BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣8

by @prettys01

> "Ruƙayya Zakariyya." ya furta akan leɓansa tare da tuno yanayinta a lokuta mabanbanta, take ya fara girgiza kai yana tabbar ma kansa da ya rasa Najlah na har abada.......

"Ka samu lokaci ka yi tunani akan haka amma karka ɗau lokaci dan za'a iya maka wuff." Da sauri ya mai da idanunsa kan Najlah, karo na farko da ya yi murmushi kenan.

"Ba zan iya rejecting alfarmarki ba, zan sanyata cikin tunanina, na koya soyayyarta kuma Nagode nagode." manyan idanunta ta sake zarowa tana murmushi.

"Da gaske?." Ya ɗaga mata kai.

"Thank You so much, gaskiya na ji daɗin haka, kun dace da juna sosai.........KE RUKKY ZO MANA." Ta kai maganar tana ɗaga murya.

Rukky dake tsaye daga gefe ta nufosu tana ma Najlah hararan ƙasa-ƙasa.

Tana isowa ta rungumeta tana murmushi.

"Ke Lafiya kike?. Ustaz bara na kawo maka ruwa."

"A'a Ruƙayya ki bari yanzu zan wuce ai." sai ta ɗaga kai ta kallesa jin muryansa ya yi sanyi.

Najlah dake murmushi ta dungure ma kai tana cewa.

"Zan shiga ciki sai kin....."

"Ke tsaya, Ustaz zai miki magana, ina zuwa Ni." Da haka Najlah ta wuce ta bar Rukky da mamaki.

"Allah yasa ba wani abu bane Ustaz." kai ya ɗaga yana ƙare mata kallo, shi sam ba ƙyau yake nema a wajen mace ba, ta zama mai qualities kamar Najlah, Rukky ma tana da ƙyau sosai, gata ba ta yi tsawo sosai ba haka ba ta yi ƙasa ba, dai-dai take, kuma take ya tuna, idan zai cire masu ƙoƙarin ajinsa tana cikin na uku, akwai mai da hankali sosai, uwa yake nema ma ƴaƴansa, kuma yana fatan ya samu, a jiyan zuciya ya yi sannan ya ce.

"Ruƙayya za ki amince na zama abokin rayuwarki na har mutuwa?." sai ya yi murmushi ganin kamar maganar ta duke ta, ba ƙarya maganar ya yi mugun dakanta dan haka ta ce.

"Ko dai na kurumce ne? Ban ma gane mai ka ce ba sam." Sake maimaita mata ya yi wannan karan harda rage murya.

"Ruƙayya za ki amince na zama abokin rayuwarki har mutuwa?." take ta zaro ido tana mamakin furucinsa, da sauri kuma ta juya ta nufa gidan su Najlah harda gudu-gudu, dariya ta bashi dan haka ya yi murmushi sannan ya kama kansa.

Kusan tumtuɓe ta kusa yi data shiga babban parlourn gidan, da sauri kuma ta hau part ɗin Najlah, tsaye ta isketa tana sana'ar wato rawa gaban mirrow.

Kai Rukky ta girgiza tana nufanta da sauri.

"Na rasa gane miki, ga karatu ga raye-raye, Alhaji Mubarak zai sha fama, zo ki ji wata banzar magana." Ta ja hannunta suka zauna, abinda Ustaz ya faɗa mata ta maimaita ma Najlah cikin mamaki.

Najlah ta yi dariya tana cewa.

"Na tura masa numberki, kuma ce min ya yi na mai budurwar shine na bashi ke saboda kun dace."

"What? Ni nace miki ina son saurayi? Ai ina da wanda nake so."

"Wanda yake sonki dai, ko nace kuna yaudarar kanku da kanku.........dan Tahir yaro ne, Classmate ne kawai, Malama ki kama dahir, ina da tabbacin har yanzu ciyar da Tahir ake, uhmmm ki dai yi nazari." Da haka ta miƙe tsaye tana sake isa gaban mirrow ɗin ta kunna waƙa ta ci gaba da rawarta.

Rukky ta yi shuru tana tunani, tabbas maganar Najlah dai-dai ne, dan kuwa Tahir ba wuci 21yrs ba, kawai tana sonsa ne sosai, ga kuma wannan maganar, tasan waye Ustaz, mutumin da ko tunanin haka bata taɓa yi ba, mutumin da mata suke mamarin tsayuwa da shi, malami mai tarin baiwar Alqur'ani, lumshe ido ta yi ta buɗe.

"Najlah shaƙwaɓa zo mana." ta kira ta da sunna da ƴan ajinsu suke kirarta.

Murmushi Najlah ta yi ta juyo ta dawo wajen da ta tashi, ta kalla Rukky tana turo baki tare da lumlumshe ido tana yin alamun za ta yi kuka.

"Bansan iskanci, ba Alhaji Mubarak bane, ki kirasa ki in kin gama mai shaƙwaɓar ma yi maganar." Da mamakin Rukky ta ga Najlah ta ɗau wayarta ta fara kiran sunan da aka yi saving da LOML 🥰..

"Menene LOML?" cewan Rukky sai Najlah ta yi murmushi ta ce.

"Love of My Life." zaro ido ta ɗan yi kafin ta kuma magana Abba ya katse kiran ya kira, ɗauka ta yi take Najlah ta fashe mai da kukan iskanci tana bubbuga ƙafafunta a ƙasa, Rukky ta zaro ido tana kallon ikon Allah.

A hankali muryar Abba ta fito ciki tashin hankali.

"Innalillah waya taɓa minke? Menene Jaririya ta...........dan Allah ki yi min bayani.......ko kina so na zo ne?." Ya kai nan yana fatan ta yi shuru da kukan na ta.

"A....Abba.....A.......abba." sai ta sake fashewa da wani kukan, Rukky dai zuba mata ido ta yi.

"Na'am Ammeen Basma, menene?." sai ta yi shuru tana ma Rukky ƙwalo, cike da zallar shaƙwaɓa ta ce.

"Uhmmmm Ba uhmmmmm ba Rukky ba ce take min ihu, kuma bana sooooo."

"Subuhanallah, ba Ni ita na mata faɗa....."

"Uhmmmmm A'a duka nake so a yi mata."

"To Jaririyata, tana kusa ne?."

"Uhmmm ga ta." Ta miƙa ma Rukky wayar tana miƙewa, gaban mudubin ta koma tana kallon kanta tana fari da ido.

"Alhajin Allah, Ango Ango mijin Jaririya." Ta faɗa tana dariya, shima dariya ya yi yana cewa.

"Ya fama da rigimarta?."

"Wallahi kullum ƙaruwa yake, mun kusa fara haɗa mata da duka." Da sauri Abba ya ce.

"Ku rufamin asiri dan Allah, ku dai lallaɓa min ita, kunsan kamar ƙwai take."

"Hmmm na ga alama ai, amma tana cika mana ciki sosai."

"A ƙara haƙuri, bansan ko kallon banza ana mata kunsan yarinya ce." sai ga ɗaga ido ta kalla Najlah, tsaye take tana ɗan karkaɗa jikinta, ta baya uban mazaunanta suna ta rawa.

"Ahhhh ba shakka Jaririya ce ɗanyan goyo." Dariya suka yi sannan ta isa wajen Najlah tana ba ta wayar.

Baki ta tura tana narkewa, shima sai ya rage murya cikin sanyi.

"Abban Basma."

"Na'am Ammeen basma."

"Uhmmm kana office ne?."

"Eh Shalele."

"To idan ka koma gida zamu yi waya."

"Shike nan, ki kula kinji Amarya."

"To Angona."

"Ina sonki."

"Ina sonka." Da haka ya mata sweet kiss yana katse wayar, murmushi ta yi ta kalla Rukky.

"Har kin faɗa min maganar banza, ga shaƙwaɓar na miki ai."

"Kinfi ƙarfina, ai ƙwanda mu aurar da ke, kut haka kike dama." Najlah ta yi mata fari tana cewa.

"Na fi haka, ki bari an jima ya kira, za ki sha kallo, kinsan yarda kaza ke zama ƙwai haka ƙwai yake zama Kaza."

"Allah ya tsare Ni, ni kaza, ba zan ji abinda zai doɗemin kunnuwa ba."

"Kinma kanki ai, ki koya cost kema ki dinga ma Ustaz Umar, nan da nan za ki narkar da shi a soyayyarki." murmushi suka yi sannan suka sauya wata hirar suna yi suna dariya, wani kuma su fara rigima.......

************** Mutane ne sosai a wajen ga sojoji ga ƴan sanda, harda ƴan jaridu masu ɗaukan rahoto, gefe guda gawan wa'inda aka kashe ne daren jiya, mutane 13, aka ma yankan rago, kuma ba'a san suwaye suka aikata haka ba, hakan yasa hankalin kowa ya tashi, aka cika unguwar, ana ta bincike, mutanen gari kuwa kowa ya shiga damuwa da wannan labarin.

Ƴan uwan wa'inda aka kashe suna ta kuka gwanin tausayi, ƴan jaridu kuma sai ɗaukan komai sune suna watsawa a duniya.

Ƴan sanda suna ta kai da komo, ga manyan likitoci da suke bincike akan gawarwakin.

Gaba ɗaya wajen ya hargitse sosai, a daidai lokacin manyan motoci guda biyar suka faka a gefe kaɗan da wajen, Range Rover guda biyu duka Black sai Lamborghini ash guda ɗaya da kuma Ferrari fari ƙal.

Take hankalin kowa ya koma kan motocin, jami'an da suke Range Rover suka fito da sauri suna buɗe Ferrari dake tsakiya.

Take shugaban jam'iyyar PRM wato Senator Tumɓa ya fito rai a ɓace, yarda yake tafiyar ma ya isa ka gane hankalinsa ba a natse yake ba, mutane suna ganinsa suka fara jin daɗi dan kuwa kowa yasa Senator Tumɓa, Mutumin kirkine, ga taimakon mutane, ko kwana biyu ba'a yi ba da ya yi rabon abinci, kuma ya hana a yaɗa al'amarin sai dai mutane suka fito suna ta nuna godiyansu akan ƙyautatawarsa.

Da shugaban masu binciken ya fara, in da suke nesa, amma ana ina hango yarda yake magana cikin tashin hankali da faɗa.

Da haka ya nufa mutanen da suka rasa nasu, ya dinga basu haƙuri harda hawaye dan tausaya musu.

Take kuma ya umarci a basu 1-1M, da haka ya tashi ya nufa motarsa yana share hawaye, mutane suka hau fata mai suna mai fatan alheri, ƴan jaridu kuma suka yi kansa da gudu suna son mai tambayoyi.

Tsayawa ya yi yana kallonsu a natse.

"Yallaɓa mutane suna ta nuna jin daɗinsu akan abubuwan da kake yi kwana biyun nan? Sai dai wasu suna tunanin campaign kake ma kanka kafin lokacin zaɓe, amma me za ka ce akan haka?." Cewan wani ɗan jarida, sai ya yi murmushi.

"Wannan maganar haka muke ji kullum, Ni a yanzu ba mulki ne gabana, mutane sune damuwata, ba zan fasa taimako ba, ina jin raɗaɗin abubuwan dake faruwa domin a ƙasata komai ke faruwa, dole hankalina ya tashi."

"Sir, me za ka ce aka masu wannan ɗanyen aiki?."

"Ina musu gargaɗi karsu bari mu kamasu, dan wallahi sai mun yi musu abinda ko dabba aka ba namansu ba za su ci ba." Ya kai nan yana nunfasawa sannan ya ci gaba.

"Kisa, fyade, garkuwa da mutane, ku sani masu wannan laifin Allah yana kwallon su, ko ku tuba ko ku haɗu da fushin Allah, daɗin abun gidan biyu ne, amma ya kuke so talakawa sune yi dan ......dan Allah." Sai ga hawaye shar daga idanunsa, nan ya fara kuka yana girgiza kai, securities ɗinsa suka shiga da shi mota tare da sallamar mutane.

Yana shiga motar ya tuntsire da dariya yana kallon abokin aikinsa David John.

"Aiki na ƙyau, yanzu dole ka ƙara shiga ran jama'a."

"Hakane David John, yanzu mu koma office zan kira *BLACK DRAGON* akan ya shiga ɓangaren kasuwa, ko huta a sanya ma wasu shagunan, kafin nan a kwashe komai ta yarda za mu dawo ma kowa da kuɗinsa kuma mu samu girmamawa. Dariya suka yi, sai dai jin abinda wani ke cewa yasa suka mai da hankalinsu kan Ɗan jaridar, da yake window ɗin be gama rufewa ba.

"Jama'a be kamata muna zagin shugaban ƙasar mu ba Alhaji Muhammad Babangida Shamaki ba, yana iya ƙoƙarinsa akan mu, kawai mugayene suka mai zayage suna neman rushesa, amma mutumin kirkine" ya faɗa yana kallon wata tsohuwa dake magana.

"Ƙarya kake, babu abinda shugaban kasa yake yi, waya sani ko dashi ake bin mu ana cutar mu........." Sai ta fashe da kuka tana ci gaba da magana.

"Yarana uku aka sace, aka nema kuɗin fansa mai yawa, sau nawa ina zuwa wajen shuwagabannin mu, sai dai babu wanda ya bi ta kaina, ga mu cikin talauci, haka na yi tattaki har zuwa wajen hasken al'umma *Senator Tumɓa* a ranar ya kira mutanen da suka yi garkuwa, ya ji nawa suke buƙata, shi ya biya aka dawo min da yara maza biyu ƴar macen sun kasheta, babu abinda zan ce akan Senator Tumɓa sai dai Allah yasa ya gama da duniya lafiya, ya kuma nuna mana lokacin da zai yi mulkin ƙasar nan." take aka fara mai kirari.

Yana mota ya yi murmushi sannan ya kalla Ɗan jaridar dake girgiza kansa.

"Uhm, David John… wancan ɗan jaridar, a kauda shi daga wannan duniyar. Ita kuma waccan matar, a sake tura mata saƙon kuɗi - aikinta ya yi ƙyau sosai."

"Ok sir… she really made it look real."

"Good. Let's move to the office… I'll contact Black Dragon regarding the children he abducted." da haka ƙwanon motocin suka bar wajen.

********

Fararen yatsunsa suna riƙe da coffee mug, a hankali kuma ya kai baki ya ɗan zuƙa, komai dake faruwa a wajen yana kallo a tv, be yi mamakin ganin Senator Tumɓa ba, saboda neman mulki yake ido rufe, yasan har ga Allah yana iya ƙoƙarin wajen ba ma Nigeria tsaro wanda ko a yanzu ya mutu yasan ya yi ayyuka na gari, mutane kawai da ba su gani, ko yace wa'inda suke ƙasansa suke rushe komai.

Gashin kansa ya shafa yana buɗe baki hankali ya ce.

"Lokaci.....ya yi, ina da yaƙinin zan rusa mugayen ƙasar nan, ya Allah ka taimaka kungiyar *BLACK SHADOW* kaba wannan ƙungiyar daman gano waye *BLACK DRAGON* da masu goyon bayansa akan rushe mana ƙasarmu." (ameen) ya lumshe ido yana nazarin abubuwan da suke faruwa a ɗan lokacin nan..

***********

A bakin get ta yi parking, sannan ta danna horn, aka buɗe ta shiga da motar har cikin gidan, Anas ya haɗiye wani kakkaurar miyau yana bin gidan da kallo.

Bayan ta yi parking ta kalla Anas.

"Me kake so?." lumshe ido yayi sannan ya buɗe.

"Ke nake so Basma, ina sonki sosai."

"Nima ina sonka sosai." sai ya yi murmushi.

"Za ki iya bani ranki?."

"Wallahi zan iya komai akan ka." Ta faɗa cikin gaskatarwa

"Ina so ki mari fuskarki da ƙarfi." Kafin ya rufe baki ta wanka ma kanta mari.

"Ƙara." Ta sake.

"Ya isa, daga yanzu duk wanda ya tambaye ki waye Ni, cewa za ki yi saurayin kine, Kuma shi kike so, dan haka ki rabu da duk Mazan da suke zuwa wajen ki." ta ɗaga mai kai.

"Ban wayarki." Da sauri ta bashi, sai ya cire mata sim ya ba ta.

"Zan dinga zuwa gidan ku, muna hira, sannan zan dinga rakaki wajen aiki."

"To." Ta faɗa tana kallonsa sosai.

"Ki dinga kiransa da Masoyi."

"Masoyi." Sai ya yi murmushi.

"Karanto min numberki." Da sauri ta karanta mai sannan ya fita daga motar, ita ma haka.

Kowa na Compound ɗin ya bisu da ido dan ganin kaman mahaukaci haka yake.

"Ba za su gaishe da masoyi na ba." Ta faɗa a tsawace, take suka fara gaishesa shi kuma ya dinga amsawa da kai.

Har waje ta rakasa sannan ta dawo gida, gaba ɗaya ji take kaman ba ita ba, da sauri ta shiga ciki, a parlour ta zauna yana jin jikinta na mata wani iri.

A'isha dake parlourn ta iso kusa da ita tana cewa..

"Hajiya sannu? Meke damunki?." Da sauri ta bar wajen ganin harara Basma ke watsa mata.

Take barci ya ɗauke mai nauyin gaske, gaba ɗaya mafarkin Masoyi Anas take yi, wasu na na tsoro wasu kuma masu daɗi, a cikin wani famarkin ne ta gansu a gajimare suna shawagi a tsakanin taurari, basu da wata damuwa sai nishaɗi suke kwanin burgewa..........

*************

Su uku ne zaune a parlourn, sunyi shiru kowa yana tunani iri-iri a cikin kansa, a daidai lokacin duk suka main door, ganin Al-hussain ya shigo riƙe da jakkar baya, ido kawai suka sama har ya isa inda suke sannan ya yi murmushi yana kallon Abbeey.

"Abbeey Barka da dare. Tweeny na yi kewarka." da haka ya ɗan tsuke fuska ganin babu wanda ya ce da shi komai.

"Daga ina kake?." Muryan Abbeey ta fito a cikin shurun wajen.

"Uhmm kai ke matsamin akan fara aiki, yanzu kuma na fara aiki sai ya zama laifi." ya faɗa yana zama gefan Al-hassan, wanda yau kowa da irin nasa, Al-hussain baƙaƙen riga da wando ne jikinsa, Al-hassan kuma farin t-shirt da wando threequater mai kauri dark blue.

"Wani aiki kake yi?." sai ya lumshe ido sannan ya ce.

"Computer Science shina karanta saboda na fi sonsa, ɗan uwana ya karanta aikin da kake so, karku manta ba'a ƙasar nan nayi karatun computer ba. Babu wani abu da ban iya a ciki ba, dan haka yanzu ina aiki biyu ne, Digital Marketer - mai tallata kaya a online, Cybersecurity specialist."

"Al-hussain ai wanna ko a gida zaka iya yi, me yasa baka zama, jiya baka kwana a gida ba, ga yau sai 12:35pm ka shigo gida, haba Tweeny." Murmushi ya yi yana riƙe hannun Al-hassan.

"Karka damu akwai shagon da nake zama ai." A tare suka kalla Abbeey dake cewa.

"Karka kuskura ka sake tsallake rana ɗaya baka kwana a gidan nan ba, sannan zuwa gobe zan so shagon na ku."

"Shike nan Abbeey sai na ganka." Abbeey ya bar musu parlourn.

"Merry Pretty na gaisheki." da sauri ta kallesa, ta ɗan zaro ido ganin Al-hassan na wajen.

"Eh wannan ƙawar ta ki manaaa." Sai ta ɗan yi dariya tana jinjina kai irin ta tuna ɗin nan.

"Al-hussain ina da magana da mai Very important, tun shekaran jiya nake so mu haɗu, ka numberka baya tafiya."

"Okay ina jinki." ya faɗa yana tashi daga in da yake zuwa kusa da in da take zaune.

Al-hassan ta ɗau jakkar Al-hussain da yake da uban nauyi ya nufa part ɗinsu. Yana wucewa Merry ta fuskance shi da ƙyau.

"Karka ce duk kwana biyun nan kana wajenta?." Sai ya ɗaga mata kai.

"Iyyeee sannu Ango." Murmushi ya yi mai faɗi.

"Me za ki faɗa min." Ajiyan zuciya ta yi.

"Gobe Abbeey ya ce na kawo saurayin nawa, na amsa mai da to, kasan bana kula kowa saboda *Promise* kai ka cika naka saura na wa." Shuru suka yi na ɗan lokaci.

"Shike nan an gama, gobe wani zai zo sunan sa Adnan, zan turo miki hotonsa, zan kira na mai bayani." Da haka ya ciro wayarsa yana kiran wani number.

"Boss barka da wannan lokacin." da sauri Al-hussain ya ɗan wayince.

"Adnan sau nawa zance maka bana son sunanan."

"Sorry Sir." sai ya lumshe ido, Merry ya kalla da take mai tambayar waye da hannu.

"A shagona yake aiki, uhm ɗauko min drink mai sanyi." Miƙewa ta yi ta bar wajen, da haka ya mai da hankali kan wayar.

"Aiki zan baka Yallow."

"Okay Boss."

"Matsashin saurayi wanda ba zai wuci 27yrs, kamili mai hankali, ya zo ya yi mana wani aiki na tsawon 20mnt zamu bashi 500 thousand."

"An gana Boss..........Sir."

"Yes." Sai na cikin wayar ya yi gyaran murya sannan ya ce.

"Ƴam mata goman nan........" Da sauri ya katsesa.

"Shike nan Adnan thank, ka turomin hoton ka da wuri, sai da safe." Da haka ya kashe kiran yana kallon Merry dake zama tana aje bashi Coke.

"Wai har ya yadda."

"Sosai ma kuwa." Da haka ya buɗe yana sha tana mai hirar abinda ya faru da bayanan.

"Yarda kasan Al-hassan ze yi hauka haka ya koma, ko aiki ya kasa zuwa hmmmm." Tare suka yi ɗan dariya.........

*Al-hassan* Tsaye yake gaban gado yana kallon hoton da ya faɗo daga ciki, hoton Senator Tumɓa ne da wani mai sanye da ɓaƙaken kaya ba'a ganin komai a jikinsa, suna zaune a parlour ne aka yi hoton, sannan ya yi dishi-dishi.

Mamakine ya kamasa akan me Al-hussain yake yi da hoton wannan mutumin da wasu suke mai kallon waliyyi wasu kuma akasinsa, shi dai ba wani yarda yake da shi ba, dan ko ɗazu sai da yaga anyi posting mota ta kaɗe Ɗan Jaridar da ya tuhumesa da safe, amma abin ya ɗaure masa kai saboda Senator Tumɓa ya fito yana faɗa akan me yasa ake mai sharri, harna iƙirarin ya fita daga harkan mulki, sannan ya ba familyn kuɗi masu yawa, gaba ɗaya dai shi abin zargi ne kuma abin girmamawa ne akan taimakon da yake yi.

Ƙofar da aka buɗe shi yasa Al-hassan juyawa yana kallon Al-hussain da ya shigo riƙe da coke yana sha, take fuskarsa ya sauya ganin abinda Al-hassan ke kallo, hoto, hoto ne wanda shekaran jiya ya ɗauka.

"Me kake yi da hoton nan?." ya tambaya yana kafesa da ido, lumshe ido Al-hussain ya yi yana nazarin ƙaryan da zai yi ma Al-hassan, baya san kowa yasan wannan fuskar na sa hatta Al-hassan ɗin, da sauri ya ƙarasa yana amsar hoton tare da ƙoƙarin zuge zip ya sanya, sai dai cikin rashin sa'a abu ya faɗi ƙasa, ƙaran da ya yi yasa suka kalla ƙasan, a lokacin guda kuma suka furta kalmar iri ɗaya amma kowa da fargaban da ya kamasa. "BINDIGA........."..............✍️ END

> WHAT!!!?????? 😯😯😯😯😯

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚

1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh 7. YARINTA Ƙanwar Yayanta.

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_