BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 2️⃣9

by @prettys01

> ......................sai dai cikin rashin sa'a abu ya faɗi ƙasa, ƙaran da ya yi yasa suka kalla ƙasan, a lokacin guda kuma suka furta kalmar iri ɗaya amma kowa da fargaban da ya kamasa. "BINDIGA........."...........

A tare suka kai hannu kan bindiga dake ƙasa, Al-hassan ne ya fara ɗauka yana ƙare mata kallo cikin mamaki. Da sauri Al-hussain ya fizge yana kallon Bindigar ta kwanta a cikin tafin hannunsa kamar an ƙera ta ne musamman domin shi, Ƙarama ce, sannan ba ta da wani nauyi, Launin baƙinta mai sheƙi. Yatsuntsa suka zagaye rikon bindigar, sannan ya tura cikin jakkarsa, da sauri Al-hassan ya riƙe sa yana tambayarsa cikin kaushin murya.

"Bindigan waye wannan? A ina ka sameta? Magana nake kana kallona." Sai Al-hussain ya lumshe ido sannan ya buɗe.

"Da zan fita shekaran jiya da daddare, na biya part Abbeey, anan na ganta, sai na ɗauka na fita, ɗazu ma na zaci ita zai tambaya, amma na dawo mai da shi yarda yake dan ban iya amfani da ita ba." gauron numfashi Al-hassan ya sauke yana gasgata Al-hussain.

"Har kasa zuciyata ta tsinke, ashe baka halina ba Tweeny." Da sauri ya girgiza kai.

"Ba haka bane Al-hussain, kawai na ruɗene sosai, ka samu ka mai da mai zuwa gobe, kaga bindiga yawo da ita matsalane, ba kowane zai maka kallon mutumin kirki ba, kawai dai karka sake dan Allah.....kaji." sai ya rungumesa yana jin soyayyar ɗan uwan nasa na ratsa sa.........

**********

Wayarta nakan sabuwar wayar da Abba ya siya mata a yau, hoton Anas ne a gaban wayar inda yake zaune kan wani dutse, ya yi murmushi yana kallon sama, idanunta ta lumshe tana tuno abinda ya faru a jiya, gani take kaman ba ita ba.

_Ko bayan da ta farka a jiyan, haka ta iske su Marwa suna zageye da ita, sai dai ba ta kula kowa ba, haka ta miƙe ta barsu suna tambayar lafiya, wanka tashiga ta sakar ma kanta ruwan daidai yarda fatarta ke ɗauka, gaba ɗaya fuskar Anas take gani a cikin kanta, tana fitowa ta sanya kaya mai sauƙi, har lokacin ta kasa magana, sai lokacin da ta ɗau wayar Marwa ta kira Abba akan tana son ya tawo mata da waya.

"Ina wayarki?." Tambayar da Marwa ta yi mata kenan tana tunanin ko ɓarayi sun tareta ne, sai Basma ta kalleta cikin rashin son magana ta ce.

"Na ƙyautar ko da magana ne?."

"Ah Ni na isa, ke mai da wuƙar bani na karzo man ba, rataya aka bani." Da haka duk suka fita harkar ta.

Babu abinda ya ɗaure musu sai ganin yarda Basma ke waya da wani cikin ladabi, ta tausasa harshen ta sosai, ba dai su sake bin ta kanta ba saboda kowa da aikin dake gabansa...._

"Bassey yau ba fita ne?." A hankali ta kalla Marwa dake gyara Rolling Vail na wata Abaya da ta sa.

"Eh sai gobe banjin daɗi jikina."

"Okay Allah ya ƙara lafiya." Ta ɗaga mata kai sannan ta raka Marwa da ido hatta fice.

Marwa suna da darasi ƙarfe 10:00am dan haka ta tsara zuwa 9:30am za ta isa, mota ta shiga ta kunna sannan ta fara tafiya a natse tana bin sautin dake tashi mai sanyi.

Tana shiga school ta yi parking tana kallon agogon dake kan farin hannunta, 9:38am sai ta yi murmushi sannan ta fita.

Rufe motar ta yi tana nufan department ɗin su, sai dai abin da idanunta suka hango mata yasa ta tsaya cak tana ɗan zaro ido alaman mamaki.

Al-hussain tsaye yana latsa wayar dake hannunsa, ya sanya wata shadda mai sheƙi da ɗaukan ido, ga kalan maroon ɗin ya ƙara haska fatarsa. Ta manta rabon da idanunta su gansa koda a waya ne, sai gashi tsaye nesa da ita, take farin ciki ya kamata, har ba ta damu da mutanen da suke wajen ba ta nufesa da gudu, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana ƙamƙamesa.

Sai dai lokaci guda ta zaro ido, tana jin sanyin nan na ratsa jikinta, rintse ido ta yi, a hankali ta sake jikinsa tana raba jikinsu, kunya ne ya kamata, hakan yasa ta kasa buɗe idanunta.

Al-Hassan kai ya dafe tana jin baƙon yanayi na zage jinin jikinsa, Allah ya so yana da ƙarfi kuma ya tsaya da ƙyau, amma yarda Marwa ta ƙamƙamesa da ya faɗi, a natse ya kalleta. Daidai nan ta buɗe idanunta tana kallon fuskarsa, take idanunsu suka sarƙe dana juna, sai kowa ya yi sauri kauda na shi.

Sun ɗau minti 10 a haka, kafin ta buɗe baki ta ce.

"Dan Allah kayaƙuri, na za ci My Love ne." Murmushi ya yi yana cewa.

"Idan ma shine tsakani da Allah haka ake oyoyo, zuwa ake gab da mutum sannan a rungumesa, balle ku saurayi da budurwa ne, sallama ya kamata mu yi." Sai ta sosa kai.

"Karo na biyu kenan da nake niyyar rumgumarsa sai Allah ya yi na faɗa maka, ba halina bane, kuma ina baka haƙuri." Murmushi ya sake yi.

"Karki damu, dama My Love ne ya aikoni." Dariya ta ɗan yi tana rufe bakinta da bayan hannunta.

"Ya ce na baki wanna." Ya miƙa mata ƙaramin kwalin da aka sanya a leda, sai ta amsa tana murmushi.

"Ka ce masa kai ba ɗan aike bane, ya dinga zuwa da kansa, be fi kowa busy ba."

"Saƙon ki zai isa."

"Godiya nake, uhmm dan Allah ka faɗa min sunan Bank ɗin da yake aiki? Zan mai bazata wani lokacin."

Al-hassan ya maimaita Banki a cikin zuciyarsa, sannan ya kalleta.

"Na manta wanne ya ce a cikinsu, amma a branch mai nisa da nan yake aiki." Sai ta jinjina kai, a hankali kuma ta ɗan matsa dab da shi har suna iya jiyi bugun zuciyoyinsu, sai ta rage murya sosai ta yi magana wanda Al-hassan yasa ya lumshe ido yana jin zaƙin muryan na ta na ratsa kwanyarsa.

"Na roƙeka wani alfarma?." be san lokacin da ya ɗaga mata kai ba dan ba zai iya magana ba.

"Gobe da misalin karfe 4pm, ka zo ka kaini wajen sa.........Dan Allah.........kaji." wani yarrr yaji dan haka ya ɗan matsa yana ɗaga mata kai.

"Na gode." Nan ma ya sake ɗaga mata kai. Da haka ta juya ta shiga class ganin saura minti biyar a fada darasi.

Kasa tafiya ya yi har sai da ta ɓace masa sannan ya lallaɓa har zuwa cikin mota, nan ma ya ɗau lokacin tukun ya kunna motar ya bar makarantar cikin wani irin yanayin da yakasa gane menene zai kira yanayin.............

****************

Wani gigitaccen kuka ke tashi cikin wata babban ƙwantena dake filin jirgin ƙasan a gefan babban wani babba kogi, gefe guda kuma maza ne tsaitsaye guda goma duk suna sanye da ɓaƙaken kaya suit, sannan kowa na riƙe da bindigu manya-manyan.

Wani ƙaramin gidan katako ne gefan su, a hankali aka buɗe ƙofar aka fito, Senator Tumɓa ne ya fara fitowa yana baza babbar riga kamar wani mutumin kirki, bayansa David John ya fito shima yana murmushi, kallon juna suka yi, a lokacin guda kuma suka matsa ma uban gayya hanya dake fitowa.

Kamar kullum haka yake sanye da ɓaƙaken kaya, komai na jikinsa a kulle, amma kansa na buɗe, idan baka sani ba za ka rantse da Allah fuskar mutumin ne, dan kuwa mask ɗin ya kwanta a fuskarsa sosai, fuskar ya yi daidai da shekarunsa, fatar akwai haske daidai misali, sannan ga ainihin idanunsa suka fito farare masu haske, a natse yake tafiya kamar Basarake, ya taka har zuwa gaban ƙwantenar, sannan ya yi ma wani security ishara da hannu, da sauri ya ba shi bindigar dake hannunsa A.K47, ya amsa da hannunsa dake sanye da safar hannu.

Bindiga ya saketa, ya harba kacar da ya riƙe kofofin ƙwantenar, take ya saki alburushi a sai tin wajen, take ihun da ake yi a ciki aka yi shuru kamar ruwa ya ɗauke.

Da hannu ya kuma alama, sai mutane biyu suka buɗe ƙwantenar, take ƴam matan da suke ciki suka razana suna ja da baya.

Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un, ƴam mata ne wa'inda a ƙalla za su kai 50, gaba ɗaya an rufe musu idanunsu da ɓakin ƙyalle haka an ƙulle musu hannaye, yawancin matan wajen ba za su haura 20-25yrs ba, wasu sanye da uniform, wasu kayan gida wasu harda hijabai a jikinsu, take muryan wata a cikin matan ta fara amsakuwa a cikin wajen.

"Mugaye azzalumi, wallahi ƙarshen ku ba zai yi ƙyau, jibi yarda kuka sace mu, kuka zubar damu anan kaman kayan wanki.........na yi rantsuwa da Allah mai ji kuma mai gani, ƙarshen......." maganarta ta koma ciki sakamako harbin Black Dragon ya yi mata a daidai goshinta.

Cikin muryan ƙirƙira ya fara magana cike da amo.

"SHIN AKWAI WACCE KE BUƘATAR MUTUWA A YANZU!?.....NACE AKWAI!!???." ba wacce ta sake tari, sai ma mammane juna suke yi.

"Black Dragon, mata 50 ake da buƙata, jiya ka kashe biyu, yau ɗaya, dama su 45 ne, sun dawo 40 daidai." cewan wani dake gefansa.

"Yausha ne za su zo ƙwashe su?."

"Boss gobe da yamma." sai ya ɗaga kai.

"Zuwa daren yau a nemo ƴam mata guda 10, koma ta yayane a kawo su, dan kaucewa zargi ku haɗo da maza 5."

"Ok Boss."

Sai ya kalla ƴam matan sannan ya sake alama da hannu, da sauri suka rufe su, tare da sanya wani kaca suka kullesa, inda Allah ya so saman ƙwantenar akwai huji-huji wanda suke ganin haske da samun iska.

"A yi order lafiyayyan abinci a ba kowa ya ci ya ƙoshi." Ya faɗa yana juyawa ya kalla Senator Tumɓa.

"Ka ƙaddara ka ci zaɓen Nigeria a wannan shekarar, ina harƙallolina hankali kwance saboda ku, muna taimakon juna a ɓangarori da dama, kuma ka cancanci na ma wannan aikin, dan haka karka damu, muna da kuɗi sauri iko, iko mai girma." Jinjina kai Senator ya yi sannan ya rage murya ya ce.

"Hakane amma matsalata da kai baka da yarda, tsawon shekara biyu kenan muna tare, amma ko muryanka na ainihi ban sani ba, balle fuskarka, kasuwanci kawai muke yi."

"Hahahaha haka rayuwata take, bani da yarda ko kaɗan, sannan sanina babu abin da zai ƙareka da shi."

"Hakane amma ina neman alfarma ɗaya a wajenka." Ya ɗaga mai kai jujjuya kai.

"Menene asalin sunan ka." da sauri Senator Tumɓa ya ja baya sakamakon irin kallon da Black Dragon ya yi mai, take ya sha jinin jikinsa yana ɗan rarraba ido, sai Black Dragon ya taka zuwa gaban Senator Tumɓa, shi kuwa gabansa ke ta faman dukan.

A gabansa sosai ya tsaya, sai ya ɗan ranƙwafa kaɗan saboda ya fi Senator Tumɓa tsayi, a daidai kunninsa ya raɗa masa.

"Wannan ya zama karo na farko da ƙarshe da za ka min tambaya akan abin da ya shafe ni, bani da yarda haka nake, duk masu min aikin nan sai da suka sha mugun ƙwaji tukunna, dan haka ka kula idan ba haka ba zan maka illa."

"To...to ba zan sake ba." Ya faɗa da ɗan rawar baki, dan kuwa yasan rashin imanin Black Dragon.

Da hannu ya musu alama, ai kuwa da sauri suka yi hanyar da suka bi dan shigowa suka bar wajen a 100 and 80.

Sun ɗan yi tafiya kafin suka cimma motocin su da securities din su, suka shiga suka bar wajen gana ɗaya, sai da suka yi nisa tukun Senator Tumɓa ya iya magana.

"Wannan mutumin sheɗain ne da kansa a duniya, tsaf zai min yankan rago, kuma ya kashe banza, hmmmm yana da mahaukaci iko, ta ɓangarori da dama, Ni kuma burina shine a lokacin da na samu iko, zan tabbatar na rabasa da ransa na mallaka dukiyarsa da kuma harƙallolinsa." Ya kai nan yana goge gumin fuskarsa da hannun babban rigarsa.

"Hmmm ai ina mamakin yarda yake juya mutane, bana son irin rashin imaninsa, ya yi yawa, da zamu shiga ka ga wasu manyan boxes ko?." ya ɗaga mai kai.

"Hmmmm na magunguna ne marasa ƙyau, ƙasashen wajen sun ga sun lalace shi kuma yasa aka komai kayan, shine ya shigo da su ta jirgin ruwa."

"Kome za'a ce min akansa ba zanyi mamaki ba saboda sheɗain ne na bugawa a jarida."

*************** "Ka ce ma Marwa aikin banki kake yi? To gobe zan kawota ta ganka, menene abin ɓoyewa a wannan sanar? Kalla shagon nan akwai kaya sosai." Cewan Al-hassan yana bin ko ina na shagon da Al-hussain ya musu ƙwatance suka zo da Abbeey.

Ba laifi shagon yana da girma, ga kaya nan sosai duk na harkan system, Abbeey ya dafa kafaɗar Al-hussain, ya mai murmushi.

"Na yi farin ciki da aikin nan da ka fara, Allah ya sa ma albarka." murmushi shima ya yi, sai Abbeey ya fita a shagon.

"Gobe na kowata nan kenan?" sai ya girgiza kai.

"Akwai wani aiki da nake yi *TAJ BANK* ka kawota can zan tura ma address ɗin wajen." Mamakine ya bayyana kan fuskar Al-hassan.

"Me kake yi a can ɗin?."

"Aikin kula ma'aikata, da masu shiga da fita, ta na'ura."

"Wow ƙanina ya dage, Bara na tafi Abbeey na jirana a mota, anjima kaɗan saurayin Merry zai zo."

"Shike nan, zan dawo da wuri yau." ya ɗaga mai kai sannan suka yi sallama.

Suna fita Al-hussain ya sauke ajiyan zuciya, sannan ya kalla saurayin dake zaune daga can gefe yanzu latsa system.

"Yellow, kira mai shagon ya dawo, ka sanar mai duk lokacin da muke bukatar zamu zo, uhmmm sannan zuwa anjima ka nema gurbin aiki a *TAJ BANK* idan zai baka walaha kamin waya, dana kira shine nan."

"Ok Boss." Sai suka yi murmushi.

"Ya aikin da na baka jiya akan ƴam matan nan?."

"Bayanan duk ya zama ready, kawai......." Sai ya yi shiru jin wayar Al-hussain na ringing. Duba wayar ya yi, take sunan *Senator Tumɓa* ya bayyana akan screen ɗin, murmushi ya sake yi sannan ya ɗau kiran yana kai kunninsa................✍️ END.

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚

1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh 7. YARINTA Ƙanwar Yayanta.

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_