PAGE 3️⃣4
by @prettys01
> "Shuwagabannin marasa kunya, kun kasa tsugunnawa kenan, karku kai ni ƙarshe, maza a gaisheta cikin girmama..............kuyi sauri, Basma za ki tafasa ma Aunty Najlah indomie tana jin yunwa ta kasa cin rice.........."...........
"Aunty sun gaishe damu duka ai." Cewan Najlah tana ƙare musu kallo daga sama har ƙasa, lokaci guda ta mai da idanunta ka tv tana mamakin rashin kunyarsu.
"Sai sun gaisheki fa, ko na sauke musu rashin kirkiri yanzu nan, kuna tsaye kenan?." Ta kuma fara ranta yana soma ɓaci.
Marwa ajiyan zuciya ta sauke, ta kalla Aunty Rumasa'u ta ce.
"Wallahi Aunty ba zan iya ba, girmama na gaba da mu aka koya mana, ba girmama na ƙasa da mu ba." da haka ta juya ta bar ɗakin duk suka bi ta ido, sai Basma ta ce.
"Ta baki amsa, dama rashin kunya tun tuni aka ce gadonsa muka yi, mun yi miki ƙoƙari da muka zo muka gaishe da ku, harda ita cikin jumla..........hmmm maganar dafa Noodle kuwa ki ma barta dan wallahi ko wacece a nan ba zanyi mata balle wannan abun ." Ta nuna Najlah da hannu.
Wani lafiyayyen mari Aunty Rumasa'u ta wanke fuskar Basma da shi, tana karkaɗa mata yatsa alamun gargaɗi.
"Sarai kinsan bana ɗaukan iskacin banza da wofi, ki kama kanki." Basma ta cire hannunta kan fuskarta, ta kalla Najlah.
"Wallahi Bashi, ko karen hauka ya cije Ni bazan rama a kan ki ba, amma ita wannan mayyar hmmmm." ta yi ƙwafa tana nufan, ƙofa a daidai nan ta tsaya sai ta juyo ta kalla Najlah da hankalinta ke kan tv, ƙwafa ta yi tana banko musu ƙofa.
Saroro Aunty Rumasa'u ta sanya tana tafa hannu, sai Fauza dake tsaye ta yi wani shu'umin murmushi.
"Aunty Rumasa'u kiyaƙuri, Aunty Ina wuni ya hanya? Fatan kun iso lafiya?." Ta faɗa tana tsugunnawa gaban Najlah, da sauri Najlah ta ɗaga tana murmushi.
" Alhamdulillah Fauza, na gode sosai." murmushi suka yi ma juna.
"Bara na dafa miki indomie ɗin."
"A'a karki damu Abba zai aiko min da shi." sai ta sake musu sallama ta fita tabar Aunty Rumasa'u na ta masifa.
A babban parlourn ta iske su tsatstsaye sai faman jijjiga suke yi, za su iya rantse wa da Allah babu wacce ta taɓa musu irin rashin Mutumci kamar Aunty Rumasa'u.
"Hmmm na ga zallar rashin wayonku..........No wonder Mom take yawan cewa na fiki aiki da hankali, ku sani nuna mata ƙiyayya tun farko shi zai ta mu rushe duk wani target ɗin mu akanta."
"Fauza kenan, ai na rantse da Allah ko daidai da ƙwayar zarra ba zan nuna ina sonta ba." Cewan Basma tana nufan stairs.
Gaba ɗaya sai idanunsu suka koma kan main door da ake shigowa.
Abba ne riƙe da wata leda ya shigo yana murmushi, yana ganinsu ya ƙara faɗaɗa murmushin.
"Fauza kira min Auntyn ku." Da haka ya zauna yana cire hular kansa.
Bassey gyara tsayuwa ta yi, sai Marwa ta isa kusa da ita ta tsaya.
Fauza umarninsa ta bi, inda ta shiga wancan part ɗin ta kira Aunty Najlah.
Fauza ta fito sai ta shiga Kitchen Dan ɗaukan abinci.
A hankali aka buɗe ƙofar, hakan yasa Abba mai da hankalinsa kan ƙofar, lumshe ido ya yi ganin Najlah ta fito tana tafiya a natse, ga wani kunya da take ji sai ya ƙara mata ƙyau.
Da sauri Abba ya miƙe ya isa gabanta, hannunta ya riƙe yana taimaka mata ta zauna.
"Kunya na miki ƙyau." ya faɗa yana zama gefanta amma ba dab ba.
Sai rufe fuskarta da tafukan hannayenta wanda suka ta sheƙi.
"Ya Salam, wannan hannun ai sai ya sa zuciyata ta buga." ya faɗa yana kallon hannun nata.
"Ga abinci, ki cinye duka dan Allah, zan wuce inda zan kwanta." fuskar ta buɗe sai ta amsa ledar.
"Uhmmm yanzu tafiya za ka yi?." Ya ɗaga mata kai.
"Kina son wani abu ne Ammeen Basma."
Basma ta ɗan zaro jin abinda ya ce, sai ta rage murya ta ce.
"Hmmm daga gani na girma wannan........wai wani sheɗain ɗin ne ya ba Abba shawarar auran yarinya hmmmmm harna tausaya mata, sai wani kunya take ji bayan ta gama........." maganar take ya tsaya mata a maƙoshi dan kuwa idanunta sun nuna mata wani mugun abu.
Abba sallama ya yi mata ya fara tafiya, Amma shegiyar ta kira sunansa a tausashe, bayan ya tsaya ya juyo, ta nufesa da gudu ta rungumesa ba ta tsaya a nan ba, har kumatunsa ta sumbata sannan ta ruga da gudu ta shige part ɗin Abba.
Abba kuma cikin jin daɗi ya shafa suman kansa ya fita yana murmushi.
Zama Basma ta yi a ƙasa tana rintse ido, Fauza ita ma ta ga komai murmushi ta yi tana cewa.
"Ƴar hannu ce, shi be taɓa ta ba amma ita ta rungumesa, hmmmm ina da tabbacin nan da 9 month za'a yi ma Basma ƙanwa......." Ai gudu ta fara yi Basma ta fuma mata, Marwa kuma ya sauke ajiyan zuciya tana bin bayansu.
*Washegari*
Ta kama Saturday duk suna gida, babu wacce ta fito babban parlour har tana ta yi, jiya ba su kwanta da wuri ba hakan yasa suka kasa tashi, sai da yunwa ya tashe su tukun suka tashi.
Wanka suka yi, kowacce ta sanya kayan da ya yi mata sannan suka fito a jere suna ɗan hira, amma duk wanda ya kallesu yasan suna cikin damuwa.
Dining area suka zazzauna, already an gama shirya komai, abincin suka fara ci suna yi suna dallama ƙofar part ɗin Abba harara, inda suke ta jiyo surutai.
Bayan sun gama suka zazzauna, a lokacin 11:45am.
"Wai nikam ina Al-hussain ne? Kwana biyu ina so na tambaye ki, gana ɗaya kun dena wannan wahalalliyar soyayya, na ga sau ɗaya kuke waya shima baku jimawa, ya dena zuwa, ke tsakani da Allah hakan ba ya fi ba?." Marwa ta kalla Basma, murmushi ta yi dan kuwa text kawai Al-hussain ke tura mata duk safiya da yammaci, da Al-hassan suke waya wanda suke yaudarar kansu da sunan gaisawa suke, amma a ɓoye kowannen su ƙaunar juna ya kamasu, sai dai sun kasa gane hakan.
Murmushi Marwa ta sake yi tana lumshe ido sannan ta ce.
"Uhmm yana lafiya kawai ayyuka ne da suka sha mai kai." kafin Basma ta sake magana sai ga wa'inda suka kwana a ɓangaren amarya sun fito kowa a shirye tsaf.
A haka suka fito suna ta rarrashin Najlha dake cikinsu tana da hawaye, haka Rukky itama hawayen take yi.
Aunty Rumasa'u ta kalla su Basma ta girgiza kai, sannan ta fice, haka duk suka fita babu wacce ta kulasu, suma haka.
Da ƙyar Najlah ta iya daurewa tana kallon motocinsu sukar gidan, hawaye ta share sannan ta gyara zaman hijabin jikinta ta juya zuwa ciki.
Tana shiga ta nufa part ɗin Abba, sai dai jin kalaman Basma yasa ta tsaya cak.
"Ke Najlah zo nan." a cikin ran Najlah ta maimaita kalman 'Zo nan.' sai ta yi wani murmushin gefan baki, take kuma ta marairaice fuska tana mai nufan cikin Parlourn.
Kujerar da babu kowa nan Najlah ta zauna tana mai kallon ƙasa ala ita uwar ladabi.
"Munga zallar iskanci, muna sama tana sama, hmmmm lallai kam." da sauri Najlah ta sauka zuwa ƙasa, tana jiran ta ji mai uwar mulkin za ta ce, dan ta gama gane Basma ita ce shugabar tantiran gida.
"Kwanda ki shiga hankalinki dan kuwa, yanzu babu kowa a gidan nan, tsab zamu kama ki mu kashe ki, kuma mun kashe banza." Cikin shaƙiyanci Najlah ta buɗe baki kamar mai rawar leɓe ta ce.
"Na sani.....kuyi ƙari idan ma na muku wani abu..........." Marwa ta katse da sauri.
"Shshshshshsh, idan muna magana karki kuskura ki dinga sa baki sai mun baki dama, tambayarki zamu yi munafuka."
"Ai kuwa munafuka tunda ta kasa kallon mu sai ƙasa, kina jinmu." Cewan Basma, da sauri Najlah ta ɗaga musu kai.
"Tambayar farko wani Bokan ne ya yi miki akan Abba? Kuma shi bokan be faɗa miki auren Abba daidai yake da kin burne kanki da kanki ba...............ke nake saurare."
"Ba boka ba Malam, daga Allah ne soyayyar Abba, a kallon farko muka fara son junan mu." zabura Marwa ta yu za ta duke ta, da sauri Basma ta riƙe ta tana girgiza mata.
Najlah kuwa ta lumshe ido, za ta yi duk yarda za ta yi a yau ba za su fara rigima ba, za ta musu biyayya kafin ta nuna musu ainiyin launinta idan suka kai gaci, da dai hannun Marwa ya taɓa ta da yau hankali kowa sai ya tashi.
"Da kin bari na durje bakinta, idan ba asiri ba uban me kika mai, nasan kuma saboda kuɗin Abba ne kika aurensa, amma me za ki yi da tsoho, to wallahi ki tanada hawayen ki dan kin tari babban masifa da bala'i a gidan nan, ke da samun daɗin aure sai a lahira, kuma ko a can ɗin ne ma ba da Abba ba." Marwa ta kai nan tana wuci, Basma ta dasa.
"Hmmmm azaba iri-iri mun tanadar miki su, naso a yanzu da kike zaune, na watsa miki acid, anjima danginki su zo su kwashe ki, sai kuma na yi wani tunani, gwanda mu nakasani tukum, shegiya mai kama da Mayu."
"Dan Allah kuyi shuru, matar Abba ce fa, Ni bana son irin haka." Cewan Fauza tana tsugunnawa kusa da Najlah dake ta share ido kaman tana kuka.
Haka ta rarrasheta, sannan ta raka ta part ɗin Abba.
Tana dawowa ta zauna tana cewa.
"Yarinyar ma ba ta da hayaniya, wallahi na tausaya mata, tana da rauni sosai, dan haka zan sassauta mata salon huƙubana." murmushi suka yi dukkansu.
"Tasan tana da tsoro shi yasa ta kasa magana, amma kalla kwanaki da muka yi waya da ita sai na ji muryarta a tsaitsaye." murmushi suka yi dan gani suke wannan ƙaramar alhaki ce a wajensu.
Najlah na shiga part din Abba ta murza key, dariya ta yi tana girgiza kai, Hijab ɗin jikinta ta cire, sai kuma kewan ƴan uwanta suka kamata, lumshe ido ta yi tana tunanin kalam na ƙarshe.
"Najlah aure ya wuce duk yarda kike tunani, a kowani aure Akwai ƙaddararsa, akwai daɗi akwai rashin daɗi, babban makamin dake cikin aure shine *Haƙuri* , da an faɗa kalmar nan sai wasu su yi dariya akan kalmar, suna tunanin auren soyayya daban yake baya buƙatar haƙuri.......hmmm kowani aure yana buƙatar haƙuri sosai, sannan *biyayya* duk abinda ya ce ki yi, to ki yi, idan ya hanaki kar kiyi, Alhamdulillah na saki islamiyya, kuma iya gwargwado kinsan hukunce-hukuncen aure.......ƙyata ki kula, dan Allah, ki zauna da mijinki da yaransa lafiya."
Hawaye ta share sannnan ta yi murmushi tana cewa.
"Tabbas ba zan baki kunya ba Mamie, sai dai yaran nan zan kowa musu zama, har ga Allah sun min kaɗan, ina so na yi rigimar da gidan nan sai ya mana kaɗan wajen dambe."
*Abinda ba ta sani shine, zuwan Abuja shine mafarin babban ƙaddarar da za ta iska, duk da tasani amma ba ta san hatsarin ƙaddarar ya kai haka ba...................*
****************
Da misalin ƙarfe 7:20pm na dare, motarsa ta yi parking a bakin get ɗin su Marwa, wayarsa ya ɗauka ya kira ta, bugu uku ta ɗauka.
"Surpriseeeee ina waje." Da haka ya katse kiran, shuru ya yi yana sauraran waƙar dake tashi a cikin motar.
Ƙasa da mintina 10 sai aka buɗe get, yana juyawa idanunsa suka kalla fuskarta dake ɗauke da murmushi.
Motar ta buɗe, sannan ta shiga da sallama, amsawa ya yi yana ƙare mata kallo.
Abaya ne jikinta sai vail da ta yafa, rabin gashinta yana waje ya kwanta luf-luf.
"Kinyi ƙyau sosai." Ya faɗa yana lumshe ido.
"Na gode sosai." Da haka suka yi shuru na dogon lokaci, amma zuciyoyinsu cike suke da jin daɗin kasancewa a tare.
Lokaci zuwa lokaci sai su dinga saton kallon juna, da sun haɗa ido sai suyi saurin kauda kai.
Ita ce ta yi ta maza ta yi gyaran murya tana cewa.
"Uhmm na faɗa maka abinda zuciyata ke rayamin?." Da sauri ya ɗaga kai, sai ta ce.
"Uhmmm dama uhmmmm, idan irin haka uhmmmmm tare......shine kawai uhmmmmm." Murmushi ya yi.
"Bangane komai ba Marwa."
"Okay, inshot ina jin ina sonka, so mai yawa bansan garin ya ba, amma na faɗa soyayyarka, dan haka a yau zan sanar ma Al-hussain da cewa kai nake so na aura." da sauri Al-hassan ya kalleta dan kuwa maganar ƙarshe ne ya bashi mamaki, amma sai ya zuba mata ido, number Al-hussain ta danna ma Kira, amma baya shiga.
"Ki bari mu tsara abinda zamu ce mai tukun, ya yi wuri ki sanar da shi, zai ga na yaudare shi ne, be kamata hakan ya faru yanzu ba."
"Hmmmm be yi ba, na ƙosa na fara morar soyayyarta da kai, kuma komai da ya faru shi ya ja." Da haka ta sake kiran number wanda cikin ikon Allah ya fara shiga, sai dai be ɗauka ba, kiran na katsewa sai ga kiran Al-hussain ya shigo wanda aka sanya ainihin sunansa aka cire *My Love.* kallon Al-hassan ta yi, sai ya ɗaga mata kai alaman ta ɗauka kawai, hannunta ya latsa alaman green *Accept*, take muryar Al-hussain ta fito raɗau cikin wayar..................
**************
Anas, a yau sai da ya tabbar ya cika duk umarnin boka, zauna yake gabansa yana bashi duk abinda ya buƙata, tsohuwar Tunkiya mara gani, ita ce ma yasha wiya kafin ya samu, amma jaririn, asibiti ya je, da dubara ya sato jaririn da aka haifa a yau, daga nan ya nufa makarantar mata, ya ja ra'ayin wata da kuɗaɗe, da haka ta shiga motarsa, abin shaƙa ya sa mata a hanci take ta ɗauke huta.
Daga nan sai gidansa, sai da ya shimfiɗa wannan ƙyallan akan gado sannan ya hayyake ma yarinyar nan, bayan ya gama kuma ya kasheta, shine ya tawo wajen boka jikinsa har rawa yake, saboda yana buƙatar aikin nan, dan Mahaifin Basma ya tara da yawa.
Boka ya kalla kayan dake gabansa sannan ya buɗe baki cike da amo ya ce.
"Ka je, gobe ka dawo kafin nan Aljanu sun gama maka aiki." Da haka ya yi tashi yar gidan Bokan ransa fes.
Bayan ya koma gidansa, ya iske gawar yarinyar nan duk cikin ƙazanta, ga jikinta duk ya saki, amma saboda rashin imanin Anas, haka ya sake shigar yarinyar, bayan ya gama ya ɗauki gawarta ya jefa ma wasu manyan karnuka guda 7 da suke wani keji, ai taruwa suka yi a kanta suka fara cinta ta ko ina.
Anas ya yi murmushi yana kallon karnukansa, sannan ya juya ya koma cikin ɗakinsa...............
*************
Shuru ne ya ratsa ɗakin, babu motsin komai sai ƙarar A.C, a hankali Abba ya ɗaura hannunsa kan hannun Najlah dake zaune kan daddumar da suka yi sallah yanzu.
Najlah duk bakinta sai ta ji ya mutu, a yau ta kasa ɗaga ido ta kalla Abba, wani nauyinsa take ji sosai, hawayen da ta rasa na menene ta ji ya zubo mata sai ya yi saurin tare su da hannayensa yana fara magana a tausashe.
"Budurwar Abba ta zama Matar Abba, a yau Najlah ina so na mai da ke cikakkiyar matar aure, amma idan kina hawaye ba zan iya komai ba, dan Allah ki dena kinji......tashi ki ci wani abu." da haka janyo wani leda da ya shigo da shi, ya fara buɗe wa yana mai jin kamar an mai bushara da gidan Aljanna................✍️ END
> Awwnnnnnnn 🙈 ba dole ba Abba, tunda kasan abinda ke jiranka.........🏃