PAGE 3️⃣9
by @prettys01
> Wannan furucin ya ƙara hura wutar rigama, dan kuwa matasa da yawa aka kulle aka hana belinsu, nan fa mutane suka ƙara tabbar da basu yi sa'ar shugaban kasa na gari ba, ga na garin can akwance babu lafiya, wasu kuma da dama sun ɗaura zargin su akan Shugaban ƙasa, dama babu wani jituwa tsakaninsa da Senator Tumɓa, sai ake ganin shi ya kai mai wannan farmaki...............
************
Babu wacce jikinta be yi sanyi da al'amarin ba, banda Najlah da hankalinta ke kwance, tana kallon duk abinda ke faruwa, ranta ya sosu sosai, amma ta shanye komai, dan kuwa daga gobe komai zai fara, daga gobe wasan za'a soma, ta ga salon wasan Senator Tumɓa, ya jira ya ga kalan wasan da za ta buga, da shi da tsinanna ogansa.
Basu jima da gama cin abincin dare ba, shine suke zaune a parlourn suna kallo labaran da ya zagaye ko ina.
Najlah tunawa ta yi da abinda ya faru ɗazu, bayan Basma ta sanya wata ash Abaya ta fito za ta wajen Anas.
A rufe ta ji ƙofar, hakan yasa ta nufa Kitchen tana tambayar waya kulle ƙofa.
"Babu inda za kije Basma, aiki kike yi." Da haka Najlah ta ci gaba da latsa waya, su kuma Marwa kowacce tana aikin gabanta.
"Bangane ba, ke karki ga ina miki biyayya kisha tsoranki nake, ban makulli?." Ta miƙa hannunta, sai dai Najlah ba ta kalleta ba.
Basma tana shakkar ta sa mata hannu a jiki, aljanunta su motsa, hakan yasa ta shiga Kitchen ɗin, akwai ƙofa wanda zai fitar da kai Compound, kofar ta nufa ta fara ƙoƙarin buɗe wa, sai dai a kulle ba dama.
Tsaki ta ja tana kowa kusa Najlah.
"Ban keys? Wai uban me na tsare miki ne? Kince na miki biyayya kuma na yi, dan haka kiban keys kar ran masoyi ya ɓaci, wallahi da ransa ya ɓaci ƙwara na kashe ki na fita, ki ban makullai." Ta faɗa tana jin ta kai ƙarshe.
Najlah ta kalleta da ƙyau, gaba ɗaya duk ta ruɗe, murmushi ta yi ta ce.
"Wallahi babu inda za ki je." Da haka ta miƙe tana duba yarda Marwa ke soya shinkafa.
Basma a fusace ta yi part ɗin Abba tasan yana nan, sai dai nan ma a kulle, hakan yasa Basma fara dukan ƙofar tana kiran sunan Abba, duk kuwa ba balle Abba ya ji ba.
Tana cikin haka, ta ji an fincikota ta baya, tana juyowa Najlah ta ɗauke ta da mari.
"Kina hauka ne Baby na barci kike wannan ihun? Ki shiga hankalinki." Basma ta fara haki kamar za ta kai mata duka, ta tsaya gabanta har suna gogan jikin juna, a kausashe Basma ta ce.
"Magana na ƙarshe, ki ban keys zan fita, duk abinda ke kanki yana kaina Najlah."
"To nuna min kalan naki." Cewan Najlah tana ɗan ja da baya.....second 1........2.......3 wayar Basma dake hannunta ta hau amsakuwa, da sauri ta amsa tana kaiwa kunneta, da yake wayar na speaker Najlah ta ji abinda ya ke cewa.
"In banda iskanci kin shanayani, tun ɗazu nake jira, na biki 3mnt ko ki fito ko na wuce, in har na wuce ba zan sake dawowa ba........"
"Maso....." ƙet ya katse kiran.
Hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, ta share, sannan ta yi wani kukan kura ta yi kan Najlah, cikin sa'a ta sureta sama, sai dai abinda be fi second ɗaya ba, Najlah ta juya sai ga Basma a sama ita kuma ta duro ƙasa tana riƙe da Basma.
Tausayi ta bata dan haka ta saketa, sai ta zauna tana cewa.
"Faɗa da Ni babu riba." lokaci guda Basma ta riƙe ƙafafunta, Najlah ta zaci damben za ta ci gaba sai ta ji tana roƙanta cikin kuka da magiya.
"Dan girman Allah ki bari na je yanzu zan dawo, wallahi ba zan sake miki abinda baki so ba, minti biyar ya isa zan dawo dan Allah ki ban keys, kar ya yi fushi kinji." Har cikin ran Najlah ta ji daci, sannan ta ƙara ɗaukan alwashi wajen hukunta Anas.
"Dan Allah ki bani." Ta sake faɗa da rauni.
Kafin Najlah ta yi magana, wayar basma ta yi haske alamun saƙo ya shi, hannunta har rawa yake ta buɗe tana dubawa.
'*Na wuce.*' shine ta gani a rubuce, take ta ji gumi ya fara tsatstsafo mata, idanunta ta sake zarewa sai ta rintse, tashi ta yi ta haura sama da gudu lokacin guda tana kiran numbers amma a kashe, tashin hankali ba'a samasa rana.
Najlah ta jinjina kai tana komawa Kitchen.
Hannu tasa suka yi aikin gaba ɗaya, Fried chicken rice, doya da miyan plantain, sai Farfesun kifi, ga kosulo da Fauza ta haɗa, sannan suka yi pineapple juice.
Su kansu farin ciki suke yi a cikin ransu wai ace yau sune suka girka abinda za su ci.
A Dining area suka jera komai, sannan Najlah ta koma part ɗinta, ba ita ta fito sai bayan isha'i, bayan Abba ya dawo daga masallaci.
Su huɗu suka haɗu a Dining area suka fara cin abinci, sun jima suna ci sai ga Basma ta sauko gaba ɗaya ta sauya, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka, zama ta yi gefan Marwa amma ta kasa zuba komai ta ci.
"Me ya sami fuskarki?." Cewan Abba yana shan Pineapple juice.
"Kaina ke ciwo." Da haka ta yi shuru.
Marwa ta yi serving na ta.
"Abba ya ka ji kosulon?." cewan Fauza tana murmushi.
"Ba magana autata, dole na baki tukwici. Ammen Basma da gaske yarana suka girma abincin nan?." Najlah ta ɗaga mai kai tana kallon wayarta da ya yi haske.
Daukan wayar ta yi ta duba saƙon da aka turo mata ta email, murmushi ta yi tana cewa.
"Daga gobe komai za fara, gobe! gobe!! Gobe faa." Sai ta yi wani shu'umin murmushi.
"Baby menene?." Abba ta kalla sannan ta ce.
"Na ƙosa gobe ta yi, na fara fita, hmmmmm Ina son komawa wancan rayuwar akwai wahala akwai daɗi." Murmushi suka yi a tare.
Sai a lokacin Basma ta fara kai abincin bakinta, wani test ta ji ya gauraye mata baki, daɗi ya zarce har zuwa cikin kanta, batasan ta lumshe ido ba, ta sake kai wani loman bakinta tana haɗawa da kosulo da tsokan nama da aka yi peices da shi.
Najlah da Abba ne suka koma parlour, da haka suka samu damar tattauna tsakaninsu.
"Abincin ya yi daɗi."
"Uhm ba laifi." Cewan Basma tana sake kai loma bakinta, har a yanzu number Anas ba ta shiga gaba ɗaya bata cikin natsuwa.
Bayan sun gama suka dawo Parlour suka zauna, a lokacin kuma aka fara haska abinda ke faruwa a yau.
Abba cikin damuwa ya ce.
"Senator Tumɓa bawan Allah, insha Allahu zaka samu lafiya, Allah ya tona asirin tsinannun nan......kai ƙasar nan akwai gyara." Da haka ya yi shuru suna kallon short video da aka ɗauko ba Senator Tumɓa, jikinsa na'urori iri-iri, ga bandage ta ko'ina, duk wanda ya gansa a haka dole ya ji tausayin shi.
"Basma babu aikin da kika yi, dan haka ki gyara Kitchen, zuwa safe za ki yi wanke-wanken duka." Basma ta kalla Najlah tana maimaita kalmar WANKE-WANKE, ita ta manta ana wani abu wai shi wanke-wanke, ba za ta iya tuna when last da ta wanke roba ba, har ƙwanda spoon, sometimes tana ɗaurayewa a wajen aiki in za ta ci abinci.
"Me? Wanke-wanke fa kika ce?." Najlah ta ɗaga mata kai tana sauya Channel zuwa star plus, Kulfi the singing star ake, hakan yasa ta mai da hankali sosai tana cewa.
"Ƙwarai da gaske, kuma idan be fita ba sai kin sake."
Basma a cikin ranta ta ce 'Hmmm lallai za ki ga hauka kuwa'
Suma suna son series ɗin hakan yasa suka natsu suna kallo, Abba kuma ya koma part ɗinsa ya kunna labarai ya ci gaba da kallo.
Marwa ta fara tashi ganin kiran Al-hussain, a yanzu waya kawai suke badan tana so ba, ba kuma dan ba ta so ba, kawai dai suna waya.
Sai bayan da ta shiga part ɗin su ta ɗauka tana kunna tvn da ci gaba da kallon series ɗin, a hankali muryansa ta fito cikin sanyi.
"My love." Sai da ya kira sau biyu tukun ta amsa.
"Uhm."
"Mena miki? Kaman ranki yana ɓace dani kwana biyun nan." lumshe ido ta yi sai kuma ta girgiza kai kaman yana ganinta, a hankali ta furta.
"You changed." da sauri ya tari numfashinta.
"I'm sorry My Love, a haka ina ƙoƙarin nemanki sosai, dakinsan aikin dake kaina da kin tausaya min, Ni kaina rasa lokacin kaina nake."
"Hmmm amma zuwa yaushe za ka dawo yarda nake so."
"Muna yin aure, kina lissafi ko?." Murmushi ta yi.
"Eh ina lissafi, dan Allah Babyna ka dawo kamar da, mai sona sosai."
"Har yanzu ina sonki sosai, kuma za ki tabbar daga lokacin na mallake ki." Kafin ta yi wani magana ya furta abinda take mugun jin haushi, take jin babu a duk lokacin da ya furta.
"Excuse me, zan kira." Shike nan da haka ya katse kiran, tasan kuma sai gobe.
Idan ta ce bata kewan Al-hassan ta yi ƙarya, sau da dama tana kiransa amma ya yi blocking ɗin ta, haka kota mai magana ta whatsApp baya buɗe wa, tana ta ƙoƙarin ganin ta ciresa a ranta amma hakan ya citira.
Fauza ta turo ƙofar tana sallama, Marwa ta amsa a hankali.
"Har za ki kwanta?." Ta ɗaga mata kai.
"Gobe school, kuma Uwar Basma ta ce 6:20am zamu shiga Kitchen, yanzu haka Bassey tana Kitchen tana aiki."
"Kai matar nan tana da shegen jaraba, iskan da suke kanta sheɗanune." Fauza ta yi murmushi shiga ciki dan barci ya kamata sosai.
Marwa na zaune har Bassey ta shigo bakinta a sama, idan ranta ya yi dubu to duk Najlah ta bi kowanne ta hargitsa mata, tsaki ta ja, sai kuma ta miƙe ta shige ciki.
Marwa ba ta kwanta ba sai 10pm, bayan ta gama kallace-kallace ta yi karatu dan yanzu sun fara Exam a school.
*Washegari*
Bayan sunyi sallar asuba, sai suka kasa komawa barci, haka suka kasa fita zuwa Kitchen, a tunaninsu Najlah za ta leƙo su, sai dai bata leƙo ba ganin Basma har barcin safe ta yi, tana farkawar, ta ga ita kaɗai ce kwance a ɗakin basa nan, wayarta ta duba lokaci, 7:15am da yake ita yanzu zaman gida take yi.
Sauka ƙasa ta yi dan ganin abinda ke wakana, tun a stairs ta fara jiyo hirar Fauza da Najlah suna magana suna dariya, ido ta ɗan zaro tana ƙara sauri, haka ta tura ƙofar kitchen ɗin ta shiga.
Najlah na juya abinci a flask, Marwa na fita da su, Fauza na zaune tana zuba surutu kamar ba ita ba.
"Ammeen Basma, haka na kama yaron na ci ubansa, ranar a office din principal na wuni, sai da Abba ya je ya bada haƙuri shine suka sake Ni, da yake yaron dana duka babanshi lawyer ne, wai sai ya kai maganar koto........karfa kisha mugun duka ne, kawai kai na fasa mai da baki." dariya Najlah ta sake fashe da shi.
Marwa murmushi kawai take yi amma ta kasa magana kar Najlah ta rainata, duk da yau aljanun basa kusa.
Bayan sun gama zamansu shine suka leƙo dan ganin waye a Kitchen, sai suka isketa tana ta aiki ita kaɗai ne, da har za su koma sai kuma suka shiga kowa ya kama nasa aiki.
"Ai da an kai ki koton tunda ba wani abu ya miki ba, dan ya ce yana sonki."
"Ammeen Basma yaron da daƙiƙi ne, kaf ajin mu an sani, kawai saboda Mom ta ce Fauza ke ji za ki gani.....kawai sai na gani." Sai a lokacin Marwa ta kalla Fauza ta ce.
"Sannu babba, wallahi in aka ce min za ki yi haka ba zan yarda ba, gaba ɗaya bakinki da idanunki sun buɗe lokaci guda......." da sauri Najlah ta katse ta.
"Ahh sanyi Aunty Babba, Banga laifin Autar Abba ba, ai nan gaba duk wanda ya miki ki ci ubansa kuma Ni zan tsaya miki." Murmushi suka yi sai kuma suka kalla bakin ƙofa jin Basma ta yi gyaran murya.
"Bassey kin fito to sannu da tashi." Da haka Najlah ta nufa Dining area da flask.
Tana fita Basma ta shiga Kitchen ɗin.
"Matar nan lafiya take?."
"Bassey yau iskan basa kusa, karki yarda muke raha da ita........" Da sauri Basma ta katse ta da cewa.
"Ya isa! Haba dan Allah, da kishiyar Mom muke hira kuna washe baki......tir wallahi."
"To menene amfanin rigimar? Tunda muke cin uban mu." cewan Fauza tana wanke hannu dan sun gama.
Basma ganin basu saurareta yasa ta yi ƙwafa tana bin bayansu, zama suka yi suka fara breakfast, a lokacin Abba shima ya fito, suka haɗu duk suka yi ana hira gwanin nishaɗi amma banda Basma da take rai.
"Fauza ki shirya zan sauke ji a school, jiya mun fita da Abba na ga wajen aikina kusa yake da school ɗin ku."
"Laaa Ameen Basma aikin me kike yi?." Kafin Najlah ta yi magana, Basma ta make Fauza.
"Sunanta Najlah, ba Ammeen Basma ba, ki gyara bansan hauka." sai a lokacin Abba ya ce.
"A gaban nawa kike kiran sunan matata, ki shiga hankalinki, kuma Ni na zaɓa mata suna Ammeen Basma." Basma ta ture Plate ɗin gabanta tana tashi, Parlour ta koma ta zauna tana cika da ɓatsewa.
Tana zaune Marwa da Fauza suka haura sama, sai Abba da Najlah da suka wuce suna ƴan wasannin banza da wufi.
Basu san rashin samun Anas a waya yana sa ta ji wani iri, ita kanta tana son zuwa aiki amma babu dama, ya hanata gashi kuma be kirata ba.
Tana zaune Marwa ta sauko sanye da Barno buubuu, ta yada babban vail bayan ta sa longslip baƙi haka ɗan ƙwalin ma ɓaki, sai jakka da takallami duk baƙi, launin kayan akwai ɓaki, marron da ja, sai ta yi wani ƙyau na musamman.
Takaddane hannunta tana ƙara duba wani darasi wanda 9pm za su rubuta exam ɗin sa.
Gefan Basma ta zauna tana cewa.
"Me yasa ranki a ɓace ne? Anas ne ko?." ba ta yi mamaki ba da Basma ta ɗaga mata kai, rungumeta ta yi tana tsine ma Anas a cikin ranta, dan kuwa yana walahar da Basma.
Fauza ta sauko cikin shirin uniform, kitchen ta nufa ta ɗauko lunch box sannan ta dawo tana jiran fitowar Najlah.
Ƙafar part ɗin Abba buɗe, sai suka kalla a tare, Abba ne ya fito yana amsa waya, be jima ya katse kiran yana kallon ƙyawawan yaran nasa.
"Basma me yasa baki zuwa wajen aiki?." Cewan Abba yana kallonta.
"Abba hutu suka bani amma gobe zan koma." Kai ya ɗaga yana kiran Najlah.
"Shalele! SHALELE!! lokaci na tafiya kiyi sauri." ya kai nan yana murmushi ma haske, dan ganin Najlah ta fito lokaci guda.
A hankali suma suka kalla inda Abba yake kallo, take duk suka zaro ido waje, suna ƙare ma Najlah kallo, dake tsaye tana kallon Abba cike da soyayya harda kashe mai ido ɗaya.
Najlah na tsaye cikin cikakkiyar shigar DSS mai matuƙar ɗaukar hankali.
Ta sanya rigar sojoji mai haɗa koren kala da ruwan ƙasa, an ɗinke tambarin hukuma a kafaɗunta cikin tsari mai ƙayatarwa. A kugunta an rataye ƙaramin pistol cikin baƙar holster, yayin da hannunta na dama ke riƙe da doguwar bindiga cikin ƙwarewa da izza, alamar cikakkiyar jaruma ce da ta saba da aiki.
A ɗaya hannun kuma tana riƙe da wayarta sai wata jakka mai ɗan sheƙi. Takalmanta baƙaƙe masu sheƙi ƙafarsa sunyi mata daidai, yayin da gyalen kanta ya zauna cikin tsari yana ƙara mata kwarjini, bayan hular dake ciki ta sojoji.
A rubuce jikin rigar an rubuta *D.S.S Najlah* cikin salo da ƙyau ga ƙawa.
Idanunta har lokacin suna kan Abba, shima cike da wani irin salo na soyayya ya ɗan saki murmushi kaɗan, kafin ta kashe masa ido ɗaya a hankali, sai ya nufeta.
"Wow Mrs Mubeey, wannan ƙyau haka, uhmmm shi kuma wannan bindigan fa?." Ya faɗa yana kallon bindigan da ta ɗauko.
Murmushi ta yi tana ɗaga bindigan ta gyara zaman alburusan ciki ta ce.
"Ina shiga Barrack za harbe wani bakin mutum, ka tuna ranar da ka rakani muka kai files can?." murmushi ya yi dan bega wani abu ba, kawai wani ya tsaida da su, ya bincike su tukun suka shiga, shine Najlah ta sa mutumin a rai.
"Haba Jaririya ki ƙyalesa, mai da bindigan ciki, ke da za ki fara aiki yau, bansan wata matsala ta bullo." Ya kai nan cikin sanyi, baki ta tura sannan ta miƙa mai jakkarta tana komawa ciki.
Gaba ɗaya suman tsaye suka yi, sai a yanzu suka auna irin ƙarfinta ashe dai Soja ce.
"A.....Abba Ammeen Basma Soja ce dama?." sai ya kalla Fauza ya ɗaga mata kai.
"Ita ce mace mafi hazaƙa a rukuninsu, kuma saboda ƙoƙarin aka turo ta nan aiki, shi yasa kike ganinta a haka, jinin soja ce, mahaifinta sojon soja, haka yayyinta biyu maza, kuna ganinta a haka ko, tana karfi sosai, tun tana ɗaliba take dambe da manyan sojoji, kuma kullum sai ta yi laifi an horeta, horo ma irin na walaha, amma haka Ammeen ku za ta sake washegari, jan wiyace sosai, ina alfahari da ita." ya kai nan yana murmushi.
A lokacin ta fito tana taunar chewing gum.
"Muje." Ta amsa jakkarta sannan ta kalla Fauza dake kallonta cikin burgewa, gira ta ɗaga mata alaman tambaya, sai Fauza ta yi sauri ta sara mata.
Dariya Najlah ta yi tana rungumeta.
"Ammeen Basma ashe soja ce ke?."
"Uhm Auta."
"Shi yasa kike da ƙarfi." Da haka suka nufa ƙofa, Marwa ta bisu tana kallon yarda take tafiya cike da ƙwarewa kuma a natse.
Har Najlah ta buɗe handle sai kuma ta kalla Basma ta ce.
"Ki gyara Kitchen, ki yi abinci kafin mu dawo, tunda kina gida." Da haka suka fice, Basma ta dafe kai tana zama tare da cewa.
"So.... soja....No wonder." ta Lumshe ido tana kallonsu ta window, Marwa ta shiga motarta ta fita, haka Abba ya shiga nashi, sai Najlah da Fauza suka hau ɗayar motar Abba sannan suka fita a ƙarshe. Jin sautin wayarta cikin sabuwar waƙar da ta sanya ma Anas, ya sa ta zabura tana nufan waya sauri, ilai shine, cikin rawar jiki ta ɗauka tana kai kunninta............✍️ END.
> Najlah za'a hau bakin aiki, fatan sa'a 🥰, ashe D.S.S ce 🤭🤭🤭