PAGE 4️⃣2
by @prettys01
> ...........haka ya dinga saƙe-saƙe har suka isa bakin get ɗin gidan sa, murmushin ɗan duniya ya yi mata yana fita dan buɗe get, Najlah ta bishi da ido tana mai kallon *Za ka ci ubanka yau, za ka san Allah huwal Waheed*..............
Yana buɗewa ya dawo ya shiga motar, sannan suka shiga cikin gidan, a tare suka fita, shi ya koma ya rufe get ɗin, Najlah kuwa ta dinga bin ko ina da kallo, karnukan ranar ta gani sai ta nufa su tana.
"Wow, ina son manyan karnuka sosai." Tsayawa ta yi jin abin da Anas ke cewa.
"Wa'innan masu hatsari ne sosai, karki je wajen." Sai ta yi baya tana nufan hanyar da ya bi.
"Baby 2mnt kinji." Sai ta ɗaga mai kai, shi kuma ya shiga ciki, minti biyar ya buɗe yana mata maraba tare da murmushi.
Da Bismillah ta shiga ciki tana bin ko ina da kallo, sai a yau ta ƙare ma ɗakin kallo, ga dai shi nan babu fasali.
Gefan gado ta zauna shi kuma ya shiga bayi, can ya fito sanye da wando kawai, Najlah ta kau da kanta tana wasa da gefan gyalenta, wayarta na cikin mota kuma ya sa a Flightmode.
"Kisha youghout ɗin mana, kinsan ba mu da lokaci sosai." ta kalla glass ɗin sai ta ɗauka tana ɗan wasa da kofin.
Take ƙirjinta ya buga ganin maƙudan kuɗaɗen da suke cikin sip na kaya, ba wannan ne ya fi ɗaga mata hankali ba, face hannayen da ƙafafaun jariri da suke a wajen, da sauri ta kalla ƙasansu nan kuwa layoyi ne da wasu ƙulle-ƙulle, tabbas irin su Anas da za su samu dama sai sunfi Black Dragon hatsari.
Idanunta ta sauke ƙasa ganin sun haɗa ido da shi, murmushi ya sake yi yana zama kusa da ita, sannan ya riƙe hannunta guda ɗaya yana cewa.
"Ki kwantar da hankalinki, dan kuwa kin shigo nan ke nan babu fita, shi yasa na bari kika ga sirrina, hmmm ba ki da sa'a sam, dan kuwa zan lalata miki rayuwa ne amma ba zan kashe ki ba saboda kin min daga sama har ƙasa, komai yaji cakwai." ya faɗa harda lashe baki.
Najlah ta fizge hannunta sannan ta tofa mai miyau a fuska tana turesa baya.
"Kar ka kuskura ka taɓani, na fasa bana son kudin." Da haka ta nufa ƙofa duk tana yi ne dan ƙara samun hujjar illatasa.
"Babu damar fita, ko da kin iya fita wa'incan karnukan za su cinye ki, ki dawo ki zauna muyi sha'anin mu cikin natsuwa." Miƙewa ya yi ya nufa Najlah.
Sai ta ƙauce tana kowa ciki amma ta baya take tafiya.
"Da kin tsaya, na rasa me yasa nake so ki amince, kin ganni nan, na lalata yara mata sama da 20, na yaudara wasu, wasu kuma na sa musu hauka, ki bar ganin ina lallaɓaki." ya kai nan riƙe hannun Najlah.
Fizgewa ta yi sai kuma ta zauna gefan gado tana fito da wuƙar dake jikinta, da haka ta sake miƙewa tana mai gargadi akan karya matso kusa da ita za ta yanke sa, Anas ya yi dariya yana ganin kaman wasa take, haka ya nufa Najlah, sai dai Kafin ya ƙarasa kusa da ita, jinin soja ya motsa, dama riga da wando ta sa, nan ta tokaresa da ƙafa, ya faɗi, da sauri ya miƙe sai ya fara waige-waige yana neman makami dan ya gaji da magiya.
