BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 1️⃣5

by @prettys01

> "To ai naga kuna ta soyewa ne kar kuyi ƙauri shi yasa zan nemo albasa, hakan zai sa man ya jima a huta yana soyuwa." Dariya suka yi dukkansu sannan ya fice, su kuma suka ci gaba da soyewa..............

**************

Su biyu ne zaune a ɓangaren General, saboda babu wanda aka bari ya shiga nan, Abinci ne a gabansu suna ci suna ɗan hira.

"Yauwa Mardiyya na ce ba?." Sai Mardiyya ta kalla Mamie ta ce.

"Ina jinki." Take Mamie ta bata labarin zuwan Abba gida wajen Najlah.

Matar Yaya ta zaro ido tana jin labari.

"Alhamdullah ashe dai da gaske ne da General ke faɗa min."

"Ai cewa na yi zan miki magana dan kuwa bantaɓa ganinsa ba, kuma na ga babba mutumin."

"Eh ƙawata, ƙarin Dadynsu, Abba babbane dan kuwa yana da yara mata uku, matarsa ta rasu tun shekarun baya, ka sake aure abin ya gagara, to yanzu kuma sai gashi ya motsa, kusan kowa ya cire rai da wai Abba zai yi maganar aure kuma."

"Ikon Allah, dama zan tambaye ki be da matsala ko? Kinga dai Najlah fitinanniyace ta ƙarshe, kar yana zamansa ta ɗaura mai hawan jini."

"Kul, a gaba na kike ma ƴar tawa sharri, karki damu, wallahi Abba mutumin kirkine, matsalar dai yaransa."

"Indai kin amince banda matsala dama ƴar ta ki ai neman gidan da za ta dinga rigima take yi." sai suka yi dariya.

"Najlah ba ta ji, yanzu dai kisa ranki a inuwa, wallahi Abba yana da hankali sosai."

"Ƙawata ba sai kin ɓata bakin ki ba na gani ai."

"To ko shiyasa ta ƙi zuwa bikin, kar su haɗu, kuma kinga na zama surikarta."

"Kinsa ba ta son shiga mutane sosai, amma za ta dinner." Daga man suka sauya hirar ta su ta koma na yarda za'a ɗauki Amare, duk da daga wajen dinner za'a wuce da su ɗakunan su, saboda General ya ce sai bayan sun fita mai daga gida ya ɗan ƙa ma mazajen su, daga nan ko ma ina ne suje babu ruwansa............

Ƙarfe 6:30pm aka fara tafiya wajen da za'a yi shagalin, mata da maza sai wucewa suke kowa riƙe da get pass.

Marwa tare da Al-hussain suka wuce, Fauza ta bi wasu ƴan gidan, Basma motar Amare ta shiga.

Suna isa wajen aka shiga ciki, wajen babbane ina da mata da maza sun cika ko ina.

Basma gefe ta koma ganin ƙawayen amarya sun fara bin sautin da M.C yasa musu, suna tafiya suna rawa iri ɗaya.

A gaba ta samu ta zauna, Amare kuma angwaye suka sauko daga stage suka riƙe musu hannaye sannan suka taka da su har sama.

Suma angwaye kaya iri ɗaya suka sanya, kamar na Amare, wajen ya ɗauka haske da walwali na daban, daga nan aka fara abin da ya tara mutane.

Abba ko da yake ɓangaren iyaye ya zauna, a lokacin kiran Najlah ya shigo wayarsa, dan haka ya ɗaga duk da akwai hayaniya.

"Ka yi ƙyau Angon Najlah." Ta faɗa a hankali, sai ya fara waige-waige amma be ganta ba.

"Ka kalla gefanka da ƙyau, ina zaune ina kallon wanda yafi angwaye haɗuwa." duk ya ruɗe dan saboda ita ne ma ya zo wajen, cikin ikon Allah yana kai idanunsa ya hangota sanye farin hijab.

"Yauwa Ammeen Basma, Allah ya miki albarka." Ba ta amsa ba sai ta katse kiran sannan ta tura mai saƙo.

"Be kamata Yarana suna sanya vail kuma nima na sanya ba, shi yasa na fito a big Mama." Dariya ya kwashe da shi yana sake karanta sauƙon.

"Wacce ke gabaki ita ce Basma ɗin." da sauri ya mai da hankalinsa kan Najlah dan ya ga ya za ta yi.

Daga wajen ya ke kallonsu.

