BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 3️⃣7

by @prettys01

> Duk wa'innan sune tambayoyi da suka cika mai kai, suka hanasa walwala gaba ɗaya...............

*Anas*

Buri ya cika inda tun washegarin ranar aikin boka ya kama Basma, ita da kanta ta kirasa akan ya zo gida tana son ganinsa, koda ya je suka haɗa ido komai ya sake rikici ma Basma.

Daga wannan ranar sai abinda ya ce take yi, a cikin sati guda ba ƙaramin dukiya ya tara da kuɗin ta ba, kuma ya hanata zuwa ko'ina, kullum tana gida.

Tsaki ya sake ja karo na barkatai sakamakon kira na huɗu da ya yi ma Basma amma wayar a kashe, a jikinsa yake ji akwai matsala, wani abu ya sami Basma, dan haka ya tashi ya ɗau makullin mota, gidansu Basma ya nufa kai tsaye.

Izuwa yanzu cikin Compound yake shiga, me gadi yaba sakon kiran Basma, da haka ya isa wajen da suka zaba zama ya zauna yana jiran fitowarta.

Mai gadi ya isar da saƙon ga A'isha mai aiki, sannan ya wuce, A'isha ta koma ciki ta isar ma Basma da sakon Anas.

Basma lumshe ido ta yi sannan ta tashi ta zura dogon hijab, yau basu fita ba, a part ɗinsu suka wuni, Fauza ce kawai ta je school, itama 1pm ta dawo da zazzaɓi.

Idanunta ne suka sauka kan Najlah dake zaune tana kallon India series a tv, tsaki Bassey ta yi ta nufa hanyar fita.

"Ina zuwa?." Ta ji muryan Najlah cikin isa, murmushin baki kai ba ta yi mata tana cewa.

"Wanda ya aje ki shi kaɗai keda hurumin wannan tambayar ba ke ba." Da haka ta buɗe ta fice.

Najlah baki ta taɓe, tana ci gaba da abinda take yi, a iya kwanakin nan ta fahimci babban raunin Basma shine Anas, hakan yasa ta sanya mai ido idan yazo, Basma na shakkansa sosai, ga wani tsoronsa dake bayyana a tare da ita, idan har ta ga kiransa ko ganinsa.

***********

"Ina wayarki?." Shine tambayar farko da ya yi mata bayan ta zauna.

"Ta fashe." Ta furta tana mai sinne kai.

"Meke damunki? Na ga duk kin sauya?." murmushi ta yi har lokacin idanunta suna ƙasa.

"Jiya ne na bige a hannu, amma da sauƙi." Ta kai nan tana nuna mai hannunta tun kafin ya gani ya isheta da tambayoyi.

"Sannu Baby, Allah ya ƙara lafiya?."

"Ameen." Da haka suka yi shuru sai kuma ya ce.

"Ina buƙatar kuɗi."

"Kamar nawa?." Murmushi ya yi.

"Million ɗaya kawai." Jinjina kai ta yi.

"Zuwa dare zan turo maka, zan koma ciki kaina yana ciwo." ba musu ya miƙe yana gyara ƙwalar rigarsa.

"Ok, karki manta dai, jeki ciki ki kwanta." Ta ɗaga mai kai tana miƙewa tsaye.

Da haka ta yi ciki shi kuma ya yi waje ba tare da ya damu da halin da take ciki ba.......

Haka rayuwa ta ci gaba da gangarwa, gidan Abba babu zaman lafiya, kullum da tashin hankalin da suke yi, har a gaban Abba idan rigimar su ta motsa haka suke yi, shi kuma baya ce da su uffan dan abinda Najlah ta roƙesa kenan.

Haka wani lokacin shaƙwaɓar Najlah baya tashi sai ta ga suna wajen, za ta hau bubbuga ƙafa tana narke mai, kamar abinda ya faru a yau Sunday.

"Baby idan har ka faɗi, za ka min jaki-jaki, za mu zagaye falon nan sau uku." Najlah ta faɗa tana murmushi, Abba dake zaune ya ɗaga mata kai.

Ƙwallon dake hannunta ta jefa mai, amma ya yi ƙoƙarin kamawa amma ya kasa.

"Jaririya cuwacuwa babu ƙyau." Dariya ta yi tana hawa bayansa bayan ya gyara jallabiyar jikinsa.

Take Abba ya fara zagaye Parlourn da Najlah a bayansa, suna yi suna shewa cikin nishaɗi da farin ciki.

Tun bayan farkawar barcin safe suka fara wasanni.

Tsayawa ya yi ita kuma ta sauka a bayan tana cewa.

"Baby motsa jiki muke fa, balle kai ya kamata ka dage da yi sosai bana so ka aje tumbin da wuri........" Da sauri ta kalla ƙofarsu jin an buga sau ɗaya da ƙarfi, kuma kafin ta ce wani abu aka buɗe aka shigo.

Marwa ce ta shigo bakinta ɗauke da sallamar data kasa ƙara sawa sakamakon yanayin da ta gansu, cikin second ɗaya....biyu ta fice ta buga musu ƙofa.

"Mtwwwsssss yaran nan basu da tunani, da ace a wani yanayi muke fa?." Cewan Najlah kamar wata babba.

Abba murmushi ya yi yana miƙewa tsaye.

"Muje mu fara breakfast, sai in ji neman me ake min." Da haka ya fara gaba, ita kuma ta ɗane wiyarsa tana cewa.

"Muje a haka Babyyyyyy." be mata musu ba dan kallon yarinya ƙara yake mata.

A babban parlourn ya zaunar da ita kan kujera yana ɗan haki.

"Masha Allah matar Abba kin fara nauyi." Sai ta miƙe ta riƙe hannayensa, suka fara takawa zuwa stairs.

"Ai daga yau shike nan, gobe zan fara aiki, duk na ƙosa gobe ta yi."

"Hmmm Insha Allah." Da haka suka zauna suka fara cin abinci yana bata a baki itama tana bashi.

A kuma dai-dai lokacin Yaran Abba suka isa wajen, kowacce ta zauna suna haɗa baki wajen gaishe da Abba.

"Lafiya lau Yaran Abba." Da haka ya bisu da kallo ganin babu wacce ta gaishe da Najlah, wanda kullum haka suke sai ya yi magana sai su gaisheta ciki-ciki.

"Ita Auntyn ta ku fa?." Ya faɗa yana haɗe fuska.

Sai da suka dalla mata harara kafin suka gaisheta, Najlah ta tura baki tana magana da sigan shaƙwaɓa.

"Uhmmm Baby Basma ta harareni." wani kallo Abba ya watsa ma Basma yana mata kashedi da yatsa.

"Kiya ƙuri." Ta faɗa tana damƙe cokalin hannunta, a kwana biyun nan Abba gaba ɗaya ya sauya, dan ya musu faɗa su yi kuka abune mai sauƙin, kuma ya kwana lafiya ya tashi lafiya, bakamar da ba har baki yake kasawa.

Shuru wajen ya ɗauka kafin Najlah ta ture abinci tana bubbuga ƙafa.

"A....abincin yaji." Sun riga sun san iskancin Najlah dan haka babu wacce ta kalleta, yam bons take ci, kuma kusan duk sun ci, babu yajin komai zallar bariki ne da iskanci.

Abba kuwa lokaci guda ya ruɗe ya fara mata sannu, yana bata duk wani abu da yasan zai rage mata yajin dake harshen ta.

"Ammeen Basma me kike so to?." Ya tambaya ganin ta ƙi cin komai.

"Dambun indomie da ƙwaiiiii" ta faɗa tana jingina hannunta jikin na Abba.

"Kee je ki sa A'isha ta girka mata sai ki kawo mata yanzu nan." Fauza kamar za ta fashe haka ta tashi ta nufa Kitchen dan ita Abba ya kalla.

"Uhmmm Marwa me ya kawo ki part ɗin mu ɗazu? Yana da ƙyau kafin ku shiga waje, ku jira a baku izini, dan kauce wa mugun gani." Najlah ta kai nan tana zuba mata lulu eyes ɗin ta.

Ƙaramin tsaki Marwa ta yi, dan tasan dole ta yi magana saboda kallon da Abba yake mata.

"Uhm dama Audu Driver ne yake nemanka urgent, shi yasa na zo."

"Bara na leƙa na ga ko lafiya." sai ya fara ƙoƙarin tashi, da sauri Najlah ta zaunar da shi, sannan ta ɗauki doyar dake gabanta gutsira ta yi sannan ta kai mai baki, be bata kunya ba ya gutsira.

Kiss ta hura mai da baki shi kuma ya kai hannu kan iska ya kama alamun ya cafke kiss ɗin, tare da kai iskan bakinsa ya haɗiye.

Murmushi suka yi, da haka ya tashi ya wuce.

Kamar jira suke Basma ta ce.

"Kinji kunya wallahi, banza shashasha." Har Najlah za ta kulata sai Fauza ta dungura mata Plate ɗin indomi gabanta.

Ido Najlah ta zaro tana kallon jaƙwalƙwalon da aka yi, indomie daga gani jiƙasa aka yi sai aka tace, sannan aka haɗa da ɗanyen ƙwai aka zuba a tukunya, maimakon a soya da mai, sai ta zuba ruwa, ruwan ma na Doya ne da aka tace. Sai gishiri da yaji abu ko ƙyan gani babu.

"Me......meye wannan?."

"Indomien da kika ce mana." cewan Fauza tana fara shan Tea.

"Waya girka?."

"Ni mana." Da haka Najlah ta miƙe tsaye.

Wucewa ta yi, sai suka kwashe da dariya.

"Kin min daidai Fauza ina sonki."

"Nima ina sonki Bassey." Hankalinsu ne ya koma kan Najlah, da mamaki suka ga ta nufa main door ta murza key, sannan ta wuce bedroom dinta da key, cikin ɗan lokaci ta fito da wannan bulalan injine.

Bayan wancan faɗan da suka yi, sau biyu suna sakewa, kuma duk ba su ji da daɗi ba wajen Najlah, sun gama yarda tana da Aljanu, shi yasa sai harara da baƙin magana, ita kuma ta adana bulalar a ɗaukinta.

Tana isa wajen ta zauna tana mai yin murmushin mugunta. Take su kuma kowacce ta shiga hankalinta.

"Ɗauka ki cinye abincin nan?." Najlah ta faɗa a kausashe, Fauza ta ce.

"Banci abinci da safe."

"To wallahi sai kin ci wannan, ko na miki matsiyacin duka." da haka ta ɗauke cup ɗin gabanta ta aje mata Plate ɗin.

"Ke wai wata irin mahaukaciya ce, kin zo mana gida kina hana mu zaman lafiya, na gaji da duk abinda kike mana, haba dan Allah." Faɗin Basma da ta kai ƙarshe.

Najlah ta bar musu Dining area ta zauna a babban parlour tana cewa.

"Kinsan Allah Fauza sai kinci abincin nan." A zafafe Basma ta yi kanta ,ta isa gabanta tana tsayawa.

Ta manta duk faɗar da suka yi, tako cacimi rigar Najlah tana kai mata mari, da sauri Najlah ta riƙe mata hannu tana cewa.

"Nasan maganinki Basma, duk abinda ke kanki zan sauke miki shi." da haka ta raruma ƙafafun Basma, ta yi sama da ita, ta nuna ma Allah sannan ta saketa kan kujera.

Take ta kuma ta yi sama da ita, ta yi hajijiya mai yawa kafin ta saki Basma, ai ɗauke huta Basma ta yi gaba ɗaya.

Ganin haka Fauza ta fara kai indomie nan bakinta, tana ci miyanta na cinkewa, ai da sauri ta tashi ta je wajen sink, sai amai.

A dispenser Najlah ta ɗibo ruwan sanyi, ta watsa ma Basma.

A gigice ta farka tana salati, Marwa dake kallonsu ta sauke ajiyan zuciya ganin Basma ta dawo hayyacinta.

Knocking Abba ne ya dawo da Najlah daga ƙoƙarin marin Basma, ƙwafa ta yi tana aje bulalan kan Center table, ta nufa main door, ta cire luck tana buɗe mai ya shiga.

Murmushi ya sakar mata.

"Baby lafiya?."

"Lafiya lau ba lafiya ba, a ta baya na yi ajiyan wasu manyan ƙarafa masu tsaɗa, shine yau ba'a ga komai ba, na yi mamakin da suka ce babu wanda suka ga ya ɗauka, kayan da yawa sosai, a ƙalla za su kai 7million."

Da haka suka zauna, sai ya kalla Basma da jikinta ya yi sanyi.

"Me ya jiƙa ki?." Ta nuna Najlah ta fashewa da kuka.

"Abba ka saketa, wallahi wata rana za ta kashe mu, mahaukaciya ce, mai manyan Aljanu, wallahi ba ta da imani." Ta kai nan tana riƙe ƙafafun Abba.

Abba ya kalla Najlah dake jikinsa, cikin sanyin halin ya ce.

"Ammeen Basma a dinga sassauta hukunci, kinga yarane." Baki ta tura, tana shaƙwaɓa.

"Uhmmmm to My Mubee."

"Yauwa Jaririyata, Marwa da Fauza ku zo nan, Ammeen Basma za ta faɗa muku dokokinta wanda idan kuka bi za ku zauna da ita lafiya." Najlah ta sake shigewa jikinsa tana cewa.

"Ina sonka, Basma ɗan matsa gefe." Basma cikin fushi ta miƙe, sai kuma ta nema waje ta zauna jin hajijiya na kamata.

Fauza ta gama amayar da komai, sannan ta iso parlourn ta zauna a ƙasa gefan Basma, tana lasan lemun tsami, Marwa ma ta zauna suna zuba ma Najlah ido.

"Baby ke ake jira." Cewan Abba yana latsa wayarsa, Najlah ta matsa daga jikin Abba tana ɗan yi miƙa sannan ta daura ƙafafunta kan Center table tana cewa.

"Daga yau na haramta ma masu girki suka aikin Kitchen gaba ɗaya." kallon mahaukaciya suka yi mata, ita kuma ta musu na kashedi tana ci gaba da cewa.

"Haɗuwa za ku yi wajen girki, dan ba zan aurar da ku baku iya komai ba, balle ke Marwa, dole ki dage wajen sarrafa abinci nau'i-nau'i, masu girki za su ci gaba da gyare-gyaren gidan kafin shima ya dawo kanku, be kamata kuna mata ba amma baku iya komai ba........." Ganin Abba ya katseta sai suka ji daɗi, amma abinda ya furta yasa suka tabbatar da Najlah ta asirce Abba.

"Uhmmm Ammeen Basma, wa zai koya musu?."

"Ni da kaina Babyna."

"Yauwa, Ni kaina zan so su iya aikin gida, kai ku gode ma Mahaifiyar ku, wallahi kunyi sa'ar Uwa." Ƙunƙunai suka fara yi ita kuma Najlah ta ci gaba da magana.

"Abu na biyu, Basma, yaron dake zuwa wajenki, ki dakatar da shi, sam be min ba, ya yi kama da marasa gaskiya.........." da sauri Basma ta ce.

"Bange me mikike nufi ba? Wai Anas? To wallahi sai ya zo tunda Ni naga Ni, na ce ya min, ke sani banga wanda zai hanani auren Anas ba, wallahi wallahi." Ta kai nan tana ma Najlah kashedi.

"Haka kika ce?."

"Eh Najlah."

"Hmmmm shike nan, Ni kuma ya zo ya gani idan za ki fita, kinsan launina banda ƙyau, Abba karka shiga rigimar uwa da ƴaƴanta." Ta kalla Abba dake shirin magana.

"To bara na shiga ciki." da haka ya miƙe tsaye sannan ya kalla yaran nasa.

"Kuyi mata biyayya, ina da tabbacin ba za ta cutar da ku ba." Da haka ya wuce ya barsu.

Marwa hawaye suka gangaro daga cikin idanunta.

"Ke yanzu bin boka abu ne mai ƙyau? Kalla yarda kika mai da mana Abba, kamar wani robot, sai abinda kika ce yake yi, wallahi ƙarshenki ba zai yi ƙyau ba." shuru ta yi ganin Najlah ta watsa mata uwar harara.

"Na uku, biyayya, dole kumin biyayya matsayina na magaifiyarku, wallahi daga irin wanna ranar ba zan sake ɗaukan rashin hankali daga wajenku ba, wacce kuwa ta ƙi ji, to tabbas zan barta a kwace........ku je part ɗin ku, ku gyara shi tsaf, daga yau gyaransa ya dawo hannunku, zuwa yamma za mu fara shiga Kitchen, kowace ta zama ready ko na nuna muku baƙaƙen aljanun da suke kaina, ku tashi zan leƙo na ga aikin ɗakin." ta kai nan tana haɗa musu da tsawa.

Lokaci guda suka tashi suka bar part din suna jin kaman su fashe da kuka.

Najlah ta yi murmushi tana gyara zamanta kan kujera, ta gama sanya ma Anas ido, duk kayan Abba da aka sace, Basma ce ta ba Anas, kuma sau da dama tana duba wayar Basma, nan take ganin maƙudan kuɗaɗen da take tura mai, bayan nan akwai wata rana da ta bi bayan Anas ɗin, sai dai abinda ta gani ya bata mamaki.

Dan kuwa wata budurwa ya sace, ya tafi da ita wani gida, Najlah sai da tasan yarda ta yi ta haura ta saman katanga ta shiga, nan fa ta ci karo da mugun abu, Anas ya buga ma yarinyar wani karfe kanta yana ta jini, a haka ya hayyake mata, ta so a ranar ta yi maganinsa sai dai wasu manyan karnuka da suna ganta, suka fara haushi da ƙoƙarin fitowa daga kejinsu, hakan yasa ta bar gidan da gudu.

Amma ta yi alwashin shafe Anas daga rayuwar Basma gaba ɗaya, daɗin daɗawa yana bin malamai, kuma akwai asirin dake cin Basma, wanda daka ambaci sunansa duk take ruɗewa. Murmushi ta yi tana tsara ta yarda za ta shafe tarihin rayuwarsa gaba ɗaya.........✍️ END.

> Najlah boom.