PAGE 4️⃣0
by @prettys01
> "So.... soja....No wonder." ta Lumshe ido tana kallonsu ta window, Marwa ta shiga motarta ta fita, haka Abba ya shiga nashi, sai Najlah da Fauza suka hau ɗayar motar Abba sannan suka fita a ƙarshe. Jin sautin wayarta cikin sabuwar waƙar da ta sanya ma Anas, ya sa ta zabura tana nufan waya sauri, ilai shine, cikin rawar jiki ta ɗauka tana kai kunninta...............
"He...........hello." Ta faɗa cikin rawar baki tana zama kan kujera, a hankali ta ji muryansa mai sanyi yana cewa.
"Baki sona ko Basma? Ni na zo har......."
"Wallahi ba haka bane."
"Me ya hanaki fitowa?." Shiru ta yi dan batasan me ya kamata ta ce ba, ba dai za ta yi gigin sanar da shi, shegiyar matan Abba ce ta hanata fita, abin ai da kunya. Lokaci kuma ta ce.
"A....Abba na ɓata ma rai, shine ya kulla main door ya fita da keys ɗin." Ajiyan zuciya ta ji ya sauke.
"Da tun farko kin faɗa min haka ai, to shike nan anjima zan zo kinji."
"To kayafe min?." Ta faɗa tana share hawaye.
"Eh Babyna zuwa yamma zan shigo." Kamar yana ganinta ta ɗaga mai kai, sannan ta dasa hirar soyayya.
Ajere motocin suka fita kan titi, Marwa ta yi hagu, Abba da Najlah suka yi dama, ta Najlah na gaba shi kuma yana bayanta, tafiya kaɗan suka yi Najlah ta yi kwana bayan ta danna mai horn sau biyar a jere, shima ya yi mata.
A gefan titi ta yi parking, Fauza ta yi mata godiya sannan ta fita, tana tsaye har ta shiga *Event intranational school* sannan ta ƙara gaba.
*Primecare Hospital*
A jiya sai da aka haɗa mutane da jami'ai kafin wasu suka bar asibitin amma wasu a Premises ɗin suka kwana. Sannan zuwa safiyar yau ma an cika sosai.
8:34am na safe motar Dr. Ashraf ta yi parking a haraban asibitin, ya fito cikin wani gezna launin ƙasa, daga sama har ƙasa ya yi marching sosai, hannunsa riƙe da I.pad da kuma waya.
Mutane suka yi kansa suna mai Barka da zuwa, ya amsa ya musu murmushi.
Yasan duk saboda Senator Tumɓa suke dan haka yana shiga asibitin shi ya fara dubawa, har lokacin be farka ba amma yana numfashi da kanshi.
Farin ciki ya yi dan an samu ci gaba, ya sanar ma jama'a da an samu ci gaba, addu'a ta karbu.
Take mutane suka farin ciki suna nuna jin daɗin su a fili.
*RED ZONE COMMAND* Da misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, motar Najlah ta yi parking a bakin babban gate na barrack ɗin DSS Barracks, fitowa ta yi sannan ta nufa bakin babban get hannunta riƙe da wannan jakkar.
Jami'an dake tsaro suka miƙe cikin girmamawa bayan ganin ID card ɗinta.
"Officer Hafsat Abdullahi?." Ɗaya daga cikinsu ya tambaya. Ta gyara tsayuwarta cikin alfahari da jin kanta a yau.
"Yes."
"Welcome to the barrack, Madam." suka sara mata, itama ta sara musu sannan suka bata hanya ta shiga ciki.
"Wow." shine kalmar da ta furta tana kallon ko ina na cikin Barack ɗin, Komai yana da tsari kamar an zana shi da layi. Gidajen sojoji suna jerin gwanin tsari, babu hayaniya sai ƙarar takun ƙafafun jami'ai da ke wucewa cikin gaggawa. A nesa, ana jin umarnin horo yana tashi sama na wasu tarin sojoji da suke parrade. "Left! Right! Left! Right!" Sojoji suna motsi cikin tsari, gumi na zuba a fuskokinsu amma babu wanda ke nuna rauni.
Najlah ta sauke numfashi a hankali. Tasan cewa daga wannan rana, rayuwarta ta fara da wani sabon babi-babin da babu ja da baya. I A nutse ta ɗaga kai sama a cikin ranta tana ƙara gode ma Allah bisa wannan baiwa da ya yi mata, daga nan ta kalla hanyar da za bi kafin ta ci gaba da tafiya.
A natse take tafiya amma sautin takalmanta kawai ake ji a wajen saboda wajen interlock ne a malale - "Kaf… kaf… kaf…" - abin da ya sa wasu jami'ai dake wucewa suka juya suna kallonta.
Wasu na mamakin kyawunta, wasu kuma na kallon nutsuwarta da yarda take tafiya sak soja a gaban shugabannin sa.
Amma ita ko a jikinta, haka fuskarta cike take da confidence irin na gogaggun jami'ai.
Da ta isa babban office ɗin shugaban barrack, ta tsaya cak a bakin ƙofa, a jikin office din an yi wasu rubutu akai *General Barkono* shine a rubuce, da haka ta yi knocking sau biyu.
"Come in." wata kakkausar murya ta amsa daga ciki.
A hankali ta shiga ta tsaya, sara mai ta yi, tana mai murmushi dan ba wannan bane haɗuwar su ta farko.
"Officer Najlah reporting for duty, sir."
Wannan mutumin mai cike da izza cikin uniform din da suka ƙara mai ƙyau, ya ɗaga kai yana kalleta na wasu daƙiƙu kafin ya nuna mata kujera.
"Sit down, Officer Najlah A.B.D." ta zauna cikin nutsuwa, tana tunawa da mahaifinta General A.B.D.
Sai Barkono ya mai da hankalinsa gaba ɗaya kanta.
"A karo na farko da tawagar Black shadow suka nema a tura musu ke, suna buƙatar ki a aikinsu.....kinyi sa'a sosai, dan kuwa jami'an sirrin hatta hukuma bata da information a kansu, suke da information din kowa, sannan umarni daga shugaban ƙasa kawai suke samu, suna nan suna yawo kamar kowa sai dai babu wanda ya sansu, a haka suke aikinsu, shekara biyu da fara aikinsu, kuma kowani irin aiki suna kammala shi cikin ɗan lokaci kaɗan........sun tabbatar da ƙwarewarki shi yasa suka zaɓeki a cikin jerin sojoji dubu dari huɗu da aka ɗauka a gaba ɗaya ƙasar nan cikin wannan shekarar." Da haka ya nunfasa sannan ya dasa.
"Ni kaina zanyi alfahari idan har kika shiga wannan kurunin, su dan ƙasa suke aiki ba dan wani abu ba, suna jefa kansu cikin hatsari domin ceton al'umma, nasan kin san komai akan aikin nan da kuma *Black shadow*." Kai ta ɗaga tana sauke numfashin a natse.
"Daɗin daɗawa ke ƴar abokina ce General A.B.D, jarumin Namiji, shi kika Gada ai, naga videon traning na ku, gaskiya kin horu sosai." Murmushi ta yi tana sinne kai.
"Thank You Sir."
"You are welcome Dear."
Da haka Barkono ya buɗe drawer dake gefansa sannan ya fito da wani jan file mai ɗauke da alamar *CLASSIFIED* ya ɗora file ɗin a gabanta a hankali.
"Wannan shine aikin farko da aka baki tun zuwanki Abuja." Najlah ta ɗan kalli file ɗin kafin ta ɗago idanunta.
"Aiki ne mai haɗari?" ya sake faɗa a natse, murmushi ta ɗan yi kaɗan.
Tura file ɗin gabanta ya yi.
"Target ɗin ku shine… *Black Dragon*, komai yana ciki, sannan shugabanki zai miki ƙarin bayani." ta ɗaga kai gana buɗe file ɗin. Sunan Black Dragon kaɗai ya isa sanya manyan jami'ai cikin fargaba, balle ace an baka aiki a kansa...… amma ita, a hankalin a kwance ta buɗe file ɗin da hannunta, ta duba sannan ta mai da ciki.
"Thank You Sir." Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
"Yauwa, daga yanzu bake babu sanya wanna kayan har sai kunyi nasara, daga lokacin za'a buɗe miki office ɗinki, idan kuma kinfi buƙatar zama cikin *Black shadow* shike nan.
Ta jinjina kai sannan ta sara mai again.
"Sir an bani lasisin aiki da makaman da aka turo min gida, shin zan iya amfani da su wajen gyara ɓarna.?" Murmushi ya yi.
"An baki, sai dai kowani irin aiki ne, ya zama baki bar hujja ba, aiki da basira shine aikin ku." Sake sara mai ta yi tana imagine ta kan Anas za ta fara aiki.
Da haka ta nufa bakin ƙofa, hannunta yana kai handle ta ga an buɗe, sannan wani matashi ya bayyana.
Suna haɗa ido, ya sara mata yana murmushi ganin kaman ta ɗan tsorata.
"Al-hassan yarinyar A.B.D ce, a nan take aure." Cewan Abbeey yana kallon Al-hassan.
"Laaa ashe sister ta ce, wata rana za ki kawo mana ziyara har gida ko?." murmushi ta yi.
"Sosai ma kuwa." Da haka ta wuce, shi kuma ya ƙarasa ciki yana sake gaishe da Abbeey.
Zama ya yi yana shafa sunan kansa.
"Abbeey gani." Abbeey ya kallesa da ƙyau sannan ya ce.
"Tambayarka zanyi akan Al-hussain, ina da tabbacin kai za kafi sanin komai kunfi kusa sosai."
"Abbeey kenan da daane zance haka ne amma banda yanzu da Ni kaina bana gane masa, kuma abinda Al-hussain ɗin ya faɗa gaskiya ne, wajen aiki biyu yake zuwa, duk na bincika ance yana zuwa, kawai lokacin neman kuɗin nasa ne ya zo, sai na shi ya zo da yawa." Murmushi Abbeey ya yi.
"Yanzu ka same shi a wajen?." kai ya girgiza.
"A'a amma yana wajen Marwa."
"Shike nan tafi aikinka." sallama da haka suka yi sannan Al-hassan ya wuce wajen aikin sa.
*Marwa*
A hankali ƙafafunta suka shiga cikin ajinsu, idanunta na kan littafi hakan yasa ba ta an kara da mutumin dake gabanta ba, karo ta yi da kafaɗarsa hakan yasa ta yi baya littafin na faɗi ƙasa, da sauri kuma ta kalla wanda ke gabanta jin ƙamshin turaren Al-hussain.
Cike da mamaki take kallonsa har tana ƙyafta ido, ta rasa me za ta yi farin ciki ko akasin haka, dan ya shammaceta sosai.
"A..... Al-hussain." Ya ɗaga mata yana buɗe mata akan ta rungumesa kamar dai yarda ta saba.
Matsawa ta yi tare da rungumarsa, duk kuwa da ajin cike yake da mutane sosai, Marwa tana shiga jikinta ta yi murmushi dan tunawa da Al-hassan, da shine da yanzu sanyi na ratsa jikinta.
Al-hussain murmushi ya yi yana jin sanyi na ratsa duk ɓargon dake jikinsa, karo na farko kenan da Marwa ta rungumesa, tabbas ya ji daɗin haka sosai.
Dama yau ya ce zai mata surprise, shi yasa duk abinda ke gabansa ya aje dan zuwa wajenta.
Ihun ƴan ajine ya dawo dasu duniyar zahiri, dan kuwa kowanne su da tunanin da yake yi.
Murmushi suka yi suna sakin juna, Marwa ta harara wacce ke musu video tana waƙar.
"I need your love, I need your time......."
Al-hussain ya ja hannun Marwa suka yi waje ana ta musu dariya.
Sun ɗau lokaci suna hira, kafin ya barta ta rubuta exam, ya mata sallama, tana komawa aji, ya kalla agogon hannunsa, da haka ya yi murmushi yana shiga mota.
Be tsaya a ko ina sai *Primecare Hospital*, kallon asibitin ya yi sannan ya ɗauki facemask ya sanya, da haka ya saba wannan jakkar ya shiga cikin asibitin bayan ya sa p-cap.
Akwai mutane sosai, kuma duk saboda Senator Tumɓa ne, murmushi ya yi sannan ya ciro wani wuƙa a aljiwunsa, hannunta na hagu, ya daba, sai ga jini ya fara fita, da kansa ya kara girman ciwon sannan ya nade da wani farin ƙyalle, take jikin gyallen ya fara jiƙewa da jini. gefe-gefe ya dinga raɓawa har ya kusa shiga ciki.
Hannusa na dama ya damƙe na hagu, ya shiga kiran Nurse's Dan su bashi kulawa, ai duk wanda ya ga wannan jinin sai ya ruɗe.
