BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 4️⃣ 1

by @prettys01

> Bayan number asusun Companyn Abba da ta bashi, ta haɗa mai da takaddun filaye masu yawa, ya amsa yana jin daɗi, a lokacin kuma ya buɗe bakinsa ya ce..........

"Baby zuwa dare zan dawo, ina zuwa ki fito da kayanki kala 10, ƙasar nan za mu bari, muje wani waje muji daɗin rayuwarmu, amma ki tabbar kin tawo min da wasu kadarorin mahaifinki masu yawa." a lokacin Basma ta watsa mai wani kallo, shi kuma sai ya yi mata murmushi, lokaci guda kuma ya rungumota jikinsa yana shafata balle Breast ɗin ta da suka fi tsole mai ido, da ƙyar Basma ta ƙwata jikinta, shine ta nufa gida da gudu.

Anas ya yi dariya dan kuwa a daren yau ya shirya kashe Basma, bayan ya tsara idan ya keta alfarmarta sannan ya kasheta, bokansa ya ce ya koma Katsina gobe dan baya ganin akwai nasara ci gaba da zama a Abuja..........

*Al-hussain*

Idanunsa a lumshe suke, amma a hankali yake jin sautin tv dake tashi a hankali, mutane suna ta koke-koke, ga shugaban ƙasa har yanzu be saki yaran da suka mai ɓarna ba, komai dai ta'azzara yake a ƙasar.

Tsaki ya ja yana mai lalubo remote a kusa da shi, yana taɓawa ya kashe gaba ɗaya.

Jin saƙo ya shigo wayarsa ta sirri, ya sa ɗauka, yana dubawa, saƙo ne gajere wanda aka turo numers kamar haka.

"7777,444,777, 444,6 777,33,23,999."

Murmushi ya yi har fararen haƙoransa suna bayyana, da haka shima ya shiga tura nasa numbers ɗin wanda Ni kaina bansan ma'anar su ba.

''666,55 88,777 9,33,555,222,666,6,33." Da haka ya miƙe ya daga kwancen, system dake gefansa ya buɗe, yana typing yana lumshe ido, dan barci yake ji sosai.

Bayan ya gama, ya kunna hasken ɗakin, take haske ya gauraye ko ina, ƙaramin ɗakine amma ya zuba tarkace sosai, na'urorin da wasu hotuna ne ta ko ina, a zanen Dragon da aka yi jikin bangon amma ƙarami mai ƙyau.

Haka gefe guda ga bindigu kala-kala, manya da ƙanana a kwali guda, rufe kwalin ya yi sanan ya kashe hasken, a hankali kuma ya danna jan alama dake wajen, nan take ƙofa ta rabe a gabansa, wanda duk wanda ya kalla zai ce bango ne sai da ƙofa ce, yana fita ya sake dan nawa, ƙofar ta kulle, sai gashi cikin clotheset irin wanda ake yi da na bango blocks, an yi shi an kuma tsara, an bi jikinsa da ƙwalliya sosai, idan ba ance maka babu mai ganewa clotheset ɗin na bulone.

Kayane a rataye masu ɗan dama, sai ya tura glass door ɗin da haka ya danyi tsalle kaɗan, sai gashi ya duro kan wani lallusan carpet.

Murmushi ya yi yana ƙare ma wajen kallo, an zuba komai a ciki, kusan ma ya dawo nan da kwana, balle yanzu da yake zaman gida sosai, hakan yasa Al-hassan zuba mai kaya tun kafin lokacin bikin yayi.

Bedroom ne mai girma, ga babban gado, mirrow da dai sauransu, harda kujeru uku a ciki.

Numfashi ya sauke sannan ya nufa ƙofar dake gabansa, yana buɗe wa sai ga madaidaici Parlour, shima an zuba kaya sosai, gashi ya ji gyara, murmushi ya sake yi yana kallon wata ƙofa dake gefan wanda ya fito, a nan Marwa za ta zauna, idan ya ce be ƙosa ba ya yi ƙarya.

Ƙafafunsa basu tsaya a ko ina ba sai a main parlour da ya fito bayan fita ta wata ƙofa, da haka ya nufa part ɗin su da Al-hassan.

Yana shiga ya iske Al-hassan yana barci a gadonsa, murmushi ya yi ya kwanta kusa da shi yana kallon hannun hagun Al-hassan.

Ɗaure yake da bandage kamar dai nasa hannun, dan tun bayan dawowarsa Al-hassan ya ga ciwon dake hannunsa shine shima ya ji ma kansa da wuƙa, haka suke rayuwa in ciwo ne kowa ya ji babu daɗi, haka tabo ma sai ya fito musu a tare.

Barci na idanunsa nan da nan ya ɗauke sa, sai dai muce a ikon Allah babu mamaki.

Su biyun barci suke amma yarda suka kwanta ma iri ɗaya ne, suna kallon juna sannan ƙafafuwan su ɗaya yana miƙe ɗaya sun lanƙwasa shi, hannu ɗaya yana saman kansu, mai ciwon kuma hana miƙe. Haka suke sauke ajiyan zuciya a natse.

Abbeey ne ya shigo ciki, ganin barcin da suke yi, ya yi murmushi, dan kuwa tun suna yara ko kwanciya suka yi to iri ɗaya suke yi, koda gadonsu ba ɗaya bane.

Hannunsu ya kalla, ya saki ƙaramin tsaki, ya rasa yaushe za su girma su dena wannan dabi'ar, sai ya kaɗa kansa sannan ya fita.

Al-hussain ya buɗe ido yana ganin fitar Abbeey, ya gyara ƙwanciya, tun tsayuwarsa akansu ya farka, haka yake ko mutum idan ya wucesa yana barci sai ya farka, balle a yanzu da yake da maƙiya masu yawan gaske.

Kwanciyarsa ya gyara ya koma barci, can Al-hassan ya gyara kwanciyar sa, sai ya dawo sak irin na Al-hussain............

> Ikon Allah 🥰

***********

Abba hankalinsa a tashe, ba shi kaɗai ba hatta Fauza da Marwa ma haka, agogo Abba ya kalla 9:20pm amma Najlah ba ta dawo ba, shi da Basma ta ce tun 5:35pm ta fice harda ƙarin gishiri a miya.

"Abba na za ci ta sanar da kai ai, dan wanka tasha sosai, sannan ta fice, nima ta window na hangi fitarta." Cewan Basma hankali kwance, tana ma fatan kar Najlah ta dawo musu gida har abada, tana ta mata addu'ar Allah yasa babbar mota ta bi ta kanta.

"Abba ka sanar da police mana, ko za su taimaka?." Cewan Marwa tana zama kan kujera. Sai Fauza ta ce.

"Eh Abba muje muyi reporting ka ji." kai ya girgiza.

"Ta tura min saƙon za ta je wani aiki, kuma ba zan iya sanar ma jami'ai ba saboda ita ɗin D.S.S ce."

"Allah yasa tana lafiya." suka amsa da Ameen.

Basma kuwa ranta fes, ita yanzu kiran Anas take jira, dan ta gama komai, kayanta ma suna a jakka ta kai Compound ta aje su, yana kira za ta fice, sai kuma sun ganta, a ɗazu ne ta shigo cikin tashin hankali bayan nan sai ta ji ranta ya yi na'am da tafiyar.

Horn suka ji anyi, hakan yasa suka yi waje da sauri, hamdala suka farayi ganin motar da Najlah ta fita ta shigo gidan.

Ko daidaita parking ba ta yi ba ta fito daga cikin motar, da gudu ta yi kan Abba, ta rungumesa tana fashewa da kuka.

Hankalinsa ya ƙara tashi, hakan yasa ya raba jikinsu yana mai riƙe hannunta suka shiga ciki da ita.

"Jini." Faɗin Fauza a ruɗe tana kallon jikin Najlah, sai a lokacin kowa ya kalla.

Gaba ɗaya jini ya ɓata kayan, duk da ɓakin kaya ne, ga ciwuka da ta ji sosai ɗaya sai ɗigan yake.

"Ku kawo mata ruwa." Da sauri Basma ta ɗibo ruwa ta kawo mata, dan yanayin da ta ga Najlah ta ba ta tausayi.

Tana miƙa ruwan ta haura sama, can sai gata da first aid box.

"Me ya same ki? Ina kika je? Waya ji miki ciwo haka?." Abba ya jera mata tambayar yana share mata hawayen da suka sake zubowa.

Basma ta ɗauki audika ta fara goge mata jikin hannunta ta tsaya cak jin furucin Najlah.

"Abba na kashe shi.............da hannayena, na kashe shi, Abbaaaa karo na farko na kashe wani kuma shine ya ja, ya ƙi bani haɗin kai, ya fara min taurin kai, Ni kuma zuciya ta ciwoyoni dan an ban lasisin kashe duk wanda ya yi ba dai-dai ba, da haka na kashe shi......." Sai kuma hawaye.

Basma baya ta ja da sauri dan Najlah tsoro ta bata, Abba kuma ya rungume Najlah yana cewa.

"Wa kika kashe? Kuma ina gawarsa take?." ai abinda ta sake furta shine yasa kowa a wajen hantar cikinsa juyawa hatta Abban.

"Na ƙona gidan gaba ɗaya."

Dum-dum-dum kirjinsu ya buga, take Najlah ta share hawaye amma har lokacin tana kuka.

"Kawai ina kuka ne saboda Ban gana ma tsinannan azaba ba, wallahi Abba so na yi, na dinga feɗe shi sala-sala, amma ya yi mutuwar sauƙi, kawai daga mai tokari ɗaya shike nan ya coke da ƙarfe, amma ba laifi na fitar mai da jini sosai, uhmmmmm Abba ba haka na so ya mutu ba, ba haka baaaaaa uhmmmmm, shike nan dai saura ɗayan." Abba ƙafafaunsa sukayi sanyi sai ya zauna gefanta yana ganin ƙoƙarin abinda ta aikata.

"Amma me ya yi wai?." ya sake faɗa yana ganin tana cire rigar jikinta, take waya ash t-shirt ta bayyana, da ɓakin rigar ta goge hannayenta, sai kuma ta ciro wuƙa daga al-jiwun rigar, sai bindiga.

"Abba zan faɗa maka......Basma mai da First aid ɗin nan, ciwon za su warke, ba wani yawa ai, Autar Abba ina jin yunwa, amma bara na fara wanka, jikina duk ya yi tsami." da haka ta miƙe tana kwasan kayanta, hatta takalminta akwai jini, haka jikin tiles duk ya diga na hannunta da yake zuba.

"Abbanaa.." da sauri Abba ya bi bayan Najlah jikinsa a mace, shi gaba ɗaya baya haɗa hanya da rigima sam baya so, ganin jini ma yana mugun ruɗasa balle ace wai kisa, amma Najlah ta yi, kuma take kuka wai ya mutu cikin sauƙi.

Basma ta sauke ajiyan zuciya tana tashi ta hau kujera.

"Mun shiga uku, wallahi ba mutum ba ce, kisa ta yi!????, Marwa kuna jinta wai ta kashe wani, kuma hankalinta a kwance.............daga yau babu ruwana da shiga harkarta dan wallahi babu imani a cikin idanunta."

"Hmmmmm na kasa cewa komai." faɗin Marwa tana rufe bakinta.

Fauza kuwa jiki a mace ta nufa Kitchen, ruwan zafi ta fito da shi, sai a lokacin suka tuna da yunwa.

Marwa ta miƙa tare da haɗa ruwan mope, ta goge ko ina, suka zazzauna suna jiran fitowar Matan Abba.

********

Abba ya taimaka mata da ruwan zafi, sannan ya fito a toilet ɗin, a lokacin Najlah ta cire kayanta ta ɗaura towel, ciwo huɗu ta ci a hannun ɗaya, wankan ta shiga Abba kuma ya shiga fito mata da kayan da za ta sanya.

Kukanta ya ji yo hakan yasa ya yi bayin yana tambaya lafiya.

"Abbaaaa ruwan da zafiiiiii neeee." Ta faɗa tana tura baki, Abba dake jikin ƙofa ya shiga bayin, ya ƙara ruwan sanyi sannan ya kalleta.

"Baby na miki wankan ne?."

"A'a." Sai ya fita.

Najlah ta shiga bathroom soso ta ɗauka ta kai jikinta, sai ta sake fashewa da kuka tana kiran.

"Babyyyyy uhmmmm." Da sauri Abba ya shigo bayin yana cewa.

"Menene Shalele?."

"Sosan akwai zafiiiiii uhmmm Ni bana son soso." Ta faɗa cikin shaƙwaɓa.

"To kiyi da sabulu kawai."

"To." Sai ya fita amma ya tsaya a bakin kofar dan yasan halinta.

Kafin Najlah ta gama wanka Abba ya shiga kusan sau 10, shi har ƙwanda ace shi ya mata ma, a hankali ya fito da ita a nan naɗe cikin towel, tana zuwa ya zaunar da ita kan gado.

Da kanshi ya shafa mata lotion da turare, sannan ya sama mata kayan barci riga da wando, Hijab ta sanya ta shiga ramakon sallar, Abba kuwa ya nufa parlour dan cin abinci.

Jikinsu duk a mace, kowa ya zuba taliya amma ya kasa ci, Abba ya zuba dankalin ya fara ci, suma dankalin suke ci, Marwa ta kalla taliyar ta cewa.

"How many minutes has the spaghetti been on the fire?" Basma da damuwar rashin kiran Anas ta ce.

"15 minutes."

"No wonder. But in the video, how many minutes did they say it should be cooked for?"

"They usually remove it after 15 minutes, that's why I hate it." ta faɗa tana kallon taliyar.

Abba ya kalla Basma ya ce.

"You tried, my daughter. One day, you will become a professional."

"Insha Allah, Abba."

"Do you have the T.T injection?"

"Yes, Abba."

"Good. When Ameen Basma comes out, give her a little injection so she will feel some pain."

"Okay."

Fauza ta kalla Abba ta ce.

"Abba headmaster ya ban receipt na school fees, sannan dana zuwa Millennium Park thank you so much."

"Ki ƙara dagewa kinji Autata, yaushe za ku je."

"On 20th this month." Ya ɗaga kai.

Kallon Najlah suka yi da ta zauna kusa da Abba.

"Kin fito."

"Eh Abba." Fauza ta yi serving nata harda haɗa mata Tea.

"Na gode Autar Abba, Tea ɗin ma is okay." Da Haka ta fara shan tea ɗin da spoon.

"No za ki ci wani abu dole, nasan haka kika wuni yau." Sai ta kalla Abba cike da soyayya.

"Baby, kwana biyu bana motsa jiki, nasha wahala wajen hawa katangar gida bara na baku labarin yarda komai ya faru." Ta kai nan tana ƙara kurɓan Tea ɗin sannan ta fara basu labarin daga farko, sai dai ba ta ambaci Anas ba.

_Labari_

Najlah motar Anas ta bi a baya, tana so ta bi sa ne dan gyara mai zama sannan ta raba shi da Basma gaba ɗaya. Sai ba gidan nan ya nufa ba, wani hanya ya ɗauka.

Ba ta karaya ba ta bishi, ganin ya sauka a mota ya nufa wani gida yasa ta bi bayansa itama a ƙasa, ba ta yarda ya ganta ba gaba ɗaya.

Gidan da ya shiga ta bisa, sai dai ta ga alamun gidan bokaye ne hakan yasa ta koma mota ta fita a layin, tasan dole ta nan Anas zai wuce.

Alai sai motarsa ta dawo, hakan yasa Najlah barinsa ya yi gaba sai ta bi bayansa.

A hanya ya tsaya shago ya siya youghout, sai ya fito ya shiga chemist, da haka Najlah ta yi gaba kaɗan ta fito daga motar ta kulle, sai ta yi kaman tana wani abu ya lalace a motar, dan daga nan zuwa gidan Anas babu nisa.

Motar Anas ta tsaya a gabanta sannan glass ya zuge.

"Ƴam mata ina zuwa ne?." Najlah ta kallesa tana yamutsa fuska.

"Mahrab hotel, ga motata ta lalace." Ta faɗa ba dan tasan akwai hotel me wannan sunan ba.

"Wow nan zanje ai, amma zan biya gida na ɗauki wani files idan babu damuwa." murmushi ta yi sannan hankali kwance Najlah ta shiga motarsa, a ranta tana mamakin halinsa.

Layin gidan suka shiga yana ce mata.

"Baby kin haɗu sosai, wajen wa za ki a hotel ɗin?."

"My Alhaji Ahmed, za mu haɗu da shi." ta faɗa tana kanne mai ido ɗaya kamar ƴar bariki.

"Ohhhh, Baby girl zan iya tambayar nawa Alhaji ke biya? Ni zan iya biyan ×3 a dare ɗaya idan za ki ban haɗin kanki." fari ta yi da ido tana cewa.

"₦200k yake biya ai."

"Ke kinfi wannan darajar, zan biya ₦1M ya miki?." Ido ta zaro cike da mamaki.

"Are You sure?." Ya jinjin kai yana ganin ya samu Najlah cikin sauƙi, shi tunda yake ba'a amsar kuɗinsa sai dai ya amsa naka, ba yarda za'a yi ya biyata 1M, ya tsara su je ya gama komai da ita sai ya kasheta.

"Baby girl, gidana babu kowa za mu iya sha'anin mu a ciki, daga nan sai na kai ki wajen Alhajin."

"Uhmm ba zai mu ɗau lokacin ba ko? Kar ya yi ta jira na."

"1h mun gama komai na kai ki." Ta sake fari da Lulu eyes ɗin ta wanda suka ƙara narkan ma Anas da zuciya, har yana raya. 'Ba zan kashe wannan zafafar ba, kawai zan mai da ita abin jin daɗina, wacce zan dinga hutawa, zuwa lokacin na gaji da ita, sai na kasheta.....uhmm haka nan zan wuce da ita Katsina.' haka ya dinga saƙe-saƙe har suka isa bakin get ɗin gidan sa, murmushin ɗan duniya ya yi mata yana fita dan buɗe get, Najlah ta bishi da ido tana mai kallon *Za ka ci ubanka yau, za ka san Allah huwal Waheed*...............✍️ END.