Najlah kuwa tana karanta saƙon Abba ta aje wayar, hannu ta sa ta ɗan daki kafaɗar Basma, tana jiyowa suka haɗa ido, Najlah ta yi yaƙe dan ganin ashe Basma ta girmeta.

"Lafiya?." Cewan Basma tana haɗe fuska.

"Uhmm sorry dama tambayarki zanyi?." Sai Basma ta ɗaga mata gira, ganin haka Najlah ta gane tambayar take jira.

"Na kasa gane amaren ne dan Allah wacece Munirah."

"Ta tsakiyar." Ta faɗa tana juyawa.

Murmushi ta yi tana tura ma Abba.

'Wow Babyna yarinyar nan ta yi, saura ta gaba.' yana gani ya tura mata alaman dariya sannan ya ce.

'Layin farko, ga wata yarinya can tana yi ma Amare video ita ce Autata.' sai Najlah ta ɗaga daga kai tana kallon yarinyar, murmushi ta yi.

'Masha Allah, saura Aunty Babba.'

"Banganta ba, ki fita waje za mu yi magana Please." da haka ya miƙa tsaye sannan ya fita.

Najlah tana ganin ya fita ta miƙe ita ma ta bi bayansa.

Gudun matsala sai suka motarsa sannan suka bar cikin wajen, bayan sun fita suka shiga wani layi sannan ya yi parking, a cikin motar suka sha soyayya.

Duk wani motsi da Najlah ke yi yana burge Abba, gaba ɗaya ta gama tafiya da imaninsa.

Labari take bashi, ta dage sai tura ƙaramin bakinta take yi, tana mai bayani harda hannu, gashin idanunta masu tsayi da cika, sun kwanta a sakamakon lumshe ido da ta yi.

"Kana ji na kuwa?." sai ya ɗaga mata kai yana cewa.

"Me yasa kike da ƙyau da yawa?, Gaskiya na ƙosa na killace wannan diomand ɗin." Murmushi ta yi.

"Ba yanzu ba kuwa, dan sai na zama soja, yanzu horo na gaba za'a tsinta masu ƙoƙari a rukunin mu, wata uku za'a ɗauka sannan a yaye su, daga nan za su zama cikakkun sojoji tare da fara aiki, ina fatan na zama ɗaya daga ciki, nima na sanya kayan nan, na ji yarda ake ji." Ta faɗa tana hasaso kanta cikin kayan sojoji, sannan tana riƙe da bindiga.

"Za su yi miki ƙyau sosai, amma harda bindiga za su baki?."

"Sosai ma kuwa, na yi ma kaina alƙawari, alburushin farko da zan fara harbawa a tsakiyar zuciyar Sir J zai sauka."

"Subuhanallah me ya miki?."

"Hmmmmm Baby ya rainani ne, nifa mutanen da zan harbe suna da yawa, hmmmm bara dai lokaci ya yi." Ta faɗa tana murmushin mugunta.

"Nifa wallahi tsoro kike bani wani lokacin, na fi son Najlah ta gida, bata Barack ba." Kai ta ɗaga mai sannan suka dasa wani hirar su duk yawanci dai na aikin na ta ne da irin burin da take da shi.....

Cikin Hole kuwa, shagali ya yi shagali, kuɗi sunyi kuka, dan kuwa kowa zagewa ya yi aka dinga wasan kuɗi dama kuɗi da kuɗi ne suka haɗu.

9:00pm aka tashi, inda daga nan motocin Amare suka zama ready, inda Allah ya so ma duk kusa suke, daga nan aka sanya kowacce Amarya cikin na ta motan, sannan masu rakiya suka shishshiga, take aka fara tafiya da su, sanan wasu suka nufa family house.

Marwa, Basma, Fauza da wasu mata biyu, aka ɗauke su a wata mota aka mai da su gida.

Su Al-hussain kuwa tun baya magrib suka wuce, ya tafi ya barta da kewansa.

Ko da suka isa gidan, suka iske motar da Abba ya fita, hakan yasa suka tabbatar ya dawo, sai suka nufa ciki kowa ta nema waje ta yi sallah sannan suka kwanta.

Abba da wuri ya mai da Najlah gida, sannan shima ya wuce, sai dai yana dawowa suka dasa waya cike da soyayya.

Abba har baya son nan da kwana biyu ta yi, dan daga nan Najlah za ta koma makaranta yasan kafin su dinga waya haka zai sha wiya, amma yasan dubarar da zai yi.

**************** Abbeey da Tweens ne suka isa gida, a parkour suka zauna, sai Merry ta fito daga Kitchen hannunta ɗauke da ruwa mai sanyi, tana zuwa ta zuba ma kowa a cup sannan ta bashi.

Abbeey ya amsa yana ƙare mata kallo, har ta miƙe ya ce.

"Maryama zauna zan yi magana da ke." Ba musu ta zauna daga gefan na hannun daman ta wato Al-hussain dan ta ganesa saboda mask ɗin da ya sa kafin ya fita, yanzu ma yana fuskarsa amma ya sauke ƙasa.

Abbeey ya yi gyaran murya sannan ya ce.

"Na yi miki shuru, na zuba miki ido na tsawon lokaci, sai dai banga alamun za ki sauya ba, tinda nake da ke ɓantaɓa ganin ki da wani ba, baki taɓa min maganar aure ba, to a yanzu Ni na miki magana akai, shin kina da wanda kike so ko a'a?." ba shi kaɗai ba hatta Tweens idanu suka zuba mata.

A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla Al-hussain, sai ya ɗaga mata kai, ita kuma ta girgiza mai kai tana cewa.

"Eh akwai Abbeey."

"Ina son ganinsa nan da sati ɗaya, ki faɗa mai haka." da haka ya miƙe ya bar parlourn.

"Hmmm shine ba gayyata, ashe dai ana soyayya shine ake ɓoye mana......oh ake ɓoye min, dan nasanki da Al-hussain."

"Al-hassan ba wani san shi nake ba."

"Ko ma dai yayane Allah ya sanya alheri yasa a yi damu." Basu amsa ba, dan haka ya san akwai wata a ƙasa, tashi ya yi ya basu waje.

Yana fita kuwa, Merry ta miƙe tana jan hannun Al-hussain, ba musu ya bita har suka fita ta ƙofar baya, sannan suka tsaya.

"Me yasa kasa na ce Eh?."

"Saboda idan kika ce baki da saurayi, da kansa zai ne moniki."

"Hmmmm na sani, to yanzu ya za'a yi kasan dai *Promise* Kuma banda niyyar aure a yanzu, kai sheda ne." Kai ya ɗaga mata sannan ya riƙe hannunta yana ɗan murzawa.

"Ki bi komai a natse, wasa zamu yi da hankalinsa kawai, sai mu ƙirƙira saurayi, in ya so ya ce zai yi tafiya na lokacin mai tsayi, kafin nan ai kin shirya ma aure."

"Hakan ya yi, amma kasan cewa maganar aurene kusan shine tonan asirin mu ko? Ba zan yarda na yi wasa da Promise ba duk ƙanƙantarsa, ƙwanda kai Namiji ne." Shuru suka yi na dan lokaci kafin ya ce.

"Ina sane da komai, kawai idan ya sake miki magana sai mu tura mai wani."

"Abbeey Soja ne, saboda zafinsa wajen aiki ake kiransa da Barkono, kasan bincike a wajensa abu ne mai sauƙi." ɗan dariya Al-hussain ya yi.

"Karki manta da jinin sa kike magana, duk wani yaji dake kan Abbeey yana kaina, ke kinfi kowa sanin haka." Tafawa suka yi sannan ya koma ciki, ita kuma ta zagaya ta shiga ta main door, a tsakiyar parlour suka haɗu, suka yi ma juna murmushi kafin kowa ya yi bangarensa.........

*************

Haka suka kwashe sauran kwanakin da za su yi a Kaduna kafin suka hau shirin dawowa gida, har ga Allah Abba be so ba, sai ya ji dama a Kaduna nan yake, gashi zai tafi yabar ruhinsa anan. Ta ɓangaren Basma kuwa, cikin ikon Allah ba su yi rigima da kowa ba, haka bayan kwana biyu da bikin suka je gidajen Amare suka musu sallama.

Yau take komawarsu Abuja, gaba ɗaya a Compound suka tsaya ana sake bankwana da juna, mota ɗaya ta ɗauke su sai airport, bayan zuwan su suka zauna zaman jiran Abba, dan ba su san in da yake ba, gashi sai kiransa suke yi amma yaƙi ɗauka.

Abba yana can yana bawa fulawa ruwa, dan a kwanakin nan ba ƙaramin shaƙuwa ne ya shiga tsakaninsu da Najlah ba, gashi itama yanzu tana sonsa sosai.

General yana cikin mota yake kallon ikon Allah, dan kuwa Mubarak ya koma kaman wani 30s yana zuba love, ita kuwa Najlah sai narkewa take tana buga ƙasa.

Abune ya isa General ya kauda kansa yana latsa waya.

"Uhmmm yanzu in ka tafi sai yaushe?." Ta faɗa tana turo ƙaramin bakinta, da shirin yin kuka.

Abba ya rasa ina zai sanya kansa, gaba ɗaya ta burkita mai tunani, ga wani masifaffen ƙyau da ya ga ta ƙara.

Jalbab ne jikinta launin Ja, kunsan yana haska farin fata, fuskarta fayau babu ko ɗigon ƙwalli, ga leɓanta da ya fara bushewa, sai ta yi wani irin ƙyau na musamman.

"Kin bani dama na riƙe hannunki?." ya tambaya yana jin kamar ya rungumeta ko ya haɗiyeta.

Kai ta girgiza tare da matsawa jikin get da ƙyau, ta jingina kanta.

"Ka tafi, Allah ya tsa....tsare." sai ga hawaye sun gangaro daga cikin idanunta.

Abba a ruɗe ya matsa gabanta sannan ya sanya hannunsa masu taushi ya share mata hawayen da yake ji kaman ana tsaga fatar jikinsa, sai dai hawayen yaƙi tsayawa hakan yasa ya rungumeta tsam a ƙirjinsa, gaba ɗaya ya rasa tunaninsa.

Ita kuwa yana rungumeta sai ta sake fashewa da kukan taɓara.

General idanu ya zaro sannna ya danna horn ɗin mota da ƙarfi, take Abba ya raba jikinsu da ita yana ɗan kame-kame.

A ƙalla ya ɗau mintoci yana rarrashinta kafin ya samu ta yi shuru, ta shiga gida, sai ya ɗan samu natsuwa.

Jiki a sanyaye ya shiga mota, General ya yi dariya yana kunna motar.

"Mubarak rashin mata ya na neman lalataka, ji yarda ka matse ƴar mutane a bakin titi da sunan soyayyar anya......" dariya suka yi dukkansu, Abba ya mazaje yana shafa sunan kansa.

"Wallahi Yaya ta gama ruɗani gaba ɗaya, ji nake kaman na dawo Kaduna saboda ita, jibi ma zan dawo na ganta." General ya dalla mai harara.

"Tab ai gobe za ta koma Barack, saboda kai na ƙara mata kwana biyu, kuma ba zan bari ka shiga Barack ba." Marairaice fuska ya yi.

"Haba Yayana, Allah ba zan iya kwana biyu bangantaba, gashi daga gobe wayar ma sai ta gagaremu inda na gode ma Allah, kana nan."

"Ni bance ka dameni da kira ba, zan dai iya cewa kullum zan baku 30mnt kuna gaisawa."

"What?." Ya faɗa a ruɗe, General ya ɗaga mai kai.

"Ƙwarai da gaske, kana gani dai jaruma ce, in na yi wasa ta zama ƴar soyayya shike nan za ta dawo baya akan komai."

"Hmmm, to kamin hanya nima na zama Soja kaji." Ya faɗa da sigar magiya, General ya kwashe da dariya yana parking a haraban wajen

"Ba abin dariya bane, serious issue ne, ka yi tunani, in ka samu Form ka min magana." Ya faɗa yana fita daga motan.

Har lokacin General dariya yake yi amma irin na manyan mutane, fita ya yi suka sake sallama da su Marwa, a lokacin aka kira jirginsu, dan haka suka yi gaba, Abba kuma ya tsaya yana jin abin da General ke cewa.

"Waya faɗa maka tsofaffi na zama sojoji, tun da ƙuruciya ake farawa, balle kai ko haɗa hanya da fitina baka iya ba, ji lokacin da mukaje asibiti, suma ka yi saboda tsoro, to ina ga an turaka faɗa cikin daji." Abba ya kuma haɗe fuska.

"Ni dai zanyi, karka ɗauka wasa nake."

"Soyayya ruwan zuma, kai sanyi ita zafi haɗin zai bada citta." sai Abba ya yi murmushi sannan suka rungume juna.

"Allah ya tsare ƙanina mijin Najlah." Abba ya dafe zuciya.

"Wash ka famamin raunin dake cin zuciyata." Suka yi dariya again sannan suka rabu cike da kewan juna.............✍️ END.

> 🤣 Kai Abba Anya kuwa.

```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI