PAGE 2️⃣ 3
by @prettys01
> "To bye, take care." Da Haka ya katse kiran yana mai son musu faɗa amma raunin da yake gani a fuskokinsu yana hanasa, amma haka ya yi dauriya ya buɗe baki ya fara magana a natse kuma cikin sanyin murya...........
"Me yasa kuke ta hayaniya kaman kaji? Najlah ba ta son faɗa, amma kunsa tana mai da muku martani, wallahi ba ta da matsala." Da haka ya gyara tsayuwansa yana jiran abin da za su ce, yasan wacce za ta fara magana, dan haka ya kalleta, ilai hawaye ta share sannan ta fara magana a raunane kamar Hajiya Karima.
"Yanzu dai ya tabbata Bazawara kake kulawa, MACE? Abba mace fa kake waya da ita a parlourn Mom, macen ma ƴar bariki." da sauri ya ɗaga mata hannu.
"Najlah ba ƴar bariki ba ce, kuma ba Bazawara ɓace, budurwar ce, mai hankali."
"Ba wani budurwa, ta dai gama yawon ta zubar, ta bi maza lungu da saƙo, ta gama lalata shine za ta zo kai ka aureta a manage, wama ya sani ko tana da H.I........." wani lafiyayyen mari ta ji a kumatunta, wanda yasa Basma ganin taurari sun haska a cikin kanta.
Kuncinta ta dafe tana mamakin marin da Abba ya yi mata, za ta iya rantse wa tunda suke ko gargaɗi da yatsa be taɓa musu ba, hasalima baya da faɗa baya da hayaniya.
"A.....Abba marina ka yi akan wancan Ƙaruwar?." Abba besan lokacin da ya mareta ba kawai ba zai jure a dinga aibata Najlah ba ce, cikin dakiya ya ce.
"Me yasa za ki dinga haɗata da mugayen kalamai, zan iya jure komai amma banda zagin Najlah, domin ita ɗin zuciyata ce, wanna haukan ba shine zai sa na fasa ba aurenta ba, idan kunga ban aura Najlah ba to wallahi mutuwa na yi, banjin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ita ba, dan haka ku kula." da haka ya karkaɗa musu yatsa alamun warning, sannan ya juya ya fara tafiya sai dai jin abinda Basma ta kuma cewa cikin kuka yasa rintse ido.
"Ta gama da mu, wallahi ƴar iskan ta cuce mu, ta shanye Abba, ta juya masa tunaninsa......to wallahi idan kana sonta ka rufa mata asiri ka rabu da ita, dan wallahi idan ka kawota gidan nan sai mun kasheta, kuma wannan marin bashi ne, akan ta zan rama." murmushi mai tarin ma'ana ya yi dan tunawa da wacece *Najlah* duk abinda ke ɗawainiya da su to na ta ya dama na kowa ya shanye.
"Idan na kawota ku kashe ta ɗin, amma aure kaman an yi ne." da haka ya shige ya barsu baki sake.
Marwa ai tun maganar Abba na farko ta ɗauke huta, numfashi kawai take amma jinta da hankalinta ba sa tare da ita, Fauza ma tuni take ta kuka.
"Najlah!!! NAJLAH!!!!!! Kin shiga uku, kin taro ma kanki masifa da bala'i, ku dena kuka, ita ce za ta yi kuka." Ta faɗa tana share hawayen da suke zuba daga idanunta.
"Bassey ina da tabbacin ta asirce shi, marin ki ya yi, wai Abba ke ɗaga mana murya." ta kai nan tana shafa gefan kumatun Bassey.
"Bashi ne, zan rama, yanzu dai gidansu za mu nema, ko ba'a Nigeria take ba sai munje har gidansu, muci mutuncinta harda na iyayenta."
"Sosai ma kuwa, wulaƙancin da ba za ta sake tsayawa da wani namiji ba."
Saboda tsabar masifa na cinsu, a nan Parlourn suka zauna kowa na saƙa da warwara a cikin ranta.
A'isha mai aiki ce ta nufo cikin Parlourn hankalinta a tashe, ta ji duk abin da ke faruwa kuma ta tausaya musu ainun.
Jiki na rawa ta zauna a ƙasa kusa da Bassey, ta rage murya tana cewa.
"Dan Allah ku ya ƙuri, ku dena damun kan......" gigitaccen mari Basma ta wanke ta da shi, sannan cikin tsawa ta ce.
"Tashi kibar wajen nan ko na miki illah, uban wa kiraki." ai da sauri A'isha ta bar wajen tana zubda hawaye.
"Mtwwsssssssss baƙar munafuka." Ta faɗa tana sake haɗe rai.
"Be kamata ki wuce akanta ba, ba ta da laifi, ta zo ta nuna kulawarta ne akan mu."
"Ya isa Marwa, haushin kowa nake ji, akan meye za ta tsugunna kusa da ni, bansan hauka wallahi mtwwwss." Da haka duk suka yi shuru, yarda cikin gidan ya ɗau shuru, dan dare ya shiga.
Fauza ce kawai ta yi barci, su kuwa yarda suka ga rana haka suka ga dare, suna zaune idanunsu sun bushe, haka zuciyoyinsu.
Ana kiran sallar asuba, suka hanga part ɗin Abba an kunna haske, da haka suka gyara zama.
A natse ya buɗe ƙofa ya fito, tun daga sama suke jiyo dariyarsa kafin suka ji yana cewa.
"Zan tafi masallaci, kema ki samu ki yi sallar yanzu, an jima zamu yi maga......" ganisu yasa ya kasa ƙarasa maganar, sai dai irin kallon da suke mai yasa ya katse wayar da yake yana nufan cikin Parlourn cike da mamaki.
"Subuhanallah kar dai ace anan ku ka kwana?."
"Hmmmmm Abba kana ban mamaki, amma nasan maganinku kai da karuwarka." Da haka ta miƙe ta wuce. Sai ya kalla Marwa, kauda kanta ta yi gefe tana cika taba ɓatsewa kamar mahaifiyarsa, sai ta yi mai kama da Hajiya Mama idan ta yi fushi, dama da shi take kama haka ita ma Marwan, yarda ta yi sai tuna mai da wani lokaci da Hajiya Mama take wannan kumburin kamar fulawar ta ji yis ta sha rana ta cika roba sukutum.
Besan ya yi ƴar dariya ba yana shafa kansa, ai wannan dariyar yasa Marwa fashewa da kuka, ta miƙe tsaye tana fara tafiya ta baya-baya tana girgiza kai.
"Abin dariya na zama? Dariya kake min Abba? Da...Dari...dariya fa?."
"Marwa ba haka bane, wani abu na tuna ne." Sai ta jinjina kai sannan ta haura sama tana share hawaye.
Lumshe ido ya yi yana jin babu daɗi, kallon Fauza dake barci tana ta sauke ajiyan zuciya ɗaya na bin ɗaya, alamun ta sha kuka sosai dan har fuskarta ta yi ja, kai ya girgiza sannan ya yi waje.................
*************
"Please Tweeny, kawai zuwa za ki yi ku gaisa a matsayin Ni, ba za ta gane ba, zanje kallon wani match ne sannan na biya asibiti na kai taimako." Al-hussain ya kai nan cikin sanyi ta sigar roƙo.
Su biyu ne zaune kan sopa, suna kallon juna, kamar kullum kaya iri ɗaya ne jikinsu, Orange ɗin riga da Army green ɗin wando.
"No Al-hussain, wannan ai haukane, ta ya zan je wajen budurwarka a matsayin kai, ka kirata kace ba za ka samu zuwa ba." sai Al-hussain ya riƙe kunnuwansa.
"Please and please, I begging you, jiya banje na ganta ba, yau kuma wayarta na katse, a jikina nake jin babu lafiya amma akwai wajen da dole ne je shi yasa, shike nan tunda ba za ka min wannan alfarmar ba." da haka ya miƙe ya juya baya.
"Hmmm Shikenan zani but in one condition." ya faɗa yana jin gabansa yana faɗi jin ya ce Kamar ba lafiya Marwa take ba.
Al-hussain ya yi murmushi sannan ya juyo baya, zama ya yi inda ya tashi.
"Faɗa min me kake so?."
"Kamin alƙawarin za ka kula min da kanka duk inda kaje, Ni kuma zanje na duba maka lafiyar Marwa." rungumesa ya yi cikin farin ciki.
"Zan kula maka da kaina, kaima ka kula min da kanka." take hawaye suka zubo mai daga cikin fararen idanunsa, yana tsoron ranar da *Promise* zai bayyana, a wannan ranar yasan zai rushe duk soyayyar da Al-hassan ke mai, yana son ɗan uwansa kuma yana son *Promise* saboda umarnin Momy ne.
Ƙara ƙamƙamesa ya yi yana jin kamar kar a rabasu, a yau zai yi aure, auren sirri, auren da ko ɗan uwansa da suka rayu na tsawon wata goma a cikin Momy, suka fito a tare, suke rayuwa a tare, sai dai *Promise* ya rushe komai.
Al-hassan jin irin riƙon da ɗan uwansa ya yi mai, yasa ya raba jikinsu yana kallon fuskar Al-hussain.
"Meke damunka?."
"Ba komai."
"Ban yarda ba, faɗa min hankali ya tashi." Ya faɗa yana share mai hawayen da suka gangaro daga idanunsa.
"Da gaske babu komai......."
"Ka faɗa min ko na fasa zuwa duba Marwa." jin abinda ya ce yasa Al-hussain furta abinda dole Al-hassan zai bar maganan nan.
"Momymu na tuna." take Al-hassan ya haɗe fuska, ya miƙe da sauri.
"Okay, zan fita daga can zan biya, kaima ka fita da wuri karkayi dare." Be jira amsar Al-hussain ba ya yi waje yana sanya wayarsa a cikin pocket ɗin sa.
Al-hussain kuma ya bi bayansa da kallo yanajin babu daɗi gaba ɗaya, da haka ya ɗau wayarsa da kiran Merry ya shigo.
"Hello Ango Ango." ta faɗa tana dariya.
"Waye Ango? Al-hussain yana wanka." Da sauri kuma a ɗan rikice ta ce.
"Ah...Ah Al-hassan Wasa nake dama, uhmm tambayarsa zan yi, in ya fito ya kira."
"Dakata ke! Me yasa kika kirasa da Ango?." Ya haɗe fuska amma kuma yana murmushi.
"Al-hassan dama ina kiransa da Angon Marwa, kuma ai very soon hakan za ta faru." ta faɗa tana ƙoƙarin kare kanta.
"Hmmmm kina yanzu haka?."
"Ina ɗaki kallo nake." yarda ta yi maganar yasa ya bushe da dariya yana cewa.
"Ƙanwar Ango ya da tsurewa, to Angon ne akan layi." take ta ƙatse kiran tana ƙwafa, ba za ta biye ma koma waye ba ya mai da ita mahaukaciya ba.
Al-hussain kuwa aje wayar ya yi dama baya son damune shi yasa ya mata haka, sai ta shafa mai lafiya.........
**************
Wani irin numfashi ta ja mai tsawo kafin ta furzar, da wani irin azama ta fizge kanta daga wajen wata soja, baya-baya ta yi ta zube a ƙasa tana ta tari, dan kuwa sojan nan shaƙeta ta yi, take idanunta suka koma launin ja, fuskar ta haɗe, ta ciza leɓanta sannan ta buga ƙasa da hannu ta, take ta yi wani juyi sai gata a tsaye, kamar ba ita ce yanzu aka lilkisata ba, take sojojin wajen suka hau mata tafi suna kiran sunanta.
Murmushin mugunta ta yi tana kallon ƙatuwar sojan da suke faɗa, wiyarta ta lanƙwasa dama da hagu suka yi ƴar ƙara, sannan ta ɗaga hannayenta ta yi miƙa, jikinta suka fara ƙas-ƙas-ƙas.
Sai dai sojoji Mazan da suke wajen, da sauri wasu suka rintae ido, wasu kuma suka ƙara ware mata ido suna kallon yarda Breast ɗin ta suka fito a cikin wannan rigar duk da yana da faɗi.
Najlah ba ta san ma suke yi ba, da haka ta nufa kan wannan sojan wacce take ma kallon kin shiga uku da Ni, yarda kasan Zakin da ya kwana huɗu bega abinci ba, sai yau ya iske akuya a ɗaure, haka Najlah ta yi mata, dukkanta kawai take, sannan ta ƙi ba Sojan daman ramawa, haka ta gama lallasata har ta kai ga ƙasa, take ta baje a sume.
Nan fa aka ƙara tabbatar da Najlah ta wuce sa'a, mace ce mai kamar Maza, Ƴar Sojo ƙanwar soja, jinin jikinta gudana yake da jinin soja.
Haka ta miƙa tsaye duk ta yi duƙun-duƙun da ƙasa, bakinta daya fashe ta goge da hannunta, sannan lokaci guda ta yi kan wani soja dake zaune, ta nufesa da gudu, gudun da wasu suka ga ta wuce makan walƙiya, tana zuwa ta kifa masa mari, Marin da be yi tsammani ba dan ya shagala da kallonta, take ya faɗi a kujerar yana mai dafe kuncinsa dan marin ya shigesa.
Yanzu kusan kowa tsoronta yake ji, General kawai take shakka, yarda take wuci yasa mutane suka san akwai wani abu da ya yi mata.
Ya Adam dake tsaye daga gefan wanda ta mara, ya ɗagosa yana cewa.
"Najlah uban me ya miki za ki mai wanna marin?." Ba ta kallesa ba, ta yi ƙwafa tana nuna mai dogon yatsanta manunuya.
"Wannan ya zama karo na farko dana ƙarshe da za ka dinga kallona kana lashe baki kamar wani maye......ba shi kaɗai ba duk wanda ya kuma min kallon da ban gamsu da shi ba, sai na ƙwaƙule ma mutum ido, na harbesa da bindiga." Ta faɗa tana ciro bindiga daga ajiyun wandonta.
Ai da sauri kowa ya fara silalewa, hatta Adam ya shafa kansa yana abokinsa suka bar wajen, yasan Najlah ba ta da hankali, tsaf za ta iya harbe mutum abin ta, tunda haka ta ruɗa Sir J da bindiga, ba ta harbesa ba amma haka ta dinga harba mai alburushi a daidai sai tin kansa, mutumin ranar sai da aka ƙara mai ruwa, ita kuma aka horeta, horon da a wajenta training.
Ji ta yi an dafa kafaɗarta hakan yasa cikin salon dambe ta juya tana kai farmaki, da sauri ta janye hannunta tana kallon Yayanmu dake sanye da kakinsa.
Miyau ta haɗiye saboda irin kallon da yake mata, hannu ya miƙa mata ta yi sauri aje mai bindigar tana marairaice fuska.
Yayanmu shine mutum na biyu da take shakka, sai dai wani lokacin ba ta shakkansa sam, kunninta ya ja guda ɗaya ta ɗan yi ƙara.
"Waya ce ki ɗauko min bindiga?." sai ta fara ƙyafƙayfta ido tana son fara kuka.
"Tambayarki nake yi? Sannna ke yanzu babu ranar da ba za ka yi dambe da wasu ba sai ka ce tinkiya." Ya sake ta yana dalla mata harara.
"Ni ce tinkiyar?." Ya ɗaga mata kai.
"Eh mana." Ya faɗa yana matse dariyar dake cinsa, taku biyu Najlah ta yi ta tsaya gan dashi, tana wani wuci kamar zakanya, ji take kaman ta kai mai hannu amma ba za ta iya ba, sai kuma take ta fashe da kukan taɓarawa tana faɗa wa jikinsa.
"Yayanmu dan kai ne zan barka, amma da wani ne ya yi gigin kirana da tinkiya sai na mai akuyanci, dan dukan mutuwa zan mai, Allah ya so kaine, kuma Yayana ne kai mai sunan Baban Mamie, shi yasa zan barka." Ta kai nan tana raba jikinsu.
"Ke ce baƙyaji sam, ko da ake jinjina Abbien mu, to wajen jarumta da gaskiya ne ba irin na ki ba, kullum rigima da neman faɗa, dan Allah Najlah ki kama kanki, gaba ɗaya kin riƙiɗe kin koma wata basamudiya, da kinfi ƙyau da jikin ki ɗan cas, amma yanzu jibi yarda kika murɗe." Ya kai nan yana ɗan dariya, a shaƙwaɓe ta ce.
"Ina siririya munce kamar kazan Mayu, yanzu kuma na ɗan yi jiki kana cewa kamar basamudiya, to ya zanyi." Ta kai nan har da buƙa ƙafa, ganin mutane suna ta kallonsu yasa ya ja hannunta suka bar haraban wajen, wajen da babu yalwan mutane suka zauna.
"Ki bar hawayen taɓarnan......na lura kin gama rainamu, da munyi miki magana sai kukan banza, amma anan ko yankaki ake yi ba za ki yi tari ba, idanunki sun gama bushewa, ba ki tsoron kowa, amma da munyi magana sai ki hau hawaye kina buga ƙafa, Allah ya shirye ki." baki ta tura gaba tana ɗaura kanta kan kafaɗarta, sai ya lumshe ido yana jin ƙaunar fitinanniyar kanwarsa.
"Ranar da za ki fara sanya kakin sojoji, ya za ki ji? Me za ki fara yi?." Ya tambaya idanunsa suna lumshe, sai dai take ya rintse ido jin yarda ta zabura tana miƙewa, yasan haukar za ta fara dan haka ya zuba mata ido yana kallonta.
"Idan na sanyasu, hmmm bayan an gama parrade, zan sa a sanya min waƙan sojoji, nasha rawa ina ɗaga bindiga sama tare da sakin alburusai dig-dig-dig-dig-DIGGH" ta kai nan tana nuni da hannunta tare da sai ta sa tana faɗa tana ɗan tsalle.
Kai ya dafe yana girgiza kai.
"Yayanmu kayan za su yi min ƙyau kuwa?." sai ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa.
"Za su yi miki sosai ƙanwata, zo na faɗa miki wani abu." Sai ta dawo ta zauna gefansa sannan ya fara magana a tausashe.
"Aikin soja aiki ne da ake yi da zuciya, aiki ne da mutum ke sadaukar da kansa domin ƙasar sa, aikin al'umma ne kuma yana san kishi da jarumta. Ina so ki zama kema wacce za'a yi alfahari da ita, domin na ga kina da kishi ƙasar ki."
"Yayanmu karka damu, burina kenan, zama babban jarwiya a ƙasar nan." Sai ya dungurar mata kai.
"Jarwiya dan kauda mugayen ƙusoshin ƙasar nan." ta jinjina mai kai cike da ƙarin gwiwa.
"Bara na je na wanke duk na yi dauɗa."
"Tom bye." ta haka ta ɗaga mai kai tana tafiya tana ɗan tsalle-tsalle, da ido ya bita, can ya ga ta tsaya ta kaima wani soja dukan wasa, ai kuwa ta bigesa a kafaɗa da haka ya bita ta ko ci ƙafa tana gudu, kai ya girgiza.
"Allah ya shirya." ya faɗa yana tashi...............
**************
Sai da ya kammala komai sannan ya nufa gidan su Marwa, tun a hanya zuciyarsa take ta bugawa, haka dai ya ƙara sa bayan ya tsaya ya siya mata fruits, Al-hussain ya ce mai idan ya je yasa a yi mai sallama da ita, sannan ko ta kirasa ba za ta samesa ba duk za su kashe wayoyinsu.
A bakin get ɗin su ya yi parking da motar Al-hussain, sannan ya fita, jikinsa duk ya yi mai wani amma haka ya yi knocking.
Me gadi na buɗe wa ya gansa, nan fa ya washe baki kamar gonar audiga ya shiga gaishesa har ƙasa.
Al-hassan ya mai ƙyau yana jin soyayyar Al-hussain sosai, dan yasa yana da ƙyauta da mutumci.
Har ciki aka mai iso, da yake baƙon gidan ne, sai da me gadi ya rakasa har wajen da sukan zauna, zama ya yi shi kuma me gadi ya isar ma A'isha da saƙon ɓaƙon Marwa ya zo.
Marwa, gaba ɗaya duniyar yau ta yi musu zafi, haka suna kallo Abba ya tafi Kaduna, sai a yanzu suka gane yawan zuwa Kaduna ashe wajen karuwar sa yake zuwa, gana ɗaya basa jin daɗin yau, sannan wanda Basma ta ba aiki ya kira ya ce da ita number ba za'a iya bibiya ba, ya faɗa mata saboda ganin number a makarantar sojoji ake aiki da shi.
Hakan ya ƙara taimaka ma yanayinsu na rashin sakewa, abu da yafi ɓata musu rai shine har bayan magrib be dawo ba.
"Mtwwssss tuna wancan karuwar har ya sanya min ciwon kai, gobe Monday in naje aiki sai na duba kaina saboda yanayin da nake ji."
"Bassey nima hala na zo maybe jini na ya hau." cewan Marwa tana lumshe ido.
"Allah dai ya ƙyauta kawai." faɗin Fauza cikin alhini, kafin wata ta sake magana suka ji ana knocking a natse.
Babu wacce ta amsa sai da aka yi sau uku, sai Fauza ta ce.
"Yes, coming." A hankali aka buɗe ƙofar aka shigo, a gefe ta samu ta tsugunna tana cewa.
"Barkanku da hutawa."
"Uban wa kika ga yana hutawa anan?." Cewan Basma tana wani hura hanci.
Aisha ta sauri ta ƙara sunkuyar da kai tana jin babu daɗi, Basma duk ta fi zafi a cikinsu.
"Hajiya ki ya ƙuri, dama ana sallama da Hajiya Marwa ne."
"Je ki ina zuwa."
"To Hajiya a fito lafiya." da haka ta yi waje.
Marwa ta miƙe, vail ɗin kanta ta yafa sannan ta ɗau wayarta tana nufan waje.
Hasken fitilu ya haska ko ina, da haka ta hangosa zaune, take Zuciyarta ta buga, sai ta lumshe ido tana jin wani yanayi, haka ta ɗaga ƙafarta ta fara takawa har zuwa wajen.
Da sallama ta isa wajen tana murmushi dan kar ya gane halin da take ciki.
Murmushi ya sakar mata wanda ba ta san lokacin da ta zauna daɓas ba, dan kuwa murmushin gani ta yi ya gilma da wani irin haske.
"Wassalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh." ya faɗa yana jan jikinsa ta yarda suka bar space a tsakaninsu.
Mamakine ya kama Marwa, dan kuwa Al-hussain be saba haka ba, bashi da burin ganin wani sashi na jikinsa ya goga nata, sannan ta mance rabon da su yi sallama ma juna haka, duk haɗuwarsu da kalaman soyayya suke fatawa ko yace ta yi Hugging na sa, muryansa ne ta dawo da ita duniyar zahiri.
"Meke damunki?." ya faɗa yana kallon ƙafarsa, dan kuwa tun kallo ɗaya da ya yi mata ya fahimci tana da damuwa, kuma ta yi kuka sannan ta motsa mai zuciya.
"Babu komai, ya hanya?."
"Karkimin ƙarya, waya saki kuka?." sai ta lumshe ido, zuciyarta tana ta mata wasiwasin ba Al-hussain bane, amma tana son ta tabbarar.
"Matsala muka samu da Abba shine kawai." Sai ya ɗaga mata kai yana lumshe ido, shuru suka yi dukkansu har na tsawon lokaci, kafin Marwa ta ce.
"Me yasa Al-hussain ya katse wayarsa? Kuma ina yaje da ya turo ka?." da mamaki ya juya ya kalleta, sai ta ɗaga mai kai.
"Kai Al-hassan ba Al-hussain ba." Murmushi ya yi mai ƙyau.
"Me yasa kika ce haka My Love." Ya faɗa kamar yadda Al-hussain yake faɗa.
Shuru ta yi sannan ta ƙyallesa da ƙyau.
"Hmmmm komai naku iri ɗaya ne amma kuma da banbanci a cikin idanuna, kai Al-hassan ne, idan ka koma ka ce mai ya kunna wayarsa na kunna nawa." da haka ta yi ƙoƙarin miƙewa sai dai aka yi rashin sa'a ta taka wani dutse mai santsi hakan yasa ta yi baya-baya za ta faɗi, cikin azama da sauri Al-hassan ya tareta ta faɗa jikinsa, take sanyin nan ya fara ratsa duk wani sassa dake cikin jikinsu, haske ya bayya a cikin idanunsu sannan zuciyoyinsu suka tsaya da aiki na wuce gadi.............✍️ END.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*
*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚
1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. MATAR YAYANMU Sa'adatu Ta Batulu. 7. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_