BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣ 7

by @prettys01

> "Kaci darajar farin gemun nan da wallahi na ci mutumcinka, kafin na dawo ka tattara kayanka ka bar gidan nan, na lura ka fara ruɗewa." da haka ta fice ko damar magana ba ta bashi da, haka ta figa mota da matsiyacin gudu............

A hanya sai da ta buga wata mota ta fasa mata glass ɗin baya, haka ta yi parking ta fita, macece mai wancan motar, ta hau tijara tana faɗa, gashi Basma kuɗin account ɗin ta wanda Abba ya tura musu ne wai na lalle da bikinsa, tsaki ta ja a lokacin sannan ta tura ma matan dukka kuɗi, ta koma mota ta nufa asibitin da take aiki yanzu *Mercy Care Hospital*, a asibitin kana aiki kuma kana dasa karatu dan suna da ɓangaren da suke koyar da dalubai, a hankali ta shiga cikin asibitin saboda akwai mutane masu shiga da fita, duk da kuwa a kallo ɗaya za ta san asibitin na masu kuɗi ne duba da yarda ginin ma yake da tsarin ciki.

Ta kashe motar sannan ta fita, a hankali take tafiya, take kuma zuciyarta ta fara bugawa ba gaira ba dalili, maimakon ta fara neman tsaki daga mutum ko aljanna daga wajen Ubangiji ma buwayi gagara kowa sai kawai ta ci gaba ta tafiya tana ɗan haɗe fuska.

Har ta wuce wani mutum dake zaune a kujera sai ta dawo baya da sauri tana kallon saurayin dake zaune ya ƙwama baƙin glass sannan ya shingiɗa a wajen.

"Assalamu Alaikum Bawan Allah." ta faɗa cikin sanyi. Shuru saurayin be motsa ba, sai ta ƙara taku uku tana ɗaukan wayarsa da ya faɗi a ƙasa.

"Ga wayarka ta faɗi." ta miƙa mai tana kallon yarda ya ɗan zabura daga kujerar.

Baya ta ɗan ja tana sake kallon jikinsa, tsofaffin kaya ne jikinsa duk sun yage sun koɗe, kana kallonsa ka ga zallar talauci, sai dai yana da haske sosai amma be da ƙyaun fuska.

Saurayin kuwa a cikin zuciyarsa ya yi hamdala yana zare glass ɗin dake idanunsa wanda ya yi kama da na makafi. Yana cire glass ɗin suka haɗa ido da shi, da sauri Basma ta yamutsa fuska tana aje mai wayar sannan ta yi ciki da sauri.

Saurayin kuwa ya yi wani irin murmushi harda dukkan kujerar, ya san an gama magana Basma ta dawo ƙarƙashin umarninsa, a yanzu za ta rasa meke mata daɗi, sannan za ta fara tausaya masa, ta janyosa jikinsa ta wadatasa da duk daɗin duniya, yasan daga yanzu babu maganar wanda za ta dinga ji sama da na sa. Murmushi ya kuma yi dan tarko ya kamata, kwanciya ya ƙyara yana lumshe ido, tare da aje ƙaramar wayarsa gefe yana hamma dama barci yaje ji take kuwa barci ya ɗauke sa.

Bassey ko da ta shiga cikin asibiti wajen da suke zama nan ta je, nurses biyu ne sai masu matakin karatunta su uku, sun girma nurse's amma ba su kai doctor's ba.

Tana zama ta lumshe ido tana karanto addu'ar da ta zo mata, sai dai idanunsa da murmushin sa sun tsaya mata a rai.

"Aunty Basma Doctor Mukhtar yana nemanki." sai ta ɗaga kai tana kallon wata Nurse da ta leƙo tana isar mata da saƙon.

"Okay." Ta faɗa tana miƙewa tare da ficewa ba tare da ta yi ma kowa wajen magana ba sabon duk sun yi faɗa da ita.

