PAGE 3️⃣6
by @prettys01
> ...............hahahaha, za ki gane shayi ruwa ne yau, taraki muka yi, daga nan sai gadon asibiti, har can kuma zan biyo ki da huƙubar gobe." ta kai nan tana raba sabuwar huƙan da ƙwalinsa, take wuƙan ya fara shining tana haske, wani abu Najlah ta haɗiye tana rayawa 'Yau akwai ƙura a gidan nan.'.........
"Bassey ta zaɓa da wanne take so a fara, acid, ko konata, ko yanka mata jiki." Marwa ta kai nan tana zama kan kujera.
Bassey gaban Najlah ta tsaya, ta tsugunna tana mata shu'umin murmushi.
"Shike nan, da wani kala kike so a fara?." Najlah ta marairaice fuska ta ce.
"Me.....me na yi muku? Kuma bangane me zaku min ba?." Dariyar shaƙiyanci suka sanya su uku, Fauza dake zaune ta ce.
"Acid a gefan fuska za mu wata miki, rushin nan kuwa, hannayenku za ki sanya a ciki, ko mu sa ƙarfe ya yi ja, sai mu fara ɗaye miki fata, bulalan nan kuma, a gadon baya zamu yi miki matsiyacin duka, da mazaunanki, hmmmmmmm komai dake nan wajen akwai aikin da zamu yi da shi a jikin ki." Ta kai nan tana sanya sabuwar wuƙa cikin rushin.
Shuru ya ratsa babban parlourn, kafin Basma ta aje wuƙan hannunta ta ɗauki wanda ke rushin, wanda ko a ido ka gani kasan ya ɗau zafi.
Da haka ta nufa Najlah dake zaune har lokacin a ƙasa.
Lokaci guda kuma Najlah ta miƙe, sannan ta zauna kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, take ta bushe da dariya tana musu kallon mahaukata.
Kallon juna suka yi, suka sake kallon yarda Najlah ke kallonsu tana dariya, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shuru tana dafe ciki, cikin dariyar take cewa.
"Kai yaran nan kuna da abin dariya wallahi." Sai ta sake fashewa da dariya sannan ta ci gaba da cewa.
"Banda lokacinku Yarana, yunwa nake ji, ku bari na sa wani abu a cikina tukun." da haka ta miƙe ta fara tafiya tana nufan stairs.
Da ido Basma ta yi ma Marwa alama da ido, nan take Marwa ta yi kan Najlah, ta sha gabanta tana turata baya, sai dai Najlah ko gezau ba ta yi ba, haka ta sa dukka ƙarfinta ta tura Najlah baya, amma yarda kasan tsayayyen dutse, ta kafe waje guda.
"Kuskure mafi muni da wani zai yi a cikin ku shine sa hannu ya taɓa Ni, tunda har kika sa hannunki a jikina dole ki yaba ma aya zaƙinta." da haka Najlah ta sa hannunta biyu ta tura Marwa baya, tare da janyota suka buga ƙirji.
Abinda be fi cikin second biyu ba, ta kuma ɗaukan Marwa ta jefa kan kujera, take Marwa ta saki wani marayan kuka tana dafe kafadunta cikin azaba.
Najlah ta yi dariya tana juyowa ta kalla Basma da ta nufota riƙe da wannan wuƙan.
Fauza da gudu ta nufa Marwa tana jera mata sannu.
Najlah na tsaye ba ta motsa ba, har Basma ta iso gabanta ta kai mata wuƙan sai tin wiyarta, cak Najlah ta riƙe hannun Basma, sannan ta haɗe bakinta waje guda tana hura mata kiss. Basma ta tofar da miyau, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta, sai dai ta kasa, gashi dai da hannu ɗaya Najlah ta riƙe mata hannu amma ta kasa ƙwacewa.
"Yau kun kaini karshe, banso taɓa ku yanzu ba amma ba yarda na iya." Ta faɗa tana ƙara matse hannun Basma, take ta yi ƴar ƙara.
Sakinta ta yi bayan ta amshe wuƙan, ta cilar gefe guda.
Basma hannunta zafi yake amma haka ta miƙe ta isa kan table, da ɗayan hannun ta ɗauki acid, ta ɓalle murfin take ya hau tururi, ba tunanin komai ta yi kan Najlah tana cewa.
"Yau sai na yi ajalinki shegiya mayya."
Najlah ganin acid a hannunta yasa ta yi wani tsalle sai gata kan kujera, nan fa Basma ta fara ƙoƙarin tare ta, ita kuma ta mai da abin wasa, sai tsalle-tsalle take kan saman kujera.
Fauza ta raruma ƙafar Najlah, Allah ya bata sa'a, tako damƙe ta da ƙarfi, take Basma ta tsaya gabanta tana sauke ajiyan zuwa.
"Zuba mata kawai." Cewan Marwa tana juyi kan kujera.
Najlah kamar mai Aljanu ta yi murmushi, ta wani zabura, bakin Fauza ta buga da haɓarta, sannan ta amshe acid ɗin tana tura Basma baya.
Da gudu ta nufa wajen Dining area, sick ɗin dake wajen Najlah ta zubar dashi sannan ta dawo cikin Parlourn tana cewa.
"Ashe baku da imani har haka, to bara na nuna muku nawa rashin hankalin." Da haka ta fizgo Fauza, ta ɗagata sama, ta yi wani hajijiya da ita sannan ta sauketa, Marika uku lafiyayyu ta zuba mata tana tureta kan kujera.
Sannan ta ɗauki bulala ta yi kan Basma, lokaci guda Basma ta fara ja baya dan gani take ba mutum ba ce, idan ma mutum ce to tana da manyan Aljanu.
Kafin ta yi wani yunƙuri, Najlah ta damƙeta, ta zuba mata bulala guda biyar a bayanta, sai ta saketa ta nufa Kitchen.
Masu aiki da suke leƙe da sauri duk suka koma bakin aikinsu, Najlah na shiga ta ce.
"Ku sa musu ruwan zafi." Ba ta jira amsar su ba ta fice, Dining room ta isa, ta zauna ta fara cin abinci ragowar na Basma.
Daga wajen take kallon yarda kowaccensu ta shiga wani irin yanayi, dariya ta kuma yi.
Bayan ta gama cin abinci ta dawo cikin Parlourn, zama ta yi kan kujera tana cewa.
"Kunsan Allah, banda mutumci, bana so na nuna muku ainiyin launina amma sai da kuka sanya na nuna muku, ban raina uwata ba dan haka ba zan yadda ƴaƴana su raina Ni ba.........Ina zuwa." Da haka ta tashi ta bar part ɗin.
Da ido suka bi ta hatta shige part ɗin Abba.
"Amma wannan ba mutum ba ce ko?." Cewan Basma wacce bayanta da hannunta ke mata zafi sai Marwa ta ce.
"Dama ba ta yi kama da mutane ba, innalillah kafaɗuna zafi, shegiyar ta karyani."
Kafin Fauza ta yi magana sai ga Najlah ta fito cikin farin hijab har ƙasa, ta ɗauko car key , hannu ɗaya kuma tana riƙe da wayarta.
Tana zuwa tsakiyar Parlourn wayar ta hau ringing, ta ɗauka tana zama kan kujera.
"My mubee, fatan kana lafiya?." Ba su iya jiyo abinda Abba ya ce, amma sunsan shine.
"Uhmmm zan kai Marwa asibiti, suna ɗan yi husuma da Ni, shine na ɗan shafa musu fuska, yanzu ina so na kaisu ko magani a basu." Murmushi suka ga ta yi sannan ta sumbaci wayar tana katse kiran.
Lokacin guda ta haɗe fuska, ta kallesu.
"Ku tashi mu tafi asibiti." Ta faɗa tana miƙa wa, Allah ya so ta iya mota, balle da ta dena zuwa barrack sai ta dage sosai wajen koyan mota, har ta ƙware.
"Babu inda zamu je, a haka zamu zauna har wanda ya ajeki ya dawo." Kallon Basma ta yi.
"Bana magana biyu, amma zan sake muku, mu tafi asibiti."
"Babu inda zamu." Ta sake faɗa harda murguɗa baki.
Najlah gabanta ta isa, ta tsugunna daidai kanta.
"Na lura bakinki be mutu ba." da haka ta kama hannun da take da tabbacin akwai gocewan kashi, ta murɗa ya yi wani ƙara. Lokaci guda ta haɗa ma murɗe mata kunne, ta ja kamar za ta tsinka.
Hawayen azaba ne suka gangaro daga cikin idanun Basma, amma ta saka kuka.
Najlah na sakinta ta nufa main door.
"Na baku 3mnt." Da haka ta fice, tana fita Basma ta saki marayan kuka tana ganin kaman hannunta ya rabe da jikinta.
Cikin walaha Marwa ta ce.
"Ku tashi muje kar mahaukaciyar ta dawo."
Ba yarda suka iya, Marwa da Fauza suka fita, amma Basma ta kafe waje ɗaya.
Farar mota suka gani kusa da main door, ganin Najlah a ciki, yasa suka shiga gidan baya.
"Ina Basma?."
"Tana ciki." Cewan Fauza, sai Najlah ta buɗe motar ta fita, cikin minti biyu da dawo, tana shiga sai ga Basma ta fito bakinta a fashe yana jini.
Duk yanayin da suke ciki sai da suka yi murmushi ganin yarda ta fito.
Baya ta so shiga, amma Najlah ta danna mata horn, haka ta zaga ta shiga gefanta.
"Kowacce ta sanya seatbelt, karo na farko da zan hau babban titin kenan." da haka ta ɗaura nata sannan ta nufa get.
Parking ta yi bakin get sannan ta ɗauka niƙaf dake cikin motar, wayarta da buɗe location sannan ta fara bin Jan danger ta nufa babban asibiti wanda ya nuna alaman green.
Ba su yarda da abinda take cewa ba, sai da ta hau kan titi, yarda ta figa motar, sai da kan Marwa da Fauza suka haɗe waje guda, da sauri suka ɗaura seatbelt ɗin suna ƙara yadda Najlah ba mutum ba ce.
Ga asibitoci nan suna wucewa amma Najlah ba ta tsaya a kowanne ba, hatta Specialist Hospital Suka wuce, wani babban asibiti wanda kaf Abuja ake ji da shi, babbane sosai wanda ya kusa cinye unguwa guda.
Asibitin akwai manyan-manyan likitoci, ga aiki cikin ƙwarewa, kuma suna da sauƙi sosai.
A babban Premises ɗin ta yi parking, tana kallon sunan asibitin dake jikin signboard, *PrimeCare Hospital* tasan asibitin a labarai, dan yarda kowa yasan 44 hospital a kaduna haka wannan ya yi suna.
Ita ce a gaba su kuma suna bin ta a baya, koda suka je wajen ɗaukan suna, sai cewa ta yi, ita da yaranta ne.
Basma ko tari ba su sake ba, haka aka shiga dasu wani ɗaki.
Mai gyaran ƙashi ya musu gyara, Basma hannunta ɗaya, Marwa kafaɗunta, sai Fauza da aka ma dressing, itama Basma an mata a baki, haka dai aka gama duba su, tare da basu umarnin nan da kwana uku su dawo.
Najlah ta biya komai sannan suka koma gida.
Jikinsu duk ya yi tsami, babu wacce ta kula Naljah, haka suka nufa bedroom ɗin su duk bi lafiyar gado, bayan sun sha alwashin ba ta duka banza ba.
Najlah kaya ta sauya sannan ta yi kwanciyarta a cikin part dinta, da biyu da bigesu na farko dan su shiga hankalinsu, ba biyu dan wani dalili na daban.
Ko da Abba ya dawo da yamma, a babban parlourn ya iske su zazzaune suna dakon dawowarsa.
Ganin ciwukan dake jikinsu yasa ya tambaya abinda ya faru, take suka fashe da wani marayan kukan.
Hankalin Abba ya tashi, ya fara rarrashin su yana basu baki, amma ina basu saurare shi ba.
Paper da biro Basma ta miƙa mai tana cewa.
"Idan har kana son mu da gaske to ka rubuta ma matarka saki.......ita ce ta yi mana wannan abun, cike da zalunci da mugunta."
"Wai Najlah?." Ya tambaya cike da mamaki.
"Eh Abba, harda ƙoƙarin kona mu da wuta." Cewan Fauza tana ƙara fashewa da kuka.
Najlah ce ta fito daga part ɗin Abba, yanzu ma riga da wando ne jikinta amma basu kamata ba, sai dai breast ɗin ta da suke tsaye ƙam. Gyale ne ta ɗan yafa tana ma Abba murmushi.
A tare duk suka kalleta jin yarda ta fara rero waƙan soyayya tana rufe gefan fuskarta.
"Wani ɗan yaro na gani, sai na jima kunya dana leƙo ahhhh..... soyayya na biyo sai na ga na faɗa a tukunya ahhhh........" ta kai ƙarshen baitin tana isa bansa.
Abba kuwa soyayya daɗi ya rungumeta yana jin daɗin waƙar ta yi mai.
Basma ta haɗiye abu mai ɗaci a cikin ranta kin an kira Abba da *Yaro* abin haushin ko damuwa da hakan be yi ba.
"Barka da zuwa Mu Mubee." Ya ɗaga mata kai yana sakar mata daddaɗan murmushi.
Tare suka zauna gefan su Basma, sai ya kalla Najlah cike da kulawa ya ce.
"Ammeen Basma me ya same su ne haka?." kallonsu ta yi ta ɗan yi fari da ido tana cewa.
"Abba tsautsayi ne ya faɗa musu, amma munje asibiti, karka damu, yanzu dai akwai abinda na shirya maka a ciki, muje ka gani." Murmushi ya yi shima.
"Da gaske Ammeen Basma."
"Uhmmm Babyna."
Da mamakinsu sai suka ga Abba ya miƙe yana fara tafiya.
"ABBA!!!!." juyowa ya yi ya kalla Basma da ta kirasa hankali tashe.
"Allah ya baku lafiya, dare ya yi kuje ku kwanta." Da haka ya yi wucewarsa ciki.
"Kin cuce mu wallahi, kuma Allah ya saka mana, kin juyar ma Abba tunani, Najlah........na tsaneki wallahi." Cewan Marwa tana share hawaye da suka zubo mata daga cikin idanunta.
Najlah ta miƙe ta fara tafiya, sai ta fara magana amma ba ta juyo ba.
"Ku kiyaye ƙarshen ku, yau zan barki da iya wanna, Babyna yana jirana, zan mai tausa." Da haka ta shige ciki ta barsu baki buɗe.
Kuka Marwa tasa tana mai ci gaba da ɗaukan mugayen alwashi akan Najlah.
*Al-hassan*
Sama yake kallo, yarda fanka ke jujjuyawa a hankali tunanin abinda suka wuce ya dawo mai sabo.
A cikin satin nan gaba ɗaya ya sauya, hatta magana ba ya wani yi sosai, be manta abin da ya faru washegari ranar ba.
Da kansa ya kira Al-hussain ya tabbatar mai da Marwa ta haƙura, kuma za ta auresa, farin cikin da ya nuna a waya, yasa Al-hassan ji sanyi-sanyi a cikin ransa.
A kuma wanna ranar Al-hussain ya dawo gida, kullum zai fita aiki daga safe har dare, amma a gida yake kwana, sannan shi da kansa ya rarrashi Marwa akan ta haƙura da shi, ta ci gaba da soyayya da Al-hussain.
Ta yi mai biyayya, haka ta ci gaba da kula Al-hussain, shi kuma ya zama ɗan kallo, amma a cikin ransa radaɗi da zafi yake ji.
"Dan uwa me kake tunani?." da sauri ya mai da idanunsa kan Al-hussain dake tsaye gefansa.
"Babu komai Ƙanina." ya yi maganar cikin sanyi.
"No faɗa min abinda yake damunka?." ya kama hannun Al-hussain ɗin ya ɗagosa gaba ɗaya.
Murmushin ƙarfin hali yana kallon ɗan uwansa da yau suka koma kamar da, suka sanya kaya iri ɗaya.
"Ɗan uwa kawai tunanin rayuwa nake."
"To Ni bana son ganinka cikin yanayin nan."
"Shike nan."
Tashi muje babban parlour, Abbeey na neman mu." Ba musu Al-hassan ya miƙe.
Ƙananun kayane jikinsu, iri ɗaya, wandon da rigar, haka suke tafiya a step by step, har suka sauko babban parlourn.
Abbeey ne zaune cikin kayan sojoji yana kallon Tv, zama suka yi hankalinsu na kan tvn.
Wani harine aka kai farmaki, aka kwashe ƴam matan garin gaba ɗaya, sannan cikin tashin imani aka ma wasu yankan rago, aka bar tsofaffi a raye.
Hankalin Al-hassan ba ƙaramin tashi ya yi ba, idanunsa suka sauya launi, mutum guda ɗaya tak daya addaba al'umma, *Black Dragon* komai dake faruwa shike sanyawa ayi, ya rasa gane me hukumar ƴan sanda da jami'an sojoji suke yi, da suka kasa kama sheɗain ɗin nan.
Hatta Abbeey jikinsa ya yi sanyi, shuru kawai ya yi yana saƙa da warwara a cikin kansa.
Al-hussain ido kawai ya lumshe, babu abinda ya ji a jikinsa dan kuwa komai da ya faru a gabansa ya afku.............
*Washegari*
Tunda 6:00am Al-hussain ya gama shiryawa zai fita, Al-hassan ne ya shigo ɗakin daga masallacin ƙofar gida, Al-hussain kuma ba'a nan yake sallaba gaba ɗaya, ace wansa Masallacin babban kan titi nan yake zuwa sallah.
"Tun yanzu zaka fita?."
"Uhm ina da aiki ne sosai." Ya faɗa yana saɓa jakar bayansa.
"Ni bangane ma aikin nan na ka, gaba ɗaya ka sauya ka yi busy sosai, yaushe za ka dawo yarda kake? Na ƙosa ƙanina." Murmushi Al-hussain ya yi sannan ya rungume Al-hassan.
"Very soon." Ya furta yana mai sakinsa, da haka ya yi waje yana mai duba agogon hannunsa.
Al-hassan zama ya yi kan gadon Al-hussain, yana kewan ƙaninsa mai kula dashi, mai sonsa kuma mai gaskiya, ba wannan Al-hussain ɗin ba, gaba ɗaya ya fara bashi tsoro, ga rashin gaskiya dake ɗawainiya da shi.
Jiya a cikin kayan Al-hussain sai da ya tsinci passport na ƙasashe daban-daban, ga wasu paroers na kudaɗe masu yawa, bayan hakan ya duba wayansa, nan ma ya iske wasu abubuwa da yawa da ya kasa yarda, ɗayan wayan nasa na kashe, kuma yana da yaƙinin akwai wasu abubuwa a cikinsu wanda Al-hussain baya so kowa ya sani.
Sai a yanzu ya fara haɗa alaƙan hoton Senator Tumɓa da ya gani tare da Al-hussain.
Ya riga ya ɗaura ayar tambaya akan Al-hussain, a ina yake samun maƙudan kuɗaɗe? Ina yake aiki? Meke kaisa ƙasashe daban-daban? Wajen wa wake zuwa? Menene alaƙar sa da Senator Tumɓa???
Duk wa'innan sune tambayoyi da suka cika mai kai, suka hanasa walwala gaba ɗaya............✍️ END.