BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣0

by @prettys01

_Previous_

> "Kana dai bukatar ta, dan mu babu abin da wata mace za ta yi mana, Abba kenan dai kan kula wata...................WATA ƳAR KUTUMAR UBA CE TAKE NEMAN MA KANTA JAFA'I, Abba kai mijin Mom ne, kuma ba ta da kishiya, kasani dan haka ko da ba ta raye babu mai zama da kai da sunan matar aure." ta kai nan hawaye na zubowa daga idonta, cikin rawar murya Marwa ta caɓe maganar tana jin kaman ta rufe Abba da duka, dan a ganinta wannan babban tozarci ne a wajensu, bayan ya yi ma Mom alƙawarkin rayuwa da ita har abadaaaaaaa................

_Continuation_

"A.....Abba yanzu cin amanar Mom kake yi? Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un, akan wani dalili ka ke neman mace a wannan lokacin?."

Abba matsawa ya yi kusa da Fauza dake zaune bakinta a buɗe, tana ganin ya zauna kusa da ita ta miƙe da sauri tana matsaya baya kaman ta ga mugun abu, kai ta fara girgiza wa.

"Kai ba Abban Mu bane? Bashi bane kai...........ba haka Abba yake ba." ta faɗa kuka na ƙwace mata mai ƙarfi, da sauri Abba ya nufeta zai riƙeta, sai ta kuma ja baya da sauri.

"Karka taɓani, bana son ganinka Abba, bana so." Da haka ta fice daga ɗakin da gudu.

Kansa ne ya sara, sai ya dafe, wajen zamansa ya zauna sannan ya kalla yaransa abin ƙaunarsa.

"Ku zauna muyi magana." Ya faɗa a tausashe kamar dai yadda ya saba.

"Mu zauna a ina? Ai daga irin wannan ranar ba zamu sake zama waje ɗaya da kai ba."

"Marwa ke ba yarinya ba ce, a ganinki ya kamata na ci gaba da zama a haka babu mace? Da Ni da ku muna buƙatar mace, ta kula da ni, kuma ta dinga baku shawara akan wasu abubuwan kafin ku yi aure ku barni da ita." take Basma ta hau jijjiga kamar mai shirin dambe.

Hannu ta tafa.

"Ka dena samu a lissafi, dan kuwa tun a baya ba mu zauna da kishiyar Mom ba balle a yanzu da muka girma.............me kake buƙata wajen mace?? Ina jin girki, gyaran gida, sune kuma masu aiki na yi, idan hira da wasa ne munayi, to me kuma kake so?."

Ba tare da ya shirya furta abinda ke zuciyarsa ba, leɓansa ya furta.

"Mu'amular aure." da haka ya miƙe tsaye ya fara takawa.

"Abba banji me kace ba?." sai ya juyo ya kalla Marwa.

"Mu'amular aure na ce. Ko kunfi so a ce ina neman mata a waje, kun girma ya kamata kusan wannan, na gaji da zama Ni kaɗai."

"Mu da muke zaune da kai ba mutane ba wai..........Abba karka rushe alaƙar dake tsakanin mu, dan kuwa daga lokacin da ka yi aure, daga lokacin mun yafeka a matsayin Uba." kalaman Basma sun cokesa a zuciya, hakan yasa ya ji wani abu ya tsaya mai zuciya, besan lokacin da ya ce.

"Aure dai kamar na yi ne, tun baya nake sonyi amma haka na fasa saboda ku, to a yanzu sai dai kuyi amma auren Najlah kamar na yi ne." da haka ya shige bedroom.

Hannu Basma ta sanya a kai ta kurma ihu tana cewa.

"Shike nan, shike nan, Marwa shike nan an asirce Abba, an gama da mu an cuce mu..........."

"Abba ya sauya, dama an ce namiji ba ɗan goyo bane, a baya mun ɗauka Abba ɗan goyo mai yawo da sanin goyo da Kwankwaso, ashe dai kurace da fatar Akuya.............a ce Mom na da rai wallahi hakan ba zai faru ba, ko ta masifa ba zai yi auren nan ba, ba boka ba Malam haka Mom take tsaye da gidanta, sai gashi mu mun kasa ci gaba da kula mata da gidanta." Ta kai nan tana riƙe hannun Basma.

Take Basma ta share hawayeta, ta sanya hannu ta share na Marwa, cike da dauriya ta ce.

"Kuka ba namu bane, kuma Mom sai tasan ta haifa masu kama da ita, idan yasan wata ai besan wata ba, mu je ki ga abinda zan yi." da haka ta ja hannun Marwa suka nufi nasu part ɗin a zafafe....................

********************

"Promise." ta faɗa tana ƙare ma ɗaya daga cikin Tweens kallo, a natse ya ɗaga idanunsa ya kalleta, sannan ya miƙe mata hannu yana zaunar da ita kusa da shi.

"Wani menene Promise ɗin nan? Ko dai sunan wani ne?." Murmushi Merry ta yi, sannan ta ja kumatun Al-hassan.

"Uhmmmm kawai game ne da baka sani ba, muna bugawa da Al-hussain, kuma ina yawon cinsa, shiyasa baya manta kalmar kamar Ni, dan duk bugawa sai ya yi alkawarin zai ka da ni, daga karshe kuma na cinye sa."

"Hmmm to Nima zan fara game ɗin."

"Wai tuni muka dena, Ina son tambayarsa wani abu, yana ina ne?."

"Yana barci kuma wallahi karki tashe shi, ki bari ya huta." ya faɗa cike da kulawa.

"Kai Ya Al-hassan, yarda kasan wani abun Al-hussain ya yi, bayan baya yin komai sai hutu."

"Eh ɗin, ina ruwanki, na dai faɗa miki." sai ta ɗaga kai tana tashi.

"In ya tashi kace ina da magana da shi gobe." kai kawai ya ɗaga mata sannan ya lumshe ido, ita kuma ta ci gaba da tafiya, kallonta ya yi, ya ɗan yi dariya tare da yi mata pito mai ƙarfi, da sauri ta jiyo baya sai ya ce.

"Promise! Promise!!." ido ta zaro, ganin ya kwashe da dariya yasa ta juyo tana tunani.

"Kaine?." ya ɗaga mata kai.

Shuru ta yi tana nazari, kar wanda ke zaune ya mai da ita mahaukaciya.

"Uhmmm sai anjima." Ta faɗa tana juyawa tare da latsa number wayar Al-hassan, da wannan ma tana ganesu, da mamaki wayar dake gefan wannan ya hau ringing, ta juyo da sauri.

" Al-hassan." sai ya sha kunu, take ya ɗaga mata wayoyi irin ɗaya guda biyu da suke gefansa.

Har za ta sake magana, sai ga Abbeey ya fito tare da ɗayan, suna tafiya suna magana a natse, murmushi ta yi ta isa kusa wanda ke zaune, ta tabbar Al-hussain ne, dan Abbeey baya magana irin haka da Al-hussain sai Al-hussan.

Kunninsa ta ɗan ja tana murguɗa baki.

A lokacin wancan ya bar Abbeey ya nufosu yana murmushi, sai ya zauna gefan ɗayan ya ce.

"Al-hassan yau ba ka dawo office da wuru ba lafiya ko?."

"Eh, Tweeny aikine suka haɗe min yau."

Baya ta ɗan ja, dan kuwa sun gama raina mata hankali.

"Wai dan Allah waye Al-hassan ne?." ta faɗa tana marairaice fuska.

"Nine Menene?."

"A'a ga Ni nan?." Duk suka faɗa da muryansu iri ɗaya.

Zama ta yi kan kushin, tana nazari.

"Kenan Al-hussain ne ya fito daga wajen Abbeey? Amma ya Abbeey ya yi magana da kai a natse, kuma wanda ke zaune ya ce shine Al-hassan daga baya ya ce shine Al-hussain, bayan kai ka fito ka kirasa da Al-hassan.....Kai dan Allah." Ta faɗa harda buga ƙasa.

A daidai lokacin Abbeey ya leƙo daga parlourn sa, ya yi magana cike da izza kamar yarda yake.

"Hassan zo." da haka ya koma.

Marry dai ta tsura musu ido tana jiran ta ga wanda zai tashi.

Kallon juna suka yi, wanda ya dawo daga wajensa ne ya fara magana.

"Na koma?."

"No, Bara naje yanzu."

"Ok." Da haka ɗayan ya tashi ya wuce.

Da ido ta raka ɗayan, sai ta mai da kan wanda ke zaune ya zuba mata ido.

"Waye kai?."

"Tweeny mana."

"Na sani, Al-hassan ko Al-hussain?." sai ya shafa kansa.

"Yau da Al-hassan dukka muke amfani, dan haka bansan waye Al-hussain ba." ya faɗa yana ɗaukan chips ɗin dake kan center table.

Merry dai ta kasa magana, dan ba tasan me za ta ce ba, gashi magana mai muhimmanci take dashi, ko ta ce babban magana.

Tana zaune tana latsa sai wayar Al-hussain ya hau ringing cikin wakar soyayya mai daɗi na India, murmushin gefan baki ta yi, sai kawai ta ga wannan ya ɗau wayar tare da yin pecking, yasa wayar a speaker.

"Ba.....Baby....... Baby, akwai matsala, wai A....Ab......Abba yaaaaa ke...." Take kuka ya ƙwace mata, zumbur Tweeny ya yi tsaye, yana jin kukan Marwa dake daukan zuciyarsa.

"Ganin nan zuwa gidan." ya faɗa yana katse kiran, duk da dare ya yi sosai.

Merry ta miƙe da sauri.

"Al-hussain zan yi magana da kai."

"Ba shi bane." Ya faɗa fuskarsa a haɗewa kaman hadari.

"Kamar ya ba shi bane, bangane ba nikam, Al-hassan babu yarda za'ayi ya fusata daga jin Marwa na kuka." cak ya tsaya, sai ta yi murmushi tana takowa kusa da shi.

Kafin ta yi magana ɗayan ya fito daga part ɗin Abbeey yana cilla key ɗin mota sama yana caɓewa.

"Meke faruwa, na ganku hankali a tashe?." ya faɗa yana tsayuwa gaban Tweeny.

"Tweeny Marwa ta kira tana kuka, gashi ka je ka sameta." Ido ya zaro ya fizga wayan sannan ya yi waje yana jin ƙirjinsa yana bugawa fat-fat.

Zaman ƴan bori Merry ta yi, ji take kaman ta kurma ihu.

"Sorry My sister, ki bishi shine Al-hussain." Da Haka ya juya ya haura sama.

Kasa binsa ta yi dan sun juya mata tunani, gaba ɗaya ta rikice.

"Dukka reaction iri ɗaya suka nuna, kowa ransa ya ɓaci, kowa damuwa da fargaba ya bayyana ta fuskarsa, kar dai Al-hussain ne ya tura Al-hassan, amma ai Al-hassan ba zai je wajen budurwar Al-hussain ba, to me yasa wanda ya ɗau wayar har idanunsa sun bayyana tashin hankali???." Da sauri ta dafe kanta dake neman fashewa yake.

Tashi ta yi ta nufa part ɗin ta dan kwanciya ta bari gobe sunyi maganar idan Al-hussain ya bayyana da kansa, dan ko da wasa ba ta sakin magana sai ta tabbar, da tana so ta nema reza ta yi ma ɗaya taɓo a fuska ta yarda za ta dinga ganewa.

Sauri ta ƙara tana shiga ɗakin kwananta, direct wajen mudubi ta nufa, ta duba make-up tools, nan ta ci karo da sabuwar reza, ɗauka ta yi sannan ta fita tana haɗawa da sauri.

Gaba ɗaya suna mugun rikita idan sun so, tana ganin da ta yi haka ta kawo karshen komai, tasan dole zuwa gobe za ta gane waye Al-hassan a ciki, saboda suna meeting akan gina wani bank da aka basu ƙwangila.

Knocking ta yi a bakin ƙofar su, sai dai ba'a amsa ba, hakan yasa ta shiga kai tsaye.

Kwance ta gansa ya rufe ido amma yana motsa ƙarfasa, sai ta yi ɗan gyaran murya.

"Merry Please ki barni, ina son zama ni kaɗai, bansan magana." ya faɗa cikin yanayin da ta tabbatar abu na damunsa.

Rezar ta gyara zamanta a hannunta, sannan ta juya za ta fita, da gangan ta haɗa kanta da ƙofa, sai ta yi baya da sauri tana ɗan ƙara tana dafe goshinta.

"Ouchhhh." da sauri Tweeny dake kwance ya tashi ya nufeta da sauri, sannu ya fara jera mata yana ɗagota, ita kuma cikin hikima ta kai hannunta wajen fuskarsa, take ta ɗan danna sabuwar rezar a saman girarsa.

"Wayyo reza ya yankeka." Ta faɗa tana ganin jini yana fitowa daga wajen.

"Karki damu, bara na duba miki forehead ɗin." Ɗaduba ya yi sannan ya liliya mata wajen da yake tsammanin nan ne, ta ko dinga ihu, bayan ya gama ya yi mata sannu, har lokacin kuma jini yana fitowa daga wajen.

Juyawa ta yi da sauri ta nufa wajen mirrow, tissue paper ta ɗauka ta nufesa, ta yaga sannan ta danne mai waje.

"Me yasa kike yawo da raze?." Ya tambaya yana kallon ƙyaƙyawan ƙanwar tasa mai kama da mahaifiyarsa.

"Drawing zan yi, pensil ɗin ya ƙarye, shine na ɗau razor blades ɗin, daga nan kuma na zo nan, I'm sorry."

"Ba komai ƙanwata, gobe na je T.T injection, je ki kwanta." Ba musu ta yi waje tana farin cikin ta yi nasarar yi ma ɗaya sheda, kuma ta tabbar Al-hassan ne wanda ke gida yanzu.

Tana fita ya koma ya kwanta, babu abinda ya tsaya mai a rai sai muryan Marwa da take kuka, ji ya yi hankalinsa gaba ɗaya ya tashi, ya rasa natsuwarsa, bai ga dalilin da yasa yake jin haka ba.

Ya dai san Marwa ta shiga ransa, a cikin watannin nan da suka wuce, sun sake haɗuwa sau ɗaya, daga nan kuma ba su sake ba, amma babu ranar da baya tunaninta, babu ranar da ba ta addabar mafarkinsa.

Kallon agogo ya yi 12:23pm, sai ya rintse ido, gaba ɗaya ya mance dare ya yi sosai, haka ya bari Al-hussain ya fita, leɓansa ya ciza yana kiran number Al-hussain, bugu uku ya ɗauka.

"Kana ina? Meke damunta?." Ya tambaya cikin tashin hankali, sai dai jin muryan Al-hussain babu rashin natsuwa ya sa ya sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya.

"Come down Bloodline, yanzu haka ma na kusa gida, tana lafiya rigima ce kawai."

"Ok, take care." Da Haka ya cire wayar yana jin kamar be yarda rigima ce take ma kuka haka ba.

Wayarsa ya ɗauka, take kuma ya yi abinda yake hana zuciyarsa amma yau kam ya kasa, tun ba yau ba yake da numberta sai da be taɓa gigin kirarta ba amma yau dole ta sa.

Number da be yi saving ba ya latsa, ya fara ringing, sai dai ba ta ɗauka ba, hakan yasa ya sake kira, wannan kuwa bugu biyu aka ɗauka.

Shuru aka yi daga cikin wayar hakan yasa ya yi shuru shima, sai can ta katse shurun da muryarta mai garɗi.

"Wake magana ne?." Yarda ta faɗa cikin masifa yasa ya shafa ka sa.

"Assalamu alaikum." ya faɗa a natse, shiru ta yi tana nazarinsa, sai dai jin abinda ta ce yasa ba shiri ya tashi ya zauna.

"Wassalamu alaikum Al-hassan."

"Ya kika gane ba shi bane?."

"Saboda haka zuciyata ta ce min." Ta faɗa harda murmushin da yaji sautinsa.

"Me ya saki kuka ɗazu?." ya tsinkaye bakinsa da furta hakan.

"Babu komai."

"Ƙarya ba halin mar'atussaliha ba ne, faɗa min gaskiya." take yanayinta ya sauka.

"Family issues ne, karka damu. Bye." Da sauri ya ce.

"Akan ƙaramin abu karki sake zubda hawayenki, dan suna da daraja, ba kisan duk ɗigo guda zai iya jiƙan maƙoshin bayin Allah da yawa ba............hmmmm kin ɗaga min hankali, Please ki kula." Yana kai wa nan ya katse kiran, sai a lokacin kuma yake jin rashin dacewar kiran na ta, take ya goge numberta daga wayarsa.

Abinda Al-hassan be sani ba shine, a iya wayar ne ya goge numberta amma ta riga ta shiga cikin tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa. Murmushi ya saki jin tana lafiya, sai ya tambaya kansa.

"Menene amfanin kiran budurwar Al-hussain?." kasa ba kansa amsa ya yi dan haka ya miƙe ya shiga restroom dan watsa ruwa kafin Tweenynsa ya dawo.................✍️ END. ★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN Ƙ*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI