BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣6

by @prettys01

> "Za ta sanya kaya launin ɗorawa, ita za ta fara magana, a lokacin za ka cire glass ɗin idanunka ka kalla cikin idanunta, daga nan shike nan." da haka ya buɗe tafin hannunsa sai ga wani ƙullin ɓakin abu, matashin ya amsa jikinsa har rawa yake, tare da bokan suka kalla sunan dake jikin tray ɗin, a tare suka furta *BASMA.* ...............

"Eh Basma ita ce sa'arka, idan har ka juya mata tunani to tabbas duniyarka za ta yi ƙyau." cewan Boka yana gyara zaman carbin da ke ƙafarsa, matashin nan kuwa murmushin kawai yake saki, sannan ya fiddo kuɗi masu yawan gaske ya aje ma boka, tare da rarrafawa har ya fita daga ƙaramin ɗakin boka.

Ashe dai matashin ba laifi yana ƙyau daidai misali, duk da kuwa hasken da yake da shine ya haskaka halittarsa, amma da be da hasken da idan ka mai kallo ɗaya ba za ka sake mai na biyu ba. A ƙalla ba zai wuci 28yrs ba, yana tsayi amma be da ƙiba sam, tafiya yake cikin ƙumbo yanayi yana murmushi, a ƙalla ya yaudara ƴam mata sama da 20, kuma duk ƴaƴan masu kuɗi, babu wacce yake aure sai dai yana ruɗa musu tunani da ƙwallin boka, da haka yake tara maƙuɗan kudaɗe a wajen matan daga ƙarshe ya ci amarsu, wasu boka ya haukatar da su wasu kuma ya lalata su ya bar garin.

Duk kuɗin da yake tarawa ajewa yake yi yana ma kansa babban tanadi, baya lissafin komai sai na samun kuɗi ba tare da shan wahala ba, shi yasa ya yarda bokonsa fiye da kowa a duniya......

***********

"Merry wai wani irin aiki ne Al-hussain ya samu? Gaba ɗaya ya sauya, kullum hankalinsa yana kan system, gashi ba ya son kowa yaga menene a ciki, abin haushin ma cemin yake tafiya zai yi, gaba ɗaya bangane masa ba." ya kai nan yana jin zuciyarsa yana mai zafi. Merry dake kallon Al-hassan ta sauke gauron numfashi ta ce.

"Bansan komai ba dangane da halin da ya fara kwana biyu, ko jiya na mai magana dana samesa a room ɗinku, sai ce min yayi wai Al-hassan ne, bayan lokacin a parlour na barka, gaba ɗaya Ni na fita sabgansa a ƴan watannin nan." ta kai nan da iya gaskiyarta.

"Hmmmm shike nan, koma office ɗin ki, ki ci gaba da aiki, zuwa anjima zamu leƙa asibitin da ake ginawa dan ganin ya aikin ke tafiya." sai ta miƙe tana ɗaga kanta sannan ta fice, shi kuma ya lumshe ido yana tunanin ɗan uwan nasa.

******* Zaune yake kan wani kujera mai numfashi, kai daga ganin ɗakin kasan na wani ƙusan ƙasar nan ne, dan kuwa komai dake babban parlourn ya haɗu har ya gaji da haɗuwa, kuma komai na Parlourn gold ne sai wal-wal komai yake, dan daga kujera, fantin ɗakin, labulaye, da komai gold colour ne.

Hannunsa dake ɗauke da safar hannu baki ya ɗau wayarsa dake ringing a kan table, a kunninsa ya kai ta cikin wayar ya jiyo muryan babban masu tsaronsa yana magana cikin girmamawa.

"Sir gaba ɗaya sun taru, za su iya shigowa ciki?."

"Uhmmm." ya faɗa yana cire wayar daga kunninsa.

Yana zaune aka buɗo ƙofa aka shigo be kallesu ba har suka shigo suka zazzauna akan kujera, sun mai sallama ya amsa da kai yana binsu da ido ɗaya bayan ɗayan, mayan mazaje masu kalama su uku suna zauna biyu musulamai ɗaya kuma chirsten.

Glass ɗin dake idanunsa ya cire sannan ya buɗe baki cike da isa ya ce.

"Opposition Party (abokan hamayya) *People's Reform Movement (PRM)* Jam'iyyar mai siffa biyu _The Voice of the Masses_ hmmmmmm me ke faruwa ne the Leader of PRM?." ya kai yana kallon wanda ke zaune a tsakiyarsu.

Babban rigar dake jikinsa ya gyara sannan ya Senator Ibrahim Lawal Tumɓa mai magana da harshen jama'a ya ce.

"A jiya an tattauna akan ƙungiyarka *BLUE PENTER* daga majiya mai ƙarfi akan shirin da wancan mutumin ke yi wato shugaban ƙasa MUHAMMAD BABANGIDA SHAMAKI, ya ce da kasan zai ɗau mataki akan ƙungiyar, bana so ƙwaɓar mu ta yi ruwa, so nake mutane su guji jami'yar mai ci a yanzu *NUJP* (National Unity & Justice Party). " Sai ya goge fuskarsa da hanki duk da babu gumin a fuskar. Babu wanda ya sake magana na tsawon lokaci kafin David John ya ce.

