PAGE 1️⃣8
by @prettys01
> "Good." Da haka ta shiga gidan, shi kuma ya sauke ajiyan zuciya, ya shafa suman kansa, iskar ya fesar, take kuma ya yi wani murmushi wanda Ni kaina bangane ma'anar sa ba..................
************
Rayuwa tafiya take kaman wucewan walƙiya, da gari ya waye zai yi duhu, da an kwanta da an wayi gari, haka ta kasance ta ɓangaren kowanne su.
Najlah tuni ta koma makaranta, inda a ranar da ta koma sai da suka yi dambe da wata, a garin damben ta karya ƴar mutane, haka aka wuni ana case ɗin nan kafin kuma aka kashe maganar, tunda daga nan kowa ya kiyaye Najlah, gashi ta mai da hankali kan kowani training da ake musu, a kowani rana sau ɗaya tak suke waya da Abba, wanda shima zai ta je office ɗin General suke shan waya na tsawon 30mnt.
Haka dai rayuwa ta ci gaba da gangarawa, Najlah an dasa training wanda ya fi na baya wahala, gaba ɗaya yanzu jikinta ya fara sauya wa daga laɓe-laɓe zuwa dakakkiyar mace, jikinta ya ƙara buɗe wa, ta yi ƙiba daidai, duk wanda ya ganta dole ya ji ta burgesa.
Sau da yawa wasu sojoji suna tareta da sunan soyayya, sai dai ba ta kula kowa, dan hankalinta da ruhinta suna kan Abba dake ji da ita kamar ƙwai.
Tsaye take cikin wando da riga makar kullum, sai wani gyalle da ta ɗaura a kai ya rufe mata kitson kanta, gaba ɗaya ta sauya, ta rage haske, dan hasken ta dake kashe ido ya rage, saboda azabar zaman rana da wahala, jikinta ya yi yanayin matan da suke motsa jiki sosai, dan kuwa a dire take, hips da Breast kuwa sun cika sun batse, a haka duk cikin wata huɗu ya faru.
Murmushi ta yi tana kallon wani dogon net na ƙarfe dake gabanta, a natse ta kalla mata ukun da zasu hau wajen, suma sun zama ready, take aka danna wani agogo mai gudu da ƙirgen lokacin.
Take suka fara hawa, Allah ya so sun naɗe hannunsu da handglobe, haka suka fara hawa wajen da mugun sauri sannan cikin takatsantsan.
Wajen yana da mugun tsawo, haka suka dinga hawa, bayan sun kai ƙarshe suka sauka ta can bangaren.
Gaba ɗaya gumi suke yi, haka suka sauka suna haƙi, daga nan ba su tsaya ba suka hau gudu irin gudun cetan rai, dan wannan training ɗin ana horasu ne dan cetan rai idan an kai musu farmaki.
Bayan sun kai inda aka basu daman tsayuwa, suka tsaya, sai aka basu wasu bindiga masu alburushin wasa, ana basu suka hau harbin wasu ice daka jera, aka musu alama da in da za su harba.
Bayan sun gama aka basu ruwa suka sha sannan aka sallame su, har ga Allah farin cikin da take ciki a yanzu baya misaltuwa, dan kuwa tana ɗaya daga cikin wa'inda za'a yi ma P.O.P *Passing Out Parade.* nan da ɗan lokaci, hakan yasa ta ƙara dagewa akan komai.
Bayan ta shiga wani waje da aka tanada dan motsa tsotsa jiki, ga abubuwan nan kala-kala, direct wajen zama ta nufa, ta zauna kan kujera sannan ta fiddo wayar daga cikin rigarta, ƙaramin waya bottles ƙiran Tecno T31, kunna wayar ta yi tana murmushi, dan kuwa bayan wayan da take yi a office ɗin General, tana yi da ƙaramin waya, wanda Abba ya kawo mata da kansa, zuwan kusan 6 Kaduna a cikin ƴan watannin nan, a haka ma tana hanasa zuwa ne.
Numbersa da tuni ta haddace ta latsa kira take ya hau ringing, sai dai be ɗauka ba, hakan yasa ta kalla lokaci 4:30pm na rana, tasan yana office a yanzu dan haka ta sake kira still ba'a ɗauka ba, a kira huɗu ta hau ringing bugu ɗaya biyu aka ɗauka, take ta zumɓura baki cikin sanyi da taushin murya ta ce.
"Babynaaaaaaaa." sai dai maimakon ta ji muryan Abba, sai ta ji wata murya mace ta lalayo ashar da faɗa.
"Kan buhun ubancan Be....Be...mene?." Aka faɗa cikin mamaki da al'ajabi.
Najlah murmushi ta yi ta ce.
"Uhmm Ina Babyna? Dan Allah bashi wayar kinji." Ta faɗa da sigar tsokana.
"Ke dalla tsaya kinsan wa kika kira kuwa? Ki duba number mana....." Da sauri Najlah ta katse ta.
"Uhmmm Dan Allah ki kaima Baby magana zan yi dashi faaaaaa."
"Ba Baby ba sai dai Uban Baby, wait wa kike nema ma?."
"Baby nake nema?." Sai ta cikin wayar ta ja tsaki.
"Wacece ke to?."
"Ammeen Basma, *BUDURWAR ABBAN MU.* " Take Basma ta ce.
"Ke bansan iskanci, wato Ammeen Basma, hmmmmm bara na yi ma mai wayan magana, idan har da gaske ne abinda kike cewa, to narantse miki da Allah, kin shiga masifa da bala'in da be da ƙarshe."
"Shhhhhh stupid scarred, started smoking, sixteen sixteenth season............. Karki ɗaga min murya, ƙaramar mara kunya, kina magana da mahaifiyarki a tsaitsaye, ki kalla sunan da akayi saving mana *ONLY ONE IN MY HEART. Nonsense, kaima Baby waya ki ce Shalele na son magana da shi." da haka ta yi shiru tana matse dariyar dake cinta, tasan duk ma wacce ke wayar huta ta ɗauke, dan haka ta kashe kiran tana jiran kiran Baby, dariya ta ɗan yi dan har ga Allah tana so ta ga tana rigima da mutane abin na ba ta nishaɗi.....................
*********
Basma ce tsaye riƙe da wayar Abba, ji take kaman an zare mata laka, tunaninta da hankalinta sun ɗauke na wani lokaci, haka ta ji kaman numfashin ta ya je break, ba tasan lokacin da kiran *01IMH* ya katse ba, dafe kai ta yi tana janyo iska dan ji take iskan ɗakin ya yi kaɗan.
Baya ta ja ta zauna daɓas a kujera tana furta magana a iya kan leɓanta.
"ONLY ONE IN MY HEART, shine 01IMH." Ido ta rintse tana tuna, tun watanni baya da suka wuce.
Tabbas a baya tana zargin Abba, amma duk iya bincikenta ba ta samun komai a wayarsa, babu whatsApp number da yake chart, Babu kira daga sabuwar number, duk da kuwa tana ganin *01IMH* sai dai ba sosai bane kiran, za ta iya cewa ya fi yin waya da daddare da Dad wato General, shine ma suke ɗaukan lokaci mai yawa.
Tun daga lokacin kuma ta dena ma binciken dan kuwa babu wani abun zargi da yake yi, in baya wajen aiki to yana gida, kuma baya fitar dare sam, haka ba kodayaushe ma yake waya da daddare ba, duk da kuwa wani lokacin yana daɗewa yana typing, amma ko ta duba whatsApp ba ta ganin komai.
Da haka kwata-kwata ta fita sabgar nan, suka ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saɓa.
Yau da wuri ya dawo aiki, dan haka ta shigo part ɗin sa dan jin ko lafiya, sai dai tana shiga part ɗin ta iske ya aje car key da wayarsa kan kushin, zama ta yi gefe guda tana jiran fitowarsa.
Take aka fara kiran wayar, sai dai wayar yana silent, ita ma Flashlight ta gani hakan yasa ta ɗauki wayar tana kiran sunana Abba da ƙarfi.
" Baseey ina zuwa, ina duba wasu files ne." Ya faɗa da ɗan ƙarfi, hakan yasa ta zauna riƙe da wayar.
Amma ganin kira hudu a jere, ta tabbatar kiran ujilace hakan yasa ta ɗauka tare da accepting, sai dai ba ta san lokacin da ta zabura ba jin wani daddaɗan murya mai sanyi tana cewa *Babynahhhhhh.*..........
"Bangane meke faruwa ba?." Ta tambaya kanta tana buɗe wayar, sai dai akwai password, ya faɗa mata tun kwanaki, hakan yasa ta sanya number 2580, da mamakinta wayar ta ƙi buɗe wa, ta sake sawa ya ƙi yi, sai ta yi ƙwafa tana kiran sunan Abba da ƙarfi.
A daidai lokacin Fauza da Marwa suka shigo suna hira suna dariya, amma jin yarda Basma ta kira sunan Abba yasa suka tsaya suna toshe kunnuwansu.
Da sauri suka ƙara so ciki.
"Lafiya? Me ya faru?." Cewan Fauza tana dafa Basma.
Kafin ta buɗe baki ta yi magana, Abba ya buɗe handle ɗin ƙofar bedroom ya fito riƙe da files guda uku.
"Basma me ya faru na ji kina magana da ƙarfi?." ya faɗa a tausashe yana isowa cikin Parlourn.
Sai dai wani irin kallo ta dake mai yasa ya isa kusa da ita yana ɗaga mata kai alaman tambaya.
Ranta in ya yi dubu ya ɓaci, ta ɗaga wayar ta fara magana a kausashe.
"Wacece 01IMH?. yarda ta yi maganar yasa Abba ya fahimci abinda yake ta ɓoye musu yau dai ya fito.
Be bata amsa ba sai ya shafa kansa yana cewa.
"Kira aka yi ne?." ya faɗa, sai Fauza ta ce.
"Bassey make faruwa ne?."
"Ma......Ma.....Macace ta kira wayarsa kuma ina ɗauka ta........" Maganar Basma ta katse sakamakon wayar Abba da ya ɗau ruru, kallon screen ɗin ta yi *01IMH* shine sunan dake kai, ai da sauri ta yi picking tana sa wayar a speaker.
Take sanyayyar muryar Najlah ta yi musu amsakuwa cikin shaƙwaɓa ko su ce taɓara.
"Baby na yi fushi da kai uhmmmmm baka kira Ni baaaa." Take suka zazzaro ido waje, Abba kuma gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan Najlah, dama yau ba su yi waya ba kewarta yake sosai.
"A....Abba wacce wannan ƴar iskan dake kiranka da Baby?." cewan Marwa, Basma ai ta kasa magana gaba ɗaya.
"Wow ashe Babies ɗina suna kusa, Please ku ba Abba wayar idan mun gama magana dashi sai na yi da ku." hankalinta a kwance ta yi maganar.
Ai cikin masifa da bala'i Basma ta buɗe baki ta ce.
"Ke uban wa ya baki daman kiran Abba mu? Kuma uban wa......" Da sauri Abba ya fizge waya yana kai kunninsa.
"Hel....hello." ya faɗa cikin kame-kame, a hankali kuma ya juya ya fara tafiya, sai dai wayar yana speaker hakan yasa suka jiyo kukan shaƙwabar da aka sanya a cikin wayar.
"Uhmmmm uhmmmmm Baby Ina jin yunwa." da haka ya shige bedroom ya rufe ƙofa harda murza key. Su kuwa kamar an sassaƙasu dan kuwa ƙamewa suka yi suka bi Abba da ido cike da tashin hankali.............✍️ END.
```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI