BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 3️⃣2

by @prettys01

> ..............shima murmushi ya yi tana ƙara tabbar da ƙwallin boka ya yi aiki a karo na biyu, wiyarta ya kalla wanda ke ɗauke da agogon gold mai sheƙi, take ya ji kaman ya mallaka sarƙanne..............

____________"Basma kullum ƙara ƙyau kike yi, gaskiya ji nake duk duniyar nan babu wanda ya kaini sa'a. Kin haɗa komai da komai, ina sonki." murmushi ta yi tana wasa da gefan gyalen jikinta.

"Sarkan nan ya zauna miki a wiya sosai, launinki sun ƙara haskaka shi." a wannan karon murmushi mugunta ta yi mai.

Dan kuwa ta gane ɗan damfare ne, a ɗan iya kwanakinsu tare, ya rabata da abubuwa masu tsaɗa wanda batasan iyakan su ba, harda motarta, da sarƙoƙi, bayan kuɗin da yake tambayar ta ita kuma ta tambaya Abba.

A yanzu ta gane komai, dan haka ta ciro glass ɗaga ajiyun rigarta, ta sanya saboda kar ta kalla cikin idanunsa ta fahimci sune rauninta.

Daga sama ta fara kallonsa har zuwa ƙasa, take kuma ta ɗaga hannunta ta wankesa da wani lafiyayyen mari. Sannan ta janyo ƙwalar rigarsa tana magana a fiffizge kamar ƴar daba.

"Bana cikin yanayi mai daɗi, da wallahi a iya yau sai na sa an ɓatar da kai, yaudarar ka ya isa, dan haka ka koma wajen duk wanda ya maka aiki ka ce ya sake..............Ni kuma ina nan ina jiranka, daga yau karka kuskura ko hanya mu sake haɗawa, banza mugu....." Ta sakesa tana son juyawa, da sauri ta kuma fuskantarsa.

"Dubeka........ Ya Salam, how ni na so ka ina cikin hankalina...... haba dan Allah, kalla kanka da ƙyau.........ba kauri sai tsayi kaman falwaya, ga ka ba wani fasali yarda kasan iyyamuri dai.........hmmmm ware." da sauri ya ɗan ja baya, ita kuma ta shige gida.

Idanunsa sun yi ja sosai, hanyar da ta bi ya zuba ma ido, sai ya girgiza kai yana cewa.

"Hmmmmm wallahi Basma sai kinyi danasanin hulakancin da kika min, zan sake shiri wanda ya fi na baya yawa, daga lokacin da kika faɗa shike nan." sai ya kaɗa kansa sannan ya bar wajen yana kallon polisawan da suka fito suna kallonsa.

Har ta wuce wani bawo dake gefen hanya a rana, sai ta dawo ta yi ƙwallo da shi, sannan ta waiwaya ko za ta hangi wani sai dai babu kowa, tsaki ta ja tana shigewa ciki.

Tana shiga masu aiki kowa ya fito daga maɓuyarsa suna murmushi, kwana biyu haka suke mata saboda faɗarta ƙaruwa yake, akan komai zai ta yi magana.

Parlourn kuwa Fauza da Marwa ne suka kallo bayan gama raye-rayen, su kuma baƙin tuni suka koma part ɗin Amarya.

Zama ta yi gefe tana cewa.

"Ina munafukan suke? Sun wani ƙwaso jiki wai jere, sai aka ce musu babu kayanne a gidan nan, bayan wahalar banza suke yi, saboda ba lallai ta yi sati biyu a gidan nan ba."

"Kin manta anan zamu nakasata kafin su zo su kwashe ta, daga nan Abba ba zai sake maganar aure ba, hmmmmmmm Wai yau Abba ke aure, Abba fa." Sai ta fashe da kuka tana jan hanci.

Rarrashinta suka hau yi, amma ta kasa shuru, dan haka suka kira number Abba, yana ɗauka Marwa ta katsesa.

"Abba......" Da sauri Basma ta amsa wayar, cikin kuka ta ce.

"Abba shike nan ka yi aure? Shike nan ka ci amanar Mom? Me yasa Abba? Yanzu wannan ba abin kunya bane.........shike nan." sai ta kashe kiran tana share hawaye.

"Raina zafi yake min sosai, amma babu damuwa Allah ya kaimu zuwa dare." da haka ta kalla part ɗin Abba sai ta yi dariya.........

***************

*Al-hassan*

Rintse ido ya yi da sauri yana girgiza kai, a hankali bakinsa ke furta.

"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un! Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un!!." sai ya buɗe idanunsa yana sake mai da idanunsa kan wayarsa dake haska wani kasuwa da aka yi gobara, a ƙalla mutane 15 wutar ta ci, ga shaguna sama da 50 sun harda kayan ciki, mutane sai kuka suke gwanin tausayi, gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, damuwa ta gama ratsa jijiyoyin sa, har ga Allah baya son ganin mutane cikin walaha.

A daren jiya komai ya faru, in da gashi yau da safe ƴan jaridu sun koma wajen, ana ɗauka, talakawa sunyi asara sosai, dan haka suke mutane roƙan da manyan ƙasar nan su duba mutanen da tsautsayi ya faɗa musu.

Har account number aka sa ga duk mai niyyar taimako ya sa, da sauri ya ɗauki number, sannan ya musu trnasfer 500thounsand.

Wayar ya aje gefe yana lumshe ido, gobarar daga Allah ne, dan kuwa an ce wayar huta ce silar tashin hutan, iska ya furzar yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali.

*Al-hussain* Gaba ɗaya rayuwarsa ta sauya, hankalinsa kullum yana kan aiki, be da wani taƙamaiman lokacin hutu.

Operating system yake yi cikin ƙwarewa, yana yi yana watsa peenut cikin bakinsa.

"Yes.....Yes........" ya faɗa yana dukan desk ɗin ɗakin.

Ɗakin duhune ta ko ina, fuskarsa dake washe da annuri, shi kaɗai kake iya hange da taimakon hasken dake screen ɗin computer.

Murmushi ya sake yi sannan ya rufe system, wayarsa ya ɗauka ya kira wata number, wanda bugu biyu ya yi aka ɗauka.

"Boss aiki ya yi dai-dai, yanzu mutanen da zasu kwasa ƴam mata sun isa wajen harƙallan, sai dai an samu matsala."

"Wani kala?." ya faɗa yana mirza ƴatsun hannunsa a cikin duhun ɗakin.

"A list mutane 2 ne masu siyan yaran amma yanzu fararen fata huɗu ne suka so daga mabanbanta jirage."

"Na sani, gani nan zuwa." da haka ya tashi ya kunna hasken ɗakin, lumshe ido ya yi ya buɗe yana kallon uban kayayyakin aikinsa da suka cika ko ina na ɗakin.

Toilet ya shiga, be ɗau dogon lokaci ba ya fito ɗaure da towel, ruwa na bin jikinsa yana gangarawa zuwa ƙasa.

A gaban mirrow ya tsaya ya ƙare ma jikinsa kallo, a kwana biyun nan da yake traning jikinsa ya ƙara murɗewa.

Wayarsa da ke ruru ya kalla, sunan Senator Tumɓa ya fito raɗau.

Ɗauka ya yi yana sa wa a speaker.

"Nan da 10mnt za mu isa wajen."

"Okay." Shi kawai ya ce yana katse kiran.....................

******************

"Ka taimaka min kaji, so nake ka yi mata aikin da ganina kawai ta yi za ta ruɗe, bansan ka haukatar da ita yanzu, amma ya zama Ni zan dinga ba ta umarni akan komai." Anas ya kai nan yana kallon Boka dake ta zane-zane a ƙasa yana sakewa.

A hankali kuma ya kallesa ya ce.

"Yarinyar duk iskancinta tana kiyaye sallah, tana da hannun ƙyauta, sai dai in tasan wata ai batasan wata ba........aiki zai yi amma yana da mugun wahala, za ka iya?." Cikin sauri ya ɗaga kai yana haɗawa da.

"Ko menene zan yi indai akan tane." Ƴar dariyar boka ya bushe da shi, sai kuma ya yi tsit yana karanto wasu kalamai wanda Anas ya rasa gane me yake cewa.

"Na farko Jariri ɗanyen haihuwa za ka kawo shi nan, na biyu tsohuwar Tunkiya wacce ba ta gani, na uku, za ka sadu da budurwar mace, ka tabbatar jinin dake ɗiga daga jikinta yana sauka a jikin gyallanne." shuru Anas ya yi yana maimaita kalaman sa.

"Shike nan, zuwa gobe zan kawo komai." Boka ya jinjina mai yana baki wani farin yadi, ya amsa hankali kwance.

Da haka Anas ya tashi ya fice, yana mai jin aikin da sauƙi akan wasu da yake yi.............

*KATSINA STATE*

_Kasuwar ƙwari_

Sai dai muce innalillah wa'inna ilaiyi raji'un, domin kuwa hutan daren jiya ba ƙaramin gyara ya yi ba, komai na shaguna sun ƙone, wasu har kwanon sama ya narƙe, shago ɗaya ne aka iske kayan shagon rabi suna nan lafiya lau, da haka aka shiga ma jama'a jajen abin da ya faru.

Sannan shugaban kasa Muhammad Babangida Shamiki ya aiko manyan mutane dan taimaka masu, sai dai duk abin da suka yi ma mutanen zaginsu ake yi, gaba ɗaya mutane sun tsana jami'ar *National Unity & Justice Party (NUJP)* basu da wani buri sai ganin Senator Tumɓa ya hau mulki.

Jama'a duk suna zazzauna ana ta mai da zance, wasu da shagunan su ya ƙone suka kasa ɗaukan tawakkali suna kadajen asibiti dan suma suka dinga yi.

Mutane take hankalinsu ya koma kan motocin biyu da suka yi parking, take fuskokin kowa ya washe da farin ciki ganin Hasken Al'umma ya fito cikin farin jallabiya mai sheƙi da haske wato *Senator Tumɓa*.

Gefansa securities ne biyar ne suna zagaye da shi ganin mutane sun nufosa.

Fuskarsa cikin damuwa ya fara musu jaje, sannan aka zagaya da shi ko ina ya duba, cikin alhini ya kalla jama'a ya ce.

"Dan Allah ku kar wani ɗan jarida ya ɗauka komai, bana so, ba komai ne ake watsawa ba, dan Allah masu wayoyi duk ku kashe, na roƙe ku dan Allah." Da haka ya ci gaba da magana da shuwagabannin kasuwan.

Mutane kuma sai suka ji sun ƙara sonsa sosai.

Abinda ba su sani ba shine, Senator Tumɓa shine ya sa Black Dragon da a ƙona rabin shagunan kasuwar, bayan sun kwashe komai na ciki, shago guda ne suka bar kaya, sannan mutanen da suka mutu, sune suka kashe su, babban abun ma shi kansa Senator Tumɓa ya zo da wani ɗan jarida, wanda ke ɗaukan komai ya watsa a duniya, bayan ya gyara hoton da sanya kalamai masu hikama.

"Mutanan nan da suka rasa dukiyoyinsu, na umarci da tura list ɗin zuwa office ɗina, zan tura zuwa gaba domin kuwa babban aiki ne ya kamata gommati ta yi muku, hatta Gomnan karin nan zan zauna da shi, idan har Tumɓa ba raye to allumma zasu samu ƴanci." da haka ya musu ƙyautan kuɗi sannan ya bar wajen.

Mutane ne suka fara yabonsa cikin nishaɗi, suna ta samai albarka.

Yana cikin mota ya yi murmushi sannan ya kira wani number.

"Ina so ka watsa video nan, cikin ɗan lokaci, za ka ji alert." da haka ya kashe kiran, yana mai umarta su nufa filin jirgin sama, domin kuwa nan da 2h za'a yi babban harƙalla a gidan Black Dragon dake gefan Kogi............

*******************

A kwanakin nan da aka sha shagali, babu ranar da take jin babu daɗi irin yau, balle a yanzu da ta kasa tsayuwa da ƙafafunta saboda wani irin nauyi da suka mata, ba kuka take ba, amma hawaye ne ɗaya ke bin ɗaya, haka kuma jikinta kaman ba nata ba.

"Amarya ɗaure ki tashi, kowa ke yake jira, wannan yanayin naki yasa Mamie ta fara kuka." cewan Yayar Mahaifinta.

Rintse ido Najlah ta yi tana karanto addu'oi, da ƙyar ta iya miƙewa, sannan ta ɗan fito da fuskarta kaɗan daga cikin Hijab, take idanunta da suka sauya launi suka sauka cikin na Mamie dake ta hawaye tana gogewa.

Da wani irin gudu ta nufeta tare da faɗa wa jikinta, sai ta fashe da kuka.

Mamie ma ta sai kuka, kuka suke irin mai tsayawa a rai, kuka ne wanda kowanne ke yi tsakani da Allah.

Barsu aka yi akan su gama kukan, sai dai ganin basu da niyyar dena kukan yasa, da ƙyar aka raba jikinsu ana mai fita da Najlah wacce ke ta tirjewa.

Dangin Alhaji Mubarak da suka zo ɗaukanta duk sai ta basu tausayi, saboda akwai ƙuruciya a tare da ita sosai.

Mota biyu ne wanda Abba ya turo daga nan za su je family house na ɗin sa sai a wuce filin jirgi.

Najlah ba'a iya ganin komai na jikinsa, dan kuwa babban hijab ne jikinta army green.

Haka aka sanya cikin mota tana ta kuka, bayan sallama da Yayansu da Adam, suna harda hawayensu.

Rukky ce gefanta tana ta rarrashinta, haka ƴan uwan Abba suka shiga mota da mata biyu familyn Najla suka wuce.

Dama mata biyar suna Abuja gidan ta.

Najlah ji take kaman ta ce ta fasa auran, ko da wasa ba ta yi tunanin haka ake ji ba, rabuwa da iyaye babu daɗi.

Ajiyan zuciya ta sauke tana ƙara matse hannun Rukky a jikinta kamar mage, Rukky ta yi murmushin jin daɗi ganin ta dena kuka.

A bakin babban get ɗin gidan su Abba motocin suka yi parking, tare da danna horn, nan take me gadi ya wage musu ƙofa, suka shiga ciki, mutane ne cike ƴan biki, take duk aka tsatstsaya, kowa fatansa ganin matar Abba, duk da kuwa da yawa sun san Najlah, amma baƙin da suka zo ba su santa ba, kowa na mamarin ganin matar Abba mai Capacity yake............✍️ END. ***

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ ***

_TAP THIS LINK TO JOIN MY TEAM GROUP👇_ ***

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️```

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S✍️* *★BUDURWAR ABBAN MU★* _by PRETTY SK CE 😍✍️_

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing na jaruman Shidoria*👇

```1. BUDURWAR ABBANMU Pretty Sk.``` ```2. WASAN KADDARA Asmeetah Writter.``` ```3. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal.``` ```4. KURUCIYA Fatima Bintu Hussain.``` ```5.MABANBANTAN ZUKATA Maryam Star.``` ```6. ƘADDARAR MASOYA Umulkhairy Hashim Abo.``` ```7. GARWASHI Hafiza Amanar Ameey Laylerh.``` ```8. YARINTA Amanar Ta Batulu.``` ```9. BOYAYYEN SIRRI Amanar Shidoria Writter.``` ```10. DAGA BAYA Sha'awanatu Farouk Diggi.```

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.