BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 1️⃣6

by @prettys01

> "Wash ka famamin raunin dake cin zuciyata." Suka yi dariya again sannan suka rabu cike da kewan juna.............

Da misalin 4:30pm suka sauka a birnin tarayya, Driver ne ya zo ɗaukan su, suka shiga mota suka nufa gida.

Tun a jirgi suka lura Abba sai cin magani yake, ko daman tambayarsa me yasa be ɗauki kiransu ba basu gani ba, dan haka suka gyalesa, sai gashi a cikin mota ma ya haɗe fuska yana ta latsa waya, bini-bini ya kuma ja dogon tsaki.

"Alhajin Allah lafiya ko?." Cewan Driver ganin tsakin ya yi yawa.

"Ba komai." Ya faɗa yana sake kiran number Najlah amma a kashe, dafe kansa ya yi sannan ya lumshe ido, a haka har suka isa gida.

Shi ya fara fita daga motar, ya nufa ciki ba tare da ya kula su Fauza ba da suke binsa da kallo.

"Meke damun sane?."

"Fauza ina jin muna tare ai, taya zan sani nikam, Maybe harkan aiki ne kunga sai latsa waya yake." cewan Marwa sai Basma ta ƙwaɗa ma masu aikinsu kira.

"Ku shigo mana da kaya." Da haka ta yi gaba, masu aikin suka hau kwasan trolley suna shiga ciki da su.

Ba su iske Abba a parlour ba Dan haka suma suka wuce nasu part ɗin, sai dai suna shiga Marwa ta fito ta wani kayan, murmushi take yi dan Al-hussain ya iso.

A Parlour ta ci karo da A'isha me aiki.

"Aisha ki kawo min drinks guda biyu masu sanyi Garden, ki haɗo da snack."

"Ok Hajiya." Da haka ta fice, A'isha kuma ta haura dan kai ma Fauza Youghout.........

*Abba* Yana shiga part ɗinsa ya sanya lock sannan ya jinjina da jikin ƙofar yana sake kiran numberta, sai dai har lokacin abu ɗaya ake cemai "* The number you Dial is switched off* "

"Me ya samu wayarki Najlah?." Ya tambaya kansa yana tuna yanda hawaye ke gangara daga cikin idanunta.

Ya jima a tsaye kafin ya nema waje ya zauna, dafe kai ya yi yana ta saƙar zuci, yanzu idan da zai samu Soja gani yake tsaf sai zama ɗan kawai ya dinga ganin Najlah.

"Najlah." ya furta a sanyaye, hotonta ya shiga, inda take sanye da sport wear red colour, wando da riga, ba ƙyar ta kai ta rikita duk girman mutum, dan kuwa Najlah tana ƙyau sosai, ga haske kamar ruwan madara, sannan ga manyan sexy eyes, ballema idan suka ɗau kwalli, hanci kuwa ya Allah, suna da masifar tsayi, balle ka gangaro zuwa pink lips ɗinta, idan tana magana da su sai ka ji kamar ka.........Lumshe ido ya yi sannan ya kalla surar jikinta, shi a iya fuskarta ma tafiya take da imaninsa, balle jikinta, tana body shape mai ɗaukan hankali......da sauri ya aje wayar gefe yana rintse ido, sosai ya natsu yana jin sautin bugawar zuciyarsa, sai dai ba _Fat-Fat-Fat_ yake ji ba, _Najlah-Najlah- Najlah_ shine sautin da zuciyarsa take yi, sai ya yi murmushi.

"Na haukace a soyayya, ikon Allah." Ya faɗa yana ma kansa dariya dan kuwa ya zurma sosai.................

********* A Garden ɗin ta iske sa zaune yana kallon kifaye da suke shawagi a wajen kiwonsu.

Ƙamshin turaren ta ne suka fara mai Barka da zuwa sai ya juya a hankali yana kallonta, tsadaddan murmushi suka sakar juna. Miƙa wa ya yi ya buɗe hannayensa alaman oyoyi, sai ta isa kusa dashi ta maƙe kafaɗa, amma ta riƙe mai hannu.

"Har yau ko Hugging juna ba mu taɓa yi ba." Ya faɗa yana turo baki.

"Hmmm wata rana da kaina zan yi maka." Ta faɗa tana tura ranar da ta faɗa jikin Al-hassan, wannan shine karo na farko da ta so ta haɗa jiki da shi, sai aka yi rashin sa'a Al-Hassan ne.

"Shike nan, ya hanya My Love?."

"Lafiya lau." Hira suke yi na yarda suka yi kewan juna duk da kuwa kusan kullum suna manne da waya.

A'isha ce ta iso wajen, dogon hijabi ne jikinta, sai tray da ta riƙe, tana isowa ta tsugunna saitin Marwa tana gaishe da Al-hussain.

Amsawa ya yi ba tare da ya kalleta ba, dan wayarsa yake kallo.

Marwa ta ba Fanta bayan ta zuba mata a glass cup.

"No banshan fanta bashi, wanna za ki samin." ta nuna Sprite.

Sai Aisha ta miƙa ma Al-hussain, a natse ya kalleta ya kai hannu zai amsa, A'isha da idanunta suka sauka kan Al-hussain ta zaro ido tana sakin Glass cup ya faɗi ya fashe.

"Meye haka?." Cewan Marwa tana haɗe fuska.

"Ki...kiya... kiyakuri." Ta faɗa da ɗan rawar murya, har lokacin kuma idanunta suna kan Al-hussain.

Miƙewa ta yi da sauri ta fara tafiya.

"Ke zo nan." sai ta jiyo tana hawaye, inda Marwa ta nuna mata ta tsugunna.

"Baby kasanta? Ta ruɗe daga ganinka." Ta faɗa ba tare da ta kawo komai a cikin kanta ba, saboda A'isha babbarce sosai, har yara biyu gareta mijinta ne bashi da lafiya sosai, dan haka ma take aiki anan.

"A'a, amma na yi mamaki daga ganina ta ruɗe."

"Ke kinsan shi?." Sai ta yi shuru ƙirjinta na bugawa.

"Ba ki jini bane?." Ta faɗa da ɗan tsawa, A'isha ta dan firgita.

"Na sanshi......na sanshi." Sai ta sake fashewa da kuka tana haɗa kai da gwiwa.

Al-hussain ya kalla Marwa cike da tambayoyi dan kuwa be ganeta ba sam.

"Amma a ina kika sanni kuma me yasa kike kuka?."

"Ba magana ake miki ba."

"Hajiya.....nasan shi, kuma dana gansa shine nake tunawa hakan yasa nake kuka?."

"Ok ina jinki a ina kenan?." sai A'isha ta share hawayeta tana gyara zama tare da cewa.

"Watanni Biyar bayan, muna tafiya a napep, mun shiga wani unguwa kenan, wata mota ta daki napep ɗin mu, Allah ya so Ni na riƙe ƙarfen dake wajen, shi yasa na ji ciwukana kaɗan, amma mahaifiya da ba ta lafiya ta yi ........mugun rauni, me wancan motar ya gudu, ya barmu cikin tashin hankali.......a lokacin wannan mutumin ya da wasu jama'a suka zo in da muke. Shi ya taimaka mana har asibi da ƴan uwansa, tabbas na sha mamaki na ganin be san mu amma ya taimaka mana, bayan haka ya bi ma mahaifiyar kuɗin tiyatar sauyin kidney, daga lokacin kuma ban sake ganinsa sama, babu inda ban dubaba dan na mai godiya amma ban samu ganinsa ba. Sai yau Allah ya nuna min shi, shine gaba ɗaya na ruɗe." Ta kai nan tana share hawaye.

Marwa ta yi murmushi.

"Ya mahaifiyar taki?."

"Hmmm bayan biyan kuɗi masu yawa akan ciwonta, ana mata aiki da kwana biyu Allah ya ɗauki ranta." ido Marwa ta rufe tana jin babu daɗi.

"Allah ya jiƙanta."

"Ameen ya Allah."

"Alhaji na gode na gode." Ta faɗa tana kallon Al-hussain.

Kai ya ɗaga mata yana jin ƙirjinsa yana dukan uku-uku, tabbas ya tuna, ta tuna komai, sai dai akwai wani abu bayan shork ɗin da A'isha ta yi, idan be manta ba...............da sauri ya kalleta, sai suka haɗa ido, da haka ta tashi ta bar wajen.

Kai ya dafe yana jin wani irin yanayi, tabbas abin da yake zargi ya gani a cikin idanunta, akwai mamaki da fargaba, a hankali ya furta a cikin ransa.

'Tasan sirrina......ta gani.....ta sani, amma ta rufamin asiri saboda taimakon da na yi mata...............tasan abinda nake ɓoye wa kowa, wannan siririn idan har ya fita, zai rusa min abubuwa da yawa, wanda na shafa tsawon lokaci ina kiyayewa........ina ba zan bari hakan ta faru ba..........INAAAA.' da haka ya kalla Marwa dake amsa waya cikin tana magana a natse.

Kai ya girgiza yana sake mangana a cikin zuciyarsa.

'Bazan bari komai ya lalace min ba, alhalin ina dab da samunki a matsayin matata.' da haka ya shiga saƙe-saƙen yarda zai ɓullo ma lamarin dan kuwa A'isha za ta iya zama barazana ga ci gaba da tarayyarsa da Marwa, ba ma ita kaɗai ba, harda Abbeey harda Al-hassan. dogon numfashi ya ja sanan ya furzar yana mai jin idea ya faɗo mai, da haka ya yi murmushi yana ƙoƙarin saita yanayinsa kar Marwa ta fahimci komai..........✍️ END

> Babbar magana 😳😳😳😳 wai menene wannan sirrin ne? Anya ba wani mugun abu yake ɓoyewaba? Hmmmmm 🤧

```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI