PAGE 2️⃣1
by @prettys01
> "Menene amfanin kiran budurwar Al-hussain?." kasa ba kansa amsa ya yi dan haka ya miƙe ya shiga restroom dan watsa ruwa kafin Tweenynsa ya dawo...............
************
Koda suka shiga part ɗin su, ganin Fauza na kuka kamar anyi mata mutuwa yasa Basma ta nufeta da sauri, ɗaga ta ta yi tana mai share mata hawayen da suke zuba kamar an buɗe panpo.
"Kuka ba namu bane, sai dai yarinyar da ta sanya mu jin babu daɗi sai ya ji haka ita ma." Haka suka zauna dukkansu, har lokacin Marwa itama tana ta hawaye, gashi ta sanya Al-hussain jiranta, hakan yasa ta kira wayarsa, sai dai ta kasa magana sai kuka, sai ta katse kiran tana dafe kanta.
Basma kuwa wayarta ta ɗauka ta rubutu wasu number.
"Kallo minti biyu na yi ma number na haddace ta, haddar da bana tsammanin zai goge a cikin kaina."
"Number ƴar iskan ce?."
"Eh Marwa." Marwa ta goge hawayenta tana kallon wayar, sai dai kira biyar suka yi wayar na kashe.
"Shegiya ta taro match dole ta kashe wayarta." Cewan Basma tana sake kira.
"Hmmm ko kuma shi Abba ya ce ta kashe ba........Abba ya cuce mu wallahi, harda wani cewa saboda mu........" da sauri Basma ta rufe ma Marwa baki.
"Ya isa, idan tasan wata ai ba tasan wata ba, number zan tura a bincike ta tsaf, a tura min bayanan, daga nan zan kwasa ƴan sanda mu tafi da su, wallahi dukka ƴan gidan zan sa a kwashe, ko sun kai nawa ne kuwa."
"Nijla take Nihlah ma?."
"Najla ya ce, wai Abba da budurwar.....kai ahayye akwai abu gobe wallahi." da haka Basma ta shige bedroom ranta fes, Fauza ta sake maimaita sunan tana zama.
"Najlah." Sai ta yi ƙwafa, Marwa kuwa mayafi ta ɗauka ta yi waje dan a part ɗin Abba ta bar hularta.
A Compound ta iske Al-hussain yana ta safa da marwa, murmushi ta yi dan kuwa Basma ta ƙara musu ƙwarin gwiwa.
Yana ganinta ya nufota da sauri yana ƙoƙarin rungumarta, sai ta maƙe kafaɗa tana turo bakinta, hankali a tashe ya ce.
"Me kike ma kuka?."
"Uhmm kawai abune ya shiga min ido." Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauke yana dafe zuciyarsa.
"Kinsa ƙirjina dukan uku-uku." murmushi ta yi tana kama kunnuwanta.
"I'm sorry Mijin Marwa." sai ya yi murmushin.
"Na ƙosa ki kammala karatun nan muyi aure, duk da ma iyaye sunyi magana."
"Very soon zan mu gama ko in ce zan gama, dan kai rakiyata kawai kake."
"To na zauna a gida wani ya yi wuff da ke, wai dana mutu kuwa." Ganin dare ya yi sai basu ja hirar ba, suka yi sallama ya wuce, da nishaɗi ta shiga ciki, har ga Allah ta ji daɗin haɗuwar Abbeey da Abba akan aurensu, kuma an tsaida Ranar da za ta yi sign-out ranar za'a ɗaura musu aure.
Ko da ta shiga ciki, Fauza ta yi barci, Basma na wanka, sai ta cire rigar jikinta ta sanya na barci, jin wayarta na ringing ta duba, ganin Number yasa ta jirkinta ɗauka.
Bayan ta ɗauka kuma aka yi shuru, har sai da aka ba ta haushi ta fara magana, amma bayan maganar da ta yi aka ba ta amsa yasa ta ji zuciyarta ta harba, balle da ya tabbatar da shi Al-hassan ne, ga kuma kalansa da suka tsaya mata a rai.
Wayar tabi da kallo bayan katse kiran, tana jin wani irin yanayi akan Al-hassan wanda sam ba ta ji tare da Al-hussain, gasu dai iri ɗaya sak, ba su da banbanci amma tana jin Al-hussain a cikin ranta, Al-hassan a cikin tunaninta.
A haka kuma ta kwana da kalamansa da suke sanyata nishaɗi.
Washegari ta kama Saturday, duk suna gida dan haka ba su fito breakfast ba sai 9:30am, Dining room suka nufa kowacce ta nema waje ta zauna, suna ɗan hira kaman babu wani abu dake cin zuciyarsa.
Kowa ya fara cin abinda yake buƙata.
"Wai ke Al-hussain ɗin nan baya hawa miki kai? Haba ki ta soyayya sai kace Romio, waya kodayaushe, Chart, zuwa fira, kai Marwa Rayuwar ki da gyara." Ta kai nan tana kai bread bakinta wanda ya ji butter, Marwa da take shan tea da yam ball ta yi dariya tana cewa.
"Hmmm ke da kike son rayuwa a haka ki yi ta yi, har yanzu ba kisan daɗi da gardin soyayya ba shi yasa, a soyayya babu takura, babu matsi, ke duk bayanin da zanyi ba za ki gane ba, Allah daga lokacin da kika fara ainiyin soyayya za ki fahimci haka."
"Allah ya tsare Ni da irin soyayyar nan, wallahi da Ni ce, shatamai layi zanyi, na bashi ƙaƙidojin hira, waya sau biyu, zuwa hira duk sati sai ɗaya, Ni fa na tsana abinda zai ta kurani." Haka suka dinga hira wani suyi dariya wani su harara juna.
Fauza dai binsu take da ido tana shan lemon tea, dariya ta yi jin abin da Marwa tace.
"Sai kin zurma da yawa ma, ya ƙi kiranki ke kuma tun safe ki dinga nemansa ya ƙi ɗauka, haka za ki haukace mana, ki kasa cin abinci." Ita kanta Bama dariya ta yi, sannan ta zagaye kanta ta hannu kafin ta haɗe yatsunta suka bada ƙara.
"God for bit....Marwa ki kiyayeni wallahi." Suka kwashe da dariya dukkansu, take kuma duk suka haɗe rai kaman hadari ganin Abba ya iso inda suke, yaja kujera yana sakar musu murmushi, ganin suna cikin walwala.
Basma ta fara miƙe ba tare da ta gama ba, ta goge bakinta, ta bar wajen, take Marwa ta ɗau na ta Plate ɗin sannan ta kalla Abba, ta girgiza kai ta bar wajen itama, be ce musu komai ba yasan hakan za ta faru ai.
"I.....Ina.....ina kwana." Cewan Fauza itama tana ƙoƙarin tashi.
"Zauna ki gama cin abincin ki."
"Na ƙoshi." Ta faɗa tana tashi daga wajen dama ba ta cin abinci da safe, sai dai abu mai ruwa zalla sai rana ta yi take cin abinci.
Da ido ya bi ta har ta ɓace mai, sai ya shafa suman kasan yana jin babu daɗi, ji yake kaman be ƙyauta musu ba, kamar ya ci amanar Karima, kaman dai Allah zai kamashi dan alkawari ya yi mata ba zai yi mata kishiya ba, da sauri zuciyarsa ta ce.
'Ai ka cika alkawari dan kuwa ba ka kula kowacce mace ba sai da ta bar duniya, yanzu ba ta raye, auren Babu Najlah ba laifi bane.' sai ya lumshe ido yana tuno abin ƙaunarsa, muraɗin ransa, uwar ƴaƴansa, Ammeen Basma mai Capacity a zuciyar Abba......
Haka Abba ya gama ya koma ɗakinsa, yana da aikace-aikace da yawa a gida, dan haka be zauna a part ɗin sa ba babban parlour ya zawo ya zauna da kayan aikinsa. Abin mamakin haka ya wuni a Parlourn babu wacce ya sake ganin ko inuwarta, har aka yi zurh aka yi la'asar, babu wacce ta sauko.
Bayan da ya dawo sallar la'asar ne ya hangi mai aiki na nufan part ɗin su da abinci, hakan yasa ya ji dama-dama, gaba ɗaya kaɗaici ya ishesa, duk da tun asuba suke waya da Najlah har gari ya waye, yasan su da waya kuma sai dare.
Ɓangaren yaransa kuwa, da sanensu suka ƙi fitowa, kowa ta yi harkan gabanta, saboda ba sason su fita haka Marwa ta hana Al-hussain zuwa zance, sai suka sha V.D.
"Ai Abba sai ya yi nadaman fara kula macen, dan gaba ɗaya za mu ja jikinmu daga garesa har sai ya janye kalmansa."
"Marwa ko ya fasa, sai mun nema yarinyar munci ubanta."
"Ya Basma me Shamo ya ce akan number?." sai Basma ta kalla Fauza.
"Tun jiya na tura mai number, to Ni ma yau nai ta kira baya shiga har na fara tunanin ko mistake na yi, amma ɗazu ya kirani wai sim din an yi amfani da shi da safe, be gama samun bayanan mai number ba aka rufe sim ɗin, dole sai an sake buɗe wa zai bani bayanai gaba ɗaya."
"Hmmmm na ƙosa na ga wata Bazawara ce ta yi ganganci tsayuwa da Abba, sai na yi mata rashin mutumcin mai wassali." Faɗin Marwa tana sanya yatsa a baki ta ciza, sai Marwa ta ce.
"A asibiti zan ɗauko acid na watsa mata."
"Da gaske za ki iya watsa ma wata acid?."
"Me ze haka Fauza, ai duk macen da ta raɓa Abba dole na azabtar da ita." dariya Marwa ta yi.
"Sai da ke ƙanwata mai kamar Mom, daga kaman har zuciyar ba ki ɗauki na kowa ba sai na ta."
"Shi yasa na zama ma'aikaciyar jinya irinta, kunsa muna da imani amma bamu da tausayi." Tare suka yi dariyar har da tafawa dan duniyar yana musu daɗi..........
***********
*Merry* Ba ta farka da wuri ba sai wajen 11am, tasan yau ba za ta fita ba shi yasa tasha barcin ta, bayan ta farka ta yi wanka sannan ta fito dan yin breakfast.
Bayan ta ci abinci, ta dawo main parlour ta zauna, news take kallo, tana sha fruit salad.
A natse ta mai da idanunta kan Tweeny ɗaya da ya fito cikin shigar ƙananun kaya, Jean's ash da dark blue shirt, ga gashin kanan nasa ya sha gyara sosai sai ƙyalli yake, ba ƙwarya Tweeny maƙurar ƙyaune.
Murmushi ta yi dan kuwa ta gane Al-hassan ne saboda saman girarsa an sa mai plaster alamun yaje an mai dressing, daɗi ta ji, tana fatan wajen ya yi tabo wanda za ta dinga ganesu.
Zama ya yi a kan kujera yana latsa waya.
"Good Morning Brother."
"Morning my sister."
"Na ce, ka tura min taswiran zanen Bello, zan gyara wasu wajen sai mu yi amfani da shi wajen aikin, zai fi sauri." Ta faɗa tana kallonsa, sai ya ɗago kai ya kalleta.
"Ki bari Al-hassan ya fito, yana ciki." Kallon ka rainamin wayau ka yi ta yi mai tana ƙara kallonsa.
"Bangane ba!? Al-hassan ka ce yana ɗaki?." ya ɗaga mata kai alaman tabbatarwa.
"Please stop joking, ka turomin a yau zanyi aiki, gobe sai a fara aiki." kallonta ya yi da ƙyau.
"Na ce ki bari ya fito, bashi bane." Da haka ya miƙe ya nufa Kitchen, ita kuma ta harara bayansa dan gani take ya raina mata tunani, ba yarda za'a yi hakan ta kasance, dan kuwa Al-hussain shine ya fita a jiya, Al-hassan ta yi ma yankan nan, gashi Al-hussan ɗin yana ce mata bashi bane.
Ƙwafa ta yi, da sauri kuma ta juya tana kallon wanda ya iso cikin Parlour yana mata magana.
"Merry na tura miki zanen Bello, make sure ki gama aikinsa yau." Ganin yarda ta miƙe tana kallonsa, yasa ya tsaya yana mata kallon mamaki.
Mamaki da zallar sarƙaƙiya take gani, a hankali ta fara takawa zuwa gabansa, ta kai hannu ta taɓa ciwon dake saman girarsa, be ce komai ba sai rufe mata baki da ya yi da hannusa.
Magana take son yi amma ta rasa me za ta ce, da sauri kuma ta kalla wanda ya fito daga Kitchen riƙe da Multina, tabbas so suke kanta ya buga gaba ɗaya, a hankali ta kuma kallon wanda ke gabanta, yana da ciwo a wajen, hakazalika wancan shima yana da ciwo, gashi a waje iri ɗaya kuma dukka an sanya musu plaster.
Baya ta ɗan ja, sai wanda ke gefanta ya nufa ɗayan, yana zuwa suka rungume juna, komai na su iri ɗaya haka suke rayuwa, dan masifa ciwo ma idan ɗaya ya ji ɗayan ma sai yaji makansa da gangan, ta manta da wannan halin nasu, dan haka ta ja dogon numfashi ta fesar tana kallonsu, zama suka yi a kujera ɗaya, suna shan Multina guda ɗaya, idan wannan yasha sai wannan ya amsa ya sha, su kaɗai ne suka san kansu, su kaɗai ne suka san banbancin kansu, dan haka ta buɗe baki ta furta abinda ya tabbata Al-hussain sai ya ji shork, sai ya bayyana kansa, sai ya kalleta, kuma tabbas sai idanunsa sun bayyana rauni. Ta yi gyaran murya tana cewa.
"A daren jiya wani dattijon mutum da ake kiransa da PA.1, yarda aka samu sunan a jikin I.D card ɗin sa kenan, ya samu hatsari, wanda aka bayyana ya ji gata sosai, dan ya rasa jini mai yawa, a halin yanzu an kwantar da shi a asibiti kuma ana cigiyan danginsa, ga wanda ya ganesa ya tuntuɓi wannan number...........social media ya yi wani lokacin." Takai nan tana ɗaga ido ta kalla Tweens da suke kallonta jin labarin da ta karanta, murmushi ta saki dan kuwa a kallo ɗaya ta gane Al-hussain a ciki, idanunsa sun bayyana mamamki da firgice mai yawa.................✍️ END.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️