BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣5

by @prettys01

>"Yau na so na mori soyayyata a filin nan amma ina zuwa, ka shirya dan kuwa wasa zamu yi sosai a filin nan harda ƴar tsare." ya mata kallon kin sha wani abu ne, ta mai da mai da kallon ƙwarai na sha da haka suka jera suna hira gwanin sha'awa.................

Ko da suka isa bakin office ɗin sai Abba ya tsaya ita kuma ta gyara zaman hularta ta nufa ciki, da sauri kuma ta dawo ta rungumesa sannan ta shige, ɗan dariya ya yi har da jin kunya Allah ya zo babu kowa a wajen.

Najlah kuwa tana shiga ta sara musu tare da ƙamewa ƙam, manyan sojoji uku ne, suna zazzaune, murmushi suka yi mata sannan suka ba ta wani daman zama, sai ta ƙi ta ƙara ƙamewa sosai, ganin haka suka shiga koro mata bayanan aikin na ta, daga ƙarshe General ya ce.

"Saboda ke ce shi yasa na roƙan miki alfarma, nan da wata ɗaya da sati biyu za ki fara aiki, kuma bikinki nan da 3weeks ne, ai 2weeks zai isheki hutu, abu na gaba an ɗauke miki kwana a Barack, amma dole 6:30am kina can, dan haka kiyi ma wanda za ki aura magana ko kusa da Barack ya aje ki in Kuma kusa ne shike nan."

"Yes Sir, thank you." sai Wani soja wanda a yanzu ƙarƙashinsa za ta koma da aiki wato Barkono ya buɗe baki cikin dakakkiyar muryansa ya ce.

"Zan baki horon aikin Military Intelligence, sanoda na lura kinda basira sosai, tare zamu yi aiki, sai Ni banson wasa, bana harka da duk wani mai wasa, dan haka ki natsu ki kama kanki, Division 3 Abuja aka yi posting na ki, ki mai da hankali."

"Thank You Sir." da haka suka mata alama da ta wuce, ta sake sara musu sannan ta juya a haka ta fara tafiya a dai ƙamen.

Tana fita ta furzar da numfashin da take ta riƙe wa, kallon Abba dake tsaye ta yi sai ta kashe mai ido guda.

"Baby wai amarcin sati biyu kawai zamu ci uhmmm haba dan Allah." ta faɗa tana tura bakinta gaba.

"Ba komai ai, amm Yaya ya ce dole mu koma kusa da barrack, duk da ba wani nisa da wajen, amma zan duba na gani." suka fara tafiya a tare.

"A'a ka bar maganar kawai, tun asuba zan shirya kafin 6:30am ai zan kai ko?."

"Sosai ma kuwa Amarsu." sai ta rufe fuska tana maƙe murya.

"Uhmm ina jin kunya." dariya suka kwashe da shi.

"Wai kunyar wa zanji? Ko bikin ku duk wanda ya ce Amarya, zan ce *Yes*, in aka ɗaura auren Ni zan sanar ma jama'ar gida ina guɗa, sannan babu faɗar da zanyi ma kuka kawai bansan yin nisa da Mamie ne." ta kai tana jin babu daɗi a ranta.

Murmushi ya yi yana riƙe hannunta.

"A'a Ni kam zan so kiyi kuka ranar dan baki kukan abu mai muhimmanci sai na wasa, da zarar ban kira ki lokacin kira ba sai kin min kuka, akan komai kuka, amma serious things baƙya zubar da hawaye, idanunnan a bushe suke, gasu da matuƙar ƙawa, ina son kallon cikinsu sosai." ya kai nan yana sake kallon cikin idanunta masu ƙyau da ɗaukan hankali.

"Me kika gani a cikin idanuna?." sai ta lumshe ido ta buɗe a cikin na ta ta ce.

"Baby ƙwansa." Ai da gudu ta nufa su Mamie, shi kuma ya yi murmushi yana bin bayanta, yana mugun son Najlah da halayenta komai dai yana so a wajenta.

Daga inda take ta ke mai ƙwalo tana zaro mai ido, Mamie na wajen shi yasa be ƙara sa ba, dan haka ya motsa leɓansa yana furta wasu kalamai wanda Najlah a furtawan farko na gane me yace.

"Kina dallo harshe kamar mai cin mutane, masu cin mutane ai Mayune." ta furta da ƙarfi bayan ta gane me ya ce, ai hularta ta cire tana ba Mamie, sannan ta nufesa da gudu kaman soja ya ga ɓarawo, yana ganin ta biyosa ta ya yi wata kwana yana neman hanyar guduwa.

Kaman walƙiya haka ta tare sa, sai ya zauna kan wani kujera yana mai da numfashi, ita kuma ta tsaya gabansa tana kallonsa.

A hankali kuma ta tsugunna daidai saitin zuciyarsa, ta ɗaura hannunta a kai, cikin raɗa ta ce.

"In akan kane na zama Maiy." sai ya rufe mata baki da hannunsa, ciwonsa ta ɗan yi ya cire da sauri yana yarfe hannu.

"Kai Baby da zafi." Murmushi ta yi ta zauna gefansa.

"Sorry, amma ƙwanda ka saba, dan ina son naga Ina cizon mutane, haka zan ta cizon fatarka kamar na samu......"

"Dan Allah ki bar wannan maganar, ke duk salon mugunta kin iya ai, kalla nan in da kika mintsileni last zuwa da nayi, sai da ya yi taɓo." Ya faɗa yana nuna mata hannunsa fari ƙal mai ɗauke da ɓaƙaƙen gashi sun kwanta, a gefe guda da wani madaidaici taɓo nan da ya yi baƙi.

"Wayyo sorry, mu gani." Da sauri ya mai da hannunsa baya dan dariyar mugunta ya ga tana yi............

************* *Fadar shugaban ƙasa (conference room)*

Misalin ƙarfe 5:30pm jami'ai ne ta ko'ina a haraban wajen da cikin office ɗin da yafi kowanne daɗi. Cikin office ɗin kuwa, jami'an tsaro da manyan gwamnati masu faɗa a ji a ƙasar nan, duk suna zazzaune fuskar kowa cike da damuwa.

Wani farin Dattijo dake zaune ya jingina kan kaɗan da kujerar da yake zaune, idanunsa na yawo kan kowa, a kallo ɗaya za ka cikar kamala da haiba a tare da shi, a saman bangon da yake an yi wani rubutu da manyan harufa launin gold, an rubuta *THE PRESIDENT MUHAMMAD BABANGIDA SHAMAKI* rubutun yana ɗaukan ido sosai.

Lumshe ido Dattijo ya yi sannan ya yi alama da farin hannunsa mai ɗauke da agogo mai tsaɗan gaske.

Take Sufeto Janar na 'Yan Sanda (IGP) ya miƙe da file a hannu sannan ya gaida kowa na waje kafin ya ce.

"Ranka ya daɗe…... da alama matsalar tsaro na ƙara ta'azzara, sannan masu garkuwa da mutane sun wuce yadda muke zato…..... kuma gaskiya, ba su jin tsoron doka, talakawa suna cikin firgici a kowani Lokaci, dan Allah a duba wannan al'amarin." da haka ya zauna sai Gwamna Bala ya daki tebur da ƙarfi ya ce.

"Koma ƙara yana ta'azzara? Mutane suna mutuwa kullum! A jihata, mutane ba sa iya fita tafiya lafiya! Saboda kullum cikin kai farmaki ake."

Ministan Tsaro ya yi saurin cewa.

"Muna iya bakin ƙoƙarinmu, ranka ya daɗe. Mun tura sojoji wurare da dama........" Gwamna Bala ya katse shi da zafi.

"Idan kuna iya bakin ƙoƙari, me yasa babu canji?!"

Nan take ɗakin ya ɗau zafi. IGP ya kalli Ministan cikin takaici. "Gaskiya akwai matsalar haɗin kai tsakanin hukumomi… that is part of the problem." Daraktan DSS ya yi murmushi mai sanyi. "Ko kuma… akwai wanda ke ba su bayanai a cikinmu." nan take shiru ya mamaye ɗakin, kowa ya fara kallon juna cikin zargi. Shugaban ƙasa ya ɗan yi gyaran murya ya ce.

"Me kake nufi da hakan?" Daraktan DSS ya gyara zama yana ci gaba da cewa.

"Ranka ya daɗe… waɗannan masu laifi kamar sun san duk wani mataki da za mu ɗauka kafin mu ɗauka. This is not ordinary." Ministan Harkokin Cikin Gida ya miƙe cikin fushi.

"Kana nufin kana zargin mu ne?! Wannan ba dai-dai bane!"

IGP ya ce cikin nutsuwa.

"Babu wanda ya fi ƙarfin zargi." Take ɗakin ya kaure da husuma kowa na manna ma ɗan uwansa laifi yana kare kansa.

Shugaban ƙasa ya buga tebur a hankali, amma sautin ya isa kunnuwan kowa. "Ya isa!" ya furta a natse take kowa ya yi tsit, ya kalli su ɗaya bayan ɗaya.

"Dole sai mun haɗa kai komai zai tafi daidai, wannan aikin al'umma muke yi, amma akwai masu son zuciya a cikin mu, ga shi zaɓe na danno kai, abokan hamayya suna yaɗa duk ƙanƙantar matsaloli suna yaɗawa...... Nasan me zanyi, kuje na sallama kowa." da haka ya lumshe ido yana jin sun ci gaba da hayaniya amma suna fita ɗaya bayan ɗaya, sai da ya tabbatar babu wanda ya yi saura sannan ya buɗe idanunsa ya ɗauki wayarsa dake kan table, wata number ya kira, bugu uku aka ɗauka, cikin wata irin murya wanda ya tabbatar da an haɗa da na'ura aka ce.

"Yallabai mun jima muna jiran wannan kiran." sai President ya yi murmushi.

"Lokaci ya yi, kai da tawagar za ku fara aiki."

"Shike nan Yallaɓai daga yau tawagar *BLACK SHADOW* za ta fara aiki domin gano su waye ƙungiyar *BLUE PENTER.* tare da duk wa'inda suke ciki."

"Good luck." da haka ya kashe kiran yana mai yi musu fatan sa'a, *BLACK SHADOW* tawagace da ya yi ma training dan ceto ƙasar sa idan har jami'ai sun kasa, leɓansa ya ɗan ciza sai ya sauke ajiyan zuciya yana aje wayar dake hannunsa.......

***********

Murmushi ne kwance kan fuskar wani matashin saurayi dake zaune gaban wani ƙaton mutum dake ɗauke da carbi masu yawa a wiyarsa, a kallo ɗaya za ka fahimci bokane domin ga layoyi a jikinsa, ɓakine sosai, mai jajayen haƙora.

Hannunsa yasa ya ja layi akan trayn dake gabansa ɗauke da ƙasa, layi biyu ya zana sannan ya ɗauki carbi ɗaya dake hannunsa ya saki kan ƙasan, take ya buɗe baki ya fara magana da muryansa mai amo.

"Zaɓa guda da hannun hagu." da sauri matsayin ya ɗauki guda yana shu'umin murmushi.

Bokan ya amsa carbin sannan ya lumshe ido yana wasu sulkulle, ya jima a haka kafin ya hargitsa ƙasan gabansa ya rubutu harfofi guda biyar a jikin tray ɗin.

"Za ta sanya kaya launin ɗorawa, ita za ta fara magana, a lokacin za ka cire glass ɗin idanunka ka kalla cikin idanunta, daga nan shike nan." da haka ya buɗe tafin hannunsa sai ga wani ƙullin ɓakin abu, matashin ya amsa jikinsa har rawa yake, tare da bokan suka kalla sunan dake jikin tray ɗin, a tare suka furta *BASMA.* ...............✍️

> Salo ya sauya, labarin ya buɗe sabon shafi 🥰

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚

1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. MATAR YAYANMU Sa'adatu Ta Batulu. 7. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_