PAGE 2️⃣4
by @prettys01
> Da haka ta yi ƙoƙarin miƙewa sai dai aka yi rashin sa'a ta taka wani dutse mai santsi hakan yasa ta yi baya-baya za ta faɗi, cikin azama da sauri Al-hassan ya tareta ta faɗa jikinsa, take sanyin nan ya fara ratsa duk wani sassa dake cikin jikinsu, haske ya bayya a cikin idanunsu sannan zuciyoyinsu suka tsaya da aiki na wuce gadi.............
_________________Second ɗaya, second biyu, har zuwa second talatin suna a haka, kafin Allah ya sa suka dawo cikin hayyacinsu, da sauri kowa ya fara raba jikinsa dana ɗan uwansa, Marwa gaba ɗaya ta ruɗe, sai ta koma ta zauna, shima zaman ya yi yana lumshe ido, a haka suka shafe mintoci, sai ajiyan zuciyar da suke fita lokacin ɗaya.
"Ka..... Kayaƙuri." Ta faɗa tana jin irin ƙamshin turaren Al-hussain yana tashi a jikinsa.
"Ba komai, amma ki dinga kulawa, ga wannan zan tafi." Ya faɗa a natse yana miƙa mata ledar baƙi, amsa ta yi ba tare da ta bari hannunsu sun haɗu waje ɗaya ba.
"Na gode." sai ya yi murmushi.
"Zan iya miki wani tambaya guda ɗaya tak?." sai ta ɗaga mai ka tana karantar yanayinsa, wannan ya fi komai a natse, wancan kuwa hmmmm.
"Ta ya kika gane Ni ba saurayinki bane? Na yi mamaki sosai, dan har yarda yake miki magana haka na yi miki?." Murmushi mai sanyi ta yi tana jin daddaɗan iskan wajen haɗida turarensa suka sanya mata jin yanayin na musamman.
Juyawa ta yi da ƙyau ta kallesa, sannan ta ce.
"Allah ya halicce ku sak, sak ɗin da za ku iya rika mutane, kuna da kama wanda na jima banga tweens da shi ba, komai fa komai naku, sai dai duk yarda kukayi kama, dole ta banbancin ra'ayi, zuciya, text da kuma ƙwaƙwalwa ya zama da banbanci. Duba nan wanne ya fi ƙyau a ciki." Ta faɗa tana nuna mai wani hoton wasu motoci masu numfashi da suke tsaye guda biyar, ɗaya ƙirar Mercedes Benz white, ɗaya Rolls-Royce black, sai sport red, ba ƙarya duk sun haɗu fiye da misali.
"Chooce your fav?." Sai ya yi murmushi.
"Na tsakiyar." murmushi ta yi.
"Al-hussain ya zaɓa Roll-Royce, while kai ka zaɓa sport, to wannan shine test, sannan har a abinci kuna da banbanci na sani, sai abu babba wanda a cikin idanunka nake gani, My Love kuma be da shi, daɗin daɗawa wannan sanyin da nake ji a jikinka....." sai ta lumshe ido, shi kuwa ya kauda kansa gefe.
"Shike nan zan shiga ciki nima, na gode a sauka lafiya." Sai suka miƙe a tare, jerawa suka farayi babu wanda ya sake magana a cikinsu, a dai-dai lokacin aka buɗe get sannan motar Abba ta kutso cikin gidan.
Take Marwa ta haɗe fuska, ta kauda kanta.
"Abba ne ya dawo?." Ta ji ya faɗa.
"Eh."
"Bara mu gaisa da shi." da haka be jirata ba ya yi wajen parking, a daidai nan Abba ya buɗe mota yana waya, ganin Saurayin Marwa yasa ya yi murmushi yana fita daga motar.
Har ƙasa Al-hassan ya tsugunna yana gaida Abba, Abba ya ɗagosa suka gaisa a tsaye cikin mutumtawa da karamci, Abba shi kansa sai da ya ga sauyi amma be ce komai ba.
Marwa ba ta ƙaraso ba, dan haka Abba ya yafitota da hannu, sai ta ƙara so tana tura baki da haɗe fuska.
"Sannu da dawowa." Ta faɗa tana kauda kanta.
Abba murmushi ya yi sannan ya riƙe hannun Marwa, sai ya riƙo na Al-hassan, take ya ɗaura na Al-hassan akan na Marwa.
A tare suka lumshe ido jin wannan sanyi, sai dai kalaman Abba yasa suka natsu suna kallonsa.
"Al-hussain, na riga na baka Marwa, dan Allah tun daga yanzu ka dinga mata faɗa, wallahi suna cazamin kai sosai, be kamata da girman nan nasu ba na dinga jin babu daɗi akan abin da suke yi, na yaba da natsuwarsa kuma gashi kodayaushe kuna tare, dan Allah a dinga mata tuni d hadisai Manzon Allah." da sauri Al-hassan ya ce.
" Sallallahu alaihi Wasallama, insha Allahu Abba zan ƙoƙarta, na gode, na gode da karamci." da haka ya jinjina kai sannan ya musu sallama ya wuce.
Kallon juna suka yi kafin ya ce.
"Mu dena barin iyayen mu suna fushi da mu akan abin da be taka kara ya karya ba, dan Allah ku kiyaye, dan su ne hasken rayuwarmu."
"Hmmm insha Allahu."
"Yauwa Allah ya miki albarka." dariya ta ɗan yi jin abin da yace.
"To ameen." da haka ta rakasa har ya hau mota, sannan ta koma ciki, ai take ta sauya mood zuwa na ɓacin rai, ta nufa ciki da sauri.
Al-hassan kuwa ya jima kafin ya kunna motar ya fara tafiya yana jin kewar Marwa na danne mai zuciya, direct gida ya nufa, bayan ya yi parking sai ya kaɗa fita, murmushinta, da haɗe fuskarta na ɗazu ya tuna, ya so ya furta mata kalma ɗaya amma ya kasa saboda tuna matsayin wacece a wajensa, sai dai a yanzu ya samu daman furtawa.
"Marwa kina da ƙyau sosai." Sai ya lumshe ido, a natse kuma ya buɗe, bayan motar ya kalla, nan ya ci karo da tarkacen Al-hussain, kai kawai ya girgiza.
"Har cikin motar sai ka zuba wa'inna tarkacen, kai matarsa za ta sha fama." Take zuciyarsa ya motsa tunawa da wacce za ta zama matarsa *Marwa.* ..............
**************** Abba duniyar yau ta mai suger har da madara, dan kuwa tun da rana ya yi Flight ya je ganin gimbiyarsa, yaje kuma sunga juna, sun sha hiran soyayya, inda Najlah ta dinga narke mai har sai da ya kasa haƙuri ya tambayeta.
"Wai Ni kam ana koya muku shaƙwaɓa ne? Kullum naki hawa yake Masoyiya, ina tsoron kar kendir ɗin ya gama narkewa hutan sama be mutu ba." Ya faɗa lokacin da yake watsa da yatsun hannun Najlah.
Najlah kuwa an samu waje, ita kanta tambayar kanta take a ina ta ƙware da zazzafan soyayya, amma tuna ta ƙware da kallon finafinan soyayya, yasa tasan a can ta iya, na tama ya fi nasu.
Baki ta tura gaba tana marairaice fuska, sannan cikin wannan muryan na ta mai da rikita Abba ta ce.
"Uhm to ni......ba ce ma na yi kawai ga fitar dani daga Barack ba, ko na 30mnt ne, muje shan Ice-cream." Take ya yi murmushin mugunta sannan ya rage murya yana cewa.
"Babu in da zamu je, na tawo miki da Ice-cream mai ɗumi kamar wanda jiya kika buƙata." ai take ta zaro ido tana ɗan ja baya.
Shi kuma ya yi sauri matse fararen yatsunta.
"Ah Abba wasa nake maka baaaaaa."
"Ai baki isa ba, dakwansa na miki kuma sai kin sha." Ya faɗa yana son janyota, ai take ta fizge kanta tana miƙewa tsaye.
"Abba General zai iya shigowa office ɗin nan at anytime."
"Ina ruwana, kawo miki abinda kika buƙata na yi." Da haka shima ya miƙe tsaye, ai take Najlah ta fara baya-baya, sai gudun wasa, nan fa Abba ya aje shekaraunsa ya dawo shekarun Najlah suka fara ƴar bi, sai zillemai take, haka suka dinga bi har ta kan desk, Suka hargitsa office ɗin.
"Ke wai Soja ko, bara na kamaki za ki sani." Ya faɗa yana ƙara binta da niyya riƙe ta, ta zille tana mai ƙwalo.
"Hehehehe Abba, idan har ka kamani Ni kuma zan sha." tana faɗin haka tana ƙara gudu, take suka tsaya cak dan ganin General, ko lokacin da ya shigo ma ba su sani ba.
General tsaye yake ya zuba musu ido, kallon office ɗin ya yi, sannan ya sake kallon Abba dake tsaye kusa da Najlah dan gab yake da kamata.
A hankali ya sake kallon Najlah, take ta ƙame tana sara mai.
"Na baku minti biyar office ɗina ya dawo yarda yake, hmmmm." Da haka ya juya ya fita.
"Ke share kawai, zo musha soyayyar mu." Ido ta zaro mai.
"Wallahi baƙin mugune General, yanzu zai sanya Ni iyo cikin ruwan taɓo ko a sani shiga rami." Dariya ya ɗan yi.
"Yayan na wa shine mugu?."
"Ai gaskiya na faɗa." da haka ta juya za ta fara takawa, sai dai Abba ya dawo da ita baya da sauri, juyota ya yi suka fuskanci juna, suka ƙura ma junansu ido kafin ya ce.
"Kullum ƙara ƙyau kike, ji nake kaman na gudu dake, gashi haka kike wayo kowa na kallon jikinki." Ya faɗa idanunsa cikin idanunsa da suke maka da sexy one, ga zara-zaran gashin ido masu tsayi da suke a tsaye.
"Baby nima na ƙosa na mallaka wannan zankaɗeɗan saurayin."
"Bazawari dai." murmushi suka yi dukkansu, rage murya ya yi sosai kaman mai raɗa.
"Ina sonki, ina sonki Babyna, Allah ya mallaka min ke, Ni kuma duk burin da kike so zan taimaka miki wajen cimma wa." kumatunsa ta ɗan ja kamar wani yaro ta ce.
"Nima ina son....." magarta ta ƙafe dan jin tafin da General ke musu.
Da sauri Abba ya ɗan ja baya, iya kuma ta juya da sauri tana ƙamewa.
General ya dawo ɗaukan abu ya iskesu a haka, tafi ya ci gaba da yi sannan ya ƙarasa ciki.
"Wato office ɗina shine wajen soyayya, kuna tsaye suna ma juna kalaman da suka sanya ku jin a wata duniyar kuke, sannan kuka yi nisan kiwo.....to daga yau na katse soyayya a Barack, karka sake zuwa zance Nan, ke kuma...."
"Yes sir." ta faɗa tana ƙyafƙyafta ido.
"Waje." Da sauri ta bi umarninsa ta fice.
Take Abba ya haɗe fuska yana kiranta.
"Baby! Baby ki dawo!! Baby." lumshe ido ya yi yana buɗe wa, sai ya sauke akan General dake mai kallon tuhuma.
"Me yasa za ka koreta irin haka? Salan ta yi kuka."
"Mubarak yaushe ka koma haka ban sani ba, oh allah."
"Yaya, please ka kira min ita." take General ya dalla mai harara.
Ai sai da Abba ya yi da gaske tukun General ya kira Najlah suka yi sallama, sannan ya ce da Abba.
"Ina da buri akan Najlah, dan Allah karka gurɓata mata tunani da soyayya."
"Yaya dukka za ta iya, ina da tabbacin haka, sannan ko wani irin buri kake da shi akanta, zan tsaya mata duk wiyarsa."
"Hmmm Mubarak auren Soja ba wani armashi, dan kuwa rayuwarta na Barack sannan ga yawan transfer daga nan zuwa nan, ba lalle ka samu kalawa 💯 ba." a lokacin murmushi ya yi.
"Yaya karka damu, Ni kawai so nake na ga na rayu da ita, ina so na ba ta kulawa sosai, ko da Ni bansamu kulawarta ba dan nasan tana aikin kula da ɗunbin al'umma ne." Murmushi suka yi, da haka suka sauya hira, yamma na yi ya dawo Abuja ta flight.
Babu kowa a parlourn Dan haka be zauna ba ya haura sama ya shiga part ɗin sa, wanka ya yi sannan ya ɗauro alwala, jin an fara kiran sallah yasa ya sauko da niyar fita.
Sai suka haɗu da Marwa, hanya ta bashi ya fice yana mata murmushi, ita kuma ta maimakon ta wuce part ɗin su sai ta nufa na Abba bayan ta aje ledar da Al-hassan ya ba ta a parlour.
Tana shiga parlourn Abba ta gansa clean kamar yarda masu aiki suka gyara, direct ta nufa bedroom ɗin sa, wanda ta mance rabon da su shiga wajen.
Tana shiga ta hangi wayarsa dake kan mirrow, sai wata jakka da ya shigo da ita.
Hannunta har rawa yake ta ɗauki wayar, ta rubuta *Najlah* take wayar ya buɗe.
"Shegiya tsinanna." Ta faɗa tana fara duba cikin wayar, sai dai duk iya bincikenta ba ta iya samun komai ba, babu a whatsApp, babu call logs, haka babu pics na wata, tsaki ta ja, kamar za ta aje wayar sai kuwa hannunta suka latsa wajen sms.
Gabanta ya faɗi, ta dafe ƙirji tana kallon saƙon dake sama na *01IMH* da sauri ta latsa saƙon da aka buɗe amma ba'a yi reply ba.
Abinda ke ƙasa kawai ta buɗe tana jin fargaban abin da za ta karanta.
(Babyna ina fatan ka koma gida lafiya, ka miƙa min gaisuwa wajen Yarana, kaga wasan da muka yi ɗazu sai da na buge a ƙafa yanzu yana min zafi, arouund 12pm zan kunna wayana karka yi barci ka barni kaji.)
Marwa ta karanta kaman sau biyar, sannan ta aje wayar tana maimaita.
"Wasa........Wasa......wani wasa Abba yake yi da wata? Innalillah." Ta faɗa tana fita ta bar part ɗin gaba ɗaya.
Ko da ta shiga part ɗin su, zama ta yi kan sopa tana tunanin menene abin yi, da sauri kuma ta miƙe ta shiga bedroom.
"Gobe zan shigo asibitin shike nan, okay." Cewan Basma tana kashe wayarta sannan ta aje gefe guda.
Marwa na isa kusa da ita ta ce.
"Ƙarfe sha-biyun dare za ta kunna wayarta, amma me yasa take haka? Ko ba ta gaskiya ne?." cikin ƙarin bayani Basma ta ce.
"Akan wa kike magana?."
"Karuwar Abba, yanzu na fito daga part ɗin sa, na duba wayarsa, kinga saƙonnin da take mai na rashin ɗa'a, hmmmm."
"Da gaske an jima za ta kunna wayarta?."
"Eh haka ta turo mai, har da cewa wai ya gaishe mata da yaranta." Basma ta yi dariya tana cewa.
"Muna amsa gaisuwa da ƙyau da ƙyau, za mu kira muma mu gaisa." da haka suka ɗau alwashin kiran number Najlah ƙarfe 12pm.
**************** Zaune yake a mota yana duba wayarsa, ganin lokacin be wani ja ba, yasa ya lumshe ido yana jin ya kauda babban abun da ke gabansa.
Sanye yake da suit black Riga da wando, yayi wani masifaffen ƙyau na bugawa a jarida, dan kuwa kayan sun ƙarbesa, sauti wayarsa ya fara dan haka ya ɗauka, sai dai ba wannan wayar ba ce, ɗayan wayar ne dake pocket ɗin sa, ɗauka ya yi yana duba wanda ke kiransa da wannan layin.
Bayan ya ɗauka aka yi magana da wata irin murya mai cika kunne.
"Sir, komai ya yi dai-dai, wayarka kawai muke jira sai dai shuru gashi lokacin na tafiya kuma akwai aiki mai yawan gaske." Leɓansa ya ɗan ciza.
"Zan kira ku." Ya faɗa yana katse kiran, take kuma ya katse wayar yana lumshe ido sannan ya buɗe, sai ya yi murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban.
Merry ce ta buɗe motar ta shiga tana cin snack.
"Muje Al-hussain." Da Haka ya kunna motar suka ɗau hanyar gida.
"Biki ya yi albarka, na za ci ko na 1h za je hotel da Amar....." hararar da ya watsa mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar tana fiskewa.
"Haƙuri za ta yi na ɗan lokaci."
"Hmmm ango kasha ƙyau, anya muka koma gida a haka Al-hassan ba zai tuhume ka ba." Sai ya lasa leɓansa kafin ya ce.
"Karki damu nasan me zance mai." Sai ta ɗaga mai kai tana duba wayarta.
"Yaushe za ka fara aiki?." be kalleta ya ce.
"Tuntuni nake da aikin yi, sannan a yau ma an ƙaramin matsayi, matsayi mafi girma na wajen aikin." da mamaki ta kallesa.
"Bangane kana da aiki ba?."
"Eh, kallonku kawai nake yi, amma da aikinsa."
"Uhmm." Ta faɗa tana mai da hankalinta kan wayarta, dan tasan wasa yake mata, mutumin da kullum yana gida, sannan duk abinda yake buƙata daga al-jiwun Al-hassan yake fita.
Murmushi ya yi yana shareta shima, ba yason damuwa gaba ɗaya, so yake ya samu ya kwanta ya yi barci ko ƙwaƙwalwarsa za ta huta...
*********
Abba ko da ya dawo be lura an shiga part ɗin sa ba, Dan haka harkokin gabansa ya ci gaba da yi, 12:10pm ya ɗau wayarsa ya kira number Najlah, sai dai tana waya, da haka ya tura mata saƙo.
"Idan kin gama ki kirani." da haka ya ci gaba da aikin da yake a system.
Abinda be sani ba shine, 12:00pm daidai Basma ta kira number Najlah, wacce kunna wayar na ta kenan, suna can ɓangarensu suna rikici kamar za su cirota ta cikin wayar su kasheta.
Su uku suke zaune a can carpet sun sanya wayar Basma a tsakiya suna kallon yarda take ringing Amma ba'a ɗauka ba, tun sha-biyu saura suke kira a kashe sai yanzu da sha-biyun ya haɗe shine wayar ke ringing.
Har sun fidda rai za'a ɗauka sai aka ɗauka, ba su yi gaggawan fara magana ba, dan haka suka jiyo muryar Najlah tana magana a hankali kamar mai raɗa.
"Baby Mubeee na ya na ga sabuwar number?."
"Ƴaƴan Mubeee ne." cewan Marwa tana jin ranta yana zafi.
"Ku bari da safe ma yi waya yanzu muryan Babu nake son ji."
"Malama in za ki saki muryanki ki sake, ki dena shaƙe mana dan ba hula ne akan mu ba." ta kai nan harda ƙwafa dan kuwa a tunaninta shaƙe murya Najlah take yi..............✍️
*********************
> "Malama in za ki saki muryanki ki sake, ki dena shaƙe mana dan ba hula ne akan mu ba." ta kai nan harda ƙwafa dan kuwa a tunaninta shaƙe murya Najlah take yi..................✍️
Numfashi Najlah ta ja mai ƙara ta sauke a natse sannan ta ce.
"Bazan kasance ɗaya daga cikin matan Uban da suke hayaniya da yaran kishiya ba, never mu dinga faɗa a waya, ku bari na shigo gidan, daga lokacin za su fahimci komai."
"Mtwwwssss kuma dena tunanin auren Abba, kima dena dan kuwa ɗan mu kasheki abu mai sauƙi." cewan Marwa, sai Fauza da yanzu ta fara magana a cikinsu.
"Ina tausaya miki Najlah, ki kama kanki, ki rabu da Abba ta hanya mai sauƙi, sannan ki koma wajen Bokan ki ta rushe aikin nan dan daga ke har shi mun tanadar muku huƙuba mai tsanani." hatta Marwa da Basma sai da suka sake kallon Fauza saboda yarda ta yi maganar, Najlah cikin shaƙiyanci tace.
"Banga laifin ku ba, dole kuyi kishin Abba sosai dan Guyen ya haɗu wallahi."
"Ke wai wata irin ƴar duniya ce, yanzu tsakani da Allah Abba ne Gaye? Ki ji tsoron Allah, ki rabu dashi ki zauna lafiya." faɗin Marwa hawaye na zuba daga idanunta, sai dai jin kalaman Basma ba ƙaramin ruɗata ta yi ba.
"Da gaske Ina son Abba kuma za ki auresa?."
"Ƙwarai da gaske, aure kaman anyi nema."
"Shike nan, ki ci gaba da shirin auren, ki yi party ki yi walima, daga yanzu daga Ni har su babu mai sake damuwa da aurenki." mamakine ya kamasu amma sun kasa magana saboda Basma ta musu alaman suyi shuru, dariya Najlah ta yi harda ƙuɗa.
"Allah dai ya muku albarka yaran nan, ya baku majaje na gari kaman My Mubee." da Haka ta kashe kiran.
Da sauri Marwa ta fara magana tana dafa Basma.
"Kina hauka ne za ki ce da ita haka? Kinsan me kika furta." murmushin mugunta Basma ta yi, ta miƙe tsaye ta yi taku uku sannan ta ce.
"Daga gani aikin asiri ke cin Abba, ko mu so ko muƙi sai ya aureta, dan haka mu bari ya yi auren, mu bari ta tako ƙafarta cikin gidan nan, daga nan wasan zai soma." ta kai nan tana lumshe ido.
"Kina nufin mu bari wata ta shigo gidan nan?."
"Eh Fauza, sai dai ba za ta ko yi kwana ɗaya ba, zamu yi mata wulaƙancin da ko kare aka bawa namarta ba zai ci ba."
"Hmmmm shike nan, wannan shawarar ta yi, amma ya zamu nuna ma Abba?." Sai Basma ta juya ta kalla Marwa.
"Ai shi ba za mu nuna mai muna so ba haka ba zamu nuna mai bamu so ba, daga yanzu mu sanya mai ido, daga gaisuwa sai gaisuwa, kunsan dai yarda ya kamata." jinjina kai suka yi kowa yana sakar zuci.
Da haka kowacce ta nema waje ta kwanta tana tuna irin mugunta da za ta yi ma Najlah dake gigin auren Abba.
★ ★ ★
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a cikin gidan Abba, idan sun haɗu da shi iya gaisuwa ne kawai, daga nan suke kama kansu, shi kuwa tun yana jin babu daɗi har shima ya fita sabagarsa, balle ma hankalinsa gaba ɗaya ya koma kan Najlah, sannan babu abin da ya fi mai daɗi irin zaman da danginsa suka yi dana Najlah, a kuma ranar aka tabbatar mai da an bashi Najlah, da yake magana ake ta manyan mutane a ranar suka biya kuɗin komai aka sanya lokaci nan da wata ɗaya da sati ɗaya masu zuwa, tsakanin Abba da Najlah sun rasa gane wanda ya fi wani murna da wannan labarin, haka suka gode ma Allah tare da ci gaba da rainon soyayyarsu cikin jin daɗi da nishaɗi.
Abba ne tsaye a parlour yana riƙe da ƙaramar jakkan baya, kallon agogo ya yi wanda ya nuna mai 10:30am na safe, ƙaramin tsaki ya ja, dan kuwa kusan minti 10 da kiran Marwa akan su fito zai yi magana da su, ta amsa amma gashi har yanzu ba su sauko ba.
Badan ya danne zuciyarsa ba da ya wuce, suna mai abubuwa wanda yake sharewa, dan baya son ya musu faɗa. Gaba ɗaya sun gujesa, ko dariyarsu ya manta ranar da ya gani, hatta idan suna cin abinci ya je wajen sai su tashi su bar mai wajen, haka dai suke rayuwa duk babu daɗi bare armashi.
Jin sautin takalma ana saukowa daga stairs, yasa ya zauna kan kujera yana mai da idanunsa ka tv dake aiki.
Be kallesu ba saboda hirar da ake yi a tv ya ɗau mai hankali.
Mata biyu ne ƴan jarida suke zaune suna hira akan kidnapers da suka addaba mutane a wannan, ɗaya daga cikin matan ce ta ke magana cikin ɓacin rai.
"Barrister Maryam, honestly a wannan ƙasar we really need more fear and control. There's no security at all, especially in villages da suke nesa da jami'an tsaro. Wallahi nothing scares me more than these kidnappers yanzu… they kidnap people, and instead of asking for ransom, they just kill them." sai ta gefanta ta cije laɓɓanta tana girgiza kai.
"Exactly, that's the reality. Kusan every two weeks ana samun new case, amma before you even understand what's going on, an rufe file ɗin. Right in front of me aka kawo report na wani mutum da aka sace masa yara huɗu… but before ka ce anything, the case was closed. From that moment na fahimci cewa, this thing has powerful people behind it… because sometimes, our own leaders are the real problem of this country."
Abbaa ya lumshe ido yana mai addu'ar Allah ya ƙara tsare su da gaba ɗaya mutane daga sharrin mugayen ƙasa.
Idanunsa ya buɗe yana mai da wa kan yaransa da suka zazzauna a ƙasa suna saurarensa.
Murmushi ya yi koma menene yana son yaransa, so wanda be da iyaka.
"Ina kwananku, tunda kun saka gaishe ni." da sauri suka haɗa baki suna gaidashi, be amsa ba sai mai shuru da ya yi sannan ya ce.
"Yanzu kuna ƙyautawa abin da kike yi? Ace saboda ina neman aure kuka janye jikinku daga Ni, yanzu hakan yana muku daɗi?." su kansu sunyi missing Abba, suna fatan su dawo yarda suke amma hakan abu ne mai matukar wahala. Sai ya sake magana bayan ɗan lokacin da suka ɗauka ba
"Kunyi shuru ina magana."
"Abba yarda kasan mu haka muke har yanzu."
"Basma wai idan na ki yi rashin kunya a rayuwarki ba bakijin daɗi? Magana ma idan kina yi sai ki yi ta fizge-fizge, hmmm kun ƙyauta, dama faɗa muku zan yi Kaduna zani wajen Auntyn ku, zan yi kwana biyu jibi zan dawo." da haka ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin fara tafiya sai Marwa ta buɗe baki cikin rawar murya ta ce.
"Wa....Wa.....wajenta za ka je , shine harda faɗa mana kwana biyu za ka je mata.........Abba me yasa kake ƙoƙarin rushe duk soyayyar da muke maka? Me yasa kake son ganin mun hawaye? Me yasa baka da buri sai na ganin ta karya alƙawarin da ka yi ma Mom.....ka sani Allah ba zai barka ba." sai g hawaye sun cika mata ido, Basma ta ce.
"Kin manta aikin asiri ne ke cinsa, Ni kome Abba ke yi yanzu ina mai uzuri wallahi." Da haka ta miƙe tana latsa wayarta ta barshi a tsaye.
Marwa ma tashi ta yi ta hau sama, murmushi Abba ya yi sannan ya ci gaba da tafiya, cak ya tsaya jin Fauza na cewa.
"A dawo lafiya, Allah ya tsare hanya." kafin ya amsa itama ta haure sama harda gudu-gudu.
"Ikon Allah, yaran nan kaman masu almatsutsai." da haka ya fice ya shiga mota Driver ya ja sai airport..
*★YANZU ZA MU FARA LABARI, YANZU LABARIN ZAI ƊAU SABON SALO MAI CIKE DA HARGITSI, KOMAI YANZU ZAI FARA, DA WASA MUKE YANZU NE LABARIN ZAI ƊAU SE TI MAI BAN MAMAKI.★*.
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, wannan rana ta kasance ranar da dubbanin ƴaƴa irin su Najlah ke farin ciki da shi, rana ce wacce ba zasu taɓa mantawa ba a tarihin rayuwarsu, domin kuwa ta zo musu da samun nasara da kuma ci gaba na rayuwa.
A safiyar da iska ke kaɗawa cikin sanyi mai daɗi sakamakon ruwan saman da aka kwana ana yi, filin horon sojoji ya cika da jama'a cikin tsari mai ban sha'awa. Tutoci na ƙasa suna shawagi a sama, suna sheƙi da hasken rana da ta fara fitowa a hankali. Tutuna (flags) suna kaɗawa a natse, suna ƙara wa wurin ƙyau na musamman.
Sabbin sojojin da suka kammala horo suna tsaye cikin cikakken tsari. Uniform ɗinsu mai tsabta gasu ya haska su ba kaɗan ba, kowanne daga cikin sojojin suna kallon gaba da cikakken ladabi sannan suna cike da kishin ƙasarsu.
A gaban filin, manyan hafsoshin sojoji sun zauna cikin layi a kan dandalin karramawa. A tsakiyar su, babban kwamandan sojoji yana zaune cikin nutsuwa, amma idanunsa suna nuna kan sojojin da suke tsaye cikin tsari.
Ba'a ɓata lokaci ba aka fara umarni fara abinda ya tara kowa.
"Parade… attention!"
A take, dukkan sojoji suka miƙe tsaf kamar ba su numfashi, Shiru ya mamaye ko'ina, sai kuma wani umarni ya biyo baya.
"Present arms!"
Nan take suka ɗaga bindigoginsu cikin tsari mai cike da horo da ladabi. Komai ya kasance cikin daidaito kamar an zana shi, Ganguna suka fara kaɗawa da ƙarfi, suna ƙara wa wurin wani yanayi na musamman.
Babban kwamandan ya miƙe wato General, ya kalli sabbin sojojin da suka tsaya a gabansa, ya buɗe baki cike da alfahiri ya ce.
"Daga yau ba ku ƙara zama 'recruits' ba. Yau kun zama sojojin ƙasa." ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ci gaba.
"Daga yau, rayuwarku ba taku kaɗai ba ce. Kun zama na ƙasa. Duk abin da kuka yi, zai shafi al'umma baki ɗaya."
Take Najlah dake layin gaba ta ɗan runtse idanu, yana jin nauyin wannan magana a zuciyarsa. Tana cike da alfahari, amma a lokaci guda akwai tsoro na abin da gaba zai kawo, domin daga wannan lokacin rayuwarta za ta sauya, cike da sadaukar da ranta wa ƙasar ta.
Take aka sake jin umarni mai ƙarfi daga speaker mai amsakuwa a wajen
"Passing out parade… commence march!"
Nan take aka fara tafiya cikin tsari, Sojoji suna tafiya daidai, ƙafafunsu suna bugun ƙasa a lokaci ɗaya, suna wucewa gaban manyan hafsoshi.
Kowa na wurin yana kallon cikin wajen cike sha'awa sanan duk wanda ke wajen dole ya ji wani abu na taɓa mai zuciya, wannan wakar ƙasar, wannan taken, wannan jama'ar, ga flags take zuƙata suka motsa da soyayyar ƙasarmu *NIGERIA 🇳🇬* .
Najlah tana tsaye cikin shigar sojoji mai kyau da tsari, irin uniform ɗin da ke nuna ƙwarewa ta zama soja, tana sanye da riga da wando na soja mai launin olive ko dark green, an dinke su da ƙyau suna zaune daidai a jikinta ba tare da wata tangarda ba. A kafadunta akwai alamar soja (rank insignia) mai sauƙi da ke nuna matsayinta. A kirjinta akwai ƙananan badge ɗin aiki, duk suna da tsafta da tsari. Ta saka takalmin soja (combat boots) baki mai sheƙi, wanda ya ƙara mata kyan tsayuwa da kwanciyar hankali. Hannunta ɗaya yana a kwance cikin natsuwa, ɗaya kuma tana riƙe da hula na soja (beret).
Fuskarta tana nuna jarumta da kwanciyar hankali amma cikin Idanuwanta hawayen farin ciki sun cika tab. Gashinta an gyara shi cikin tsari mai ƙyau, Bayanin haɗuwarta ɓata lokaci ne dan kuwa ta cinye shigar ɗari bisa ɗari.
A sansanin horon soja gaba ɗaya, sun cire wacce ta fi kowace jarumta a shekaran nan ita ce Hafsah Abdullahi, wadda ake kira Najlah, ta yi fice sosai a cikin horo saboda ƙwazonta da jarumta a cikin batch ɗinsu.
An karrama ta a gaban sojoji, sannan aka ba ta sabon matsayi. A take aka tura ta zuwa Abuja Barracks domin fara aikin soja na gaskiya, bayan an yi mata laƙani da *Zakanya.*
Haka a ka dinga karrama sojojin wajen, sannan aka tashi taro, nan fa iyayen yara suka cika da alfaharin ganin ƴaƴansu a wannan muƙamin, ciki harda Mamie wacce har kuka ta yi saboda murna.
Gefe guda suka tsaya suka sanya Najlah kowa na tayata murna, murmushi kawai take musu, amma hankalinta baya kansu, sai waige-waige take ta yi ko za ta ci karo da Abba, sanyin idanunta.
"Zakanya." da sauri ta juya dan jin muryan Abba cikin nishaɗi, take ta ruga da gudu sai jikin Abba, ba ta damu da idanun da suke kanta ba, ta ɗane jikinsa tana mai jin soyayyarsa.
Mamie ta girgiza kai tana juyawa, Ya Adam kuwa dariya ya yi yana cewa.
"Yarinyar nan sai mun sanyata a addu'a sosai, ita ko kunya ba ta ji, ke dalla sake ɗan mutane karki kashe sa." sai Najlah ta sauka tana juyawa ta dalla mai harara.
Abba kuwa ya sosa kai yana mata raɗa.
"Innalillahi Mamie tana wajen nan ai." dariya ta ɗan yi.
"To menene, ai Angona na runguma ba wani ba." sai ya jinjina kai yana jan mata hanci.
" Congratulations My Sweet, Ina miki fatan alheri da kuma......." da sauri ya ja baya yana juyawa dan kuwa Najlah sumbatar kumatunsa ta yi.
Da sauri ta koma gabansa.
"Meke damunki? A gaban Mamie ɗin?." sai ta ɗaga mai kai.
"Uhmmm to Ni yau uhmmmmm." ta fara buga ƙafa a ƙasa tana son fara taɓara.
Kafin ya ce wani abu sai ga wani soja ya zo wajen, sara mata ya yi yana cewa.
"General na nemanki." Ta ɗaga mai kai ya wuce, sai ta lumshe ido.
"Yau na so na mori soyayyata a filin nan amma ina zuwa, ka shirya dan kuwa wasa zamu yi sosai a filin nan harda ƴar tsare." ya mata kallon kin sha wani abu ne, ta mai da mai da kallon ƙwarai na sha da haka suka jera suna hira gwanin sha'awa.................✍️. END.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*
*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚
1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. MATAR YAYANMU Sa'adatu Ta Batulu. 7. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_