BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 1️⃣9

by @prettys01

> "Uhmmmm uhmmmmm Baby Ina jin yunwa." da haka ya shige bedroom ya rufe ƙofa harda murza key. Su kuwa kamar an sassaƙasu dan kuwa ƙamewa suka yi suka bi Abba da ido cike da tashin hankali...........

"Meke shirin faruwa ne?." t faɗa tana ɗan ja baya, da sauri Marwa ta riƙe ta, sannan suka zauna suna jikinsu ya yi sanyi.

"A.....a....a....Abba mace yake nema kenan? Aure wai yake son ya yi? Inaaaaa wallahi babu mai yi ma Mom Kishiya." Ta faɗa tana girgiza kai.

Take Marwa ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na yi mata suya, Fauza kuwa kai ta dafe tana tuna kalmar *Babynahhhhhh.*

"Kar kiyi kuka, kar wani ya yi kuka, ku tsaya ya fito mu tabbar da abinda muka ji, daga nan koma menene sai mu yi."

"Wani irin tabbatarwa kuma! Kina gani ya shige bedroom harda murza key, haba dan Allah."

"Marwa come down, kunsan Ni yarda nake ji kuwa? Zuciyata ci yake da balbalin huta, narantse da Allah idan haka ne al'amarin dole Abba ya fuskaci tashin hankalin da be taɓa tsammani ba, sannan ita ƴar iskan da take wata da Uban mu harda kiransa da *Babynahhhhhh* mtwwwss KAIIIII." ta kai nan tana buƙa ƙafarta a ƙasa tare da ciwon leɓanta.........

Abba daɗi soyayya, tsabar hira ya yi suger ya baje kan gado yana ta juyi yana dariya da hirar Najlah, ya manta shaf da wasu yara na parlour, Kuma ya manta shaf ana jiransa a office.

"Baby zan koma aji, sai zuwa dare."

"Shike nan, ki kula da kanki, ina sonki ina sonki." ya faɗa cike da soyayya.

"Na gode Abba, uhmmm yau na jiƙa maka aiki, My Daughters sun ɓaro ƙurar." sai ya ji zuciyarsa ta motsa.

"Hmmmmm tun ba yau ba na gane kana shakkar Yarana? Akan me? Kace ina da uban aiki, ga gyara yara ga saita miji ya dawo tsayayyen namiji a gidansa, idan ƙurar ta yi sanyi ma yi waya, amma karka kuskura ka bari wata ta ɓata maka rai, na lura zuciyarka tana da taushi." Da haka ta kashe kiran, sai ya furzar da iska daga bakinsa, take kira daga office ya shigo, haka yasa ba shiri ya miƙe yana sanya hula tare da ɗaukan files ɗin.

"Ganinan zuwa." da haka ya kashe kiran yana buɗe motar ya fita.

Idanunsa ne suka sauka kan idanuwansu da suka sauya launi, sun kafesa da ido kamar barawon dabba.

Mazewa ya yi ya tako sannan ya wuce su yana shirin fita.

"Za mu yi magana da kai mai muhimmanci." cewan Marwa cikin kakkausar murya.

"Koma menene ku bari na dawo office, ana jirana urgently." Da Haka ya fice ta rufo ƙofa.

Marwa ta miƙe da sauri tana ƙoƙarin bin bayansa.

"Dakata!!! Menene amfanin binsa, duk dare zai dawo muna nan muna jiransa."

"Gaba ɗaya kaina ya kulle, ta ina muka bari haka ta kasance bayan duk idon da muke sa mai, ta ya muka yi sakacin da wata mace ta shiga rayuwar Abba? Hmmmmm Abba ya taro ma kansa masifa dan wallahi wallahi zai ya yi nadaman fara kula kowa ta irin mace." da haka ta miƙe ta wuce Marwa, ta fice a zafafe.

Fauza ma kanta hankalin ta ya yi mugun tashi, komawa ta yi ta jingina kanta da kujera.

"Yaaa Abba zai mana haka tsakani da Allah...........Da sake, dan wannan maganar ba ta samu waje a cikin kaina ba."

"Ai har ita yarinyar ta shiga uku, nemanta zamu yi a ko ina, ku ci ubanta ko mu sa ƴan sanda su kamata, daga wannan ranar ko jariri ba za ta sake kiransa da Baby ba."

"Insha Allah Ya Marwa, muje part ɗin mu." da haka suka jera suka fita zuwa ɓangaren.

Yarda suka fito afujajan yasa A'isha dake riƙe riƙe da tray ta matsa daga hanya, wucewa suka yi ta bisu da ido tana cewa.

"Allah yasa lafiya." da haka ta nufa Dining area Dan aje abin dake hannunta.

Abba kuwa direct office ya nufa sannan ya ba sectaryn Miss Ayo files ɗin sannan ya ci gaba da aikin dake gabansa, amma rabin hankalinsa yana kan gida, yasan yau akwai ƙura mai zafi, gashi yana mugun son yaran, haka kuma bazai musu karya ba, daɗin daɗawa yana son Najlah, so mai yawan gaske.

Wani gauron numfashi ya sauke yana dafe kansa, gaba ɗaya ya rasa me ma zai yi, sai ya ture system gefe guda, wayarsa ya ɗauka ya shiga settle, wani waje ya danna sannan ya dawo kan screen ɗin, take wani app da baya kan wayar ya dawo, Freezer sunansa, ya latsa ya shiga, sai ga file manager a ciki, Unfreez ya yi, da haka ya yi back take File manager ya bayyana, shiga ya yi, bayan Video, Audio, da sauransu akwai More, ya danna sai ga abubuwa sun fito, direct ya latsa Safe file, sai ya sanya key numbers biyar, take hotunan Najlah suka bayyana, murmushi ya yi ya latsa na farko, daga nan ya fara dubawa yana jin ranshi yana fas, Safe File, waje ne da yake adana duk wani abu da ya shafa Najlah, sai ya ɓoye, balle in ya sanya app cikin Freezer, Kuma Freezer ɗin ya batar dashi akan waya, to duk nemanka ba za ka iya samun komai a cikin wayar ba.

Kallon hotunan Najlah shi yasa Abba ya manta da duk wani damuwa, sannan a cikin folder ya shiga wajen record na wayoyinsu, yana wayan saurara idan yana kewarta, shaƙwaɓarta da yanayin maganarta yana mugun tsuma shi cikin tafkin kogin soyayyarta.

Ba shi yabar office ba sai 6:30pm maimakon ya nufa gida, sai ya nufa gidan abokinsa, ai kuwa sun jima ba su haɗu ba suka shiga ciki suka hira, a nan sukayi sallar magrib da isha'i, Abba be bar gidan ba sai 10pm yasan kafin ya kai gida 11pm za ta yi.

Koda ya shiga mota, haka ya dinga Draving very slow, sai 11pm ɗin kuwa ya kai gida, sannan koda ya yi parking ya ɗau lokaci yana zaune cikin motar.

Bayan ya gama tsara bayanan zuciyarsa, ya fita, a natse yake tafiya har ya isa ciki.

Ji ya yi kaman ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan ganin babu kowa a parlour, murmushi ya yi sannan ya nufa ƙofa stairs, yana mai jin sanyi a ransa.

Yana shiga kuwa ya murza key, take ya sauke ajiyan zuciya mai sanyi, sannan ya kunna globe, haske ne ya gauraye ko ina, jiyowa ya yi sai dai yake ya tsaya cak, yana ji tsoron amma fuskarsa ba nuna ba, yarda yake binsu da ido haka suma suke bisa da idanuwa.

Basma na kwance kan doguwar kushin, tana latsa waya tare da karkaɗa kafa, Marwa kuwa akan carpect take shingiɗe tana aikin wayar da Al-hussain, sai Fauza da barci ya fara ɗaukanta a kujera mai biyu, tun bayan isha'i suke ɗakin suke jiransa, sannan su suka kashe globe ɗin dan karyayi tunani da mutane a ciki.

Baki buɗe yake kallonsu, Fauza da hasken globe ya sa ta miƙe daga kwance, a yanzu ita ta tabbar da Abba yana da budurwa dan kuwa gashi yana gudunsu.

Cikin kame-kame da dan mamaki ya ce.

"Ah ashe kuna nan, Yarana abin ƙaunata."

"Ɗan dakata Abba." Cewan Basma tana miƙewa tsaye.

"Mun gani amma tabbatarwa muke so, shin da gaske kana kula wata mace a yanzu?." Ta kuma faɗa cikin kakkausar murya.

Gaba ɗaya suka zuba ma Abba ido, sai ya lumshe ido yana zancen zuci. 'Menene amfanin ɓoye musu gaskiya bayan duk daɗewa dole su sani.'

Da haka ya ɗaga kansa sai ɗaya kuma har lokacin idanunsa suna lumshe, sai dai ƙaran fashewar abu yasa ya buɗe ido yana kallon wajen da Marwa take.

Daga kan Abba shi yasa ta ji shork, shork ɗin da ta ji daga yatsar ƙafarta har zuwa cikin kanta, hakan yasa ta ɗauki kwalban fulawa dake gefanta a kusa da Tv, ta maka akan center table take suka fashe gaba ɗaya.

Yasan haka zai faru ko yace fiye da hakan ma, sai dai ko da me suka zo zai shanye.

"Wai meke damun kune? Haba dan Allah kaman baku da ilimin addini, abin da na yi Haram ne ko halal? Ba macen banza nake kulawa ba, matar aure nake nema mai hankali wacce za ta rayu da mu saboda muna buƙatar ma................" da sauri Basma da katse sa.

"Kana dai bukatar ta, dan mu babu abin da wata mace za ta yi mana, Abba kenan dai kan kula wata...................WATA ƳAR KUTUMAR UBA CE TAKE NEMAN MA KANTA JAFA'I, Abba kai mijin Mom ne, kuma ba ta da kishiya, kasani dan haka ko da ba ta raye babu mai zama da kai da sunan matar aure." ta kai nan hawaye na zubowa daga idonta, cikin rawar murya Marwa ta caɓe maganar tana jin kaman ta rufe Abba da duka, dan a ganinta wannan babban tozarci ne a wajensu, bayan ya yi ma Mom alƙawarkin rayuwa da ita har abadaaaaaaa...............✍️ END

> Nikam na ce ina mutum ya mutu yana dawowa ne?🤔

```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰 *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI