PAGE 1️⃣7
by @prettys01
> 'Bazan bari komai ya lalace min ba, alhalin ina dab da samunki a matsayin matata.' da haka ya shiga saƙe-saƙen yarda zai ɓullo ma lamarin dan kuwa A'isha za ta iya zama barazana ga ci gaba da tarayyarsa da Marwa, ba ma ita kaɗai ba, harda Abbeey harda Al-hassan. dogon numfashi ya ja sanan ya furzar yana mai jin idea ya faɗo mai, da haka ya yi murmushi yana ƙoƙarin saita yanayinsa kar Marwa ta fahimci komai............
Cire wayar ta yi daga kunninta, ta kalla Al-hussain, hannunsa dake kan fuskarsa ta cire tana mai kallon hannu.
"Ina alfahari da kai, kana da zuciya mai ƙyau, ga taimako a gabana da wanda nake jin labari, Baby Ina sonka soyayyar da nake ji in babu kai bazan iya yaruwa ba." murmushi ta ku yi mai, shi kuma ya mata yaƙe yana jin duk minti ɗaya dake wucewa kamar A'isha na sanarma ƴan gidan ne sirrin sa ne.
Gira ta ɗaga mai alaman tambaya sai ya gyara zama.
"Nima ina alfahari da ke My Love, yarda nake jinki a zuciyata baya misaltuwa, akanki zan iya aikata komai."
"Na gode, to kaban labari mana."
"A'a yanzu zan wuce saboda na bari ki huta nasan akwai gajiyan hanya a jikinki."
"Uhmmm, na ce ba.....Yaushe ya kamata a fara maganar........" sai ta yi shiru sakamakon wayarsa ta fara ringing.
Da yake wayar yana tsakiyan su ne, hakan yasa sunan *My bloodline* ya bayyana.
Tasan waye, Al-hassan ne, tunasa yasa ta tuna sanyin dake tare da shi, lumshe ido ta yi tana jin Al-hussain yana cewa.
"Kasan in bana gida ina wajen Baby Marwa." Ta cikin wayar Al-hassan ya ce.
"To ka gaisheta, in ka koma gida ka kira Ni."
"Ok." Da haka ya kashe kiran.
"Rayuwarku yana burgeni, yana ji da kai fiye da kowa, gaskiya kaima ka ƙyautata masa." Ta faɗa cikin kulawa.
"Hmmm ina da target akansa sosai, kuma yarda kika faɗa ɗin ne yana sona, irin soyayyar da Uba kema ɗansa, be ɗauke a ƙani ba sai kaman ɗansa, shi yasa nake sonsa." Murmushi suka yi.
"Ai na gani, a cikinku waya fi zafi?."
"Halinmu sauya wa yake kaman jikin Ɗawiesu, yau na yi zafi gobe ya yi, duk da babu wanda yake Iyayenmu zafi."
"Uhmm Abbeey dai nasan ana cemai *Barkono*."
"Eh, ita kuma Mahaifiyar mu Guguwa muke ce mata, soja ce itama, macece dakakkiya." Sai ya yi shuru yana tuna ta.
A hankali kuma ya latsa wayarta yana shiga wani waje, sai ya miƙa mata, amsar wayar ta yi tana dubawa.
Babban macace zaune cikin kayan sojoji wanda suka amsa jikinta, tana da duhu amma Choculate ce, ga jiki ga tsayi.
"Wow he's beautiful."
"Ina sonta sosai." sai ya sauke ajiyan zuciya.
A hankali ya miƙe tsaye yana gyara zaman agogonsa, sai itama ta miƙe suka fara takawa a natse.
Har waje suka isa bakin motarsa, sai ya riƙe murfin motar yana cewa.
"To, My Love zan wuce, uhmmm in kin shiga ki kira min mai aikin nan, Ina son na taimaka again."
"Shikenan Allah ya saka da alheri." Da haka ta juya ta koma gida, shi kuma take ya haɗe fuska yana ciwon leɓansa, jira yake ta fito a yi mai kankat...............
*Najlah*
Bayan tafiyar Abba, ɗaki ta koma ta kwanta tana jin duk babu daɗi, sai ta janyo wayarta, ganin network ya ɗauke yasa ta sanya wayar a Flightmode, take kuma ta lumshe ido sai barci.
Ba ita ta farka ba sai misalin 5:30pm, shima Mamie ce ta shigo jinta shuru, ganin tana barci ta tashe ta.
A natse ta miƙe tana miƙa.
"Biyar da rabi, kinyi sallah ma kuwa?." Ido ta ɗan zaro, sannan ta kalla agogo, ganin har da rabin ya fara gotawa yasa ta zabura ta nufa bayi.
Alwala ta yi sannan ta fito ta yi sallah, bayan ta idar ta yi addu'a sosai, daga nan ta miƙa ta cire Hijab sai ta zauna kan gado tana duba wayarta.
Ganin wayar yana jirgi yasa tasan Abba ya nemeta dan tasan sun isa.
Cirewa ta yi ta shiga wajen kira, sai dai kafin ta latsa numbersa kiransa ya shigo, ba tasan lokacin da ta yi ɗan dariya ba, sanan ta yi picking tana kai kunninta.
"Me ya sami wayarki ne dan Allah?." Abba ya faɗa kamar zai yi kuka, murmushi ta yi sannan ta marairaice murya.
"Uhmmm Baby barci ne ya ɗauke Ni, yanzu na farka."
"Shine wayarki a kashe, akan ne kinsan yarda hankali ya tashi kuwa." wannan karan cikin faɗa ya faɗa.
"Haba Babyna da wanne zanji, ciwon da zuciya take min ko faɗar.....ka.....haba dan Allah." Ta fashe da kukan rigima.
Shuru ya yi sai jikinsa ya yi sanyi.
"I'm sorry Ammeen Basma, kiyakuri."
"A...... a'a." Ta maƙe kafaɗa.
"Dan Allah na ce fa, Ni ba faɗa nake miki ba." Ya faɗa a tausashe.
"Ba wani nan har da ɗan tsawa ka min fa, ni....Ni da...."
"Shalele Please ki yi shuru." Sai ta tsagaita da gunjin kukan da ko hawaye ba ta yi, sannan fuskarta ɗauke yake da murmushi.
"Shike nan, ya kuka koma gida?."
"Yauwa Babyna, Alhamdulillah." Daga haka suka afka kogin soyayya.
Sun ɗau dogon lokaci suna hira kafin suka yi sallama da juna. Tashi ta yi ta fara haɗa kaya tana sauraren waƙa wacce take ji kaman dan ita aka yi wannan baitin, tana yi tana kaɗa kai da tunanin ranar bikinsu shi za ta sanya M.C ya sanya mata ta yi shi.
Dariya ta ɗan yi sannan ta ci gaba da aikinta cikin raha da nishaɗi da Abba ya barta a ciki.
Tana gamawa ta fita Parlour, Mamie ta iske tana kallo, sai ta zauna kusa da ita, kanta ta ɗaura kan cinyar Mamie.
"Zanyi missing naki Mamie, gashi General da kansa ya ce, ko na yi laifi a can zasu horani bani ba dawowa gida da wuri, sai dai ke ki dinga leƙoni, dan Allah ki sani a addu'a na samu daman kammala training ɗin nan." Ta kai nan cikin sanyin murya, Mamie ta shafa mata kai.
"Kema ki dena laifi, bansan kina rashin ji, fuskarki ne kawai babu tabo amma jikinki tabon ciwuka suna da yawa."
"Hmmmm zan rage Mamie."
"Yauwa Autata, zan dinga zuwa duba lafiyarki."
"Tom."
"Najlah." Yarda Mamie ta furta sunan na ta yasa ta ɗaga Mamie tana kallonta.
"Na'am."
"Ba zan iya hanaki abin da kike so ba, amma dole na tambayeki, ƙanin General, Mubarak ya miki a matsayin mijin aure?." Najlah dama batasan menene kunya ba, murmushi ta yi.
"Eh Mamie, ya min 💯, kuma ina sonsa, duk da ba yanzu zan yi aure ba sai na zama cikakkiyar Soja."
"Hmmm shike nan, amma me yasa baki jin kunyata ne?." dariya Najlah ta yi ta miƙe tsaye.
"Mamie na zanji kunya wai....hmmm sai ma ranar aurena, Ni da ke za'a bamu fili, ina taka rawa kina yi." Pillow Mamie ta jefa mata tana dariya.
"Allah ya shirya ki, ɗauko abinci na baki a baki, nasan ba wani ci za ki yi ba."
"Mamie na girma fa, amma bari na ɗauko." da haka ta ɗauko abincin sannan ta dawo ta zauna gefanta.
Mamie ta fara ba ta a baki, suna yi suna hira....................
************* Ƙafarsa ya tsura ma ido kaman yana nazarin gudun jinin dake yawo a wajen, jin an buɗe get yasa da sauri ya ɗaga idanunta ya sauke kan A'isha, daurewa ya yi ya saita yanayinsa yana kallon duk wani motsinta.
A'isha ba ta yi mamakin ba da jin kiran da yake mata, sai dai abinda ya zo mata a cikin ranta shine ta tabbatar, dan kuwa da ba haka bane ba zai nemeta ba.
Tana zuwa ta tsugunna daga ƙasa.
"Alhaji, gani ance kana kirana."
A jiyan zuciya ya sauke sannan ya ce.
"Shiga mota." Da haka ya shiga yana rufe ƙofa, cike da mamaki ta ɗaga idanunta ta kallesa.
"Magana za mu yi." Ya faɗa a kausashe, ganin haka ta miƙe ta shiga motar tana mamakin maganar da zasu yi a mota, tana shiga ya kulle motar.
Jin ya kuna motar ya ɗau hanya yasa a ɗan ruɗe ta ce.
"Alhaji me na yi? Dan Allah ka sauke ni." bema san tana yi ba, dan kuwa a 360° ya figa motar.
Bashi ya faka ba sai ya bar unguwar su Marwa gaba ɗaya, yana shiga wani layi ya yi parking, sannan ya juyo kansa ya kalleta.
Tsoro ya gama cikata, ga kuma tunanin abinda ya gani.
Wayarsa ya ɗauka ya kira wata number, bugu uku aka ɗauka.
"Hello Sir." Aka faɗa daga cikin wayar.
"D.P.O Umar Bala, kana Station ne?."
"Eh, Sir."
"Yauwa, akwai wata mata ce idan ta yi min gardama akan wani issues, zan kawo maka ita, ku ɓatar da ita gaba ɗaya, ko ku manna mata laifin da zai sa a kaita jail ta kare Rayuwarta a can."
"Ba matsala, in har da familynta ma zamu ɓatar, dama yanzu muna neman mata biyu da zamu mai da laifin kisan kai."
"Kun samu ɗaya, amma zan kira idan mun gama." da haka ya katse kiran yana kallon yarda duk ta tsure ta jeme kamar tsumman da aka jiƙa a ruwa.
"Dan.....Dan girman Allah, idan kana ma Allah da manzansa.......dan....." Da sauri ya ɗaga mata hannu.
"Kinsan meyasa na tawo dake nan?." Sai ga girgiza kai, yana mata wani kallo, sai ta ɗaga kai cike da tsoro.
"Sunana Al-hussain, Ni ƴan biyu ne, ina da Yaya wanda muke kama da shi, a ranar da abin ya faru, ya ban labari, hakan yasa da kika furta na tuna, nasan kin ga wani abu daga ɗan uwana ɗaya ɗaure miki kai bayan ganina a nan, to ki sani abinda kike tunani haka ne, kuma abinda idanunki suka shaida gaskiya ne, Al-hassan yana ɓoye mana wannan sirrin, sai dai besan na gane ba, hakan yasa nake ta bibiyan komai da ya shafesa."
"Ya...ba kai bane? Kuma kasan me nagani?."
"Eh, ɗan uwana haka yake, ina mugun takaicin haka sai dai saura kaɗan komai ya wuce, roƙo ɗaya gareni shine ki rufa wannan asirin na har abada, sirrin ba abin tonawa bane abin gyara ne, kuma ina gab da gama gyaran." ya kalleta, sai ya ga kaman ta ƙaryata haka ne, yasan ba balle ta yarda ba dan haka ya kira Al-hassan V.D call.
"Zan nuna miki wancan, amma karki nuna kin ganesa." Ta ɗaga mai kai.
Yana fita ringng Al-hassan ya ɗau kiran.
"Rabin jikina, ka koma gida ne?."
"A'a yanzu zan ƙarasa, Madam ku gaisa." Ya faɗa yana matsar mata da wayan gabansa.
Ba idanu kaɗai ba hatta baki da hanci duk ta buɗe, dan kuwa ganin sak wanda ke zaune a gefanta hatta kayan dake jikinsu iri ɗaya, ba dan tasan waya ba, tasan Video call da ta ce haɗawa aka yi.
"Ina wuni Aunty?." Cewan na cikin wayar yana mata murmushi, tama kasa magana gaba ɗaya.
Al-hussain ya janye wayar.
"Ta ruɗe da ganinka, zan kira ina zuwa." Da haka ya katse kiran.
"Hmmmm yanzu kin fahimta?." Sai ta ɗaga mai kai.
"Wancan shine kenan?." Ya ɗaga mata kai.
"Amma meyasa? Yana da tausayi ga halin ƙwarai amma me yasa yake......." da sauri ya katse ta.
"Ƙaddarar sace, yana hali masu ƙyau fiye da Ni, ƙaddara ce ta mai da shi haka, kuma Very soon zan shawo kansa." take hawaye suka gangaro mata, ta share.
"Zan ta ya sa da addu'a, karka damu daga nan maganar ta mutu." Murmushi ya yi sannan ya ta da motar.
"Shike nan." Ya faɗa ransa fes.
Daga nan supermarket ya kaita, ya shiga ya yi mata siyayya sosai, sai dai yana duba card ɗin sa ya iske ba ko sisi.
Take ya tura ma Al-hassan saƙo, cikin ɗan lokaci 500k ya shigo mai, ya biya sannan suka nufa gida.
Bayan ya sauke ta, ta yi ta mai godiya har za ta wuce ya kirata, ta juyo riƙe da ledojin siyayyan.
"Ki sani shi ɗin rayuwata ne, idan har ta dalilin wani ya yi ƙunci ba zan mutum ba, ina miki gargaɗin ki kula."
"Alhaji wallahi billahil-lazim na rantse da Ubangijin ka'aba ba mai jin maganar nan."
"Good." Da haka ta shiga gidan, shi kuma ya sauke ajiyan zuciya, ya shafa suman kansa, iskar ya fesar, take kuma ya yi wani murmushi wanda Ni kaina bangane ma'anar sa ba............✍️ END.
```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI