PAGE 1️⃣2
by @prettys01
> "Momy ina kewanki, kuma ina ƙoƙarin ganin na yi duk wani abu da kika ɗorani akai, ina dai fatan hasken aikin nan ya iske ki, da haka ya juya ya fita daga ɗakin yana jin zuciyarsa na mai raɗaɗi.........
*************
Kwance tashi asaran mai rai, yau a jera kwana huɗu kenan Abba da Najlah suna waya cike da kulawa, amma har zuwa yanzu ba ta furta mai tana son shi ba, ta dai amince mai za ta auresa.
Kamar kullum sai bayan ya iso office suke fara waya, haka yau ma ta kasance, bayan ya shiga ya zauna, sannan ya kira wayarta, sai dai har kira uku ba ta ɗauka ba, da haka ya bari zuwa anjima za ta biyo kiran.
***************
Najlah jikinta ya warware sosai, amma sai Monday za ta koma school, sannan a cikin kwanakin nan ba ƙaramin sabawa ta yi da Abba ba, har cikin ranta ya yi mata, ballema da ta samu labarin su Basma, sai ta ji gaba ɗaya Abba ya yi mata.
Zama ta yi kan kujera dake Garden, tana mai da numfashi, dan kuwa duk girman wajen ta dinga zagayewa tun safe tana motsa jiki.
Fuskarta ta wanke da ruwa tana jin gina da kujeran.
"Ashe dai horo da daɗi, wallahi na yi missing makaranta." ta faɗa tana miƙa wa sannan ta ƙara sa cikin ɗaki.
Bedroom ta shiga, tasan Abba ya kirata zuwa yanzu, dan haka ta ɗauki wayarta, ilai 5 missed called ta gani, sai ta yi murmushi tana bin kiran.
Kiran na katsewa sai ga kiransa video call, sai ta yi murmushi tana kallon jikinta.
Riga da gajeren wando ta sa, amma masu girma ta yarda shafe ɗin jikinta be fita ba, sai gashin kanta da yake a gyare ya kwanta har baya, ta ɗan ɗaura band akai.
Pecking ta yi tana jingina wayar da jikin mirrow.
A lokacin guda kamilalliyar fuskarsa ta bayyana yana zabga murmushi, sai ita ma ta mai da mai sannan ya ce.
"Yabo da godiya su ƙara tabbata ga Ubangijin wannan halittar."
"Kaima haka, dan kuwa Masoyina na wa Allah ya mai cikar kamala da haiba." Dariya suka dan yi.
"Wallahi Baby kina da ƙyau." ya faɗa ba tare da yaji nauyin kalmar ba.
"Na gode Babyna." Ta furta a karo na farko, wani dan ihu Abba ya yi yana cewa.
"Sake faɗa dan Allah." sai ta shaƙwaɓe fuska, sannan cikin muryan nan mai fizgar mai zuciya ta kuma cewa.
"Babyna." Lumshe ido ya yi, sai ya ce.
"Baby kina sona?." ya tambaya yana ƙare ma fuskarta kallo.
Kai ta ɗaga mai tana ɗan rufe fuskar da tafin hannunta.
"Gobe zan shigo Kaduna, sannan ina zuwa zan zo dan na ga sanyin idanuna."
"Awwwwnnnn shike nan Babyna, Allah ya kawo ka lafiya."
"Ameen, amma dai ƴan gidan ku ba za su hanani ke ba ko?."
"Nikam me yasa kake kallon kanka a dattijo, Babyna ka dinga kallon mudubi, kai Very handsome Guy ne, ga ƙyau, ga gayu, ga murmushi mai sanya natsuwa." sai ya yi dariya.
"Hira da ke na sanyi nishaɗi, gashi aiki nake yanzu, kuma bansan barin ki." Sai ta lanƙwaɓa kai.
"Karka damu, ina jiranka idan ka gama." Da haka suka yi sallama suna masu jin soyayyar junan su.
Najlah ta aje wayar sannan ta shiga restroom dan watsa ruwa................
***************
Su uke suke zaune suna cin abinci a Dining, amma hankalinsu yana kan Abba, wanda a kwana biyun nan gaba ɗaya ya sauya, baya iya ɓa ta lokaci yana hira da su, bini-bini kuma yana latsa waya yana murmushi, ko abincin kirki baya ci sosai, da ya fara in yaga sun zuba mai ido sai bar wajen.
"Me ya samu Abba ne? Gaba ɗaya ya sauya."
"Baseey ashe kin gani, tun ba yau ba na lura da haka." cewan Fauza, sai Marwa ta ce.
"Hmmm zamu gano ko ma menene, dan ba faɗa zai yi ba, na ma fi ba da ko game yake yi." Sai suka bar zancen duk da kuwa kowa da abin da ke cinsa a zuciya.
Bayan sun kammala suka dawo parlour, duk suka zauna suna kallon Abba, ganin haka sai ya aje wayar yana dubansu.
"Ku shirya da wuri zamu tafi goben, ku kwanta da wuri kar mu makara, nima barcin nake ji." Da haka ya miƙe, yana ɗaukan wayar, take kira ya shigo sai ya ɗauka yana tafiya tare da cewa.
"A'a kawai ku tura mai dukka kayan in ya so sai ya su raba." Da haka ya yi nisa har basa jinsa.
"Hmmmmmm." Basma ta yi ƙwafa tana sauya channel.
Marwa kuwa waya ta ɗauka suka ci gaba da chat da sahibin ruhinta.
A daren suka haɗa kayansu, washegari kuwa da misalin 9:00am jirginsu ya ɗaga sai Kaduna, Fauza ce kawai ke murna dan za ta ga ƴan uwanta, Marwa da Basma kuwa sun haɗe rai suna ta cin magani.
Cikin ikon Allah suka sauka lafiya, Motoci biyu ne su ka ɗauke su, sannan suka nufa family house ɗin su.
A Compound suka iske su, suna tsaye suna dakon ganinsu, motocin na parking, Suka nufa wajen motan dukkansu.
Marwa ta dafa Basma ta ce.
"Ko dan farin cikin Abba, mu saki ranmu dan Allah." Sai ta ɗaga mata kai tana yin yaƙe.
Suna fita aka fara musu maraba cikin soyayyar dangi, sai dai murmushi kawai suke yi a fuska, Fauza ce kawai ta zage suna wasa da dariya.
Hatta Amare suma suka fito suna cike da murna ganin su Basma.
Gida kuwa ya fara cika dan washegari ɗaurin aure, jiya suka yi Fulani day gobe kuma dinner, yau da yamma kuma akwai *Yaumul Quran*.
Ɓangare na musamman Matar Yaya ta sa aka sauke su, bayan an taimaka musu da kayansu ciki, babban ɗaki ne mai ɗauke da manyan gado guda biyu.
Fauza tana dire kayanta ta yi waje, Basma kuma ta kwanta dan ba ta son hayaniya kwata-kwata.
Abba kuwa a part ɗin General ya sauka, bayan ya zauna ya kira Najlah tare da shaida mai ya iso, nan fa ta mai Barka da zuwa, sannan zuwa yamma zai shigo.
Gida ya cika sosai, ana ta shirin *Yaumul Qur'an* in da mata ɗaluban islamiyya suka cika gidan, duk cikin Hijab kalan Blue, sai niƙaf, Amare kuma suka sa fararen hijabai.
Gidan yana da girma sosai, dan haka gefe guda aka yi decorations wajen, ana suka zauna aka haɗa speakers, aka fara karatun Alqur'ani, kowacce in da za ta karanta in da take so a cikin Alqur'ani.
Take gidan ya saukar da wani irin ni'ima na musamman, Fauza ma sai da aka ba ta irin Hijab ɗin ta shiga cikin su.
Marwa tana daga gefe tana musu video dan ba ƙaramin burgeta suka yi ba, tana musu tana zabga murmushi.
Basma kuwa tana cikin ɗaki ko fitowa ba ta yi ba.
Sai magrib aka kammala bayan an ci an sha an raba Qur'anai da prayer mat, bayan jakka na abubuwan ciye-ciye da aka raba.
Fauza ana tashi ta ci karo da Abba ya sha wani gezna sai ƙamshi yake zubawa, sai ta tsura mai ido tana cewa.
"Abba sai ina da wannan daren?." Sai ya yi murmushi sannan ya ce.
"Autata, Walima aka haɗa ta ɓangaren angon Aneesa, shine za mu je, yanzu haka General nake jira."
"To a dawo lafiya."
"Ameen Autata." Da haka ya yi waje, ita kuma ta bi ƙawarta wacce a cikin familyn na su take.
Abba yana fita, ya shiga mota, sanna ya ba Driver address ɗin da zai kaishi.
Nan take ya ɗau hanya, Abba kuma ya dinga jin ɗan fargaba dan besan ko mahaifiyar Baby za ta amince da shi ba, Maybe ga mai kallon tsoho.
A bakin wani babban gida, Driver ya fama yana cewa.
"Alhaji mun iso."
"Yauwa, bara na shiga na fito." da haka ya fita yana Kiran number Najlah.........
Najlah, less ta sanya blue and pitch, wanda ya ji stone sosai, riga da skirt ne kuma sun kamata tsam tsaf, ba ta sa komai a fuskarta ba sai lips gross, wanda ya ƙara fitowa da pink lips ɗin ta, murmushi ta yi dan tasan ta yi ƙyau, gashi ta jima sosai rabonta da manyan kaya, kullum cikin riga da wando take, sun ma fi mata daɗi a jiki, dan manyan kaya suna damuna sosai.
Ture ka ga tsiya ta yi sannan ta yaga vail, kwalli ta ɗauka ta ɗan zizara a cikin fararen idanunta, take wani ƙara ƙyau, wayarta ta shiga ruri, dan haka ta janyo tana kallon sunnan dake yawo a cikin wayar *Fav* sai ta ɗauka.
"Ok gani nan zuwa." da haka ta miƙe ta zura flat shoe ta fara tafiya ɗaya bayan ɗaya.
Tun daga stairs ta fara jiyo hirar su Adam, dan kuwa ita ta roƙesu da su zo, kuma dama Abba yana son su yi magana, tana sauka daga stairs ta yi wani fari da ido tana cewa.
"Mamiena look at me."
"Wow my dearest girl, you look so beautiful."
"Thanks, Ya Adam." Ta faɗa tana ɗaga mai gira, sai ya harareta yana cewa.
"Sai wani yauƙi kike keba kuɓewa ba, Yayanmu yarda kasan ba Najlah a Barack ba." Sai tayi ɗan dariya.
"Wallahi kam, ƙarfi da yaji Autata ta koma jar wiya, kaman ba mace ba, Amma ku kalleta yau dan Allah, kinyi ƙyau sosai." sai ta isa kusa da Mamie sannan ta rungumeta .
"Ki je kin shanya bawan Allah." sai ta ɗaga kai tana fara tafiya, har ta wuce Yayansu sai ta dawo ta ce.
"Magana yana kisa, wani lokacin ƙwanda mu fesar da abinda ke mana ƙaiƙayi, to na hutashe, nasan cewa za ka yi *Kinyi ƙyau.* " Ta faɗa tana kaurara murya. Sai ya yi murmushi yana ci gaba da latsa wayarsa.
Tana fita compound ta yi ma ɗaya daga cikin sojojin wajen magana, sai ya nufa get, yana zuwa ya buɗe tare da yi ma mutumin da ya gani iso.
Abba ya biyo bayan sa, tunda daga nesa futulun wajen suka hasko mai Najlah, take zuciyarsa ta tsaya da aiki na wani lokaci, kafin ya ci gaba da aikinsa.
Tana tsaye tana jifansa da tsadaddan murmushi, ba ƙyarya ya yi mata ƙyau sosai.
Yana isowa in da take ta sunkuyar da kai tana gaishe sa a tausashe, sai ya amsa yana cewa.
"Tsaf zan iya faɗi idan ban jingina ba, wannan ƙyau haka zai sa na makance." Sai ta yi dariya tana nuna mai hanya.
A hankali suke tafiya, suna ɗan hira sama-sama, duk wanda ya gansu yasan zaren ya hau yadin 💯, dan kuwa sun fito kamar wasu ɗawisu, kamar amarya da ango haka suka yi kama.
Parlourn baƙi ta shiga da shi, inda aka jera kayan ciye-ciye masu yawa, a kushin mai uku ya zauna, yana bin Najlah da kallo, kallon da shi kansa ya kasa fassara na menene shi.
Zama ta yi a kujeran dake kallon nasa, tana ɗan wasa da gefen gyalanta.
"Haka kike da masifaffen ƙyau?." Ta ji ya faɗa a hankali.
"Duk ƙyawun da na yi ai ka fini." sai ta ɗago idanunta suka haɗa ido, murmushi ta yi, shi kuma ya dafe saitin zuciyarsa.
"Wannan murmushin sai ya sa zuciyata ta tsaya da bugawa." Kau da kai ta yi dan ya ba ta dariya sosai.
Da haka suka sha hira sosai, abinci ta gabatar sai ya girgiza kai.
"Kallonki ya cika min tumbina, murmushin ki kuma ya jiƙa min maƙoshi." take ta turo baki, ta fara halin na ta.
"Uhmmm uhmmm Mamie zan kira, na ce kace ba za ka ci ba." Ta faɗa da sigar shaƙwaɓa mai shiga rai.
"Na ƙoshi ne shi yasa."
Ai kaman tana jira ta fara buga ƙafa a ƙasa tana turo baki.
"Da hannuna na yi maka fa, amma...amma shine ba za ka ci ba."
"Ah gaskiya zanci, ashe hannun Babyna ya girka, ki bari idan zan wuce sai kimin takeaway."
"Yauwa ko kaifa." Ta faɗa tana murmushi, sannan ta miƙe ta koma kusa da shi.
"Baka lura da wani abu ba?."
"Kaman mene?." Sai ta ja gyalenta ta rufe fuska.
"Uhmmm ka cinka mana." Shuru ya yi amma shi bega wani abu ba.
"Kin yi ƙyau fiye da kullum, manyan kaya suna ƙara fito da surar da Allah ya miki."
"Ba shi ba, wani abu na daban."
"Wani abu....kaman mene?." Sai ta yaye gyalen sannan ta ce.
"Tsakani da Allah, har jin yunya na koya yau, saboda zuwanka, baka ga sai faman kunya nake ji ba, an ce yana ƙara ma soyayya armashi amma kai ko gani baka yi ba." Ta faɗa a taɓare.
Dafe kai ya yi.
"Sorry Baby, na gani, kuma ta yi miki ƙyau sosai."
"Ni kam ba zan sake ba, sai na ta tsugunnar da kai ina rufe fuska kamar munafuka, inaaa dama yaune kawai amma ba zan kuma ba." Da haka ta miƙe ta fice shi kuma ya bi bayanta da ido yana dariya.
Ko da ta isa babban parlour, ta yi ma Ya Adam magana akan zai shigo, sai ta koma ta mai iso, Abba babban mutum ne amma har ga Allah sai ya ji nauyi ya kamashi kuma kunya ya ta mai rumfa.
A ƙasa ya zauna yana gaishe da Mamie dake sanye da hijab, ta amsa tana mai Barka da zuwa.
Sai da Yayansu ya yi da daske shine ya hau kujera, nan suka sake gaisawa a mutumce, kafin ya miƙe suka fita, already Najlah ta haɗa mai komai a wani jakka ta riƙe suna ɗan jerawa suna hira.
A bakin motarsa suka tsaya, sai ya amsa jakkar yana mata godiya.
"Yanzu idan suka ƙi yarda da Ni ba?."
"Ba matsalata bane, kai nake so kuma ka yi min, saura me?." Sai ya girgiza kai.
"Hmmm shike nan, ina sonki Baby."
"Nima haka."
"Ki kulamin da kanki, sannan Ni zan zo na kaiki dinner gobe."
"Ah ka bari zan bi su Ya Adam, amma za mu haɗu ai." Sai ya ɗaga mata kai, jigina ya yi da jikin motar.
"Kamar na ɓata tsawon rayuwata ina kallon wannan tauraruwar." sai ta yi daku uku ta matsa kusa da shi sannan ta mai raɗa.
"Ni kuma ji nake kamar na cinye ka, dole Yarana su dinga kishi da Abbansu, dan Allah ya mai ƙyau ne." zaro ido ya yi ita kuma ta juya ta shige gida da sauri.
Sai ya ja dogon numfashi ya furzar.
"Wa ya ga Mamansu Basma." Ya faɗa yana hasaso wanan ranar, da haka ya shiga mota Driver ya kunna suna barin unguwar........✍️ END. ```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.