"Muna so komai ya ƙaru, sace mutane, kisa, cin hanci da rashawa, walahar abinci da komai da komai, saboda mutane su yi tir da jam'iyar *National Unity & Justice Party (NUJP)* ." da haka sauke ajiyan zuciya suna kallon matsayin saurayin da ke zaune yana kallonsu, wannan mutum da ko su kansu basu san ya fuskarsa take ba dan kuwa rigan fuska yake sawa na fata a duk lokacin da za su zauna da shi, duk kuwa da shine ogansu gaba ɗaya, babban tantiri da ya gagara Nigeria, mutum guda da yake kashe-kashe kuma ya kwana lafiya, sunansa kawai aka sani amma babu mai taƙamaiman bayaninsa, shi kalma ɗaya ne tak be yarda da shi ba wato *Yarda.* Be yarda da kowa haka yake yaruwa, kusan shekara biyu kenan suna aiki da shi amma basu san waye ba, sun san bayan su yana da wasu manya-manyan a ƙasar nan da suke bayansa, babu laifin da bayayi, sunan sa kawai ke yaro a zagayen shu'umin azzalumai wato *BLACK DRAGON, shugaban ƙungiyar BLUE PENTER.*

Murmushi Senator Ibrahim Lawal Tumɓa ya yi dan jin BLACK DRAGON yana magana da muryan tsofaffi wanda da shi yake musu magana dan yana sanya wani abu a maƙogaronsa da haka ka zaɓa muryan da kake so, idan har ka yi magana to babu mai gane muryanka.

"Ku kwantar da hankalin ku, ku koma gida ku kwanta, ku ƙaddara ku za ku yi nasara a zaɓe mai zuwa, dan kuwa lokacin da zan gama hargitsa ko ina, ku zaku fito wa al'umma a matsayin inuwa, ku basu kuɗi ku basu abinci, ku nuna ku bakuson mulkin, daga lokacin komai zai sauya."

"Black Dragon wannan shawarar ya yi, kuma kuna farin ciki da zama mabiya bayanka, ka yi komai yarda kake so, mu kuma muna nan dan ba ka kariya." cewan Senator Tumɓa.

"Za ku iya tafiya." Sai suka miƙe suka mai sallama sannan suka fita.

Suna fita ya miƙe tsaye, sannan ya yi sannan cikin isa da tunƙawo, yana tafiya kamar ba zai taka ƙasa ba, a natse ya shiga wani bedroom Wanda ya komai na ciki Ja da baƙi ne, sannan anyi zanen Dragon Mai feshin huta a jikin bangon ɗakin.

A gaban mirrow ya tsaya sannan ya fara cire boturan rigarsa, take ya zare rigar yana daga jikinsa da yake a murɗe, ko ina nasa a cike ba ƙarya, fatan bayansa kuwa an mai zanen Dragon launin ja da baƙi.

Fatar da ya sanya a fuskarsa take ya sanya hannu ya cire yana mai sakin mask ɗin a ƙasa. Hutar ɗakin ne ya ɗauke dan haka ban iya gane fuskarsa ba saboda duhu, sai dai na hangi tarin gashin gemunsa da Lulu eyes ɗin sa masu sheƙi da annuri, a natse cikin muryar ɗazu ya ce.

"Ina da ƙarfin ikon da babu wanda zai iya shiga gabana a duniyar nan, BLACK DRAGON mai feshin huta, hmmm hmmmmm bani da burin da ya wuce sai ganin na rushe gaba ɗaya dokar ƙasar nan na hana kowa sukuni, na fitina kowa." da haka ya juya ya shiga toilet da wannan tafiyar na sa mai tsayawa a rai................

*************

Breakfast suke yi su uku a Dining room, suna cin abinci suna hira.

"Aikin asibiti babu daɗi Marwa, jiya aka kawo mana wata mata tana naƙuɗa, da yake muna bin doctors suna ganin komai, hmmmm Allah Allah ne, kinga yarda matan ke nishi wajen haihuwa kuwa." Ta kai nan cike da alhini tana ture Plate ɗin gabanta.

"Hmmmm shiyasa duk wacce ba ta ma iyayenta biyayya ba to wallahi jahila ce."

"Hakane Marwa, amma in kika ce iyaye harda maza kenan, kuma sam bama yi ba Abba biyayya expecally akan auren da yake shirin yi." Marwa da Basma suka kalla Fauza suna murmushi, sai Basma ta ce.

"Wake haihuwa?."

"Mace mana."

"Yauwa Fauza, to mahaifiyar muna mata biyayya kuma ita ta haifemu ba Abba ba."

"Hakane, kuma ai bamu sake shiga harkan Abba ba, kina dai kallo duk sati sai yaje Kaduna wajenta, namu ido kawai." cewan Marwa sai suka yi murmushi.

