BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 3️⃣3

by @prettys01

> ..........kowa fatansa ganin matar Abba, duk da kuwa da yawa sun san Najlah, amma baƙin da suka zo ba su santa ba, kowa na mamarin ganin matar Abba mai Capacity yake............

*Abba*

Tun ƙarfe 5pm ya isa Abuja, Driver ya ɗauke sa har gida, bayan sunyi sallama da abokansa biyu da suka je ɗaurin aure a hankali ya fito daga mota cikin wani Kaftan Mai shegen tsaɗa, sai zuba ƙamshi yake, ai ma'aikatan gidan suka nufesa suna mai Barka da zuwa.

"Alhajin Allah Barka da zuwa, Ango mijin Aunty Amarya, Uba ga Hajiya Marwa, Basma da Ƴar auta, Alhaji mai ɗunbun nasara." Murmushi ya yi yana fiddo kuɗi a ajiyunsa ya fara rarraba musu, sukuma take suka fara jera mai addu'o.

"Sunanta Aunty Najlah." Ya faɗa yana murmushi, take suka fara.

"Alhaji mijin Aunty Najlah." Abba murmushi yake yi, take ya ji sun yi shuru suna daddarewa kowa na kama aikin da ya saki.

Ko be kallaba yasan Madam ce ta leƙo, ilai yana juyawa ya hangi Basma tsaye ta jingina da main door tana dalla ma ma'aikatan harara.

A hankali kuma ta kalla Abba, sai ta ji wani abu ya tsaya mata a rai, wai yanzu Mahaifinsu shine ya yaudara Mom, ya ƙara aure, bayan shi da kansa ya mata alƙawarin rayuwa da ita ɗaya.

Tasan da Mom na raye ba ƙaramin rigima za'a yi ba akan auren nan, dan a dake take sai gashi su sun kasa komai, har suka bari igiya uku na wata ya hau kan Abba, yanzu wata tana da kusanci da shi fiye da su ƴaƴansa, wata tana da ikon raɓarsa, har ma ta ya yi soyayya da ita......

Take ƙirjinta ya fara dukan uku-uku, da sauri ta juya baya ta koma ciki, Abba ya girgiza kai yana bin bayanta.

Be iske kowa a parlour ba sai Aisha da take kwashe kayan Dining room.

Gaishesa ta yi tana mai Allah ya sanya alheri.

"Ameen A'isha na gode, menene aka dafa a gidan?."

"Farar shinkafa ne kawai Hajiya Basma ta ce a dafa, ta ce kowa yau ya ci garau-garau da latas." Mamakine ya kamasa.

"Yauzu mai da yaji aka ba ɓakin Amarya?." ta tsugunnar da kai ƙasa.

"Eh Alhaji."

"Hmmm jeki." Da haka ya juya ya fita, be dawo gidan ba sai da wasu manyan ledoji guda huɗu, ya san ana za su kwana kuma wasu na zuwa hakasan yasa ya yi take-away guda 20 ga kuma gasassun kaji.

Da kansa ya nufa part ɗin sa, ya knocking, Jim kaɗan sai aka buɗe, matar na ganinsa ta washe baki baki tana murmushi.

Gaisheta ya yi saboda yasan ta girmesa, ya miƙa mata ledojin yana cewa.

"Dan Allah ku ya ƙuri da abinda Basma ta yi, aka baku mai da yaji, ga wannan idan be isa ba, zan ƙaro muku zuwa dare."

"Wallahi babu komai, duk haka yaran suke ai, Allah ya saka da alheri." Da haka ya juya baya, ita kuma ta rufe ƙofar harda murza key.

Tana shiga ta aje musu abinci tana yabon kirkin Abba.

"Hmmm dan besan harda ƴan sanda ta kawo mana ba, uhm daɗin abun ma Najlah ce, robar wando ce daidai take da ƙuƙun duk marasa kunya, balle wannan ɓakar cikinsu, waiiii duk ta fi jaraba." Da haka suka sauya hirar.

Leda guda na kayan Tea ne da manyan slize bread har da butter, leda guda na kaji da balango, sai babban leda na abinci fried chicken rice, ta yi yellow Sosai saboda spices ga ƙamshi dake tashi, a ido kawai abincin kasan zai yi daɗi, ai take kowacce ta ɗau roba ɗaya ta hau ci, sai dai sun cika cikinsu da abinci, haka Bamsa ta sa aka shaƙe ma kowa babban Plate da abinci, ga uban koren latas daka zuba, yarda kasan Akuya zai ci, dan ma yajin akwai daɗi, haka suka dinga tusa abincin nan, sai da suka cinye.

"Kai har na cikina ya cika sosai, ga abinci mai rai da lafiya amma babu halin ci, saboda wancan ƴar mai kama da ƴar Habashawa." dariya suka yi sai wata tace.

"Hmm tana da ƙyau halin ne dai kaman na karufan farko."

"Aunty Jummai amma wa'innan zabga-zabga ne ƴaƴansa? Kai ai shi ba wani babba bane sosai na gaji."

"Rakiya irin masu auren wuri ne nake gani, kuma yaran yanzu girman agric garesu, ku dai kalla Najlah ita kanta, 19yrs amma yarda kasan 25yrs take." Sai a lokacin Aunty Jummai ta ce.

"Ba dole ba yarinya ta zama riƙaƙƙiyar soja, duk ta buɗe, wa ya yi tunanin za ta yi wannan jikin? Yarinyar da kasan kaman ka wure."

"Sosai fa, haka take da kaman wannan mai ɓakin ɗankwalin." suka kwashe da dariya, mai baƙin ɗankwali wato Aunty Hanafiyya ta yi dariya tana cewa.

"Tubarkallah, Eheyy." Harda fari da ido, gaba ɗaya ba ta da auki gaba ɗaya a fige take..............

*************

"Taka a hankali." ta ji an furta a lokacin da ta tabbatar sun sanya ƙafafunsu cikin babban parlourn, ta jin yarda mutane ke ta rangaɗa guɗa.

A kan wani lallausan carpet aka zaunar da ita, ta zauna da ƙyau tana jin fargaban da take ji ya rabu, mutane biyun da suke gefanta, ɗaya yayar Mamie ce, ɗaya kuma babbar yarinyar Ƙanwar mahaifinta.

Tana jin hirar da ake yi, tare da mallaka ma danginsa ita, suna ba da ita amana, su kuma suna roƙan Allah ya basu ikon riƙe amana.

"Muna son ganin fuskar Amarya." Cewan wata budurwa cikin zumuɗi.

Aneesat da Suhailat sun zo bikin amma ɗayar ba ta zo ba, Aneesa ta ce.

"Murja fuskar Amaryar Abban mu yana da tsaɗa, ku biya sai ku gani."

"Na biya dubu ɗari." Cewar wata Hajiya dake zaune.

"Ah ya yi kaɗan Hajiya Turai."

"Dubu ɗari biyar." Cewan Aunty Shamsiyya. Aneesa ta yi murmushi.

"Yanzu ace Amarsun Alhaji Mubarak, za ku ga fuskarta a dubu ɗari biyar, haba Auntie's, Najlah ce gimbiyar ƙyawawa." Take aka buɗe sabon chapter yarda kasan suna hall, Aneesa dama ta ƙware wajen surutu, haka aka haɗa ma amarya kuɗi milayan ɗaya da rabi, kuɗi cash, aka sanya mata a jikinta, sannan aka buɗe mata fuska.

Ya Allahhhhh, kar ku harda yake guɗa ana yana watsa mata kuɗi, tare da sanya wani sauti mai sanyi, wasu kuma turaruka aka dinga fesa mata masu daɗi.

Ita kanta Najlah ba ta san ranta ya yi fes ba har da ƴar dariya, balle da take kusa da Aneesa dama tun can suna mutumci sosai.

Kowa video yake ma amarya ana rububin sanyawa a status.

Aneesa ma ɗaurawa ta yi tana tagging Basma da Marwa, sannan ta rubuta *Alhamdulillah, Ga Amaryar Abban mu, Allah ya kawo zuri'a ɗayyiba.* da haka ta yi posting short video na fuskar Najlah inda take murmushi.

Aneesa mai da hankalinta akan amarya da ake nufan part by part Dan gaisawa da manyan dangin miji.

Zama ta yi gefe tana jin babu daɗi, ace bikin Abba guda su Bassey ba su zo ba, ko da ta tambaya Abba yau da safe.

"Aneesa kema kinsan halinsu ai, suna gida." Shi yasa ta yi tagging nash suga amaryar dake tafe.

Sai dai jin wayarta na ringing yasa ta duba, ɗan zaro ido ta yi tana ɗauka kiran *Sis Bassey.*

Kafin ta yi magana, ta ji muryan Basma ciki ɓaci rai da masifa ta tari numfashin ta.

"ANEESA! ANEESAH!! ANEESAH!!!........."

******

Su uku ne zaune a ɗakinsu kaman masu zaman makoki, sunyi shiru kowa na saƙar zuci, jin shurun ya yi yawa yasa Bassey ta miƙe ta kunna tv, sai dai basa fahimtar komai.

Marwa ta sake jan tsaki wanda daga zamanta zuwa yanzu ta yi yafi a ƙirga.

"Yanzu nan ɗan lokaci wata ƴar iska za ta shigo gidan nan."

"Ku dena damun kanku da yawa, da ƙafafunta za ta bar gidan nan." Cewan Fauza, sai Bassey ta ɗau wayarta, dama data na kunne.

Saƙon Aneesa ne a farko, dan haka ta latsa status ɗin, take idanunta suka yi ƙyaƙƙyawan gani, amma saboda masifa da kishi sai ta ga kaman wata halitta take kallo kamar ba mutum ba.

"Ga Bazawarar Abba, kun ganta, kutumuar ubancan." Ta faɗa tana kallon yarda fuskar Najlah ke sheƙi, ta yi murmushi har dimple ɗin ta suna lotsewa.

Suma kallonta suka yi, ba su taɓa tunanin Bazawarar Abba tana da ƙyau ba, sun ba da asiri ta yi mai ya so ta, sai gashi fuskarta kaɗai ta tafi da imanin su.

"Ah lallai kam, hasken tane ko bleaching?."

"Fauza taya zamu gane, bayan flitter aka sanya."

Da haka Basma ta kira Aneesa direct.

"Aneesa Hmmm kin ƙyauta, yanzu ku dan ana ma Mom Kishiya shine kike ta wannan abun, tabbas Mom ta yi gaskiya da ta ce baku sonta....wallahi na yarda........" Da sauri Aneesa ta katseta ta cikin wayar.

"Wani irin magana kike yi haka? Ina jin Mom Allah ya jiƙanta ta jima ta rasuwa......"

"Koma menene, a wajenku me ta rasu ba'a wajen mu ba.........ku da kuke murna akan auren nan, ku da kanku za ku zo kwasan gawarta ƴar iskan Bazawarar." Dariyar shaƙiyanci Aneesa ta yi dan dama ba ta jiran ta kwana.

"Ke Basma karki manta sati biyu na baki, dan haka na garme miki, yarda banza iya ɗaga ma Aunty Marwa murya ba, haka bazan yarda ke kimin ba, ki sarrafa harshenki akai na........da kuma kine cewa bazarawa, to wallahi Najlah sa'ar ki ce, budurwa ce shakaf, ƙyaƙyƙyawa mai cikan diri.........."

"a'uzubillahi minal shaidannil rajieen, Aneesa Allah ya isa, idan har abin farin ciki ne, ya sa Dad (General) shima ya yi ma Aunty (Mahaifiyar Aneesa) kishiya......" da sauri Marwa ta ce.

"A'a ai ita kanta Allah ya sa mijinki ya ƙara aure anan za ki fahimci halin da muke ciki." take Aneesa ta yi sanyi, daban kalaman Marwa ba sai dan tuna su ɗin ƴan uwantane.

"Ina mai baku haƙuri, Allah ya sassauta muku zuciyoyinku." Da haka ta kashe kiran.

"Munafuka ashe dai kishin babu daɗi." Cewan Marwa tana komawa ta zauna.

"Kice babban shagali dangin Abba suke yi, hmmm Ya Allah duk wanda yake da sa hannu a kan auren Abba, ka ƙwaso fitinar duniya har da na lahira ka ɗaura musu, idan ba su da kishiya kasa mazajensu su yi musu, idan su huɗu ne a wajen mijin kasa a sake ɗaya." A tare suka ce *Ameen.*

********

Zaune suke huɗu duk fararen fata, dan daga gani ba ƴan Nigeria bane, Gefe guda Black Dragon na zaune cikin shigarsa na baƙin kaya kamar kullum, ya sanya mask a fuskarsa, da turenci suke magana sakamakon turawan ba su iya Hausa ba.

"Plus-sized women are more enjoyable in this business. I'd like you to start selecting them for me-at least 30." sai ya lanƙwasa kansa gefen dama da hagu wanda ya zama mai ɗabi'a ya ce.

"We currently have 120 girls on the ground. I won't sell each for 1 million-no, 2 million. As for the ones you want whose wombs will be removed, they are kept separately. I personally examined each of them to confirm they can conceive, so their wombs are in perfect condition." murmushi baturen ya yi alaman yaji daɗin maganarsa.

"Black Dragon, doing business with you is always a pleasure. I'll come visit you again." ya suna sake gaisawa da juna.

"No problem… but what brings you here, Alexander?" ya kalla na gefan wannan.

"Valuable goods are about to be delivered into the hands of Ubandaba Israel Ustad. You know his nature-he won't sell anything until he distributes them first. That's why I want them seized by force. I trust you, Black Dragon. If those goods get into my hands, I'll reward you with 30 million." He nodded." Senator Tumɓa ya yi murmushi duk be gane meke ake nufi da Kaya masu daraja ba.

"The deal is almost complete. What remains is to finalize the medicines-they are ready. I've sent the money. Continue gathering the defective drugs for me."

Da haka aka kammala komai, ya rarraba musu Yaran da ya sace, aka tafi da su wasu ƙasashen, sannan ya amsa kayan da aka kawo mai.

Bayan duk sun watse sai Senator Tumɓa ya buɗe baki ya ce.

"Ban gane wasu kaya mai daraja yake nufi ba." A hankali ya ce.

"Hodar iblis da Hausa, da turenci Cocaine."

"Ohhhh I understand sosai, gaskiya working with you yana kawo great progress." be ce komai ba suka miƙe tare suna ɗan takawa, sai kuma ya tsaya yana kallon Senator Tumɓa.

"Next target na shine this - zan kai attacking rayuwarka, so that za a kwantar da kai a hospital. A lokacin zaka samu sympathy sosai from people."

"Wow wow wow Black Dragon, ka haɗu sosai… I really like you." ya yi ƙoƙarin rungumesa, da sauri ya tsaya ganin irin kallon da Black Dragon take mai.

"Ka tafi zan zaka samu kirana."

"Ok." Da haka ya mai sallama yana barin wajen, shi kuma Black Dragon ya sake lanƙwasa wiyansa sannan ya ci gaba da tafiya.

********

Daga Kaduna International Airport zuwa Nnamdi Azikiwe International Airport - Abuja, tafiyar 50mnt ne, daga nan motoci suka ƙwashe su sai wani tsantsararren gidan.

Parking aka yi wanda Najlah ta buɗe idanunta dan tana da tabbacin sun iso, sun iso gidan aurenta, an kawo ta gidan da za ta rayu.

Motar aka buɗe ana ce mata.

"Amarya fito a hankali." Ba musu ta matsa daga jikin Rukky ta fita, tana mai jan hijab ya rufe mata fuska.

Rukky ma fita ta yi tana tana ƙarema gidan kallo, duk kuwa da yamma ta yi.

A hankali Najlah ke taka interlock ɗin da ya mamaye tsakar gidan.

Ana zuwa daidai ƙofar shiga matan suka fara guɗa, sannan suka buɗe suna ce ta shiga da ƙafar dama.

Daman ta fara sanyawa a cikin babban parlourn, sannan na hagu, a natse suke tafiyan, ita dai idanunta suna rufe, har aka shiga da ita wani bangaren, sannan aka sake shiga da ita bedroom, Wanda komai na ciki Abba ne ya yi.

A kan gado aka zaunar da ita, sai ta ji wani abu ya tokare mata zuciya, take wasu siraran hawaye suka gangaro daga cikin idanunta.

Da yake a nan duk za su kwana hakan yasa ta samu sakewa, amma har lokacin tana zaune kan gado, a lokacin aka fara kiraye-kirayen sallar magrib.

Ɗaya daga cikin Familyn Abba, suka umarci ta tashi ta yi wanka, ba musu ta tashi ta shiga restroom.

Wanka ta yi tana mai jin daɗin ruwan zafin na ratsa mata jiki, bayan ta fito sai ta iske babu kowa a ɗakin, murmushi ta yi tana kallon kayan dake kan gadon.

Doguwar riga ce mara nauyi shi ta zura, sai dogon hijabi orange, sai a lokacin ta ƙura ma ɗakin ido, komai na ci pink and white ne best colour ɗin ta, lumshe ido ta yi tana jin soyayyar Abba na ƙara ratsa ta, dan kuwa kusan komai irin na ɗakinta ya yi mata, dan yana gani idan za su yi Video call.

Inda aka shimfiɗa mata dadduma anan ta yi sallar, tana idarwa barci ya ɗauke ta, sai kiran sallar isha'i ya tashe ta, sai ta tashi ta sake alwala, sannan ta gabatar da sallar.

Tana idarwa ta miƙe ta fita Parlour inda take jin shewarsu.

Alai nan ta iskesu wasu na sallah wasu na na kallo a tv sai dariya suke.

"Amarya zauna ki ci abinci." cewan Aunty Hanafiyya sai ta girgiza kai tana zama gefan Rukky.

"Tun safe ba ki sake cin komai ba, Please ki ci." sai ta kalla Rukky ta mata hararan wasa.

"Aunty Hanafiyya ban iya cin abinci mai nauyi da daddare ba.". cewan Najlah tana tura baki sai Aunty Rakiya ta ce.

"Ke bansan iskanci, ba filin sojoji kike ba, tashi ki ci abinci." Sai Aunty Rumasa'u ƴar uwan Abba ta ce.

"A'a ƙyaleta, ƴata me kike so? Ga kayan tea, ga chincin ko me kike so?"

"Uhmmm Aunty indomie nake so." Da sauri Aunty Jummai ta ce.

"Duk kayanki suna store, babu Kitchen a nan, dan haka a can muka sanya wasu, wasu na kasan gado, Kitchen din ma da kaya mai yawa, masu girki suka tayamu sanya su, idan indomie kike so bara a kira mai aiki ta dafa miki." Sai ta jinjina kai.

"Yau naga jalala, su Basma ba su san mun zo bane? Ina zuwa zan ci uban yaran nan, ko gaishe da Auntynsu ai sun zo yi idan mu basa ganin girman mu......Bara na kirasu, in yaso ɗaya ta girka miki indomie." Da ido suka raka Aunty Rumasa'u har ta fice tana ta faɗa.

Murmushi Najlah ta yi a ranta tana cewa

'Tab sune za su min girki lallai kam.'

Aunty Rumasa'u part din su Basma ta fara bugawa da ƙarfi tana kiran sunayensu.

Buɗe ƙofar aka yi, take idanunta suka shiga cikin na Marwa dake tsaye.

Marwa murmushi ta yi a ranta tana cewa. 'Waya kawo wannan fitinanniyar matar.' tasan Aunty Rumasa'u ba ta da wasa, ita ce autan su Abba, masifafiya ce sosai.

"Na zo gaishe da kune tunda ku ba kusan meke muku ciwo ba, ina sauran suke?." Ta faɗa tana shiga cikin Parlour.

Duk suna zazzaune, Basma na latsa waya, Fauza kuma kallo take a tv.

Suna ganinta suka haɗe fuska suna gaisheta kaman an musu dole.

Aunty Rumasa'u ba tasan suna yi ba, faɗa ta fara musu kamar za ta ara baki, inda take shiga ba nan take fita ba.

"Ku tashi kuje gaishe da sauran, da Matar Abba." babu wacce ta iya musu saboda duk masifar da suke fama da shi, ta shanye su.

Haka suka miƙe suna ta muzurai, balle Bamsa.

"Basma zo ki bugan, hmmmm ashe ba za ku sauya ba, har yanzu kuma nan jiya eyau, kunji haushi, Fauza buɗe ku shiga mana." ta kai nan tana huci.

Fauza ta bude kofar tana shiga, haka suka bi bayanta ba tare da sunyi sallama ba.

Tsayawa suka yi har dai Aunty Rumasa'u ta shigo ta ce.

"Ku rage tsayi ku gaida kowa." Kaman za su fashe suka koma.

Gaishesu suka yi ciki-ciki, wasu suka amsa wasu suka bar musu kayansu dan ba su ji ba, Da sauri suka miƙe suna shirin wuce.

"Ku dawo ku gaishe da Auntyn ku, gata nan." Ta faɗa tana nuna Najla.

Su ba su lura da ita ba, dan basu kalla kowa ba.

A hankali suka juya suna mai kallon Najlah dake zaune gefan Rukky, itama su take kallo a ranta tana cewa 'Ashe ma yarane sosai.' Wani mugun kallo suka watsa mata, suna isa kusa da ita, a tsaye suka tsaya dan harga Allah ba za su iya tsugunna ma yarinyar nan ba. Sun kasa magana haka sun kasa tsugunnawa, ƙare mata kallo suke yi, duk hasken da Marwa ke da shi dai suka ga sun koma baƙaƙe saboda Hasken farar Najlah, fuskarta sai annuri take, ga hasken jikan ɗin sai ya ƙara mata hasken sosai, ga ta yarinya sosai.

Itaa dai Basma data gaisheta ta ƙwammaci komai ya faru.

"Shuwagabannin marasa kunya, kun kasa tsugunnawa kenan, karku kai ni ƙarshe, maza a gaisheta cikin girmama..............kuyi sauri, Basma za ki tafasa ma Aunty Najlah indomie tana jin yunwa ta kasa cin rice.........."............✍️ END ***

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_ ***

_TAP THIS LINK TO JOIN MY TEAM GROUP👇_ ***

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️```

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*THE SHIDORIA WRITER'S✍️* *★BUDURWAR ABBAN MU★* _by PRETTY SK CE 😍✍️_

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing na jaruman Shidoria*👇

```1. BUDURWAR ABBANMU Pretty Sk.``` ```2. WASAN KADDARA Asmeetah Writter.``` ```3. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal.``` ```4. KURUCIYA Fatima Bintu Hussain.``` ```5.MABANBANTAN ZUKATA Maryam Star.``` ```6. ƘADDARAR MASOYA Umulkhairy Hashim Abo.``` ```7. GARWASHI Hafiza Amanar Ameey Laylerh.``` ```8. YARINTA Amanar Ta Batulu.``` ```9. BOYAYYEN SIRRI Amanar Shidoria Writter.``` ```10. DAGA BAYA Sha'awanatu Farouk Diggi.```

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.