BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 4️⃣3⃣ ⏩ 4️⃣4

by @prettys01

> ɗaga kai Ashraf ya yi sannan ya fita yana duba agogon hannunsa ganin lokaci yana tafiya, ga majinyaci can ba lafiya yana buƙatar ganinsa, hakan yasa da sarsarfa ya dinga tafiya har zuwa Premises ɗin wanda ke ɗauke da sojoji masu manyan bindigu suna ta kai da komo dan ba Muhammad Babangida Shamaki kariya...........

*Basma* Tunda da garin Allah ya waye take ta kiran Anas, sai dai baya shiga, haka yasa jikinta ya yi sanyi, tasan suna can suna aiki Kitchen dan tun asuba suka sauka ƙasa, tashi ta ji jikinta duk babu ƙwari, ta shiga toilet, wanka ta yi sannan ta fito ta sanya doguwar, bayan ta fito da wani shadda less ya ji aiki sosai, yau dai za ta je asibiti, ta gaji da zaman gida.

Sauka ta yi, ta tura ƙofar kitchen ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Murmushi ta yi ganin yadda suke aiki suna raha.

"Ke ba ki tashi zuwa sai mun magana aiki ko?." Cewan Marwa dan sun gama komai.

"Uhmm ban jin daɗi ne." Najlah ta kashe gas sannan ta kalla Basma.

"Za ma ki warke ne, dan bashi kika ci, haka jiya na kwana hannuna a saƙe, yanzu ma dauriya nake." Ta nuna hannunta. Murmushi Basma ta yi.

"Nifa aikina na yi, kuma yanzu babu wani ƙwayar cuta dake jikinki, balle idan na miki na yau."

"Wallahi ba zaki sake min allura ba, hmmmm."

"Na ji amma dole na ƙarasa miki na yau." Harara Najlah ta watsa mata.

"Bara muje mu shirya." Da haka Fauza da Marwa suka wuce suka barsu.

Basma ta taka kusa da Najlah ta ce.

"Me aka dafa yunwa nake ji."

"Lallai, za ki haɗu dana dare ne ai." Baki Basma ta taɓe tana dudduba abinda suka dafa.

"Na ga jikinki ya yi sanyi? Menene?" Basma ta Lumshe ido ta buɗe.

"Har yanzu na kasa aminta dake, ke kishiyar Mom ce, idan na tuna haka raina zafi yake min, ohhhh gashi kina mutumci wani lokaci." Najlah ta yi murmushi sannan ta dafa kafaɗarta.

"Ni ba Kishiyar Mom ba ce, ƴar uwar ku ce, mai ƙaunar ku."

"Amma ke matar Abba ce?." Ta ɗaga mata kai.

"To kinga, kin mu'amalanci Abban mu, Ni kuma ina jin haushin duk macen da zanga tana rayuwa da Abba."

"Bassey ina sonki, Ina son halinki, bara na je na shiryarya Abba, nima zan fita dan yauwa ina da aiki." Da haka ta fara tafiya, amma ta tsaya jin abinda Basma ke cewa.

"Ina da mugunta, amma ba na iya illata mutum, koda nake son illataki, na tana da duk wani magani da za ki warke, amma ke bansan wani irin zuciya gareki ba, jiya kin fita, kin kashe mutum, yanzu kina cewa za ki wani aiki, hala nan ma ki kashe wani." ta kai nan cikin sanyi. Najlah ta jiyo ta kalla Basma, a hankali ta tako kusa da ita.

"Bassey hakane, sai dai Ni banda tausayin marasa imani, haka na taso, kuma har zuwa yanzu, zuciya ta bushe take, kuma alƙawari na yi ma kaina idan har ina raye rai da lafiya sai na shafe tsinanun ƴan iskan da suka addaba al'umma." takai nan cikin zafi-zafi har tana cizan leɓanta, sai Basma ta ce.

"Kina bani tsoro wallahi." Da haka ta kewayeta ta fita.

Najlah ta yi murmushi tana bin bayanta.

Da misalin 7:32am, Marwa, Fauza da Basma suka fita, Abba kuwa sai 10:12am, ya shirya tsaf Najlah ta rakasa har bakin mota, ya shiga yana cewa.

"Ƙarfe nawa za ki fita?."

"Sai Basma ta dawo tare zamu je da ita, ina so na rama abinda ta min ne." Abba ya yi murmushi.

"Babyyyy karki sa min ita kuma." Ta ɗaga mai kai tana dariya ƙasa-ƙasa.

"Ina alfahari da ke, ki dage da addu'a, Allah ya tsare, Ni sai dare zan dawo." Ta tura mai ƙafa tana cewa.

"Hmmm ina sonka da yawa kuma Insha Allah, kaima ka yi addu'a, Allah ya tsare min kai."

"Ameen." Da haka ta ɗaga mai hannu har motarsa ta fita.

Abba cike yake da farin ciki, harga Allah yana alfahari da Najlah, yana kishinta sosai, amma aikin al'umma take yi, zai barta ta yi, domin a wanna ƙasar ana buƙatar irinsu.

Najlah ta koma ciki, a babban Parlour ta zauna, ta ɗauki wayarta ta kira Rukky, duk bayan kwana biyu sukan yi waya da ita, a cikin wayar ne Rukky ke sanar mata da Ustaz ya turo magabatan sa kuma an tsaida lokaci nan da wata biyu.

Kiranta ta yi suka hira, sannan ta kira Mamie, nan Najla ta dinga zuba mata rigima, Mamie kuwa tana rarrashinta cike kewar ƴartata.

*Basma*

Tana shiga cikin asibitin kowa ya ƙananun magana, dan kuwa magana ɗaya keta yawo a asibitin 'An ce Basma ta yaudara Dr. Mukhtar, bayan ta gama tozarta shi, shine ya koreta daga aiki.'

A office ɗin da take zama ta zauna tana bin kowa na wajen da kallo, dan kuwa zance duk ya koma kunninta, a group ma haka suka dinga surutu kuma tana ciki.

"Hmmmm komai da kuka faɗa a kai na ya dawo min, sai dai babu wanda ya koreni daga aiki, yaudara kuma na yi idan akwai uban zai hukuntani to bismillah." ta kai nan tana taunar cinkam cikin tsiwa.

Babu wacce ta ce tak, har ta kai aya.

Sai ta ɗauki wayarta ta kira number Dr. Mukhtar wanda ta yi blocking nasa, unblock ta yi, ta kirasa, ringing ɗaya ya katse kiran, take kiransa ya shigo murmushi ta yi, batasan dalili ba daga safe zuwa yanzu ta yi tunaninsa ya da yawa, gashi ita kanta san ganinsa take yi.

"Ba...Basma......ke ce da gaske? Kirana kika yi?." ya faɗa a ɗan ruɗe, wayar yana hand-free hakan yasa matan wajen iyayana gulma suke ji.

"Ni ce."

"wow Alhamdulillah, kai masha Allah, addu'ata ta ƙarbu, zan iya zuwa gida na ganki?." Lumshe ido ta yi tana jin kewarsa sosai.

"A'a, babu bukatar, yanzu haka ina office ɗina, na dawo aiki yau." cikin farin ciki ya ce.

"Bassey da gaske? Karki min waya, zuciyata za ta iya bugawa wallahi."

"Ka tawo min da abu mai sanyi, ina jin zafi." Da haka ta katse kiran tana jan dogon tsaki.

"A duku ba zan bugu ba, kallon banza ko daga nesa ba zan ɗauka ba, harara kuwa sai a duhu." wata ce a cikin matan dake sanye fararen kaya ta ce.

"Sister Basma ba wani abun tada jijiyoyin wiya bane, shi wanda kike magana akan wasa wato Dr. Mukhtar, ba'a ce miki ya kai kuɗin aure ba."................

*********** "Dole a yau ne yi magana da Dr. Ashraf, amma ta ya ya? Idan har na fito mai ido da ido akwai matsala, ta ya zan samu keɓewa da Dr. Ashraf?." ya faɗa da ƙarfi yana dukan table ɗin gabansa, sai kuwa wata idea ta faɗo mai, da sauri ya ɗau wayarwa ya shiga tura saƙo kamar haka.

"46662233, 66255533, 7777666, 55444, 33327772." yana turawa cikin minti ɗaya aka mai reply.

"88877." Murmushi ya yi sannna ya aje wayar yana jin ransa ya yi fes..............

*Najlah*

Ta jima tana zaune kan kujera tana karanta littafin *ƳAR NOLLYWOOD* ta kasa tashi daga zaune saboda Chakwakiyar dake cikin littafin, ba ta taɓa karanta littafin Hausa ba, sai ɗazu da ta ga ana ta maganarsa a tiktok, hakan yasa ta bibiya number dake ji har maruciyar ta tura mata.

Kanta ya kulle da littafin, hakan yasa ta ɗau dogon lokaci a zaune ba ta sani ba, Chakwakiyar da ya fi tsaya mata shine *Ƙaryar da Yayar jarumar littafin suka yi da saurayin akan za su yi pretending suna da juna biyu, dan a ɗaura musu aure.* Haka tai ta shan karatu, har sai da ta yi da gaske ta aje wayar sannan ta yi sallar la'asar.

Bayan ta idar ta daure ba ta ɗau wayar ba, ta shiga kitchen, cikin natsuwa ta fara haɗa girkin dare.

Creamy garlic pasta ta fara ɗorawa, haɗe da grilled chicken mai ƙamshi da aka yi wa garnish da parsley. A gefe kuma ta haɗa buttered potatoes da sautéed vegetables masu launuka iri-iri da suka ƙara wa abincin armashi.

Ba nan ta tsaya ba, ta kuma yin seafood fried rice mai cike da prawns da shrimp, sannan ta haɗa creamy chicken soup mai kauri da ɗanɗano na musamman. Kitchen ɗin gaba ɗaya ya cika da ƙamshi mai ɗaukar hankali.

Da ta gama komai cikin tsari, ta shirya abincin a manyan kuloli masu kyau, tana kallon yadda komai ya yi matuƙar haɗuwa tamkar girkin hotel na alfarma.

Daga nan ta gyara kitchen ɗin fes duk da cewa su A'isha sun zo sunyi aikinsu gaba ɗaya.

A Dining ta jera komai, tana gamawa Basma na shigowa cikin fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi.

Take ta tsaya cak jin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko ina, numfashi ta sauke tana haɗiyan miyau.

"Abincin Mijina ne, babu ɗanɗano." Cewan ta tana mata fari, Basma data kwaso yunwa ta saki murmushi.

"Haba Ameen Basma, wannan ƙamshin ya ruɗani, kuma ance ido guba, ko ƙanzo zan ci nikam." Ta faɗa yana nufan Kitchen, sai dai babu komai hatta tukwanen duk an wanke.

Fitowa ta yi riƙe da Plate da spoon ta ce.

"A taimaka yunwa nake ji."

"Shike nan, ki yi sauri za ki rakani amso saƙon Abba."

"To, to." Murmushi Najlah ta yi tana cewa.

"Wannan na mijina ne, ki ɗiba wannan." Ta nuna mata babban kula.

Basma zama ta yi tana duba abincin, ido ta zaro.

"A ina kika yi order ne?." Najlah ta harareta tana nufan part ɗin ta.

"Tun baki ci ba kin fara santi, Ni wanka zanyi."

Basma tuni ta fara kai abincin bakinta, lumshe ido ta yi, sannan ta miƙe ta buɗe kulan Abba, ido ta zaro tana cewa.

"Wallahi sai na ci wanna, komai sai na ci, ai abincin Abba na mune." Da haka ta ɗiba nashi, ta ɗiba dukka nau'in abincin kowanne ludayi ɗaya, ta zuba a plate ɗaya.

Ba wani ci take sosai ba, amma da mamakinta ta ci abinci har da ƙarawa, ji ta yi kaman ta cinye dukka, tsaɓar daɗin abinci, take Zuciyarta ta ce. 'Oh Basma abincin Kishiyar Mom kike ci.' murmushi ta yi tana furta.