"Wani abun ma sai an kawota gidan nan daga nan Abba zai fahimci shurun mu." da haka suka sauya hira suna ci gaba da cin abinci hankali kwance.

Jallabiya ce jikinsa fara ƙal, mai dogon hannu, murmushi ne kwance a fuskarsa sakamakon hango yaransa zaune suna hira, yana son ya ga suna cikin wannan farin cikin hakan yana sa ya ji duniyar yana mai daɗi, tun daga lokacin da suka fahimci auren zai yi basu sake yi mai maganar ba, da har kulasa suka dena sai kuma suka sauko daga fushin.

Yana isa wajen ya zauna yana fiddo wani ƙaramin envelope daga ajiyunsa, kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya.

A tare suka gaishesa suna sauya yanayin su gaba ɗaya, be amsa ba sai can ya ce.

"Bansan me yasa kuke gudu na ba, tun last 2week nake so mu yi magana da ku amma bana samun ku lokaci guda, sannan ga aikin office da ya yake riƙeni, yanzu dai kuna da lokaci ko?."

"Abba asibiti za ni kuma na yi latti." Sai ya kalla Basma sannan ya yi murmushi.

"Shike nan dama ba wani magana bane, ga I.V nan ku ba wa'inda za ku gayyata." ya tura envelope ɗin zuwa kusa da Marwa dake gefansa.

"Menene I.V kuma?." Ta tambaya tana jin kamar ba ta taɓa sanin kalmar ba.

"Invitation card, na aurena.........ranar juma'a ne in Allah ya kaimu, dama maganar kenan a can Kaduna za'a yi bikin sai ku shirya zuwa jibi Wednesday ku tafi ko.. .........." ya lumshe ido jin Basma ta daki desk tana fizgan envelope ɗin ta fara buɗewa.

Take katika masu yawa fitowa ƙanana masu ƙyau da tsari, babu idan da idanunta suka fara sauka sai sunan da yafi kowanne girma.

" *Alhaji Mubarak Adam & Hafsat Abdullahi.......... what?." ta saki I.V ɗin tana ɗan ja baya tare da girgiza kai.

Marwa tuni idanunta sun kawo ruwa, ta ɗauki ɗaya ta duba date nan da kwana biyar ne bikin Abba.

"A....Abba auren za ka yi da gaske?." ta faɗa bakinta yana rawa.

Kai ya ɗaga yana miƙewa tsaye.

"Insha Allah, na tura ma kowacce 50k ta yi lalle da ƙyaran kai, anko kuma duk an yi muku suna Kaduna." Da yaka ya juya ya fara tafiya.

"Wallahi babu in da zani, kuma bansan kuɗin bana so, ka dai rantse sai ka sa munyi aljalin ƴar mutane ko, hmmm shike nan." ta ɗauki wayarta sannan ta haura sama da sauri.

Da ido ya bi Basma har ta ɓace masa, sai ya juya baya ya koma kusa da Fauza da ta rintse ido tana kuka.

A hankali ya rungumeta yana rarrashinta da kuma mamakin wannan halin na su, Marwa dai zaman kujera ya gagareta, a ƙasa ta zauna tana rero kuka.

Suna tsaye sai ga Basma ta fito da wani doguwar riga na material, Babu wani hayaniya a jikin rigar, ga launin ya haska ta dan Choculaty ce sosai, launin kayan kuwa ruwan ɗorawa ne sai ɗigon ja-ja, sai ta yafa gyale ja.

A fusace ta fice tana mako musu ƙofa.

Abba ya girgiza kai yana mai mata fatan dawowa lafiya, ci gaba da rarrashin su ya yi yana ta musu nasiha da faɗa amma cikin hikima.

Basma kuwa tana fita ta fara tafiya a zafafe, gaba ɗaya hankalinta ya yi nisa, ba ta lura da mai aikin dake tsugunne yana tattara dattin da ya tara.

Karo ta yi da shi, da sauri ta ja baya tana ƙare haɗe fuska, shi kuma ya miƙe da sauri yana ba ta haƙuri duk da ba shi ne da laifi ba, sai dai bai kai ƙarshen maganar ba ta wankesa da lafiyayyen mari sannan ta ja tsaki ta shiga motarta.

Da sauri matashin ya ja baya ganin tana ƙoƙarin bigesa, haka ta isa bakin get ta dinga zuba horn har mai gadin sai da ya ruɗe, cikin ikon ya buɗe yana kallon ta gangaro da motarta ta tsaya a daidai inda yake, glass ta zuge sannan ta ce.

"Kaci darajar farin gemun nan da wallahi na ci mutumcinka, kafin na dawo ka tattara kayanka ka bar gidan nan, na lura ka fara ruɗewa." da haka ta fice ko damar magana ba ta bashi da, haka ta figa mota da matsiyacin gudu.............✍️ END

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚

1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. MATAR YAYANMU Sa'adatu Ta Batulu. 7. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_