PAGE 3️⃣8
by @prettys01
> Amma ta yi alwashin shafe Anas daga rayuwar Basma gaba ɗaya, daɗin daɗawa yana bin malamai, kuma akwai asirin dake cin Basma, wanda daka ambaci sunansa duk take ruɗewa. Murmushi ta yi tana tsara ta yarda za ta shafe tarihin rayuwarsa gaba ɗaya.............
Kamar yarda Najlah ta ce, bayan 30mnt ta nufa part ɗin su Najlah, ta iske sun gyara ko ina dama ba wani datti ya yi ba, a lokacin ta ji daɗin ganin sun fara mata biyayya, da haka ta barsu, ta koma wajen Abba aka dasa sha soyayya.
5pm dai-dai ga shiga Kitchen, ta iske suna ciki suna tsatstsaya, dan ta sanar musu 4:50pm su shiga Kitchen.
Murmushi ta sakar musu, su kuma suƙa ƙare mata kallo, su kansu sun san Najlah ƙyaƙyƙyawa ce, a ƙyawawan ma wannan dabance, ko wani irin kaya ta sanya sai sunyi mata ƙyau, yanzu sanye take da riga da skirt na atamfa, sunyi mata ƙyau sosai, haka kuma sun ƙara haska fatarta.
Fauza da zuwa yanzu ta fara son su shirya da Najlah ta yi murmushi, har ga Allah ta kwammaci ta zubar da duk makaman yaƙinta, dan ba ƙaramin wahala Najlah ke bata ba, kullum sai ta sha magani kafin ta kwanta saboda ciwon kai, ta kwammaci su shirya ta yi biyayya.
Da mamakinsu suka ke kallon Najlah ta zauna kan kujera tana cewa.
"Basma ki fara blanding kayan miya, Fauza ki yanka mana Albasa slize mai yawa, ke Marwa kuma nama za ki wanke ki tafasa." Sai suka fara kallon kallo, dan kuwa duk abinda ta faɗa basu san taƙamaiman wajen da zasu gani ba.
Ido Basma ta zare tana ganin abinda Najlah ta fito da shi daga gefan skirt ɗin ta, lokaci guda suka haɗa baki wajen furta *Bindiga.*
"Eh shine, ko kuyi yarda nake so, ko na alburushe ku har lahira." ai lokaci guda suka ruɗe, kowacce ta fara dube-dube.
Marwa ta fara ganin albasa da kayan miya, ta miƙa musu, ta buɗe fridge ta ɗauki nama.
Take kowacce ta hau aiki babu tsayawa, bayan Marwa ta sanya naman a huta, ta cika ruwa, sai da Najlah ta sa ta rage.
"kisa magi 8, curry kala biyu da mai ƙamshin da mai citta da garlic." cewan Najlah, sai Marwa ta ɗau robobin da suke farko, ta zuba kaɗan, ɗayan har za ta zuba ta ji ƙamshin daddawa, sai ta aje ta duba wani, har dai ta samu na garlic, ta zuba sannan ta rufe.
"Fried rice zamu yi yau, sai Farfesun kifi, wanda Basma ke za ki yi mana shi, ki ɗau kifi ki wanke, zan miki bayani, Fauza yanke-yanke shine aikinki, Carrot, green beans, green pepper, da duk wani abu na yanka ke za ki yi, bayan kin gama za ki haɗa kosulo dan haka ki sanya eggs 10 a huta yanzu." Ba musu Fauza ta fara abinda ta ce, amma Basma na tsaye, jin wai kifi za ta wanke.
"Ya na ganki a tsaye?."
"Bana son ƙamshin kifi, damuna yake yi, kiban wani aikin dai." Cewan Basma tana jin bakin ciki na cin zuciyarta.
"Ayya, shi na baki dan haka shi za ki yi, kuma dole. Marwa yanka plantain, na ga kina tsaye." Da sauri ta ɗauka plantain ta shiga yankawa.
Basma ganin Najlah na gyara bindiga yana ta ɗan ruɗe, ta buɗe fridge ta ɗau kifi guda biyu, sink ta nufa, ta aje su, sannan ta ɗauke hancinta da ɗan kwali, tashiga wanke su tsikan jikinta na tashi.
Najlah murmushi ta yi, dan abinda Basma ta yi ranar nan ya tsaya mata a rai, ta tsinke A'isha da mari, Wai akan me yasa da soya kifi bayan tasan da yamma take dawowa gida, daga wannan ranar Najlah ta yi alƙawarin sai tasa Basma aikin kifi.
Wayar Basma ne ya hau ringing, da sauri ta ɗauka ganin Anas ne.
"Dan Allah ka ya kuri, gani nan zuwa Masoyi." Da haka ta katse kiran, sannan ta wanke hannunta harda sanya hypo.
Kallon Najlah ta yi ta ce.
"Yanzu zan dawo, dana dawo zan ɗaura." Hanya Najlah ta bata, ganin haka Basma ta fice harda gudu-gudu, sama ta haura dan sauya kaya.
"Auta kulle main door ki kawo min keys ɗin." Ba musu Fauza ta fice ta cika Umarninta, amsar keys ɗin ta yi ta sanya cikin drower tana ba Marwa umarnin duba nama...............
*Al-hussain*
Cikin wata aniyar mota yake Bugatti Chiron Super Sport 300+, launin ɓaki mai sheƙi, agogon hannunsa ƙirar Rolex ya kalla, kafin kuma ya yi wani motsi sai ga motar Merry ta faka a gabansa, murmushi ya yi yana mai da p-cap kansa.
Merry ta shigo motar tana cewa.
"Promise."
"Promise! Promise." Da Haka ya yi ma motar key suka fara tafiya.
"Uhmmm Al-hussain ina so na tambayeka abu guda ɗaya tak?." Kai ya ɗaga mata, sai ta ci gaba da cewa.
"PA.1 ya faɗa min cewa Naira miliyan huɗu ka tura mai ɗan yi ma Momy addu'a, bayan wasu maƙudan kuɗaɗen da kake tura mai ɗan gyare-gyaren wasu waje a ........." Katseta ya yi da cewa.
"To me ya faru?."
"A ina kake samun kuɗi? Ko Ni kaina 2M ka turamin jiya, kasan kuwa a halin yanzu Al-hassan ya fara zarginka, iya sanina *Promise* ne siriin mu, amma bayan haka akwai wani abu da Ni bansani ba akanka." Ta kai nan tana ƙare mai kallo.
Murmushi ya yi yana laƙwsa wiyarsa hagu zuwa dama sannan ya ce.
"Kin yarda da Ni?."
"Uhm."
"To ki ci gaba da yadda dani ba zan baki kunya ba, dangane da inda nake samun kuɗi kuma, halal ne, babu kuɗin haram a ciki, sanin kanki ne ina da tausayi sosai, ba zan iya cin amanar ko dabba ba bare mutum." Kai ta jinjina tana yarda 💯.
A wajen da suka saba tsayawa duk weekedn nan suka tsaya, sannan suka yi murmushi suna kallon wajen.
"Ki sauya kaya sai ki shiga, na zo miki da wani gashi." Ya faɗa yana aje mata wani leda kan jininta.
Da haka ya fice yana murmushi, da kanta ta kulle motar bayan ta fito, sannan ta shiga Opposite Inda Al-hussain ya shiga...
Bayan minti 40 suka bar unguwar ransu fes, a inda ya ɗau Merry ya ajeta, sanna suka yi sallama ya yi hanyarsa itama haka..........
* Senator Tumɓa*
Shuru ya yi a cikin motar yana murmushi, jin harin da aka kawo musu, harbi kawai kake ji tas-tas-tas, kusan gaba ɗaya securities ɗin sa aka kashe, kafin yaga an buɗe motarsa, idanunsa suka sauka kan na *Black Dragon* kamar kullum cikin baƙaken kaya yake, sai fuskarsa da ya rufe da kyalle.
"Black......" Wani abu ya shaƙa mai, sannan ya jimai ciwuka sosai, sakin sa ya yi, lokaci guda kuma yasa aka kunna ma motar huta, ƙaran jiniyan sojoji yasa ya yi ma yaransa alama da su gudu, nan suka bar wajen a cikin wata mota, shi kuma ya samu ya ɓoya.
Da yake a kan titine suka kai ma Senator Tumɓa farmaki, sai ga mutane da jami'ai sun fara cika wajen, harda motan asibiti an zo inda aka fara ƙoƙarin ceton Senator Tumɓa wanda motarsa take ci da wuta.
Baƙin wando ne jikinsa da farin riga, ya cire na bayan, sai P-cap baƙi shima dake kansa, murmushi ya yi yana zuba kayayyaki cikin jakkar bayansa, sannan ya ja fask mask ya rufe fuskarsa, shiga cikin mutanen da suke tsatstsaye suna kallon abinda ya faruwa ya yi, a kan leɓansa ya furta.
"An gama da wannan." Da haka juya yana barin wajen dan ƴan sanda sun cika ko ina, sai bincike ake baya an sanya Senator Tumɓa a gadon asibiti cikin motar asibiti sannan suka bar wajen, cikin gaggawa dan Senator Tumɓa ya ɗauke huta gaba ɗaya.
*Primecare Hospital*
Cikin sauri Nurse's Suka tura gadon da aka kwantar da Senator Tumɓa, sannan aka nufa emergency world da shi, ana shiga aka fara bashi taimakon gaggawa, lokaci guda kuma wani doctor ya shigo cikin farar rigar Doctors.
Ganin halin da yake ciki ya girgiza kai yana cewa.
"Ku kira Dr. Ashraf."
Da sauri Nurse ɗaya ta yi waje cikin sauri-sauri har tana tumtuɓe dan kuwa idan har Senator Tumɓa ya rasa ransa hakan zai kawo babban matsala a ƙasar nan, yanzu haka ma cikin asibitin cike yake dam da mutane suna ta kuka ta ƙara tabbar da cewa shi na gari ne, tunda har aka kai mai farmaki.
Knocking ta yi sau uku, kafin ta yi na huɗu, ta ji anyi gyaran murya, hakan yasa ta murɗa handle din ta shiga hankali a tashe.