"Ai ba sonta nake ba, kawai yunwa nake ji, amma bana son Najlah, Kuma ba zan taɓa sonta ba." ta faɗa tana ƙara tabbar ma kanta haka.

Najlah na shiga part dinta, kaya ta cire ta nufa restroom, ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito ɗaure da towel, ruwa ne ke ɗiga daga gashinta, lotion ta shafa sannan ta busar da gashin kanta da handryer.

Turare mai sanyin ƙamshi ta fesa sannan ta sanya riga da skirt na Swiss Voile, mai ƙyau da tsada, ɗinkin ya hau jikinta sosai, Dan have gown ne da skirt. Ta ɗaura gyale mai laushi mai ƙyau, wanda ya rufe kanta da rabin jikinta kuma ya hau kayan.

A ƙafarta ta saka takalmi flat mai ƙyau, Daga sama har ƙasa shigarta ta yi kyau kamar ka sace ta la gudu, jakka ta ɗauka ta sa wayarta a ciki, key ta ɗauka sannan ta fita parlour.

Basma ta iska ta gama cin abinci, ta kunna Tv, tana ganin Najlah ta miƙe tana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, shigar matan aure ne, irin na manyan mata masu aji da class.

"Bassey bansan kallo." dariya Basma ta yi.

"Tsakani da Allah haka za ki fita?. Ki ɗau wanka ki kashe ɗauri? Ko biki zamu je ne?."

"A'a saƙo kawai zamu amsa." Basma ta jinjina kai.

Gyalenta ta mai ta a kai tana ɗaukan wayarta, ta kashe Tv sanna suka fita, Fauza ta kusa dawowa dan haka ba su kulle gidan ba.

Sabuwar motar Abba Lexus LX 600, ita suka shiga, suka nufa get, a hankali motar ta fita suka hau kwalta.

"Ya kikasan garin Abuja da ƙyau, bayan ke ƴar Kaduna ce?."

"Hmmm ai ina ga zan iya ɓatar da ke a garin nan, nasan waje da dama balle yanzu da ake amfani da location." Da haka suka yi shuru, Basma ta mai da idanunta kan titi.

Basma murmushi ta yi tana lumshe ido, tare da tuna abin da ya faru a ɗazu, bayan abinda Sister Bara'atu ta faɗa cikin gatse.

A zafafe ta miƙe tana ƙara maimaita kalman Sister Bara'atu.

"Kuɗin aure!?." sai ta ga sun kwashe da dariya.

A dai-dai lokacin Dr. Mukhtar ya iso bakin ƙofarsu, sannan ya buɗe dan showglass ne ana ganin na ciki dana waje.

Suna ganinsa kowacce ta yi shuru tana kama kanta, jingina ya yi da jikin ƙofar yana kallon Basma dake tsaye.

Yadi mai laushi ne jikinsa launin kore, rigar ma ƙaramin hannu, sai aikin da aka yi da launin ɗorawa, haka hular kasansa launin ɗorawa ne da kore-kore, idan ta ce be yi ƙyau ba ta yi ƙarya, daga sama har ƙasa ya haɗu.

Kafin ta buɗe baki ta yi magana, ya tako a hankali har zuwa gabanta, karo da na farko da ya riƙe mata hannu, ya kai bakinsa, sumbata ya yi.

Yarr Basma ta ji, ta rintse ido tana tauna kalaman da suke bakinta.

"Wai.......wai ance ka kai kuɗin aure?." Ta faɗa cikin wani yanayin da ta kasa fassarawa.

Kai ya ɗaga mata, take ta sauke mai lafiyayyan mari a kuncinsa, Dr. Mukhtar ya lumshe ido, su kuma mutanen da suke zaune suka fara fita da sauri-sauri.

Basma za ta sake magana ya rufe mata baki da hannunsa sannan ya zagayo da ita daga kujerar da take.

Hannunta ya riƙe, ya fara tafiya ita kuma ta bi bayansa, haka suka fita kowa ya zuba musu ido, be tsaya da ita ba sai a office ɗin sa, yana shiga ya kulle ƙofar.

Basma ta nema waje ta zauna tana tunanin me ya kamata ta yi, idan har tana jin kishin abin ya yi to har yanzu tana son sa, kuma ai ita ta koresa, ta liƙe ma Anas.... *ANASS* ta tuna sunan tana jin ranta yana ɓaci.

Jin an dafa ƙafarta yasa ta kalla gefanta, Dr. Mukhtar ne ya zauna a ƙasa, ya dafa ƙafafunta, sannan cikin sanyi ya ce.

"Tabbas na kai kuɗin aure, amma ba yanzu za'a yi ba, sai nan da wani lokaci." Cikin wani irin rauni Basma ta ce.

"Hmmmm shike nan, banga laifin ka ba, zan wuce." Da sauri ya ƙara matse ƙafarta.

"Kinsan ba zan Ina so ki zaɓa, na fara aurenki ko idan na aureta na aurenki." ya faɗa yana matse dariyar dake son kamasa jin wata uwar ashar ɗin da Basma ta yi.

"Kan babban bala'i, me.....mene?......hmmmmmmm kai kasan cewa ba zan zauna da kishiya ba wallahi, ƙarya ne Mukhtar, ko kaine autan maza na yafe, kasan Ni da kishi kuwa.........hmmmm na yafe, wallahi bana so." Da haka ta fizge ƙafafunta sannan ta miƙe tsaye, ranta in ya yi dubu ya ɓaci da maganmagun sa, haka ta danne komai, dan za ta iya rufesa da duka.

Idanunsa ta kalla sai ta yi ƙwafa ta juya ta fara tafiya, da sauri ta dawo baya dan kuwa janyota jikinsa ya yi, ta faɗa ƙirjinsa, ba ta saurin kuka ta yanzu ta fara, amma yarda take jin zuciyarta kaman yana ci da wuta.

"Baby relex! Komai kike so shi zanyi, kinsan ina sonki." Kasa raba jikinsu ta yi amma ji yake kaman ta daɓa mai wuƙa.

"Na tsaneka, karka sake cewa kana sona, karka sake."

"Mahaifin yarinyar da kansa......"

"Zan zage ka, ka dena faɗa min shirme." Murmushi ya yi sannan ya ce.

"Ki bari ki ji ƙarshen mana.........iyayena suka je suka ga mahaifinta wancan satin, kuma ya ce yaban ita, sukayi alƙawarin aure, aka biya komai, amma ba'a sa lokaci ba saboda ita........." kuka ta fashe da shi mara sauti tana cewa.

"Mukhtar zan maka Allah ya isa, wallahi zanyi maka baki, i hate you" sai ya rage murya ya ce.

"Hankalina a kwance yake, saboda Abba ya ban Basma." da sauri ta turesa tana nufan hanyar fita.

"Abba da kansa ya ban Basma, dole kika hankalina a kwance, kema kinsan banda mata a duniyar nan sai Basma." Ta kasa juyawa haka ta saka ci gaba da tafiya.

Wayarta dake hannunta ta latsa number Abba, ɗauƙa ya yi.

"Ina meeting zan kira ki." da sauri ta ce.

"Abbana wai ka bada aure na?." Jin yanayinta yasa ya tsaya daga katse kiran.

"Eh, ban faɗa miki bane saboda wasu dalilai......." abinda ta iya ji kenan daga kalaman Abba, wayarta ta cire a kunninta tana katse kiran.

A hankali Dr. Mukhtar ya tsaya a gabanta yana murmushi.

"Na ji daɗi, kina so har haka?." Baki ta tura gaba.

"I hate youuuuu."

"I love you."

"I hate youuuuu My life." Murmushi ya yi sannan ya rungumeta.

Bayan nan ta koma wajen aikinta cike da nishaɗi, magulmata suka dinga bin ta ido, ita kuma ta dinga zuba murmushi kamar sabuwar kamu.........

★ Parking Najlah ta yi, hakan yasa ta buɗe idanunta tana kallon inda suka zo, cike da mamaki take kallon unguwar ta da kasance shuru-shuru, mota ma babu hanyar bi.

"Mu je." Basma jikinta ya yi sanyi, amma haka ta fita tana cewa.

"Ina zamu je?."

"Can gidan." Da haka Najlah ta yi gaba.

Basma tsoro ta ji kar ace sai da ita za ta yi, haka suka isa bakin get ɗin gidan.

"Ina ne nan? Tsoro nake ji." murmushi Najlah ta yi.

"Ki saki jikinki, babu komai, kuma ina tare da ke." Kai Basma ta ɗaga sannan suka shiga cikin gidan.

Babu kowa, sai wata ƙofa dake buɗe, Basma batasan ta maƙalema Najlah ba.

Take wata murya ta daki kunnuwansu mai ƙara da amo.

"Ku shigo, banda sallama." Dum kirjin Basma ya buga, Najlah ta sauke ɓoyayyen numfashi, sannan ta fara karanto addu'ar da ta zo bakinta.

Shiga suka yi ciki, take Basma jikinta ya fara rawa, a ranta tana ta maimaita, *'Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un, mun shiga uku, ashe Abba ya yi gamo da matsafiya, ko dai jinina za ta bayar, Wayyo Ni Wayyo Allah na.'*

Zama suka yi, gaban wannan mutum, dake baza babban riga.

Kallonsu ya yi yana washe jajayen haƙoransa, Basma ta yi yaƙe mai kama da kuka, Najlah ce ta buɗe baki ta ce.

"Ƙanwata ce, ba ta saba zuwa irin wajen nan, nima wata ce ta min ƙwatance, ance aikinka kaman yankan wuƙa." Murmushi ya yi.

"Meke tafe da ke hajiya." sai ta nuna Basma da hannunta, take Basma cikinta ya juya, ta matse cibiyoyinta dan fitsari ta ji ya matseta.

"Aikin akan wanda yake son aurenta ne, ina so a mallaka mana shi, sai yarda muka ce haka zai yi, sannan nima mijina ina so a ƙara mallaka min sa." Ta kai nan tana istigfari a cikin ranta, tare da ɓoye tsoron da take ji, dan tabbas Bokan abin tsoro ne.

"Aikin zai kammala nan da gobe, amma Aljanu suna buƙatar, gashin hamtar saurayin, dana gabanta, sai Akuya wacce ba ta tafiya, na ki kuma Hajiya, muna buƙatar jinin al'adarki, tare ruwan ni'imarki, da shi zamu yi muku aiki." Basma miyau mai kauri ta haɗiye, sannan ta kalla Najlah dake murmushi.

"An gama, zuwa gobe zamu kawo, duk da na saurayin zai yi walaha, amma boka karka damu, yanzu dai bara na baka wani abu." Da haka ta buɗe jakkarta ta fara cire kuɗi, 200k ta aje tana sake mai da hannunta cikin jakkar, boka ya washe baki yana kallon kuɗin, Basma ma idanunta suna kan kuɗin, take Basma ta sake sanya hannunta cikin jakkar lokaci guda ta ciro bindiga tare da danna kunamar ya ba da sautin *Fas.* Take Boka ya kife a wajen, dan saitin zuciyarta ta harba, Basma kuwa ta tafi luuuuu ta suma, Najlah ta sauke ajiyan zuciya tana fara karatun Alqur'ani cikin ƙira'arta mai daɗi, da sanya natsuwa, suratul jinni da fara daga.................✍️ END. *★BUDURWAR ABBAN MU★* _by PRETTY SK CE 😍✍️_

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing na jaruman Shidoria*👇

```1. BUDURWAR ABBANMU Pretty Sk.``` ```2. WASAN KADDARA Asmeetah Writter.``` ```3. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal.``` ```4. KURUCIYA Fatima Bintu Hussain.``` ```5.MABANBANTAN ZUKATA Maryam Star.``` ```6. ƘADDARAR MASOYA Umulkhairy Hashim Abo.``` ```7. GARWASHI Hafiza Amanar Ameey Laylerh.``` ```8. YARINTA Amanar Ta Batulu.``` ```9. BOYAYYEN SIRRI Amanar Shidoria Writter.``` ```10. DAGA BAYA Sha'awanatu Farouk Diggi.```