Office ɗin Doctor Mukhtar ta shiga kai tsaye ba tare da neman izini ba saboda tsakaninta da shi babu shamaki, soyayya suke yi da shi sosai kuma kowa ya sani a asibitin, Doctor Mukhtar dakakken mutum ne, kuma asibitin na mahaifin sane, kowa yana shakkarsa amma banda Basma, wacce a ranar da ta fara aiki ta ƙi gaishesa..

_Flash back._

A ƙalla sun kai mutane 20 a cikin wajen Doctors, nurse da ƴan team ɗin su, tattauanawa aka akan yarda aikin kowa zai gudana.

Bassey na zaune tana jin tsare-tsaren, a lokacin suka ji shigowar Doctor Mukhtar, sai kowa na wajen ya miƙe tsaye suna gaishe da shi cikin girmamawa.

Kafaɗarta ake dan duka akan ta tashi, sai ta yi banza da su, haka ta ci gaba da duba system ɗin ta, a hankali kuma ta ɗaga idanunta ta sauke kan wani saurayi dake sanye da manyan kaya yadin Wool (Ulu), Brown mai ƙyau da shining, sai agogon hannunsa Rolex Submariner, Babu hula akansa sai tarin gashinsa da ya kwanta sosai, tsaka-tsaki yake shi ba fari ba shi ba baƙi ba haka yake. Kallonsa ta yi cikin ido ta ce.

"Good morning." be amsa ba sai ma cema ya yi.

"Haka kika ga an gaishe da Ni?." rufe system ɗin gabanta ta yi ta ture gefe.

"Abbana ne kawai nake ma wannan ladabin dan haka ba zan iya maka ba, kuma ma kalleni dududu ka bani 5yrs, kawai sai na gaisheka da wannan respect ɗin." ta faɗa cikin tsantsan rashin kunya dan kuwa a sama ta zo ranar.

Take mutanen wajen suka fara mata faɗa suna nuna ba ta ƙyauta asibin sa ne kuma dole a mai biyayya.

"Ni Dalla karku dameni, ku koreni mana sai ne, na ce sai me, haba." Da haka ta tashi ta fice ta barsu baki buɗe.

Daga wannan lokacin ba su sake haɗuwa ba sai bayan kwana uku, nan ma ta nema ta bangajesa da ta zo wucewa, sai ya matsa mata yana murmushi.

Daga kuwa ya kamu da soyayyarta sosai, daga lokacin kuma duk lokacin da za su haɗu sai sunyi rigima, dan har sau biyu tana korar kanta sai kuma ta dawo, kullum cikin faɗa suke kafin ya koma soyayya, soyayyar da kowa ya sani na asibitin dan Doctor Mukhtar baya ɓoye-ɓoye, a gaban kowa yake nuna matsayin ta a wajensa, duk da kuwa ita zafi shi sanyi...

_Ci gaba._

Ƙofar ta rufe sannan ta nufa sopa dake office ɗin ta kwanta tana dafe kanta.

Tun da ta shigo yake kallonta, har ta kwanta, sannan ya cire farin glass ɗin idanunsa ya miƙe akan kujerar yana taku a natse.

Yau ƙananun kaya ne jikinsa wanda suka karɓi fatarsa sosai, a natse yake tafiya har zuwa gabanta, sai ya zauna kan Center table.

" What's wrong Dear?." shuru babu amsa, sai ya kai hannunsa ya taɓa goshinta, jin akwai ɗimu sai ya lumshe ido sannan ya buɗe.

"Meke damunki?." cikin sanyi-sanyi ta ce.

"Kaina......kaina kamar zai rabe biyu." da haka ta sake dungulewa waje guda tana dafe kanta.

Damuwa ne ya mamaye fuskarsa sosai, sannan ya sake kai hannu sai gyara mata vail ɗin ta da ya zame ƙasa, ai cikin sauri da masifar nan tafara magana a hankali.

"Karka taɓa Ni, dan na yi ma shuru harda taɓa min goshi karka sake na dai gaya maka Ya Mukhtar." Ta kai nan tana rufe idanunta.

Duk da yana cikin damuwa amma sai da ya yi murmushi, sannan ya miƙe ya sa waje da yake sagale fararen rigunar aikinsa, guda biyu ya ciro sannan ya dawo wajen da ta ke, ya zauna yana kallon yarda take sauke ajiyan zuciya.

"Fitinanniyar Abin ƙaunata, ina sonki duk da kin iya hayaniya da faɗa." ya faɗa a hankali sanan ya ɗauki wata waya dagensa ya kira wata number.

"Turomin Nurse biyu da kayan aiki harda gado zuwa office ɗina." Ya katse kiran bayan na cikin wayar ya amsa mai da To.

Ba'a ɗau lokaci ba ya ji an fara knocking sai ya bada umarnin a shigo, Nurse's biyu mata suka shigo tare da gadon da suka turo zuwa ciki, baki suka haɗa suka gaidashi ya amsa yana nuna musu inda zasu ake gadon.

"Ku mai da ita kai, sannan ga paper nan ina buƙatar komai a yanzu." Suka amsa paper sannan suka mai da Basma dake barci kan gado sannan suka fita.

Da kansa ya mata duk wani gwaje-gwaje, sannan ya sa mata drip, yana da surgery amma yasan ba zai iya ba saboda halin da take ciki hakan yasa ya umarci wani Doctor ya zama ready.

A ƙalla ya ɗau dogon lokaci yana kallon yarda ruwan ke shiga cikin hannunta, a lokaci guda kuma ya miƙe da sauri yana isa kusa da ita ganin ta zabura tana tashi daga kwance.

"Subuhanallah ki yi addu'a, meke damunki?" ya faɗa dan ganin kaman mugun mafarki ta yi.

Basma gumi kawai take dan kuwa mutumin ɗazu ta gani yana zaune kan kujera yana shan ruwa a cikin daji sosai, ita kuma kishi ya kamata sosai tana ta neman ruwa ba ta samu ba, cikin ikon Allah suka haɗu sai ta roƙesa ruwan, ba musu ya ba ta tasha yana murmushi, sai dai ruwan be kai cikinta ba ya dawo tare da amana jini, haka ta dinga amayar da jinin nan a ƙasa, shi kuma ya tsugunna yana latsa jinin dake zuba.

"Bassey." da sauri ta kalla Mukhtar dake tofa mata addu'a.

A lokaci guda kuma ta ji wani abu ya daki kanta, zabura ta yi ta fizge canular dake hannunta ta fara ƙoƙari tashi duk da tana jin jiri.

"Kina mawiyacin hali, ki kwanta ki huta, wai ina za ki ne?." turesa ta yi tana jan ƙafa.

Da sauri ya sha gabanta yana tare ƙofa.

"Babu inda za ki je, koma ki kwanta." wani irin kallo ta yi mai ne yasa tsugunna a wajen ya ɗauki gyalenta yafa mata ya yi sannan ya ba ta hanya yana cewa.

"Muje na mai da ke gida, ba zan bari kiyi Draving ba." ba ma tasan yana yi ba, direct haraban asibitin ta nufa.

Idanunta ba sa ganin kowa sai matashin dake zaune kan kujera yana latsa wayarsa, wajensa ta nufa harda gudu-gudu, tana isa ta rage tsayi tana ɗan haki.

Lokacin da Doctor Mukhtar ya iso, lokacin matashin ya ɗaga idanunsa ya kalla idanunta.

"Me yasa sai yanzu kike fito." ya faɗa da muryansa mai amo, amma a cikin kunnuwan Basma sai ta ji muryan yana da sanyi da daɗi.

Cikin ɗan rawar murya ta buɗe bakinta tana magana.

"Kayaƙuri kaina yake ciwo shine aka........" hannu ya ɗaga mata sai ta yi shuru.

"Basma waye wannan?." cewan Doctor Mukhtar yana ƙare mai kallo, ita kanta ba ta san waye shi ba dan haka ya ce.

"Me zance?." sai ya yi murmushi sannan ya ce.

"Ki ce masa masoyin kine Anas." Da sauri ta kalla Doctor Mukhtar.

"Masoyina ne Anas."

Doctor Mukhtar sam be yarda da saurayin dake zaune yana ƙare ma Basma kallo.

"Kai waye kai? Tashi ka fita, securities." Ya faɗa da ƙarfi yana kiran masu tsaron asibitin da suke sanye da uniform iri ɗaya, wasu da sanda wasu da bindiga.

Anas ya miƙe tsaye yana wani murmushi.

"Basma waye wannan?."

"Uhmm Oga nane shi." ta faɗa itama ta na miƙewa tsaye.

A lokacin securities ɗin suka iso wajen suna ƙoƙarin kamasa, da sauri Basma ta matsa gaban Doctor Mukhtar ta riƙe kwalar rigarsa.

"Ka gargaɗe su da kar wani ya yi gigin taɓa shi, dan wallahi idan wani abu ya sameshi zan ransa raina, sannan zan iya komai akansa." Da haka ta saki rigar tana kama hannun Anas suka nufa motarta, shiga suka yi ta kunna ta bar asibitin.

Doctor Mukhtar kuwa gaba ɗaya ji ya yi duniyar ta tsaya mai cak, wai macen da yake mugun so, yake ƙaunarta ita ce take ce mai wani ne ranta.

"Ya Allah." ya furta yana jin ƙafafaunsa suna mai nauyi, a haka ya dinga dagawa yana taka ƙasa, har dai ya shiga officer ɗin sa ya murza key sanan ya kwanta kan sopa yana maimaita kalaman Basma wa'inda suke cakan zuciyarsa sosai.

Basma kuwa bayan fita daga asibiti ta hau titi da ƙyau, a hankali ta saki kallon Anas.

"Fatan ranka be ɓaci ba, yanzu ina zamu je? Umarninka kawai nake jira." Sai ya yi murmushi yana juya kansa ya kalla taga, tabbas Basma ta yi daidai da shi, sannan a duk matan da ya yaudara babu mai ƙyau irinta, sai dai ba zai yi aure ba, wannan aƙidarsa sa ce.

"Tun safe nake zaune waje ɗaya ina jiranki Masoyiyata amma ba ki zo da wuri ba, yunwa nake ji sosai." ya kai nan yana lumshe ido.

"Wayyo sorry, me kake so? Me za ka ci?." Ta faɗa hankalinta yana kansa.

"Ki kula da driving ɗin dai."

"Karka damu, kace kana jin yunwa, me kake so? Ka faɗa min yanzun nan zan nemo maka shi."

"Koma menene kika ban da hannunki zan ci."

"To...To....to." take ta nema waje ta yi parking, sannan ta fita zuwa shagon dake wajen ko za ta samu wani abun ci, sai dai babu komai sai snacks, haka ta siyan mai Multin Dew mai sanyi guda ɗaya, Allah ya so tana da canji a jakkarta.

Awara ta hangi ana soyawa, da sauri ta isa wajen tana miƙa duba biyu.

"Ban awara." Yarinyar ta amsa kuɗin, sannan ta ce.

"Na ₦600 ne a nan dole sai na soya kasko biyu zuwa uku."

"No samin wannan ya isa." Da sauri ta zuje mata aleda tana ƙoƙarin mai da mata dubu ɗaya kafin ta haɗa ƴan canji ta bata.

"No ki barshi." Ta faɗa tana sauri-sauri, motar ta koma sai haki take yi, tana shiga ta mai murmushi tana cewa.

"Kana jin yunwa sosai, ka ci kaji ko zan samu natsuwa."

"Ki ban a baki." Ba musu ta buɗe ledar sai kuma ta tsaya.

"My hand is not clean."

"Ki ban a haka." sai ya ɗau guda ɗaya ta kai mai bakinsa, ya gutsira yana kallon cikin idanunta.

Tari ya hau yi, da sauri ta ture ledan gefe tana bubbuga mai kai tare da jera mai sannu.

Dama tarin iskanci ne, sai ya yi shuru sannan ta ci gaba da bashi awarar, suna gamawa ta ce.

"Ka ƙoshi?." Ya ɗaga mata kai.

"Yanzu ina zamu je?."

"Gidan ku." sai ta ɗaga mai kai tare da figan mota zuwa gidan su......

*******

Abba be bar Fauza da Marwa ba sai da ya lallashe su sosai, sannan suka ɗau I.V card ɗin duk da babu wanda za su ba, Fauza tana gida ba school dan haka part ɗin su ta koma ta kwanta bayan fitar Abba da Marwa.

Marwa 1:30pm ta dawo gida, a babban parlour ta zauna tana ɗaga kiran Al-hussain da ya shigo mata, murmushi tana zama kan kushin.

Zazzaƙan muryarsa mai daɗi ta yi mata amsakuwa cikin taushi.

"Baby Love idan na ce 2dys bana missing na ka nayi ƙarya, tunda ka fara aiki bana samun ganinka sai sau ɗaya a sati, shima baka jimawa, sannan waya ma sai lokaci zuwa lokaci, duk da kodayaushe nama saƙo kana reply, hmmm gashi ka saba min da kai sosai." Ta kai nan tana lumshe ido da kewar rayuwarsu ta baya.

"Sorry Babyna, yanzu haka ma ɗan dama na samu na kiraki daga ke zan kira Al-hassan mu gaisa shima."

"Hmmm ina kewanka Baby."

"Nima haka sosai Baby Marwa, I love you, please excuse me."

"Kashhhh uhmmmm Okay." Sai ya yi murmushi sannan ya katse kiran.

Tashi ta yi ta haura sama, ta tambayesa wani irin aiki yake yi, a lokacin ce ma ya yi aikin banki yake yi, ta so ya faɗa mata sunan bankin ko zuwa ita ta dinga yi ganinsa sai dai yaƙi faɗa mata. Sallama ta yi tana shiga bedroom ɗin su.........

*Al-hussain.* Wayar ya aje gefe guda yana kallon wata mace wacce ta kasance matarsa, murmushi ta yi mai shima ya mai da mata yana janyota jikinsa, be iya ɓoye-ɓoye ba a gabanta yake waya da Marwa, dan tasan ita ya aureta ne saboda Momy.

Magana take son yi duk da fuskarta fayau yake, sai ya yi saurin haɗe bakinsu waje ɗaya, ya jima yana kissing ba ta a hankali, kafin ya zare leɓansa daga bakinta yana rungumeta cike da ƙauna.

"I love You Gentle." Ta furta cikin taushi.

"I love You Pretty." sai ya tashi da sauri.

"Zan wuce, take care." Kai ta ɗaga mai sannan ya sanya rigarsa ya ɗau jakkarsa ya fice.

Macen da ke zaune ta lumshe ido tana jin soyayyar Gentle ɗin ta, ƙananan kaya ne jikinta masu bayyana tsiraci sosai, haka kanta yasha kitson attachment har baya.................

************

"Amarya! Amarya!! Amarya!!!." cewan Rukky tana shiga parlourn Mamie, sai ta tsaya cak tana riƙe ƙugu, ƙwafa ta yi sannan ta isa kujerar da Najlah ke kwance, tana kallon sama, fuskarta an shafa mata lalle da kurku da wasu abubuwan aka ƙwaɓa aka shafa mata, sai Cocumber daka mai yankan slize aka ɗaura mata su a ido, sannan kunninta ta maƙala earphone, tana jin karatun Alqur'ani cikin kira'ar Shaikh Muhammad Afif.

Hannu Rukky ta sanya tana cire Earphone ɗin tare da dungure kan Najlah.

"Amarya tun ɗazu nake nemanki, ashe kina nan kina hutawa, tashi Ustaz ya zo miki Allah ya sanya alheri, jiya da nake raba cinkam ya ji, ayya karki so kiga yarda ya koma, wallahi har aka tashi baya cikin natsuwarsa." Najlah ta tashi ta zauna tana cire Cocumber dake idanunta.

"Ayya, bara na wanke fuskarta." Da haka ta shiga toilet ɗin dake ɗakin, ba ta jima ba ta fito tana tsane ruwan dake fuskantar.

Rukky murmushi ta yi tana miƙewa tsaye.

"Yabo da godiya su ƙara tabbata ga Ubangijin talikai, wato Najlah Alhaji Mubarak ya yi mugun sa'a, mace iya mace, diri sun ƙara cika sun tumbatsa, hip ba magana, ga wani masifaffen ƙyau da dilkan nan ya ƙara miki, gaskiya Amaryar nan kin......" Da sauri Najlah ta daki kafaɗarta cikin waya tana murmushi, ita kanta ta ga sauyi sosai, dan hasken fatarta ya ninku akan na da.

"Ba dole na ƙara fresh ba, na dawo gida bana fita, can kuwa rana kaɗai ya ishe ka." Suka yi dariya suna fara takawa.

Gidan ya fara mutane duk da kuwa saura kwana biyar ɗaurin aure, gobe za ta wankin kai, jini lalle, Laraba kuma walima, Alhamis akwai sisters day, Friday biki, ta so suyi dinner Amma Abba ya hana, har faɗa suka ɗanyi dan kuwa ta so ta yi bura-uba wajen diner, sai gashi ya hana wai babu mai kallon mai ita, kuma yasan in ya je dole ta sha casu, gashi kwana biyu ƴan raye-raye sun kamata ko ita kaɗai sai ka ga tana rawa balle ta tsaya gaban mirrow hmmmm taba abu sosai.

Ɗakin Najlah suka shiga, ta sanya dogon hijab akan riga da wandon jikinta, sannan suka fita tare suna hira akan walimar za su yi.

Tsaye yake cikin ash colour ɗin jallabiya, kansa babu hula sai kashi da ya ɗan taru, kallo ɗaya za ka mai ka hangi rashin natsuwa a tare da shi, tunda suka buɗe ƙofar suka fito ya zuba musu ido yana jin wani iri balle da Najlah ta sakar mai murmushi.

Lumshe ido ya yi sannan ya buɗe yana mai janyo a'uziyya.

Da sallama suka iso wajen, ya amsa yana mai yi musu yaƙe.

"Sai na ji labari ashe aure za ki yi?." yarda ya faɗa cikin rauni yasa Najlah jin tausayinsa.

"Eh Ustaz, ranar juma'a ne, ina fatan za ka zo mana." faɗin Rukky ganin Najlah ta kasa magana.

"Ina miki fatan alheri, Allah Ubangiji ya sa a yi lafiya kuma taro ya watse lafiya." Wannan karan ma Rukky ta amsa da ameen tana faɗaɗa murmushi.

Daga haka suka yi shuru na ɗan lokaci kafin ya yi magana, Rukky ta hangi ƙaninta dake ƙoƙarin shiga gidansu.

"Al'ameen tsaya na baka saƙo." Da haka ta wuce su.

Gyaran murya ta yi, sai ya ɗaga idanunsa ya kalleta, da sauri kuma ya janye yana mai kollon wacce take kallo.

"Da ina da dama tana roƙeka wani abu guda ɗaya tak."

"Karo na farko da kika roƙa alfarma a wajena, na yi miki alƙawarin zan yi miki koma menene." sai ta jinjina kai.

"Ƙawata Rukayya, tana da hankali sosai, ga ibada da riƙe amana, a wajenta ina koyan abubuwa da yawa, me zai hana ka nemeta ." sai ta yi shuru tana kallonsa, idanunsa yana kan Ruky dake magana da ƙaninta tana mai dariya shi kuma ya haɗe fuska.

"Ruƙayya Zakariyya." ya furta akan leɓansa tare da tuno yanayinta a lokuta da dama, take ya fara girgiza kai yana tabbar ma kansa da ya rasa Najlah na har abada..............✍️ END

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚

1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh 7. YARINTA Ƙanwar Yayanta.

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_