Najlah ta cilla mai wuƙar hannunta tana cewa.
"Nuna min ƙarfinka." cike da mamaki ya ɗau wuƙan sannan ya nufa Najlah, kaucewa ta fara yi, har ya yanke ta sau biyu a hannu, murmushi ta yi tana cewa.
"Ka gama naka saura." Anas take zuciyarsa ta raya mai ko dai ba mutum ba ce.
Take Najlah ta sa mai ƙafa ya faɗin tim, sannan ta yi wani kukan kura ta kai mai tokari, ta fizge huƙan, ƙirjinsa dake buɗe ta kai mai yanka, ya dafe wajen yana kallon bindigan da Najlah ta ciro.
Hankalinsa ya tashi, ya fara ja da baya yana girgiza kai.
"Wa.....wa....wacce ke?." ya tambaya yana isa daidai jikin bango.
Najlah ta sakar ma alburushi ɗaya a hannu. Cikin rashin imani ta fara cin ubansa, duka kawai take mai, sai da ta gama lillisa shi sannan ta tsaya sauke ajiyan zuciya, ga hannunta da ta sake jin ciwo.
Cikin ciwo da azaba Anas ke tambayarta wacece ita.
A hankali ta isa kusa da shi ta tsugunna sai tin kunninsa ta ce.
"Akan rayuwar Basma, akan abubuwan da kake yi, ba zan kashe ka, amma kai da matacce babu bambanci har sai ka yi sha'awar mutuwa amma ba zan kashe ka ba, yanzu jikinka zan fara yanka, zan maka mugun illah, a kai ka asibiti kasha jinya har na tsawon abada." Da haka ta miƙe, gefenta guda bindiganta dake ƙasa ta nufa dan ɗauka.
Anas kuwa ganin ta juya yasa ya lallaɓa cikin ƙarfin hali, yana miƙewa ya ɗaga ƙafarsa ɗaya zai nufa Najlah, sai santsin tiles dana youghout da ya zube ya ja shi, baya kaɗan ya yi, sai dai anger na ƙarfe dake wajen ya cake wiyarsa *chak*
Da sauri Najlah ta juyo, ido ta zaro ta yi kansa da gudu, ta janyosa, amma rai ya yi halinsa, a ruɗe ta fara cewa.
"Anas ka tashi.....ba haka za ka mutu ba, wannan ya yi sauƙi,. Anasssssss." ta sake sa tana miƙewa.
Numfashi ta ja sai kuma ta buɗe drawer ɗin, takaddun da suke sama ta ɗauka, tana dubawa ta ga na Abba ne, sai ta naɗe su ta sa a pocket.
Da haka ta fita Compound ɗin gidan, motar Anas ta buɗe, ta duba boat, ta ɗauki petir, ta koma ciki dan ta ga ashana.
Cikin drower ta zuba sannan ta bi ko ina ta zuba, Allah ya so yana da yawa sosai, ta fita ta saki sauran petir ɗin ya gangara wajen karnuka.
Ba ta yi tunanin komai ba ta cinna ma gidan huta.
Daga nesa ta tsaya tana ganin gidan ya fara tashi da huta, dan har da gas ta kwance, shi yasa sai da ya hau katangar ta cinna ma gidan ashana, shine ta yi tsalle ta duro ƙasa.
Haka ta koma ta shiga motarta, ta jima tana sauke nannauyan ajiyan zuciya, kafin ta kunna motar ta nufa gida lokacin dare ya yi ma.........._
_Ci gaba._
Kowa ido ya zuba mata a lokacin da ta kai ƙarshen maganar, sannan ta kai Tea bakinta, kuma hankalinta akwance.
Abba zuciyarsasai dukan uku-uku take, shi gaba ɗaya baya son tashin hankali, haka ya goge zufan dake fuskarsa sannan ya ce.
"Ammeen Basma, a gaisheki, amma da ba ki ƙonasa." Abba ta kalla sannan ta ce.
"Idan na bari gidan akwai matsala, haka idan na ɗauke shi, karka damu nasan babu abu guda za'a samu a gidan da sunan sheda." da haka duk suka yi shiru.
Abba yana so ta ci abinci amma ya kasa mata magaan, yau sai ya ji yana shakkarta.
"Basma ɗauko." Abba ya faɗa, Basma da jikinta ya yi sanyi, ta miƙe a hankali, sannan ta haura sama.
"Ba kowa na kashe ba face Anas wanda ke zuwa wajen Basma." Da haka ta miƙe ta bar musu Dining, su kuma suka bi ta kallon tashin hankali.
A kujera mai uku ta zauna tana kallon Tv, Abba da ya biyota ya zauna yana cewa.
"Najlah..... Anas......why?." Yarda ya yi maganar hakan yasa ta kallesa, sai ta ja mai dogon gemunsa sannan ta ce.
"Ɗan iska ne, yana sace yara ya lalatasu, sannan ya kashesu, bayan nan yana bin malamai, gaba ɗaya ɗan iska ne, Ni kuma idan har irin su Anas suna raye ba zan bari su ji daɗin duniya ba.......kar ku ce da ita komai." Ta kalla Marwa da Fauza wa'inda suke tsaye cikin sabon tashin hankali.
"Abba asiri ya yi ma Basma, hakan yasa idanunta suka rufe a kansa, komai da kake nema ita ke kai masa, hatta kayan da aka kwashe shi duk ta ba, yanzu haka akwai takaddun filaye masu yawa baka wanda na tawo da shi." ta kai nan tana mai da idanunta kan tv.
murmushi ta yi ganin Abba ya rungumeta kamar yana kuka ya ce.
"Ƴata kika taimaka Najlah, ƴa ta kika....." da sauri ta toshe mai baki, tana girgiza kai.
Marwa da Fauza suka yi kanta suna kuka, hannu Najlah ta buɗe musu, nan suka rungumeta da ƙyau suna hawaye.
A hankali Najlah ta zame jikinta tana cewa.
"Ku ƴan uwana ne, babu wacce zan gani tana matsala na barta, babu wacce zanga tana cikin tashin hankali na zuba mata ido..........dan Allah nake komai." sai Abba ya ƙara matse hannusa a cikin na Najlah.
Murmushi ta yi tana cewa.
"Dan Allah ku kulle idanunku." Da sauri Fauza da Marwa suka kulle suna kauda kai.
Najlah ta sakar ma Abba peck a kumatu, murmushi ya yi, yana nuna mata yara, sai ta ɗaga mai gira.
Basma ce ta sakko riƙe da allura guda biyu.
"Lafiya na ganku a haka?." Cewan Basma tana kallon su Fauza.
"Lafiya lau Baseey." Baki ta taɓe tana kallon Najlah dake cewa.
"Wannan labarin ya zama secret, bana son kowa ya sani, ko aikin da nake yi."
"Insha Allah." suka faɗa a tare.
Abba yasan Najlah ba ta son allura hakan yasa ya ce.
"Ammeen Basma ga ƴarki nan za ta miki allura guda ɗaya tak, karki bani kunya kinjiii." Najlah ta kalla Abba ta kalla Basma, sai ta girgiza kai.
"Basma, do it gently." sai Basma ta nufa Najlah.
"What are they going to do to me?"
"An injection."
"No way, I don't take injections. Nobody is giving me one."
"Haba ba zafi ai." Zumbur ta miƙe tsaye, tana son guduwa, Abba ya riƙeta sannan ya janyota jikinsa.
Riƙe ta ya yi da ƙarfi yana mata magana a tausatse, ita kuma tuni ta fara kukan banza tana bubbuga ƙafa.
"Sorry babu zafi, innalillah a gaban yaranki kike kuka."
"Abbaaaa bana so, wallahi banso." Ta fara kokawan fizge jikinta.
Basma murmushi ta yi, kusa da Fauza ta nufa tana cewa.
"Ki je ɗakin mu, akwai allura guda biyu ki ɗauko min karki bari ta gani." Cikin raɗa ta ce.
"Na menene?."
"Paracetamol ne, sai na kashe virus, wannan kuma T.T ne da wanda zai sa ciwon ya dena raɗaɗi." Da haka Fauza ta haura sama.
Abba yana ta rarrashin ta amma ta kasa yarda, hannun Basma take kallo dake ɗauke da allura.
"Matso ki yi mata." Cewan Abba, sai Basma ta ƙaraso kusa da ita tana murmushi.
"Ki kwantar da hankalinki mana, babu zafi."
Najlah ta haɗe rai tana nuna Basma da yatsa.
"Kar ki ƙaraso nan! Na san zaki caccaka min sosai, ban yarda da wannan murmushin ba."
Abba ya sake cewa cikin dariya.
"Basma, kada ki tsoratata. Ki yi aikin ki kawai kuma ki dena dariya."
"To Abba." Ta faɗa tana matse dariyar, dan kuwa saboda mugunta guda huɗu za ta mata.
Najlah ta turo baki gaba tana share hawaye.
"Abba shike nan ta yi min ɗaya."
"Yauwa Najlah, minti ɗaya ne kawai."
Najlah ta lumshe ido tana girgiza kai.
"Wallahi idan ta caccaka min da ƙarfi zan ramaaa"
Basma ta kasa riƙe dariyarta, yayin da Abba ya girgiza kai.
"To wa yace zan caccaka mi ki da ƙarfi? Ba wuƙa bane fa, allura ne kawai." Basma ta faɗa tana ƙoƙarin kama hannun Najlah.
Najlah kuwa ta ja jikinta baya da sauri.
"Kar ki taɓa ni! Ban yarda da ke ba wallahi"
Abba ya ɗan ɗaga murya kaɗan.
"Najlah!" Ta tsaya cak da kukan tana kallonsa kamar yarinya da aka kama da laifi.
"Na'am Abba…"
"Ki zauna a yi miki kawai. Kina ba Basma wahala."
Najlah ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zamanta da ƙyau.
"Shikenan… amma a hankali fa." Basma ta gyara safar hannunta tana murmushi.
"Yanzu kin zama good girl."
"Ni ba good girl ba ce idan akwai allura." Najlah ta faɗa tana turo baki.
Abba ya juya yana ɓoye dariyarsa.
"Basma, kiyi kafin ta sauya ra'ayi ta guduwa." Da jin haka, Najlah ta zaro ido.
"Gudun ma zan yi yanzu kuwa" Basma ta riƙe hannunta a hankali.
"Relax… ba zai ɗauki lokaci ba." Najlah ta lumshe ido gam tana riƙe hannun Abba da ƙarfi. Marwa da Fauza dariya suke yi daga gefe suna kallonsu.
"Abbaaaaa ka gaya mata ta rage girman allurar nan mana, kuma ta min a hankali."
"To matar Abba, Basma kin dai ji Ko," Basma ta ɗaga kai tana matse dariyarta.
Kafin Najlah ta sake magana, Basma ta yi mata allurar cikin sauri.
"Auchhhhhhhhhhhh!" Najlah ta ɗan yamutsa fuska sannan ta buɗe ido a hankali. Da mamakinta ganin allurar na jikin hannunta, sirinjin Basma ta cire tana tana ƙoƙarin sa wani.
Ihu Najlah ta fasa tana son fizge hannunta.
"Karki motsa, dan kuwa allurar za ta ƙarye, idan ta ƙarye sai an yi miki C.S, an yanke naman wajen an cire allurar sannan ya yanka kamar matacce a dasa a wajen a ɗinke" ta faɗa tana ɗura mata paracetamol cikin jikin Najlah.
Najlah hawaye suka zubo mata ta kalla Abba.
"Ga ga Basma ko, a hankali take yi yana zafi, kace ta matsa dukaaaaaa." Ta kai nan cikin taɓara da shaƙwaɓa.
Abba ya rufe mata ido yana hura mata iskan bakinsa.
"Yanzu za'a gama, Basma ki yi sauri." da mamakin Abba ganin ta sake cire sirinjin ta kuma sa wani, Najlah na gani ta hau ihu amma ta hannun na waje ɗaya.
Basma ta samu yarda take so, haka ta yi dukka huɗun tana cewa.
"Shi kenan?" Basma ta gyada kai tana dariya, a hankali ta cire alluran tana sanya audiga ta danne mata wajen.
"Abba zafi......hannuna........Basma kinci bashi, wallahi zan rama uhmmmmmm."
"Sorry Ammeen Basma, gobe da safe zan yi miki guda 5, sai kuma da daddare........" wani harara Abba ya watsa mata yana rarrashin Najlah.
Ganin yana buƙatar rarrashinta da ƙyau, yasa ya ce.
"Basma ba za ki sake mata allura ba, ai wannan mugunta ne, ku tashi ku wuce tana kuka kuna mata dariya ko?." da dariyar aka haura suna rufe baki.
Abba kuma ya ɗauki Najlah suka shige part ɗin su.
Yarda kasan Jaririya haka ta koma, ya dinga rarrashinta harda goyata amma ta ƙi shuru, haka ya rungumeta jikinsa yana shafa mata kai, hannu ɗaya kuma yana kan wanda aka mata alluran yana shafa hannun.
"Abbaaaana gobe zan ma Bamsa shegen duka."
"To zan ta yi nima."
"To kuma nima zan caccaka mata irin yarda ta min uhmmmm."
"Sorry ki yi shuru." Da haka ta yi shuru, sai sauke ajiyan zuciya kawai take yi.
Da haka barci ya ɗauketa, sai a lokacin Abba ya samu natsuwa, ya gyara mata kwanciya akan kirjinsa, shima ya lumshe ido, a haka barci ya ɗauke su.....
Suma kowacce gadonta ta hau, suna dariya.
"Basma wallahi harda mugunta ke cikinki, in Banda iskanci, allurar ki matsa kin ƙi, ruwan kaman baki so haka kike sa mata."
"Marwa Allah ne yaban dama shi yasa na dama."
"Za ku haɗu gobe ai."
"Fauza ba sai ya gani ba." Da mamaki Fauza ta ce.
"Ina za ki?."
"Wajen aiki mana." Ta faɗa a baki amma a zuciya, tana tunanin sai gobe za su bar ƙasar da Anas. Kowacce ƙwanciya ta yi...............
*Primecare Hospital*
Senator Tumɓa ne zaune kan gado, yana cin abinci mai rai da lafiya, yana yi yana dariya, tare da kallon videon mutane, sun shiga damuwa da tashin hankali a kansa.
Gasasshen nama ya yaga, ya tauna yana kurɓan Fearless mai sanyi.
Idanunsa suka kalla wanda ke zaune a gefensa, ya sanya kayan Doctors, sannan fuskarsa a kulle rufe yake.
Kamar yarda ya saba, ya lanƙwasa wiyansa dama da hagu, ya buɗe baki waye.
"Komai ya tafi yarda ya dace, yanzu ka sa a ranka ka ci zaɓe, dan kuwa text target ɗina shine kashe Shugaban ƙasa Muhammad Babangida Shamaki." ido Senator Tumɓa ya zare.
"Kai wasa kake? Kasan tsaron dake gidansa kuwa? Hmmmm ko fita zai yi da rundunar sojoji yake fita."
"A cikin gida zan kashe shi, kuma na riga na samu hanya, ta wajen Babban Doctorn asibitin nan Dr. Ashraf."
"Hmmmm karka yi tunanin Dr. Ashraf yana amsar cin hanci, bayan hakan ka bincika alƙar su, mutum ne mai gaskiya, jiya da ya zo nan yana duba Ni, har hawaye sai da ya yi saboda ganin halin da nake ciki."
"Kai dai naka ido, babu abinda zai ba black Dragon wahala. Zan wuce akwai Meeting ɗin da zanyi, mutane da dama sun buƙaci zan yi musu aiki, na tura musu wani address so a hotel ɗin zamu tattauna da su."
"Shike nan Black Dragon, hakan ya yi." da haka Black Dragon ya miƙe sannan ya amsa plate ɗin hannun Senator Tumɓa, ya mai da mai komai yarda yake, sannan ya kwanta.
"Har na gaji da barci a asibitin nan, zuwa tsawon wani lokaci zan fara nuna na samu lafiya?."
"Sati ɗaya ya rage maka, na wuce." Ya sake lanƙwasa wiyansa dama da hagu sannan ya fita riƙe babban basket................
*Al-hussain*
Idanunsa yana kan system, da sauri sauri yake tura saƙo, yana gamawa ya rufe, sai kuma ya kalla cikin asibitin, har yanzu akwai masu zama duk dan Senator Tumɓa, ajiyan zuciya ya sauke sannan ya lumshe ido, ya buɗe, sai kuma ya kunna motar ya bar layin gaba ɗaya.
*Sir Muhammad Babangida Shamaki.*
Dattijon arziƙi, zaune yake yana jan tasbeeh, gaba ɗaya duniyar ta yi mai zafi, a yanzu ya riga ya san cewa, *Babu babban ɗan walaha a duniya sai wanda ya mai da burge mutane aikinsa*, yana ina ƙoƙarinsa amma basa gani, da haka ya zuba musu ido, yana fatan aikin da ya ba jami'an sojojin sirri su yi, yasa a dace, a yi nasara.
Ƙofar ɗakin aka buɗe, hakan yasa ya kalla wanda ya shigo, murmushi ne ya wadatu a kan fuskarsa, yaro ɗaya tilo wanda yake jinsa har cikinsa.
"Ashraf har ka dawo?." Ashraf ya iso kusa da shi, zama ya yi a ƙasa gefan Shugaban ƙasa, cikin ladabi da natsuwa ya buɗe baki ya ce.
"Papa bana jin daɗin ganinka cikin yanayin damuwa, kasan kana da hawan jini, amma kasa damuwar mutane a cikin ranka, wallahi da badan ina da zuciya mai ƙyau ba, da kaina zan ƙarasa Senator Tumɓa kowa ya........" da sauri ya yi shuru, jin Papa ya bigesa a kai.
"Karna sake jin haka, kowa ya yi mai ƙyau ya sani, mutane sun kasa gane dai-dai, ta ya Ni zan kai mai farmaki, kuma ɗana ke kula da lafiyarsa, hmmm da nine makashin da a yanzu ne ma zai fi, sai dai Allah ya tsare Ni da kashe rai." Ya kai nan cikin damuwa.
"Papa akwai Allah, bara na kawo maka maganin ka, zuwa gobe zan kawo ma sababbi na ga sun ƙare." Ashraf ya miƙe yana nufan drower.
"Nasha ɗazu, ai maganin ina jin daɗin sosai, zuwa dare ina za ka shigo ka tawo min da wani." Murmushi Ashraf ya yi.
"Insha Allah Papa, ina da surgery anjima, zan je asibiti." sai Papa ya buɗe hannayensa, da sauri Ashraf ya dawo ya shiga jikinsa cikin so da ƙanar mahaifin na sa.
"Ka ci gaba da addu'a komai zai wuce."
"To Yaron, kaima ka ci gaba da addu'a, kuma ka dinga fita da masu tsaro." ɗaga kai Ashraf ya yi sannan ya fita yana duba agogon hannunsa ganin lokaci yana tafiya, ga majinyaci can ba lafiya yana buƙatar ganinsa, hakan yasa da sarsarfa ya dinga tafiya har zuwa Premises ɗin wanda ke ɗauke da sojoji masu manyan bindigu suna ta kai da komo dan ba Muhammad Babangida Shamaki kariya.........✍️ END.