rayuwa wajen da ake rigima shima wani abu ne, ina so na ga tsantsar kishin wacce zan aurar wa miji a fili, kai na aureshi na zauna mata a gida, ta yi haukan kishi Ni kuma na biye mata mu hargitsa gida.........kasan Allah ko yayane Ina son rayuwa a gidan da zanyi rigima ko yayane, kawai ka haƙura gaskiya." Ta kai nan tana jin sautin dariyarsa, sai na tashi daga bed ɗin ta nufa wajen mirror ta tsaya.

"akwai mace irin haka? Wake aure dan neman abokiyar rigima?."

"Ni, hmmm ko da nake yarinya, idan ina kallon Film ɗin da ake zuba kishi na bala'i, sai na ji ƙaunar gidan ya kamani, haka nake son irin gidan, da zarar Abbu ya dawo daga wajen aiki zan tambaye sa *Yaushe za ka yi ma Mamie Kishiya*, sai ya yi dariya kawai, Mamie kuna ta kamani da dukka, haka washegari zan kuma tambaya, da na ishe su Abbu, sai ya tsambayeni. 'Me yasa kike son a yi ma Mamie Kishiya?. Ba kunya zan ce 'Saboda a dinga rigima ina kallo.' sai Abbu ya ɗaya min kai, daga wannan lokacin ya dinga min ƙaryan wai an kusa bikin, ko da na girma ban dena tambaya ba amma ba'a kusa da Mamie ba, haka dai har Allah ya jiƙansa be mana kishiya ba.." ta faɗa cike da kewan Abbu.

"Allah ya jiƙansa."

"Ameen Nagode, to ga bazan yarda na aura mara mata ba." sai ya yi gyaran murya sannan ya ce.

"Kin kawo kuka gidan mutuwa, tabbas banda mata, amma ina da yara mata, wanda suka yi gadon kishin mahaifiyarsu, sai na su ma ya ɗara na uwar................" daga nan ya shiga ba ta labarin damar da yake sha idan ya ɗauko aure, hatta mace be isa ya yi mu'amula da ita ba, labari ya ci gaba da ba ta Najlah kuwa sai dariya take yi, sai a ƙarshe ya ce.

"To kinga ina da jarabbun ƴaƴa, balle ma Basma."

"Wayyo cikina, wai dama akwai yara irin haka? Ikon Allah, gaskiya yaranka sun burgeni, zan yi tunani a kai." Take farin ciki ya cika Abba, besan lokacin da ya fara gode Allah ba, Najlah kuma ta yi dariya tana cewa.

"An jima zan baka amsa, yanzu zan yi wanka." ba dan ya so ba ya ce.

"Shike nan, zan jira kiran na ki dan bansan na takura miki." murmushi ta yi sannan suka yi sallama.

Tana aje wayar ta tashi dan sake watsa ruwa.

Abba kuwa tsabar farin ciki rungume pillow yana ɗan dariya ƙasa-ƙasa, yarda kasan an mai bushara da gidan Aljanna haka yake ji.

Tashi ya yi ya koma kusa da mudubi fuskarsa ya ke kalla, sai ya ga kaman ya fi ko yaushe ƙyau, kalmar da ta furta mai ranar nan shi ya tuna *Zuƙeƙen saurayi.* Sai ya lumshe ido, a hankali ya furta.

"Allah yasa ta amince da ni." da haka ya tashi ya shiga restroom dan watsa ruwa..................

**************

Babban hotone da ya cinye kusan bango ɗaya, Al-hassan da Al-hussain suka tsura ma mahaifiyar ido, suna kallonta kowa da abin da yake saƙawa, Al-hassan kallonta yake kawai, daban yana farin ciki da kasancewar a matsayin mahaifiyar su, sai dai babu yarda ya isa, ita ce dole ɗin sa, ko ya so ko a'a. Wani abu ya tuna akanta hakan yasa ya juya yabar ɗakin da sauri.

Al-hussain kuwa da idanunsa suka sauya launi saboda tunanin mahaifiyar ta su, sai ya bi bayan Al-hassan da kallo, yana tuna kalaman mahaifiyarsu na ƙarshe.

_Flash back_

A wani lokaci a can baya, Mom tana kwance a gadon asibiti, cikin mawiyacin hali, a haka ta umarci doctor da ya kira mata yaranta, ba musu ya fita ya kira su, su uku, a lokacin Tween suna da shekara 17, ita kuma Merry tana da shekara 13, suna shiga suka nufa Momy da sauri, hannunta duk suka riƙe suna hawaye.

Momy ta kalla Al-hassan, haɗe fuska ta yi tana cewa.

"Al-hassan kira min Abbeey." Sai ya ɗaga kai, da sauri kuma ya fita, yana rufe ƙofa idanunta suka sauka kan Al-hussain da Merry.

Cikin ƙarfin hali ta share musu hawaye tana ce musu.

"Ku kula da kanku, ku riƙe wannan sirrin dana baku, ko Al-hassan bana son da yasan komai akan *Promise* ..............badan kai ba Al-hussain, da ko kulashi ba zan dinga yi ba, bana ƙyaunarsa sam, na tsanesa fiye da yarda kike tunani, kawai dan kai da kuma kar Abbeey ya fahimci komai akan *Promise* ɗin nan ne, amma ku yi min alƙawarin za ku riƙe sirri nan?." ta kai nan tana jin zuciyarta na yi mata zafi.

"Momy, karki damu, har abada zamu kasance masu bin duk wani abu da kika ɗaura mu, muna alfahari da ke." Sai ta ɗaga musu kai tana ƙara matse hannun Al-hussain cikin na ta.

A take kuma ta fara shaƙuwa tana yi kaman numfashi ta na ɗauke wa.

Merry ce ta fita da gudu tana kiran Doctor, shi kuma Al-hussain ya ruɗe yana jera mata sannu.

" Ka kula da ƙanwarka, ka kula da PA.1, sannan kar kowa yasan menene promi......" Daga nan komai ya tsaya cak, Momy numfashi ta ya tsaya, wanda ya tsaya da buguwar zuciyar Al-hussain, dan take ya suma.

Wanda sai da akayi da gaske ya dawo dai-dai, daga wannan lokacin kuma Al-hussain ya fara sauya ma Abbeey, duk umarnin Abbeey baya bi, wani lokacin ne ma yake sassauta yanayinsa saboda Al-hassan, haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya..........

_Ci gaba._

Hawaye ne suka gangaro mai, ya sanya hannu ya share, sannan ya ce.

"Momy ina kewanki, kuma ina ƙoƙarin ganin na yi duk wani abu da kika ɗorani akai, ina dai fatan hasken aikin nan ya iske ki, da haka ya juya ya fita daga ɗakin yana jin zuciyarsa na mai raɗaɗi.....................✍️ END. ```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.