Idanunta suka sauka akan matashin dake zaune kan table yana latsa system, Choculate skin karesa, mai shaning da cika ido, a kallo ɗaya za ta za ka fahimci ma'abocin murmushi ne, dan murmushi yake yi a yanzu ma.
Yana da ƙyau mai sunan ƙyau, dan daga sama har ƙasa Doctor Ashraf maƙurane wajen ƙyau ga tsafta.
Glass ɗin dake idanunsa ya cire tana zuba mata fararen idanunsa.
"Sir, Senator Tumba has been brought in in critical condition. We have done everything possible to stabilize him, but there has been no improvement." Kai kawai ya ɗaga mata, ta yi waje sannan ya miƙe daga kujerar.
Manyan kayane jikinsa, wanda kodayaushe cikinsu yake, babu wanda ya taɓa ganinsa da ƙananun kaya, haka rayuwarsa take.
Ƙofar ɗakin ya buɗe da sauri, gaba ɗaya hankalin su ya koma kan Dr. Ashraf, mamallakin asibitin kuma Babban Likita (Chief Consultant). Mutum ne mai girman matsayi, wanda ya gina sunansa wajen ceton rayuka da ƙwarewa ta musamman. A cikin wannan asibiti, shi ne na ƙarshe wajen yanke hukunci.
Sanye da farar riga mai tsabta, stethoscope na rataye a wuyansa, ya nufi gadon Senator Tumɓa kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba. Da shigowarsa kawai, sauran likitocin da Nurse's suka ja bayan kowanne ya gaishesa.
Kallom Na'urorin duba lafiya da suke ci gaba da ƙara sauti a hankali, yayin da yake duba bugun zuciyarsa, numfashinsa, da sakamakon da ke kan allo.
Shi yaba da umarnin da a kawo mai wasu allurori tare da ƙarin Oxygen, nan da nan aka fara shiga da kowa ma duk dan su rasa ran Senator Tumɓa.
Dr. Ashraf be samu natsuwa sai da Senator Tumɓa ya farfaɗo amma yana cikin mawiyacin hali, gode ma Allah ya yi sannan ya cire farar rigar aikin sa da ya ɓaci da jini.
Har zai wuce office, wani Doctor ya ce.
"Dr. Ashraf ga jama'a can suna cikin damuwa da rashin sanin madafa akan Senator Tumɓa, haka jami'ai sun zo, ya kamata kaje ku gana da su tunda komai a ƙarƙashin yake." Kai ya sake jinjinawa sannan ya nufa haraban asibitin.
Idanunsa ya ɗan zaro ganin mutanen da suke wajen, ai kuwa ana ganinsa ƴan jaridu suka yi kansa da tambayoyi.
Jami'a suka takarar da su, sai da suka daidaita tukun kamilalliyar muryasa ta fito.
" Senator Tumɓa yana cikin wani hali sosai, ku dage da mai addu'a, dan kuwa ba ƙaramin jigata shi aka yi ba, bawan Allah ya farfaɗo amma baya cikin tunaninsa, dan haka ku dage da mai addu'a shine kawai." Da haka ya yi ciki, jami'a suka rufa masa dan ba Senator Tumɓa kariya.
Wata ƴar jarida ta share hawaye tana cewa.
"Ya kamata a kama mugayen ƙasar nan, yanzu ace Senator Tumɓa Hasken Al'umma shi aka kawo ma mafarki, duk saboda ba'a son ya rayu, kuma Insha Allah zai ya rayu, sai ya zama shugaban ƙasar nan, da haka muna roƙan Allah ya tashi kafaɗunsa......." Sai kuka ya ƙwace mata, nan fa kowa ya fara fesa albarkacin bakinsa, wasu na kuka wasu na cikin damuwa.
Ƴan jaridu suna ta yaɗa abinda ke faruwa.
"Me yasa kowa kansa ya sani? Me yasa mutane basu damuwa da talakawa ne? Har ga Allah duk abinda ya samu Senator Tumɓa, sai munyi zabga-zabga akai, wannan farmakin ma ba za mu bari ya tafi a banza." Cewan wani matsayi yana share hawaye, dan kuwa Senator Tumɓa me ya biya ma yara 83 kuɗin shiga jami'a, harda wannan matashin.
Ai take matasa suka har ziƙa, suka fita kan titi, aka fara ta da husuma suna ɓarna, ba su tsaya iya nan ba, sai da suka je gidan gommati suka fara fashe-fashe.
Saƙo daga shugaban ƙasa MUHAMMAD BABANGIDA SHAMAKI "Duk wanda ya yi ɓarna a kamashi."
Wannan furucin ya ƙara hura wutar rigama, dan kuwa matasa da yawa aka kulle aka hana belinsu, nan fa mutane suka ƙara tabbar da basu yi sa'ar shugaban kasa na gari ba, ga na garin can akwance babu lafiya, wasu kuma da dama sun ɗaura zargin su akan Shugaban ƙasa, dama babu wani jituwa tsakaninsa da Senator Tumɓa, sai ake ganin shi ya mai wannan farmaki...........✍️ END.