PAGE 3️⃣0
by @prettys01
> "Bayanan duk ya zama ready, kawai......." Sai ya yi shiru jin wayar Al-hussain na ringing. Duba wayar ya yi, take sunan *Senator Tumɓa* ya bayyana akan screen ɗin, murmushi ya sake yi sannan ya ɗau kiran yana kai kunninsa...........
************
Kallon screen ɗin wayar dake hannunta take yi, sai ga hawaye sun gangaro daga cikin idanunta, hannu da suka ɗauka Henna ja da baƙi suka fito suka zanu akan farin hannunta, kai ka ce manna lallen aka yi da inji, dan kuwa baƙin ya zamu sosai, haka jan wanda ya koma maroon ya tsaru, an yi mata safa da shi kamar ka sace ka gudu, idanun ta share da su, sannan ta ja dogon hancinta tare aje wayar a gefe.
Najlah tana da rauni ta ɓangaren ƴan'uwa mata, a duk inda ta ga ana cin mutumcin mace ko da yarinya ne sai in da ƙarfinta ya ƙare, ta tsana taga ana wulakanta mata, sai gashi a wannan zamanin wani ya mai da mata kasuwanci, ya sace su ya sai dai su a wasu ƙasashen a matsayin bayi, wasu kuma karuwanci ta ƙarfi ake kaisu, gana ɗaya duniyar sai addu'a kawai kowa kansa ya sani.
Cikin muryan kuka ta ce.
"B........Black Dragon, sheɗanin da ya addaba al'umma, ya Allah ka tona asirin koma waye, kasa hukuma ta yi aiki akansa." (ameen) kafin ta sake magana wayarta ta hau ringing, ɗauka ta yi saboda sunan (LOML) Abba ne ya fito, ta ɗauka tana kai kunninta.
"My Jaririya gobe zan shigo, daga nan bazan dawo Abuja ba sai da babban Diomand mai daraja." yaƙe ta yi tana lumshe ido, cikin sanyin murya ta ce.
"Abbaaana."
"Na'am Shalele, ya naji muryanki a haka? Komai lafiya? Ko kina buƙarka wani abu ne?." ya faɗa cikin yanayin damuwa.
"Babu komai, kawai dai na gode sosai.
"Godiya? Akan me Jaririya."
"Akan signing ɗin da ka yi a paperna, ɗaya daga cikin hangen da na yi ma rayuwata kenan, da ace matashi nake shirin aura ko na aura, inada yaƙinin ba zai ban wannan damar ba, amma kai ka amince ka yarda kasa hannu........har na tura gaba." sai ta yi shiru tana jin soyayyar Abba na ƙara ratsa ɓargon jikinta.
"Haba Shalele, na za ci wani abu ne ma, karki dama kanki, Ni Mubarak mai tsaya miki ne akan komai insha Allahu." Take ta yi murmushi, sai kuma ta fara shaƙwaɓa.
"Uhmmmm my Mubeeey."
"Na'am Matar Mubeey."
"Uhmmmm ka min jaki-jaki ko na yi ma kuka uhmmmmmm."
"Ah subuhanallah, zan miki zo ki hau bayana."
"Uhmmmmmm banso ka min waƙa."
"Me?." Ya faɗa da ɗan ƙarfi, murmushi ta yi tana kwanciya.
"Uhmmm uhmmm waƙa nake so?."
"Jaririya kinsan ban iya waƙa ba." sai ta fara Turjiya tana son fara kuka.
"Ni dai waƙa nake so.........waƙa kaji.........Kajiiiii."
"Wallahi ban iya ba, bana tunanin ko waƙa ɗaya yana kaina."
"Uhmm Ni fa Baby zan ma kuku...........Baby Dan Allah....... Baby kamin waƙa." Da sauri ya ce.
"To ki yi shuru, alhamdulillah na tuna wani, na miki?." Ta ɗaga kai.
"Uhm." tana ji ya yi gyaran murya sannan ya fara waƙar.
"SHURUM-SHURUM BAJI NE BA ......HANGEN DALA BASHIGA GURMI NE BA.....BABAAAAA..........." da sauri ya yi shuru sakamakon Kukan da ta fashe da shi na shaƙwaɓa.
"Wayyo Allah na.......waƙan soyayya nake so, amma ka min ba waƙan alaba, uhmmmmmmmmm uhmmmmmmm."
"Ya Salam Shalele!? Wannan da ya na tuna, ina ga waƙan soyayya, Please ke kimin, zuwa dare zan yi searching wani na miki."
"Alƙawari."
"Cikawa." Sai suka yi murmushi.
"Zan yi mama sai ka yi amshi ka ji."
"Tayaya?." Sai ta tura baki sannan ta ce.
"Komai ma ka yi, kawai wanda ya hau waƙar da zanyi maka." Ba tare da yasan me zai ce ba ya amsa.
"To."
"Hehehe a zuciyarka duk Ni ce..........An haifeka dan Ni ce............kaji a ranka Ni ɗaya ce.......dan an raineka dan Ni ce......... Amaryar ka ai Ni ce......ta ɗayan....ta biyun.....ta ukun Ni ce.......ta huɗun duk Ni ce, na ceko akwai Maganaaaaaa na ce ko Akwai Maganaaaaaa." Da sauri Abba yace.
"Wallahi duke kece Jaririya......." Dariya ta yi tana lumshe ido.
"Ka kuɓuta abin so, zan sauka ƙasa, an jima za mu yi waya ai kana gida ko?."
"Eh na ɗau hutun aure ai."
"Iyyeee Ango ango."
"Za ki fara tsokana ko." da haka suka yi sallama cikin soyayya suka rabu...........
**********
Abba ya yi murmushi yana aje wayar tare da mai da hankalinsa kan tv, Jin mutane suna fitowa daga part ɗin sa ya sa ya kalla masu aiki.
"Alhaji mun gama."
"To masha Allah....... A'isha! A'ISHA!!." Da sauri A'isha ta fito daga Kitchen, a ƙasa kaɗan ta tsugunna.
"Ki kai musu abinci a wajen hutawa, yanzu."
"To Alhaji." Da haka ta koma Kitchen da sauri.
"Yauwa ta waje za ku ga hanya ya ɗan miƙa a nan za ku zauna."
"To Alhaji mun gode." ya ɗaga musu kai, suka fita, sai ya miƙe ya shiga ɓangaren na sa.
Wow komai a rayuwa yana son gyara, wato Alhaji ya yi ɓarin kuɗi, dan kuwa komai na Parlourn sai da ka sanya sabo, ko ina sai walwal yake yi, ga ƙamshi na musamman da yake yi. Daga kan kujeru, kayan kallo, penti da komai an sake.
Murmushi ya yi yana hasaso ganin Najlah zaune a kan kujera nan da kwana biyu.
Sai ya shiga kowani bedroom ya duba, nan ma an gyara ko ina, ya so gaba ɗaya gidan zai sa a sake gyara, amma fitinanniyar ƴarsa Basma, ta kafe akan babu mai gyara musu ɓangaren su, da ya so ɗaga murya, har da tura maza biyu su fara fita da kujeru, Sai da Basma ta wanka ma ɗaya mari ta musu hauka-hauka da mucciya shine suka bar wajen.
Da haka ya share su, ya ci gaba da harkokin sa.
*Bassey*
Daga sama har ƙasa ta mai wani Banzan kallo, sai ta juya kai tana sake haɗa fuska.
"Za ki iya faɗa min abu ɗaya na miki, wanda na cancanci cin mutumci daga wajenki?." kalmar da Doctor Mukhtar ya furta kenan yana jingina da motarsa ƙirar sport.
Wani abu ta ji ya tsaya mata a rai, tabbas be yi mata komai ba, kawai haushinsa take ji, haka ko da ta je aiki ba ta kulasa ba, sannan Anas ya rakata, amma a wajen asibitin ya jirata har ta tashi, shine suna dawowa gida ya wuce, sai ga sallaman shi.
A take ta kira Anas ta faɗa mai, sai ya ce.
"Ki gaggasa mai baƙar magana, ki mai tijara ki koma gida." Da haka ta fito.
Kuma tunda ga fito kallon banza take jifansa da shi.
"Kin ƙi magana, dan Allah me na miki?."
"Hmmmm baka min komai ba, kawai lokaci ɗaya na ji bana sonka, banjin hayaniya, dan haka ta ɓace min a ido, tun kafin na maka tijara a wajen nan." Sai ya ja dogon numfashi ya furzar.
"Zan tafi, amma ina nan ina dakonki, ina jiran ranar da za ƙi dawo cikin tunaninki...........zan karɓeki hannu biyu, abu guda biyu zan faɗa miki.........na farko, Ni Mukhtar ina sonki, so na har abada......na biyu, ki dage da addu'a, ki yi sadaka." Da haka ya shiga motarsa ya barta tsaye cikin tunanin kalamansa.
Kaɗa kai ta yi ta shige cikin gida, daga bakin get zuwa main door ta yi ma mutane huɗu faɗa har ta kusa marin wani.
Tana shiga babban parlourn ta zauna kana jin ƙamshin kifi ya cika parlourn, da sauri ta toshe hancita, sannan ta haura sama tana ƙwafa akan anjima za ta haɗu da masu girki.
Tana shiga ta zauna kan sopa, sai aka sake buɗe ƙofar aka shigo, Marwa ce ta shigo riƙe da manyan ledoji biyu, ta aje a ƙasa tana cire Hijab ɗin dake jikinta.
"Murmushin me kike yi?." cewan Basma tana kallon yarda Marwa ke ta blushing, Dan a ganinta be kamata suna dariya a cikin gidan nan saboda Abba.
"Oh Allah, Basma jaraba, murmushin ma karna yi kenan, hmmm bara na shiga restroom marata ta cika." da haka ta shige ciki.
Tana shiga bayi ta kulle ƙofa, sai ta jingina a ƙofar tana murmushi, fuskarta ta lumshe tana tuno abubuwan da suka faru daga safiya zuwa yanzu, sai ta ga kaman komai a mafarki yake faruwa.
_Daga makaranta Al-hassan ya zo ya ɗauke, babu wanda ya kula kowa har suka isa *TAJ BANK* suka iske Al-hussain yana ta aiki, kansa ya ɗau zafi, dan haka ba su ɗau wani lokaci ba, suka mai sallama, da yake bata ɗau mota ba ana Al-hassan take zaune, suna cikin tafiya sai aka mai kiran gaggawa a office, gashi suna kusa da wajen, sai ta amince da su je tare.
Koda suka isa Company ta yi mamakin ganin irin girmansa amma Al-hussain ya zaɓa aikin waje, a officer ɗin sa ya aje ta sannan ya fita.
Sai ta nema waje ta zauna tana jiran dawowarsa, a ƙalla tun tana ƙirga mintoci har barci ya yi gaba da ita.
A hankali take ji ana kiran sunanta ana cewa.
"Marwa Please wakeup.... Marwa! Marwa....Marwa." sai ta gyara kwanciya tana jin kaman a mafarki ne komai yake faruwa, ba tasan garin yayaba, dan har ga Allah barci take bil-haƙƙi.
Hannunta ta ji ya taɓa abu, kaman fuska haka, sai ta yi murmushi tana magana a haka.
"Waye kai? Wancan ko wannan? Bana gane muku gaba ɗaya, zuwa kuke min a mafarki, uhmmm kai wancan ne ko?." Ta ji an ce.
"Uhm." sai ta kuma magana.
"Me yasa kake damun ƙwaƙwalwa ta ne Al-hassan." Sai kuma ta yi shuru tana shafa gemunsa.
Lokacin guda kuma ta buɗe ido, me za ta gani.........
Al-hassan zaune a ƙasa, ya ɗan ɗaura fuskarsa kan sopa yana fuskantarta.
Zaburar da ta yi ne yasa ta ji kaman an hankaɗata ƙasa gaba ɗaya, sai ta faɗa mai jiki.
Take aka ɗauke hutan nepa, office ɗin ya yi duhu, sai ɗan hasken dake ratsowa ta tsakanin labule ne a ciki.
Gaba ɗaya a jikinsa take, har fuskarta yana gogan nasa, sai ta yi ƙoƙarin tashi, amma ta kasa saboda ya riƙe ta, a hankali muryansa ta sauka cikin kunnuwan ta.
"Yanzu za'a kunna solar, karki motsa, za ki iya bigewa da wani abu." Sai ta ɗaga kai tana jin daukan numfashin sa.
Ya ce yanzu, amma a minti huɗu suna a haka kafin ya kuma cewa.
"Bansan meke fizgan zuciyata zuwa gareki ba, alhalin ke wacce ƙanina zai aurane, wallahi Marwa bazan iya fassara yanayin da nake ciki ba." sai ya yi shuru, ita kuma sanyin jikinsa na ratsa ta ta ce.
"Ni kaina kana cikin raina, bansan dalili ba kafin na tuna Al-hussain na tunaka sau ba adadi."
"Me kike ji a jikinki Yanzu?."
"Sanyi nake ji n shiga fatata........." take haske ya gauraye ko ina.
Marwa ta tashi a jikinsa da sauri, kallon wajen ta yi babu komai, tasan ko ta miƙe ba za ta yi karo da komai ba, sai ta lumshe ido tana jin ƙamshin turaren ta da ya kama mata Hijab.
Zama ta yi gefe, tana saton kallonsa, ya lumshe ido yana shafa gashin kansa.
A ranta ta tuna laushin da gashin gemunsa yake da shi, ga santsi ga laushi.
Da haka suka yi shiru sai ya miƙe ya ce.
"Muje." Ba musu ta ɗau wayarta ta bi bayansa, ko da suka shiga mota sai ya nufa supermaket da ita.
"Bana buƙatar......" sai ta buɗe motar ga fita saboda kallon da ya yi mata.
Yana gaba tana bayansa dan gaba ɗaya yanayin ɗazu ya tsaya mata a rai.
Ta rasa me za ta siya dan haka ta nufa wajen Choculate, kowanne ta ɗau guda ɗaya, yana ganin ta sa ɗaya sai ya ɗiba kalansa guda 10 ya zuba, sai ta yi murmushi, haka ta cika leda ɗaya da Choculate leda ɗaya kuma da su snacks.
Ta yi gana ta tsaya wajen biya, shi kuma ya je ɗauko turare, yana zuwa ya ɗauko huɗu, shi da Al-hussain.
Sai ya tawo a natse, amma kafin ya ƙaraso ya tsaya jin wata mace na mai magana, yana juyawa ya yi mata murmushi yana cewa.
"Amrah, yaushe kika dawo ƙasar?." Budurwar ta yi ɗan dariya.
"To ai ku baku ziyara, kusan 2 month dana dawo, Abbeey kaɗai ke zuwa Amma ku sai a hankali." sai ya shafa sunan kansa.
"Amrah a ba Hajiya haƙuri muna nan shigowa."
"Ƴan biyu haka kuke cewa ai, ina ɗayan yake?."
"Yana wajen aiki."
"Kenan Al-hussain ne gabana ko, sarkin tsokana." Ta faɗa tana ɗan kai hannunta kafadarsa, sai dai ta ji an riƙe mata hannu.
Amrah da Al-hassan suka kalla Marwa dake tsaye fuskarta babu yabo babu fallasa.
"Na gaji da tsayuwa." Ta faɗa tana hararan yarinyar.
Al-hassan gaba ɗaya ya manta suna tare.
"Sorry Ga...." Hannu ta ɗaga mai sannan ta wuce, ko ta kan kayan ba ta bi ba ta fice.
"Ƴan biyu, wacece wannan? Oh an ce za ka yi aure ko?."
"Eh Amrah, Bara naje, kaman ta yi fushi." Da haka ya nufa wajen kayan, ya biya sannan ya fice.
A cikin mota ya isketa zaune ta haɗe fuska.
Ya shiga sai ya kasa driving, a hankali ya ce.
"Yarinyar ƙanwar Abbeey ce, na jima ban ganta ba, an ce bata ƙasar shi yasa na yi mamakin ganinta." Sai ya yi shiru yana jiran ya ji me Marwa za ta ce.
Kallon waje take yi, murmushi ta yi sannan ga haɗe rai, ta juya ta kallesa.
"Ban tambayeka ba, ka mai da Ni gida dan Allah." sai ya kunna motar ya fara tafiya a hankali.
Ko tari babu wanda ya sake har zuwa bakin get ɗin su da ya zo, sai ta ji ƙoƙarin buɗe ƙofa amma a rufe, kallonsa ta yi.
"Zan fita." lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe yana kallonta.
"Na ɗauke ki kina farin ciki, ba zan rabu da ke ba sai kin dawo yarda kike."
"Lau nake ai." Ya girgiza a hankali.
"Kishi ki ka ji dan na tsaya da wata?." Ta ji saukar maganar kamar daga sama.
"Akan me zan ji kishi bayan ba Al-hussain bane, da shine ma ba zai yi wannan giginba." Ji ya yi maganar ta ya tsaya mai a rai.
"Amma me yasa kika hassala?."
"Bana ce ba......kawai rai ne ya ɓaci ne."
"Hmmmm shike nan." Ya furta yana kallon agogon hannunsa.
"Ka buɗe min pls." ajiyan zuciya ya sauke, sannan ya janyo ledoji biyun da suka baya.
"Wa za ki bar ma wannan?." baki ta ɗan tura dan akan jikinta ya aje su.
"Na gode...... uhmm na ce ba."
"Ina jinki." Sai kuma ta kasa magana ta zuba idanunta kan wayarta tana ɗan latsawa.
"Magrib ya kusa, zan so na koma gida kafin lokacin, amma tunda ga masallaci a can a nan zan yi sallah na kulleki idan na dawo sai ki faɗa min......" da sauri ta ce.
"Uhmmm dama turaren nan nake so guda ɗaya." Ta faɗa tana nuna ledan dake baya.
"Na maza ne kuma yana da ƙarfi."
"Na sani ina so ne." sai ya kalleta.
"Kinsan haramcin sanya turare ga mace ta fita, wa'inda ba muharramanta ba su shaƙa ƙamshim?.......na jikinki shine daidai, mai sanyin ƙamshi, ba'a ji sai ana dan sosai dake." Ya kai nan yana tuna yanayinsu na ɗazun, ita kuma kunya ya ɗan kamata.
"Eh ƙamshi nake so, zan dinga sa a hannuna ina shaƙane." Kallon ban gane ba ya yi mata, sai ta lumshe idanunta ta furta kalaman da suka sa Al-hassan ya daskare waje ɗaya kaman kakide.
"Da ina da iko, da zan ɗauki cleaner na je daidai wajen da muka fara haɗuwa da shi, na goge harrufai kaɗan daga sunansa, na sauya da wani ya zama *Al-hassan ba Al-hussain* ........ Why you're special?." da haka ta yi shuru sannan ta juya ta ɗau turare guda ɗaya ta buɗe ta fesa a hannunta sannan ta shinshina.
"Me yasa da banbanci da na jikinka?." Ta kallesa sai dai ya kasa magana gaba ɗaya, sai ya rufe idanunsa.
Kusan ɗauke huta ya yi jin ta matso dab da shi, har sai da jikinsu ya goga juna, ta ɗauki ta yi unlocking motar sannan fita, tana murmushi.
Ya jima jikinsa a sanyaye kafin ya kunna motar yabar unguwar._
"Lafiya banji motsin ruwa ba?." Da sauri ta dawo cikin tunaninta, ƙirjinta ta dafe tana ɗaga murya.
"Lafiya lau Bassey, Yaaa?."
"Abba ke neman mu, ki yi sauri."
"Okay." Da haka ta matsa ta wanke fuskarta sannan ta yi uzurinta ta fita hankali a kwance, tana nazarin mai Abba zai ce, duk da kuwa maganar ba zai wuci kaman tsinanniyar yarinyar da yake shirin kawota kushewarta ne wato gisb *Mom*................✍️ END.
> Tashin boom 🤣
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*
*Zazzafan Littafin da suke ongoing* *THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*📚
1. BUDURWAR ABBAN MU Pretty Sk 2. WASAN ƘADDARA Asmeetah Writer 3. FANSAR NAILAH Umulkhairi Hashim Abo 4. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal 5. WARƘIYAR SO Fatima Bintu Hussain 6. GARWASHI Hafiza Amanar Ammey Laylerh 7. YARINTA Ƙanwar Yayanta.
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI_