PAGE 3️⃣1
by @prettys01
> "Okay." Da haka ta matsa ta wanke fuskarta sannan ta yi uzurinta ta fita hankali a kwance, tana nazarin mai Abba zai ce, duk da kuwa maganar ba zai wuci kaman tsinanniyar yarinyar da yake shirin kawota kushewarta ne wato gidan *Mom*.............
Bayan Basma ta bi tana kallon jakkar makarantar Fauza dake kan kujera, fita ta yi ta kulle ƙofar, tun daga stairs ta fara jiyo maganar Basma cikin masifa da hayagaga.
"Ban hana a dinga soya kifi ba idan ina gidan nan...........ba magana nake muku ba?." Cewan Basma tana kallon mata biyun dake kallonta.
"Da kurmaye nake magana?." Da sauri A'isha ta ce.
"A... Alhaji ne ya ce na sanya ma masu aiki a abinci wallahi bansan za ki dawo da wuri ba." sai ta watsa mata harara.
"Hmmmm zan yi maganin ku, ku jira ni, ke kinyi da fari kaman zabiya ke kuma kinyi da ɓaki kamar baƙin zunubi hmmmmm." da haka ta fice daga Kitchen ɗin tana mako musu ƙofa.
Kallon Marwa ta yi dake tsaye tana kallonta.
"Bassey masifar ki ta yi yawa? Ki dinga sassautawa dan Allah."
"Hmmm muje part ɗin Abba muji menene, Ni gaba ɗaya raina a ɓace yake." Ta kai nan tana yin gaba, sai Marwa ta bi bayanta tana murmushi.
Durus suka yi suna bin ko'ina na part ɗin da kallo, ganin yarda ya sha uban gyara, baki suka taɓe suna isa cikin Parlourn, Abba da Fauza ne zaune suna magana.
"To ki haɗa kayanki, gobe da safe za mu wuce."
"To Abba."
"Yauwa Fauza, autata mai ƙaunata." suka yi murmushi suna mai da hankalinsu kan su Marwa da suka shigo.
Duk iskancinsu suna da ladabi, a ƙasa suka zauna gefan Fauza.
"Abba gamu." Faɗin Marwa tana murmushin da ita kanta ta rasa na menene.
"Dama akan maganar bikin Maman kune, Momy Najlah, gobe Ni zan tafi da Fauza, ku kuma ko ranar bikin ne sai ku leƙo." da sauri Basma ta ce.
"Abba wallahi babu inda zanje........ba Ni kaɗai ba hatta su.........babu mai zuwa Kaduna."
"Sannu Hajiya Karima, na ce sannu, ko dai Hajiya Mama ce na tsugunna a ƙasa." Fauza ta kauda kai tana ɗan dariya.
"Babu ko ɗaya, kawai matsayinsa na yayar Fauza da ƙanwar Marwa na yi maganar." Ta faɗa tana tura baki da haɗe fuska.
"Tsakani da Allah ace a can family house ana shagalin bikin na, ƴaƴana su kasa zuwa, haba dan Allah."
"Uhmmm Abba Gaskiya nima babu in da zanje, saninkan ka ne ba ƙaunar auren nan muke ba, kaine ka dage......" da sauri Basma ta tari numfashin Marwa.
"Komai ya faru bayan aure babu ruwana."
"Wallahi kuwa, kamata zamu yi mu murɗe ma ƴar iska wiya kowa ya huta.............."
"Marwa ai wannan mai sauƙi ne, ai mugunta zamu yi mata cikin salon azabtarwa, kinga kashi na farko, ko mudinga ɗaye mata fata da huta, na biyu acid, yana ɗaki na ɗauko a asibiti, a fuska za mu watsa mata, yarda za ta sha jinya kafin ta mutu, na uku, hmmmmmm ƙaryata zamu yi, mu hana a ɗaure mata sai in ya yi tsami zamu nakaɗa mata na kaji......na huɗu, akwai magungunan da na zo dasu, a ruwa zan zuba mata, da kaɗan-kadan za su haukatata.........na ƙarshe shine Duk wani farin ciki da take fatan samu a gidan nan ba zamu bari ta samu ba, Ba boka ba Malam, da basira zamu ci uban ƴar air, Kuma wallahi mu kwana lafiya." shewa suka yi suna tafawa.
"Ahayye chassss." Suka faɗa hankali kwance.
"Aunties ko da nake son zuwa bikin, bakusan me na shirya bane, na so naje, ta yarda zan hana kowa zuwa ɗaurin aure, tun sati biyu Baya nake tsara komai, a ƙalla Ni da yara uku za'a kaimu asibiti, bayan na bi ko wani mota na lalata tayoyi, sannan zan zuba maganin barci na 24h, kowa ya ci da safe shike nan sai washegari za su farka, wanna shine plan guda biyu, ina da irinsu guda 10." ta kai nan tana musu fari da ido, Abba kuwa kasa magana ya yi yana kallon ikon Allah.
"Wayyo ƙanwata, ina sonki Ummaaaahhhh ." Basma ta sumbaci kumatunta.
"Ai kallona kuke so silent ko?.......na fi ku iya masifa, jira nake bazawarar ta shigo gidan nan, ai sa'ar yi na ce, ku dube ni tsab, na fi ƙarfin bugu, bare zagi, harara kuwa sai a bayan idona." ta kai nan tana miƙewa tsaye tare da yarfa yatsu fararen yatsunta, ta kashe musu ido, tafa mata suka fara yi suna masu washe baki har kunne.
"Ai ki bari ta shigo gidan nan, sai a yita ta ƙare, ko za ki je ɗin......."
"Babu wanda zai je...... innalillah, Fauza yaushe bakinki ya buɗe? Haka kike dama?." Duk sai suka kalla Abba.
"Laaa Abba yana nan ashe, ku bari sauran maganar sai an jima, Abba na janye maganata Fauza za ta bika, aje asha biki lafiya." harara ya watsa mata.
"Ku yi zaman ku, babu mai zuwa........." sai wayarsa ta fara ringing, murmushinsa ya faɗaɗa yana ɗaukan wayar.
"Wassalamu Alaikum, Amarya.....Amarya baƙya laifi, ko kin kashe ƴaƴan masu gida." ya faɗa da biyu dan su ji haushi, sai dai inaaaa dariya ƙasa-ƙasa suke yi.
Muryan Najlah ce ta daki kunnuwansu cikin shaƙwaɓa da iskanci.
"Uhmmmm My Fine Babyyy, ka ga Aunty Zulfa sai ba Ni wani magani take mara daɗi, wai dole na sha saboda kai ........Ni kuma bana so......uhmmmm Ni banso........" lumshe ido ya yi yana ji tsakin da Basma ta ja mai shegen tsayi sannan suka tashi suka fice suna buga mai ƙofa bayan Marwa ta ce.
"Da gaske dai ƴar hannu Abba zai ƙwaso, hmmm za ta ci ƙwal ubane." girgiza kai ya yi.
"Babyna ki daure kisha, kinga ba zan iya musu magana ba, kuma kema kinsan zan buƙaci haka, na jima sosai babu mace, dan haka ki shirya a daren farko sau......" Ƙet ta kashe kiran, shi kuma ya yi murmushi yana ɗaukan remote amma har lokacin mamakin kalaman Fauza yake .....................
**************
Hausawa suka ce, *Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.* Wannan magana ta tabbata a yau Juma'a, lokacin da farin ciki ya lullube zuciyoyin al'umma, da ƙulla alkairi na ƴaƴansu, dan ci gaba da haɓɓaka sunnan Mazan Allah Sallallahu alaihi Wasallama ❤️.
Da misalin ƙarfe 1:40 na ranan jumma'a, ɗumbin jama'a suka hallara wajen ɗaurin aure musulmai guda goma sha biyar (15), wanda ya gudana cikin natsuwa da albarka, bayan sallar jumma'a.
A cikin jerin wa'inda aka ɗaura ma auren, an ɗaura auren *ALHAJI MUBARAK ADAM Da kyakkyawar amaryarsa HAFSAT ABDULLAHI (NAJLAH).* An ɗaura auren ne bisa sadakin Naira dubu ɗari biyar (₦500,000), cikin farin cike da fatan alheri daga dangi da abokai.
Wannan rana ta zama abin tunawa, rana mai cike da farin ciki, addu'o'i da fatan samun zaman lafiya da soyayya a sabuwar rayuwar aurensu.
Bayan kammala ɗaurin auren, ko wani ango yana ɓangaren danginsa ana ta hoto dan tarihi, kowani ango zaka ɗaga ido ka kalla, za ta iske farin cikin da yake ciki ba'a magana.
Gefe guda jama'a ne suke, ana ta hoto, a tsakiyan mazan, Abba ne tsaye yasha ado iya ado daga saman har kansa, ango ya sanya hula mai ƙyau ta zamani, wacce aka yi da yadin da ya dace da kayan jikinsa, ba mai hayaniya ba amma mai ɗaukar ido.
Fuskar sa cike take da annuri, gemunsa an gyara shi fes sai ƙyalli yake yana ƙara masa kwarjini da tsafta.
A jikinsa, ya sanya shadda mai tsada sosai, mai nauyi da laushi, wacce aka ɗinka da salo na zamani mai tsari. Launin kayan ya haɗu da kyau-mai sanyi amma mai daraja, light brown amma mai shining.
Babbar rigarsa na zaune jikinsa daidai, ɗinkin ya fito da tsari da ƙyan gani, ba wuce gona da iri ba amma komai a daidaitacce.
A hannunsa akwai agogon fata mai tsada, wanda ke nuna da agogon kayan ne.
A ƙafafunsa, ya sanya takalmin fata mai inganci, mai launin baki da ratsin kayansa.
Annurin da yake yi ya zama na musamman yau, hoto aka ɗauka na ƙarshe, sai ya matsa gefe yana fiddo wayarsa daga ajiyunsa.
Murmushi ga saki yana ƙara gode ma Allah da ya nuna mai wannan lokacin na auren Najlah a matsayin matarsa ta sunna.
Numberta ya kira dan ya shaida mata ɗaurin auren.
Bayan ta ɗauka ya kai kunninsa ya yi mata dogon sallama cike da farin ciki.
"Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh Rayuwar Mubarak." take muryanta cikin sanyi ta ratsa shi.
" wassalamu Alaikum."
"Baby an ɗaura......an ɗaura na zama mijinki mai iko da ke." Sai ta yi murmushi.
"Allah ya sanya alheri a cikin auren mu, ya bamu ikon hakuri da juna."
"Ameen Shalele, kina ina yanzu haka?."
"Ina zauna cikin ƙawayena a ɗakina."
"Yauwa, to Ni Mubarak mijinki na ce karki motsa daga wajen har sai na zo gidan ku, ikon zan fara." Tare suka kwashe da dariya suna tuna ranar da ya ce da ita.
'Karki je kasuwa, ki bari masu zuwa suje.' buɗan bakin Najlah sai ta ce.
'My Mubee, sai an ɗaura za ka fara ikon na ka, yanzu kam ƙarƙashin Mother nake.' da haka ta kashe wayar kuma ta je kasuwar, ashe yana riƙe da wannan.
"Babyna wasa kake ko?." Ya ji ta faɗa bayan gama dariyar.
"Ga gaske nake, karki motsa daga wajen, ina sonki ki kula." Da sauri ya katse kiran dan jin ƙawayenta suna ihu da tafi lokaci guda.
"Mubarak! Mubarak zo mana." sai ya juya, wajen Kanin mahaifinsa ya nufa dake suke kiransa.
Nan wasu ɓakin suka sake mai fatan alheri, daga nan sai family house, Wanda ya cika tab kai ka ce bikin wani yaro ake yi, amma da yake kowa fatansa ya yi auren, sai shagalin ya zama babba.
Motocin su suka faka a gefan gidan, dan kuwa ciki babu wajen parking, Suka jeru wajen shiga, Abba na tsakiya sai murmushi yake yi, gaba ɗaya kunya ma ta kamasa.
Ana ganinsu aka hau guɗa, mata suna fitowa ana ganin Ango, sai ya ji yanayin baƙo, tunawa ya yi da aurensa na farko, be ga wannan soyayyar ba sam, sannan a lokacin da mutane biyu a rayuwarsa wanda a yanzu babu su, Karima da Hajiya Mama. Addu'a ya musu sannan ya ɗan saki jiki yana amsawa da ameen wanda leɓansa ne kawai ke amsawa..............
***************
Toshe kunnuwanta ta yi tana dariya, sai da ihun ƴan ajin islamiyyarsu ya yi sauƙi sannan ta kallesu tana cewa.
"Ai sai ku sa mutum kunninsa ya doɗe. Bara naa......" da sauri Umaima ta riƙe ta kafin ta tashi.
Haɗa baki suka yi wajen cewa.
"Be bada izini baaaa."
"Kaii kuna tunanin karna motsa har sai kira?." M. Salis ta ce.
"Garantee umarni ne daga sama." Sai suka kwashe da dariya, sai Rukky dake tsaya cikin Angon bikin, wanda ta yi riga skirt ta ce.
"Amarya kar tun yanzu ki fara take karatun ki, ance idan ya ce a'a kirki......"
"KIYIIII." Duk haɗa baki suna dariya.
Baki ta fara turawa tana bubbuga ƙafa a ƙasa.
"Ah taɓarar ya motsa." Da sauri Najlah ta bugi kafaɗar Rumaisa.
Nan fa amarya ta rantse sai ta tashi, su kuma suka rirriketa suka hanata tashi.
Cikin ikon Allah sai ga kiran Abba, da haka suka saketa ta ɗau kiran.
"Baby ka hanani tashi, ga Mamie sai kira na take." Da sauri ya ce.
"Ya Salam, Ni wasa nake miki ai, sorry, tashi ki je, ga munan zuwa."
"To Allah ya tsare hanya."
"Ameen My Dearest." da haka ta katse kiran tana musu fari da ido.
"Najlah sauya kaya kafin ya iso, wow makeup ɗin nan ya ƙara haskaki." sai ta yi fari da ido." cewan Rukky tana aje wata arnen less Mai shegan ƙyau.
Da haka aka ba amarya waje ta sauya shiga.
Babban parlour kuwa, ƴan uwa da mutanen arziƙi ne suka cika tab da gidan, kowa ka kalla fuskarsa a washe da farin ciki.
Yawancin mutanen suna sanye da golden atamfa mai kala uku, ja, ɓaki da brown, atamfar ta yi ƙyau sosai, sannan kowa ya ƙure ɗinki, dan style ne sai kin gaji da gani, wani ya burgeki wani kuma ya baki haushi.
Hatta Compound akwai jama'a sosai, rumfa wajen biyar ne a tsakar gidan kuma kowanne da mutane, a gefe guda can ga sojoji suma da suke kwasan dabge, dan kuwa Mamie da kanta ta kawo masu girka abinci da masu rabu, yarda kasan a hall haka, dan abincin ma kala-kala ne suka girma.
Mamie ta yi dariya tana kallon ƙawayenta tun na makaranta.
"Allah na tuna Najlah nawa take da za'a kaita gidan hayaniya, hmmmm matansa basu da ta ido, ace kaman su Aunty Jummai suje jere, matan nan su musu rashin kunya." Cewan wacce ke zaune gefan Mamie tana jin babu daɗi, wata da suke kira Mario sunan tun suna makaranta ta ce.
"Gaskiya ba su ƙyauta ba, da munsan hakane da kince ya neman mata gida daban, yauwa ga ƴar albarkan can..... Amarya!! Amarya zo." Dukkansu suka kalla Najlah da ta nufo su, tana tafiya a natse.
Wani Less ta sanya mai kyau da tsari, wanda ya ji duwatsu daga sama har ƙasa, fitted gown me rigar in da ya bi ko ina tudu ƙwari ya zauna a jikinta team tsaf, ta gaba da baya, ga wani irin cika da ta ƙara sai masha allahu kawai, wani mayafi mai laushi da tsada, da aka yafa mata ya ɗauka ta baya har ƙasa, kanta da yasha ƙananan kitso ya kitsu ƙanana kuma cikin tsari.
Fuskarta kuwa, kwalliyarta ta kasance mai kyau sosai gashi babu wani hayaniya, idanunta da suke fari ƙal sun ɗau Kajol ya yi wani ƙyau sosai. Sannan gashin idanunta sun ƙwanta sun ƙara haskaka idanun nata, lip-gross aka shafa mata kawai, amma ya yi wani light pink saboda yanayin leɓanta. Kai gaba ɗaya Najlah ta cinye wankan, dan tsayawa bayanin ƙwalliyar zai ɗau lokaci.
Murmushi mai haɗe da kunya ta isa wajensu, ta tsugunna tana gaishesu, cikin farin ciki suka amsa suna washe mata baki.
"Najlah me yasa kika yarda aka haɗa ki da kishiyoyi? Tun kafin a kaiki sun fara nuna halinsu."
"Maman Tweens me ya faru?." Cewan Najlah ta lumshe sexy eyes ɗin ta, wanda ya yi kaman ruwa sun kwanta a ciki, Sai Mamie ta ce.
"Ba wani abu bane, kawai yaran mijinki ne suka yi ma su Aunty Jummai rashin kirkiri, amma ya wuce, tashi ki je."
"Yayansa ne wai dama?." Cewan ɗaya, sai Najlah ya tashi ta bar wajen.
"Kuna kallon Autata kaman shuru-shuru, itama gogaggiya ce, kome ya faru ita ce, da bakinta ta roƙa zama da yaran, sannan tasan halinsu, ku barsu mu dai mata fatan alheri kawai, su kuma zan kira Aunty Jummai din ku kulle part ɗin, har masu kai amarya su kaita." da haka suka ci gaba da jujjuya maganar.
Najlah murmushi kawai ta yi, ba za ta kira su ba, hasalima su gama duk iskancin da za su yi, tana shiga an gama magana.
Duk wanda ya ga amarya sai sun tsaida ita sunyi hoto, kusan suna da farin jini.
Ƙawayenta suke zage da ita har suka fita Compound, wajen sojojin ta fara zuwa, inda tana zuwa suka sara mata itama haka, take suka hau hauka wasu harda harbin sama da bindingu.
Taso ta amsa bindiga aka hanata, ta dinga ƙunƙunai, da haka suka yi waje dan Abba sun iso.
"Ke wai ko hawayen baki yi, tsakani da Allah tun safe idanunki a bushe, jiya dai kinji kuka amma yau ko hawaye, anya najlah."
"Ohhhh Rukky, kukan me zanyi, yau ranar farin ciki ce a gare Ni, wallahi dauriya nake amma dana kalla Mamie sai na ji damuwa ya kamani." take hawaye suka zubo kaɗan daga idanunta.
"Yauwa ko kefa." Cewan wata ƴar familynsu, murmushi Najlah ta yi tana kallon Abba ta yi dake tsaye cikin wasu manyan maza dan gaba ɗaya babu yara a ciki.
Wani abu ta ji ya tsaya mata a rai, sai ta rintse ido tana jin kaman ba za iya ci gaba da tafiya ba, ganin ta tsaya yasa Abba ya fara takowa a natse.
Launin kayansu iri ɗaya, sunyi ƙyau, har sun gaji da ƙyau, a gabanta ya tsaya yana kallonta, sai ƙawayen suka basu waje, lumshe ido ya yi sannan ya buɗe.
"Kinyi ƙyau sosai, wannan ƙwalliyar nawa ne Ni kaɗai, be kamata kowa ya gani ba, koma gida." Da sauri ta ɗaga idanunta ta kallesa.
"Kayan nan sun matsaki, ki koma kawai, 4:30pm za mu wuce, ku kuma jirgin 7pm ne." Sai ta ɗaga mai kai.
"Ki bar zubar min da hawaye a banza, bana so." Nan ma ta sake ɗaga mai kai sannan ya juya, itama ciki ta koma.
Da yake abokansa duk manyan mutanen ba irin rawar kai, haka suka shiga mota suka wajen suna mai shaƙiyancin ya hanasu ganin amarya.
Bece musu komai sai murmushi da yake yi.
Take kuma ya tuna can gida, yana fatan masu jere har su gama su zauna lafiya, ba tare dasu Basma sun kulasu ba..............
*************
Bassey ta yi dariya tana ƙara saita remote kan fankan sama dake aiki irin mai M.P ne, wanda yake duka sosai.
Ƙara ta ƙara na waƙar Ido kwanja tana bi, Marwa da Fauza suma suna yi suna rawa.
Mata biyar ne zaune suna cin abinci kan Dining room, idanunsu na kan su Basma, balle ita Basma da suka ɗauka matar gidan ce, dan tun safe da su zo, ta fara musu rashin kirkiri, da kyar ta barsu suka shiga part ɗin Abba suka jera kayan Kitchen, amma sai da ta caje kayansu wai kar a shiga da laya ciki.
Yanzu kuma sun fito cin abinci shine suke waka suna mai da musu habaici.
Rawa suke cikin tsari kuma a natse, amma ana zuwa wani baiti nan take Basma ta kallesu tana yi tana dalla musu harara duk kuwa da sun girmeta sosai, waƙan take bi tana nuna su da yatsa.
*"............A bugan salon kiɗan wane yaro.....ke wancan........... ba ke ba............. ta kusa dake mai ɓakin ɗan ƙwali............ tafi daga nan............. canza waje.......... ko kinsa Ni ne kike kallona....."* Aunty Rabi dake yafe da gyale ta yi saurin kau da kanta tana kai loman shinkafa da mai da yaji wanda shi aka basu.
Sun so tun a farko su yi mata tijara sai suka ga ƴan sanda uku a tsakar gidan, wanda Basma ta kawo su akan duk wanda ya mata hauka za ta miƙasu wajensu.
Wayarta ne ya hau ruri hakan yasa ta duba *Masoyi.* Tsaki ta ja tana cewa.
"Bara naje wajen wancan uban takurar." Ta faɗa cikin ɓacin rai, batasan dalili ba sai ta bi maganar Doctor Mukhtar, ta yi sadaka sannan ta dage da addu'a, lokaci guda ta fara jin yana fita mata a rai, sai me duk yanayin ɓacin ran da take ji, tana fita waje suka haɗa ido shike nan, take ta yi mai murmushi tana isa gabansa, shima murmushi ya yi tana ƙara tabbar da ƙwallin boka ya yi aiki a karo na biyu, wiyarta ya kalla wanda ke ɗauke da agogon gold mai sheƙi, take ya ji kaman ya mallaka sarƙanne.............. END.
> 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 An ɗaura Jama'a.