PAGE 3️⃣5
by @prettys01
> "Budurwar Abba ta zama Matar Abba, a yau Najlah ina so na mai da ke cikakkiyar matar aure, amma idan kina hawaye ba zan iya komai ba, dan Allah ki dena kinji......tashi ki ci wani abu." da haka janyo wani leda da ya shigo da shi, ya fara buɗe wa yana mai jin kamar an mai bushara da gidan Aljanna...............
Da kanshi ya ba ta abinci a baki, cike da soyayya da annashuwa, ita kuma ta ɗan saki jikinta, amma kunya duk ya rufe ta.
Bayan sun gama, da kansa ya ɗauke ta ya zaunar da ita kan gado, sannan ya zauna gab da ita, ɗago fuskarta ya yi, suka haɗa fuska waje guda, a hankali ya furta.
"Kin shirya amsan mijinki a wannan daren?." Shuru ta yi ƙirjinta na dukan dari-dari, haka ta ɗaure ta ɗaga mai kai sau ɗaya, murmushi ya yi.
"Na gode Sweetiena." Da haka ya miƙe ya isa wajen makunnan hutar ɗakin, ya danna take duhu ya mamaye cikin ɗakin.
> Ba zan iya ɗauko rahoto a cikin duhu ba 🙈🙈🙈.
************
Gaba ɗaya sun kasa barci, Fauza da Basma tunanin abinda ke faruwa tsakanin Abba da wannan yarinyar suke, hankalin su gaba ɗaya a tashe yake, sai dai Marwa ta fi su shiga tashin hankali sakamakon abinda ya faru ɗazu, ɗazu da ta kira Al-hussain a waya, bayan kiranta da ya yi sunan da ya saba, ita kuma ta furta kalmomi dan ba su fi adadin yatsun hannunta ba, amma kalamansa da suka biyo baya sune suka zama silar tarwatse mata zuciya....
"My love." Abinda ya furta kenan, sai ta kalla Al-hassan, sannan a natse ta ce.
"Al-hussain na fasa aurenka, na samu wanda nake so........" Cikin sauri ya katseta.
"Me..... mene? Marwa kinsan bansan irin wasan nan, kinsa sautin bugawar zuciyata ya sauya." Ya faɗa cikin rauni sosai.
"Ka zaɓa aiki sama da Ni, ka manta da ni, ko maganar aure baka min, kuma sanin kanka ne saura wata biyu dai-dai na kammala makaranta."
"Marwa ina sane da komai, daidai da second ɗaya be taɓa wucewa ba tare dana tuna ki ba, idan akan aiki ne, daga yau zan rage, zan dawo kamar yadda kaki so, sannan aure kuma next week za'a kawo akwati ya miki?." ya faɗa har muryansa na rawa.
"Ni fa nafasa, shine magana kawai, ba zan aureka ba." Da haka ta katse wayar, sai ta kalla Al-hassan, take ta rintse ido ganin idanunsa sun kaɗa sunyi ja, hatta jijiyoyin kansa sun fito raɗau.
Ta manta shaf, Al-hassan ba zai iya juran a taɓa mai ƙani ba, a hankali ta buɗe baki ta ce.
"Al....." hannu ya ɗaga mata, take wayarsa ta fara ringing, yana kalla yaga sunana *Bloodline.* Ɗauka ya yi yana sanya wayar a speaker.
Cikin wani irin amo, wanda ya girgiza zuciyar Al-hassan harma da Marwa, Muryar Al-hussain ta fito cikin wani irin yanayi kaman mai kuka.
"Dan uwa kana ina yanzu? Taimako za ka min.....kana ina?." A karo na farko Al-hassan ya mai ƙarya, bayan ya danne duk wani abu dake taso mai.
"Ina gida."
"Ka taimaka min, gidansu Marwa nake so kaje, na rasa gane me take cewa, kaman wai ta fasa aurena........nasan kai kasan cewa duk duniyar nan babu yarinyar da nake so sama da Marwa, idan ban sameta wallahi zan iya rasa raina, ita ce komai na wa, Al-hassan ka taimaka min ka ji." A cikin muryan nasa za ka fahimci rauni sosai.
Al-hassan ya kalla Marwa da itama jikinta ya mutu.
"Zan je, kuma insha Allahu, babu wani abu da zai faru, ina Allah ya yarda Marwa ba da ta wani miji sai kai."
Daga wannan kalmar komai ya tsaya cak, idan na ce komai ina nufin komai, abin da su ukun ba su sani ba shine wannan shine babban matakin ƙaddarar kowannen su, ƙaddara mai ruɗani da hatsari, wanda idanuwa za su yi kuka, zuciyoyin za su raunana.
A wannan daren mutane da dama sunyi barcin ɓacin ɓakin ciki, wasu kuma ko iya barcin ba su yi, kamar Al-hassan wanda tunda ya koma gida ya kasa aikata komai, har kira uku Al-hussain ya yi mai amma ya kasa amsawa, daga ƙarshe ya kashe wayan, haka ya kwanta ko kayan jikinsa ya kasa cirewa, babu abinda yake tunawa sai hawayen Marwa na ƙarshe bayan kalaman da suka fito daga bakinsa.
"Mu haƙura, mu mance da munsan juna, farin cikin Al-hussain shine muradina, wallahi Marwa bazan iya kuntata masa ba, ba zan iya aure masa wacce yake so ba, ba zan iya cin amanar sa ba." Da haka ya yi shuru.
Marwa kuwa hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, a haka kuma ta fice daga motar ta shiga gida da gudu.
*Al-hussain.*
Shi kansa ya kasa barci a wannan daren, domin kuwa yarda yake jin Marwa ba zai iya faɗa ba, sai dai a yanzu yarda ya ɗau aikinsa da muhimmanci ba zai saki ba, zai san dubarar da zai yi kawai, duk da haka tunaninta ya kasa barinsa, gashi sai kiranta yake amma kiran baya shiga.
Bindigan dake hannunsa ya ji an amsa, hakan yasa ya buɗe idanunsa, sai suka sauka cikin na matarsa Pretty.
Murmushin ƙarfin hali ya yi mata yana kallon yarda ta kwanto a jikinsa gaba ɗaya.
Dai-dai yanayinsa ya yi, a hankali ya ke shafa gadon bayanta har barci ya ɗauke ta, shi kuwa ya kasa barcin gaba ɗaya, tunanin Marwa ya tsaya mai a rai gaba ɗaya.
**********
Ɓangaren Abba da mutumiyar kuwa, wannan daren ya zamo musu dare mai cike da soyayya, daren da ya shiga Tarihin rayuwarsu, suka haɗa jiki, jini da zuciya, suka ƙulla ƙyaƙƙyawan alheri tsakaninsu.
Abba abinda ya fi ruɗewa ma ya yi saboda rigimar Najlah, abin ku da uwar shaƙwaɓa.
Ta yi kuka har fuskarta ta kumbura, idanunta sun kara firfitowa, rarrashinta yake amma ba ta san yana yi ba, yarda kasan ana mata wani abun haka ta dinga zuba kuka mara sauti.
Abba da kansa ya yi mata wanka, ya dawo da ita ya kwantar amma har lokacin kuka take yi tana ta kiran sunan Mamie.
Abba jin ta yi shuru yasa ya leƙa fuskarta, barci ne ya ɗauketa, hamdala ya yi yana gyara mata kwanciya, sannan ya tashi ya shiga wanka.
Koda ya fito jallabiya ya sa, sannan ya hau kan dadduma fara sallah, bayan ya idar ya dinga miƙa godiyansa ga Allah da ya mallaka mai Najlah.
Ya jima a haka sosai kafin ya koma kusa da ita, ya zuba mata ido yana jin soyayyarta na ƙara ratsa ɓargon jikinsa, da ta motsa *Wash* zai ce *Sannu, sannu.*
Kafin ka ce har an fara kiraye-kirayen sallar asuba, tashi ya yi ya ɗauro alwala, sannan ya dawo kusa da ita, a tausatse ya fara shafan fuskarta yana kiran sunanta .
"Jaririyata, Babyna." Ba ta da nauyin barci, dan haka ta ɗan yi miƙa, take ta haɗe jinyoyinta sai ta fashe da kuka tana riƙe Abba.
Murmushi ya yi yana mai lallashinta, amma ina cikin kuka take cewa.
"Abba kamin da zafi, bayan ka ce babu zafi, kuma kuma kuma shine......" Sai kuka.
Bakinsa ya kai saitin kunninta ya ce.
"Najlah ta jaruma ce, kuma soja, sannan kina yara manya har uku, haba tawan ki yi shiru kinji." Ganin ta ƙi yin shurun yasa ya kai bakinsa kan na ta ya sakar mata light kiss, take ta yi tsit.
"Ka tafi zan iya tashi." Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi.
Miƙewa ya yi sannan ya riƙe mata hannu har zuwa cikin bayi, sai a lokacin ta lura towel ɗin jikinta wanda har saman ƙirjinta sun fito, zaro ido ta yi, tana mai sauri mai da towel ɗin sama, sai ta kalla Abba, ganin yana murmushi yasa ta marairaice fuska ta ce.
"Ka tafi dan Allah ka fita."
"Zan miki wankan ne." Kuka ta fara yi tana turo baki.
"Na tafi kiyi shiru to." Ya fita yana rufe mata ƙofa.
Najlah tunawa ta yi shi ya yi mata wanka ɗazu, ya riga ya gama ganin komai, sai ta lumshe ido sannan ta buɗe.
Gasa jiki ta fara yi sannan ta yi wanka tare da alawala, a hankali ta fito, tana jin wajen ya rage zafin sosai, wardrobe ta nufa, ta buɗe, kayane cike an jera mata su, ba ƙyarya akwaiti 12 Abba ya yi mata kuma duk a cike taf.
Doguwar riga ta sanya, sai Hijab har ƙasa, sannan ta hau kan prayer mat ta yi sallah.
Tana zaune Abba ya shigo, sai ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba, wajenta ya nufa ya ɗagota gaba ɗaya.
"Barci nake ji, kuma ajikin zanyi kinji." Shuru ta yi dan ta rasa ya aka yi Abba ya fetse haka.
Ailai a ƙirjinsa ya kwantar da ita, barci ya ɗauke su gaba ɗaya.
Daga wannan ranar Alhaji Mubarak suka fara more amarci, amarci suke mai rai da lafiya, idan ka cire masallaci babu inda Abba yake zuwa, yana gida tare da gimbiyarsa, tabbas Abba ya zama ɗan gatan Najlah domin kuwa yarda take kula shi, da nuna damuwarta a kansa, balle shi da yake ji da ita kamar ƙwai.
Abinci dare ne kawai suke ci tare da yaran Abba, idan suka haɗu, sai Najlah ta yi ta rarraba ido tana muzurai, su kuma su yi ta Banka mata harara, suna tsara duk ranar da Abba zai koma aiki, a ranar za su kwantar da Najlah su yi mata mugun duka.
Itama Najlah ta gama tarasu, jira take akai lokacin da wata za ta yi ƙoƙarin kai mata hannu, sai kuma ba su yi wannan giginba.
Abba da kansa ya tambayata wata rana.
"Me yasa kike nuna ma yaran nan ke ba ruwanki, bayan ke jan wiya ce?." Murmushi ta yi tana ce mai.
"Lokaci dai, amma koda wasa karka faɗa musu Ni soja ce." da haka shima ya sa musu ido.
Tsaye suke a tsakiyar Parlourn su, kallon juna suke cike da murmushi, Abba sanye yake cikin wani shadda coffee brown, ya sanya hula da takalmin wanda suka yi matching ɗinsa.
Najlah kuwa riga da wando jeans ta sa, wandon sky blue, crazy, ya matseta sam sai riga mai ƙaramin hannu, ta yi ƙyau sosai cikin shigar, ga gashin kanta da Abba ya gyara mata, ya zuba a baya.
Rungumeta ya yi.
"Ina sonki sosai Babyna."
"Nima haka, ka kulamin da kanka." Da haka ya ɗaga mata kai.
Fita ya yi, ita kuma ta nufa ciki, sai ta hanga keys ɗin sa a hannun kujera, ɗauka ta yi ta bi bayansa dan tasan be yi nisa da ƙofar ba.
"My Mubeeee." ta furta tana shiga babban parlourn.
Abba da ya kusa fita ya juyo yana sakar mata murmushi.
Da sauri ta isa gabansa rungumesa ta yi.
"Ana jira a office." Ya faɗa ba tare da shi kansa yasan akwai wasu halittu da suke zaune a Dining area ba.
"Mantuwa ka yi, kuma yana ajiyun wando na ka duba ka gani." ba musu ya kai hannunsa kan boom-boom ɗin ta, ya sanya hannu ya ciro keys ɗin.
"Thank You My Love." Sai ta raba jikinsu sannan ta yi mai Bye.
Fita ya yi da haka ta juya za ta wuce.
"Karki kuskura ki sake ɗaga kafa ɗaya daga wajan nan, hmmmm lallai, wato gamu ƴan iska, haka kike mana yawo ke ala dole mai miji, to a yau za ki fara fuskantar azabar da muka shirya miki."
Najlah ta juya a hankali ta kalla Basma dake nufota rai ɓace.
Kafin ta ce wani abu, sai ga Marwa da rushin gawayi a babban kasko wanda suka sa masu aiki hura musu.
Bayanta Fauza ce riƙe da wata bulalar inji kaman na dukan jaki, sannan ɗayan hannu riƙe take da wani ƙwalba mai kauri, a jikinsa alaman danger na hatsari a jiki, sannan a rubuce jikinsa an rubuta *Acid*
Najlah mamaki suka bata har batasan ta yi zaman ƴan bori ba.
A gefanta suka aje komai, sannan Fauza ta koma part ɗin su, wata leda ta dawo da shi, Basma ta amsa ta zazzage kan center table, me Najlah za ta gani.
Sabuwar ruƙa, almakashi, rezors, da wasu kayayyakin da suke kama da kisan kai.
Dariya suka yi ganin Najlah ta zuba musu ido, a ganinsu kamar duk ta tsure.
"Wannan azabar duka na yau ne matar Abba, a yau za ki yi danasanin sanin waye Abba, da gigin aurensa, ke daɗi miji, akwana bakwan nan sai rawar kai kike yi, yau saboda kin riƙa, da wa'inna kayan kika fito............hahahaha, za ki gane shayi ruwa ne yau, taraki muka yi, daga nan sai gadon asibiti, har can kuma zan biyo ki da huƙubar gobe." ta kai nan tana raba sabuwar huƙan da ƙwalinsa, take wuƙan ya fara shining tana haske, wani abu Najlah ta haɗiye tana rayawa 'Yau akwai ƙura a gidan nan.'...........✍️ END.