BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣2

by @prettys01

> ...........Takai nan tana ɗaga ido ta kalla Tweens da suke kallonta jin labarin da ta karanta, murmushi ta saki dan kuwa a kallo ɗaya ta gane Al-hussain a ciki, idanunsa sun bayyana mamamki da firgice mai yawa.................

Al-hussain take kansa ya sara, lokaci guda idanunsa suka sauya launi, kallon Merry ya yi cike da ƙarin bayani.

"Allah ya bayya danginsa ya bashi lafiya." Cewan Al-hassan yana kauda idanunsa daga kan Merry.

Ido ciki ido suke kollon juna, hakan ya sa ta ɗaga mai kai alaman tabbatar da abinda ta furta, miƙewa ya yi tsaye ya shafa tarin gumusa masu cika da laushi.

"Uhmmm Merry zo ki rakani supermarket." Ya faɗa yana haɗiye kakkaurar miyau daga maƙoshinsa.

"Fita za ka yi?."

"Eh Al-hassan amma yanzu zan dawo."

"Shike nan, Merry kuje tare Ni zan jira fitowar Barkono." Ɗan dariya Merry ta yi, shi kuma Al-hussain ya yi murmushin da ya tsaya kan leɓansa jin sunan da ya kira Abbeey.

Da sauri Al-hussain ya nufa ƙofa zai fita, sai ya tsaya cak yana jin abin da Al-hassan ke cewa.

"Na tura ma kuɗi, komai ka siya nima ka siyomin irinsa."

"An gama ɗan uwa." Da haka ya fice, Merry ma da sauri ta bi bayansa harda haɗawa da gudu.

Al-hassan ya gyara zamansa yana duba wayarsa, be ɗau lokaci ba sai ga Abbeey ya fito cikin shigar kayan gida, kamar kullum fuskarsa a haɗe kamar hadari.

Da sauri ya gyara zamansa yana sake gaishe da shi cikin girmamawa.

"Alhamdullah, waye a ciki?."

"Al-hassan ne Abbeey." sai ya ɗaga mai kai.

"Ina shashashan ƙanin naka?." ya faɗa yana zama.

"Sun fita da Merry yanzun nan."

"Okay." Da haka suka yi shuru na wani lokaci, kafin Abbeey ya sake kallon Al-hassan.

"Nasan a ranka yana yawan tambayar kanka me yasa na zaɓa muku Momy a matsayin mahaifiya?...............kai kaɗai kake wannan tunanin banda ɗan uwanka da ƙanwarka, a baya har na fara zargin kaman akwai wani abu da su biyu suke ɓoyewa bayan mutuwarta, sai dai daga baya na gane babu komai. Hmmmmm ka sani kowa da irin nasa ƙaddarar a rayuwa, kuma tunani mara ƙyau akanta be da ce, Momynku tana da tausayi, mutumci, kyautatawa al'umma, shi yasa nake ƙara sonta, kawai babban matsalarta shine......" maganarsa ta tsaya sakamakon wayarsa da ta fara ringing.

Al-hassan lumshe ido ya yi, shi har ga Allah baya yason tuna yana da uwa, baya son tuna komai dangane da ita, tabbas tana da halaye masu ƙyau, matsalar ɗaya kamar yadda Abbeey ya ce, wannan matsalar ne yasa ya komai da take yi bata burgesa, hatta magana a baya sai suyi kwanaki ba su yi ba, amma idan ba ta da lafiya, hatta Al-hussain baya shiga tashin hankalin da yake shiga, ko da ta mutu, ya yi kuka, Kukan da ya kusan haukatasa, ya shiga tashin hankali, ya zama yana keɓe kansa daga kowa, be suma kaman Al-hussain ba amma ya ɗau watanni ko ya ce shekara yana jin yar haka, sannan a duk lokacin da ya tunata baƙin ciki da na addabar ransa.

"Shikenan General, nan da kwana goma ze kasance...........zan shigo a tabbatar sun ƙware da kowani training duk da nasanka............ eh...... shike nan, thank you my friend." Da Haka Abbeey ya katse wayar, a natse ya mai da idanunsa kan Al-hassan.

"Me nake ce maka?."

"Uhmmm maganar kasuwanci kake min." sai Abbeey ya yi murmushi.

"Kana min kallon Tsohon da ya fara rikicewa ko?." sosa kai ya yi.

"Shike nan na bar maganar tunda ba kaso, amma a duk yarda take ina sonta, ina alfahari da ita, gashi ta bani ƙyauta mafi daraja, wato ku."

"Hakane Abbeey, bara na ɗauko abu ina zuwa." da haka ya miƙe ya nufa part ɗin su, shi kuma Abbeey ya bi shi da ido yana murmushi.

"Anya ba Al-hussain bane? Na ga kamar ya sauya mood da na yi magana akan halayen Shalelensa, uhmmm ku kuka sani, yara makan aljanu." ya girgiza kai kawai, dan ɗazu duk ya gansu da wannan ciwon, yasan ɗaya by Mistake a ka ji, ɗaya kuma da ganganne.....

Ko da suka fita, motar Al-hussain suka shiga, ya figa mota kamar ana yaƙi.

"Meyasa baki faɗa min PA.1 ya yi accident ba?." Ya faɗa cikin amo da masifa, sai ta dafe kai tana cewa.

"Ba accident ya yi ba wasa nake yi." Wani irin burki ya ci wanda yasa dukka su biyun suka kusa bugewa da glass ɗin motar, dan ma babu wani mota a bayansa da ya buga nasa motar.

A fusace ya kalleta da idanunsa suka yi jajur.

"Me....me kika ce?."

"Yes, wasa nake maka, kawai ina so mu yi magana ne akan......." wani tsawa ya yi mata yana wuci.

"Kinsan duk abinda ya shafa Momy bana wasa da shi, kinsan hankali na ya tashi, karki sake min irin wasan nan." sai ta dafa hannunsa, da sauri ya janye nasa yana kifa kansa akan sitiyari.

"I'm so sorry Al-hussain, dama maganar is very important shi yasa, na so tun jiya ka kulani amma sai raina min hankali kuke yi." ta faɗa kamar ta yi kuka.

Sai ya ɗago ya riƙeta yana jin soyayyar ƙanwar tasa.

"Da Ni kika fara magana jiya, sorry faɗamin menene." sai ta sauke ajiyan zuciya.

"Akan dai PA.1, munyi magana akan aurenka da za'a ɗaura gobe, an sauya lokaci zuwa 7:30pm na dare." Rintse ido ya yi sannan ya buɗe.

"Na sani, bana son auren nan, amma babu yarda na iya tunda yana cikin *Promise* na Momyna, ba zan ba ta kunya ba, haka nan zan riƙe amanar duk abinda na ɗauka, plan ɗin mu ba zai rushe ba."

"Ya za ka yi da Marwa?."

"Marwa ita ce wacce nake so, kuma zan aureta duk da Momy na raye ba za ta bari ba saboda dalilin da na sani kema kika sani." Ya faɗa cike da rauni.

"Hakane, abu na gama Amaryarka ta amince za ga ci gaba da zama a gidan iyayenta har zuwa lokacin da za ka bayyana ma duniya hakan, a ganina lokaci ya yi da ya kamata ka fara neman kuɗi kodan iyalan da za ka tara." sai ya furzar da iska daga bakinsa.

"Zan ƙoƙarta hakan, kin yi angon dinner?."

"In banyi ba to waye zai yi, tun last week na amsa, kuma kaima kayan da za ka sa suna a shirye." Sai ya kaɗa kai yana kunna motar sannan suka nufa supermarket, baya da buƙatar komai amma saboda Al-hassan ya siyan musu turare iri ɗaya da wasu agogo na fata, da haka suka nufa gida suna ta tsara yadda goben zai zo musu............

**************

Abba tun yana jiran fitowar su har ya cire rai, dan haka ko da Najlah ta kirasa, a zaune a parlourn suke waya V.D call a wayar General, kallonta ya yi da ƙyau ta cikin wayar.

Tana zaune kan kujera, Black t-shirt ne jikinta da wani farin p-cap, Lollipop take sha mai tsinke, hakan yasa ya ƙura ma lips ɗinta ido.

Leɓansa ya ɗan lasa yana lumshe ido, a natse kuma ya buɗe yana mai rage murya.

"Najlah kin shirya kasheni da rai na ko, tsaki da Allah ji yarda kika tsotsan sweet, wayyo Babyna." Najlah ta yi ƴar dariya tana wani fari da ido.

"Uhmmm to in ban sha sweet ba me zansha? Ina son teste ɗin abu mai zaƙi ne."

"Hmmmm Ina son na cija leɓan nan masu taushi." Murmushi ta yi, take kuma ya kai wayar ya summaci ciki yana mai jin nishaɗi da farin ciki. Jin wani gigitaccen sauti yasa ya juya yana kallon hanyar da zai kaika part din su Basma.

Marwa ce tsaye, ta fasa ihu jikinta yana rawa, da sauri ta sake kulan dake hannunta ta yi sama da gudu tana kuka, gaba ɗaya ya manta a inda yake zaune, Najlah ta rikitasa da yawa hakan yasa ya rasa natsuwarsa gaba ɗaya.

"Baby meke faruwa ne?." ya jiyo Najlah ta faɗa tana ƙara narkewa.

"Marwa ce."

"Oh sorry, ya kamata su dinga sallama kafin su shiga waje, dan wani lokacin zasu iya shigowa part ɗin mu su iske muna wasan gudu ko kuma ƴar kokawa." besan lokacin da ya yi murmushi ba.

Take suka dasa hirarsu takan ba za'a mutu ba.

Marwa da kusan maganganun Abba da na cikin wayar ta ji, hakan yasa ta faɗa ihu, da gudu kuwa ta koma bedroom ɗinsu, tana shiga ta faɗa gado tana sake fashewa da kuka.

Basma sallar iska ta gama kenan tana cire Hijab sai ga Marwa, da sauri ta yi kanta tana tambayar ba'asi, Fauza ma ta ɗago fuskarta tana tambayar lafiya, sai dai Marwa ta kasa magana, sai ta yi da ƙyar tukun ta haɗa kalaman bakinta.

"A...Abba......Abba ne yake waya da karuwa..... har.....harda sumbatar ta, ga kalmar na rashin ɗa'a da take masa shi kuma sai dariya yake." Ido suka zaro dukkansu.

Da sauri Basma ta ɗauki wayarta tana kiran number nan sai dai a kashe take, tsaki ta ja mai tsayi.

"Lallai ma, muje ƙasan." Da haka ta yi gaba a zafafe, su ma suka rufa mata.

"Mu tsaya daga nan wallahi komai da take cewa ana ji." Da haka suka sauka daga stairs Suka tsaya a bayan Abba suna saurarensa.

"Shalele me kike so to? Kin fa sha sweet yanzu, kinsa magiyan da nasha kafin aka siyo miki." Ya kai nan harda gyara zama.

Basma da masifa ke cinta ta yi ƙoƙarin nufan Abba, sai Marwa ta riƙe ta taɓa girgiza mata kai, sai ta dagata, take suka jiyo sanyayyar muryar Najlah cike da shaƙwaba tana cewa.

"Uhmmm uhmmmm uhmmmm Ni ice-cream nake so mai ɗumi."

"Baby Ice-cream kuma? Please ki bari gobe, ko jibi da kaina zan kawo miki, amma yanzu a ina za'a samu Ice-cream? Ba lallai Ogan ki ya bari ba." Yarda ya yi magana yasa Basma jin wani irin jiri na kamata, ta yi baya, Fauza ta riƙe ta tana share hawaye.

Duk motsin da suke Abba baya ji domin ya yi nisan kiwo a cikin duniyar soyayya, maganarta ce sake dakansu.

Abba gaba ɗaya yau ta cazamai kai, kallonta ya yi, duk ta haɗe fuska ta yi kalar tausayi, sannan tana gab da fara mai kuka.

"Baby Ni dai wallahi yanzu nake son shan Ice-cream ɗin, kuma bance ka zo jibi ba ka bari ranar walimar mu, amma yanzu dai nake son ko wallahi na yi maka kuka." marairaice wa ya yi.

"Karki kuka, zan sa a siyo miki, amma a ina ake sai da Ice-cream mai ɗumi?"

"Uhmmm Ni kai za ka siyomin ba wani ba." ta faɗa hawaye suna cika idanunta.

"Wayyo Najlah ya zanyi wai, tsakaninmu akwai nisa, ya zan yi?." Ya faɗa kamar zai yi kuka, sai ta yi magana kaman yarinya

"To ai Ice-cream ɗin yana wajenka yanzu haka." Da mamaki ya kalla kansa yana nuna kansa, ta ɗaga mai kai.

"Eh Ice-cream mai ɗimu ga zaƙi sai miyan bakinka." Dariya ya bushe da shi dan yarda ta faɗa cikin solon burgewa.

Gaba ɗaya ji suka yi duniyar ya tsaya musu cak, an sauya musu Abba, ba shi bane zaune a parlourn Mom yana waya da karuwa, sai dai karuwar kuwa ɗan wannan maganar ya girme musu.

Basma haƙurinta ya ƙare ba ta jin zata ci gaba da sauraren hirar da suke yi dan yana ƙona mata zuciya, cikin wani irin sauri da kuzari ta nufa Abba, ta fizge wayar tana wuci.

Hannunta ya latsa katse kiran hakan yasa kirar ta katse, Abba da sauri ya miƙe yana kallonsu, daga ganin yananinsu ya tabbata mai da sun saurara hirarsa, sai ya ji ransa ya sosu, baya son suna fushi da shi.

Magana zai yi ta ɗaga mai hannu tana kallon wayar da ya shiga key.

Hawaye suka cika mata ido, haka ta shanye tana cewa.

"Menene password ɗin?."

"Ba yarda kike tsammani bane, ku zo na muku bayani ba wani abu bane a......"

"Abba...... password." Zama ya yi yana jin rarrashin su zai yi ko ya sharesu amma ba zai iya musu faɗa ba.

"Ki sanya sunanan ƙaruwar Maybe ya buɗe." kalaman Marwa sun dakesa sosai, amma be ce komai ba.

Kafin ta gama sa sunan Najlah sai ga kira voice call daga *My Brother ❤️* harda alaman soyayya a jiki.

Kallonsa ta yi tana girgiza kai, a ranta kuma yana cewa 'Wato budurwar ce ya sanya mata sunan Brother.' ta yi ƙwafa tana accepting call ɗin.

Yasan Najlah wankesu tas za ta yi, kuma ba zai iya hanasu waya da ita ba, balle yarda suke ji.

Marwa da Fauza suka sanya Basma a tsakiya suna jin abinda ta cikin wayar ke cewa.

"Darliiiiiing."

"Ƴaƴan sane." cewan Basma a kausashe.

"Lah Basma ya kike? Ina Abba?."

"Dalla dakata ƴar iska karuwa kawai."

"Karki kuskura ki ɗaga wa Mahaifiyar ki ta gobe murya, ba za ki yi albarka ba." Kamar ta sake kunna Basma ne ma.

"In ji dudum, dan Allah in ji bugu, a wajen mai albarka ne ake neman albarka, ina miki gargaɗin da babban murya ki fita sabgan Abba, tun kafin mu yi muki illa." Da sauri Marwa da tasa.

"Karki bari mu gane wacece ke, dan haɗuwar ba zai miki ƙyau ba sam, kin samu nasarar mallake zuciyar Abba, dan haka ki ce ma malaminki ya yi ƙoƙarin, amma ya baki maganin mallakar ƴaƴansa...........hmmmm kina wasa kunama." Basma ta sake amsar maganar.

"Ko ta arziki ki gujesa ko ta bala'i, kin gama yawon bariki, shine za ki liƙe mai, to ki kama kanki, Abba mijin wata ce, daga ita babu ƙari." ta kai nan tana wani wuci.

"Shegiya dole ki yi shuru tunda kin gama ƙisi-sina a wajensa, ki shafa ma kanki lafiya ki rabu da shi na har abada." Faɗin Marwa, Fauza dai ba ta ce ko kanzil ba.

Wani dariyar shaƙiyanci Najlah ta yi, sannan ta daidaita muryar ta ta ce.

"Yau na ga lukutar masifa, ashe ina da babban aiki, dan har lafazi sai na koya muku yarda za ku dinga furta min...........ba buƙatar ku sha wahalar nemana dan na muku nisa, ina Kaduna, ku ɗan yi haƙuri nan da ɗan lokaci zan shigo gidan, sai ku ganni da ƙyau........" da sauri Basma ta katseta.

"Yarinya bakisan da wa kike magana ba ne........."

"Da yaran mijina nake magana, sannan ki sassauta kalamanki a kaina, sai dai akan Abba zan iya shanye komai, Ina son simulmulun Gayena, Mai cikar haiba da ƙyau, Wayyo Allahna ina matukar son Abba, ku kula min da shi kunji." a fusace Marwa ta ce.

"Ke mahaukaci kisan me bakinki zai furta, ci gaba da tarayya da Abba daidai yake da........." Abba ne ya fizge wayar ransa ɓace, ya kallesu da ƙyau yana musu kallon da suka kasa fassarasa.

"Ki kwanta gobe zamu yi waya." kafin ya kashe ta narka murya tana cewa.

"Gobe Ina son ganinka kaji Baby."

"To bye, take care." Da Haka ya katse kiran yana mai son musu faɗa amma raunin da yake gani a fuskokinsu yana hanasa, amma haka ya yi dauriya ya buɗe baki ya fara magana a natse kuma cikin sanyin murya...............✍️ END. *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️