Nurse's biyu suka yi kansa da gudu, sannan aka nufa wani waje da shi.
Nurse's suka duba ciwon suka mai dressing, sannan bashi magunguna.
"Thank You." Ya faɗa yana tashi a hankali, su kuma suka bishi da kallon tausayi.
Yana fita maimakon ya yi ƙasa, sai ya nufa Aminity word, yana ganin wani Nurse ya kirasa.
"Toilet zan shiga, ina so ka taimaka min, jiri nake ji ga wannan ciwon." Ya faɗa yana nuna hannunsa, saurayin cikin tausayi ya dafa shi suka shiga toilet ɗin.
Second 1....2.....3.......zuwa minti 5, sai ga Al-hussain ya fito cikin kayan Nurse din nan, ya mai da faskmask ɗinsa, sannan ya riƙe jakkarsa da ya mai dashi akwaiti yana ja, dan jakkar yana da tayoyi, tray ɗin hannun wancan Nurse ɗin, shi ya riƙe a nasa hannun sannan ya yi wani shu'umin murmushi yana nufan ɗakin da aka kwantar da Senator Tumɓa, duk da kuwa ga Sojoji biyu da suke bakin ƙofar riƙe da bindigu...........
Yana isa wajen jami'an sai ya yi ƙoƙarin shiga, suka dakatar da shi.
"Dr. Ashraf ne kawai mai iya shiga ciki." Cewan soja guda ɗaya.
"Okay shi ya aikoni amma bara na kirasa." Da haka ya matsa gefe, da leɓansa ya fara furta.
"1,2,3,4,5." sai ya lumshe ido, yana buɗe wa, sautin harbe-harbe suka fara tashi a cikin asibitin, nan fa asibiti ya ruɗe, da sauri Sojojin nan suka yi waje, suna barin wajen Al-hussain ya shiga ɗakin sannan ya rufe.
Mutanen da suke haraban asibitin suka ruɗe jin harbe-harbe, nan kowa ya fara neman wajen ɓuya, amma a haka an harbe mutane biyar kuma duk sun mutu, asibitin be dawo daidai ba sai bayan 30mnt, inda kowa yasan an sake kawo ma Senator Tumɓa farmaki ne.
Sai a lokacin aka nufa ɗakin da aka kwantar da shi, Dr. Ashraf da wasu ne a kansu sun rufa mai suna duba abinda ke damunsa.
Hankalin mutane ya sake tashi bayan saƙon Dr. Ashraf ya iske su.
"An farmaki Senator Tumɓa, Amma be mutu ba sai dai yana cikin wani hali." Ai nan mutane aka hau kuka wasu na ta sume-sume.
Al-hussain riƙe da hannunsa ya fita a asibitin, ya shiga motarsa, minti biyar ya ɗauka kafin ya kunna yana ma motar key.
*Basma*
Ita kaɗai ta wuni a gida, dan Najlah ko da ta dawo part ɗin ta tashige, bayan gajiya da zaman ta shiga Kitchen, Taliya ta dafa bayan ta yi searching a YouTube, ta yi miya wanda yaji uban mai da magi, taliyar kanta ba ta nuna ba, da haka ta ɗauki dankali ta fare, soyawa ta yi ta haɗa da eggs, murmushi ta yi dan ita kanta daɗin hakan , ta jera a Dining sannan ta koma part ɗin su.
Wanka ta yi tasha wata atamfa, a lokacin kiran Anas ya shigo wayarta, ta amsa tana isar mai da gatanan zuwa.
Da haka ta fice, cikin minti 15 ta dawo ciki da sauri ƙirjinta na mugun faɗi, da gudu ta haura sama, Najlah dake zaune cikin riga da wando baƙake ta yi murmushi tana cewa.
"Ke da sake ganin Anas sai a lahira." Da haka Najlah ta miƙe tana sanya gyale sannan ta fita, bayan ta maƙala bindiga a kwankwasonta.
Basma tana shiga ɗaki ta zauna a ƙasa tana dunƙulewa waje guda, babu abinda take tunawa sai kalaman Anas na ƙarshe.
Bayan number asusun Companyn Abba da ta bashi, ta haɗa mai da takaddun filaye masu yawa, ya amsa yana jin daɗi, a lokacin kuma ya buɗe bakinsa ya ce............✍️ END.