BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 4️⃣5⃣⏩4️⃣6

by @prettys01

> ..................Lokaci guda ta ciro bindiga tare da danna kunamar ya ba da sautin *Fas.* Take Boka ya kife a wajen, dan saitin zuciyarta ta harba, Basma kuwa ta tafi luuuuu ta suma, Najlah ta sauke ajiyan zuciya tana fara karatun Alqur'ani cikin ƙira'arta mai daɗi, da sanya natsuwa, suratul jinni da fara daga................

A hankali ta miƙe tsaye, kuɗin ta ɗauka ta mai da cikin jakka, sannan ta kalla cikin ɗakin da ƙyau, har lokacin kuma tana ta rera karatun Alqur'ani nan babu tsayawa.

Za ta iya ɗaukan Basma har mota, amma ta nema ruwa ta yayyafa mata, a firgice ta farka tana salati, lokaci guda ta miƙe ta yi waje da sauri.

Najlah ta bi bayanta, kafin ta fita a gidan har Bassey ta shiga mota ta duƙunƙune waje ɗaya tana ta addu'a da ƙarfi.

Jin Najlah ta figa mota yasa ta rintse ido tana ƙare matse jikinta da jikin kujera kamar za ta shiga ciki.

Najlah parking ta yi a Compound ɗin gidan, a dai-dai lokacin aka fara kiraye-kirayen sallar magrib.

Kafin ta fita a motar har Bassey ta fice ta nufa ciki da gudu, kai Najlah ta girgiza sannan ga fito hankalinta kwance, ta nufa ciki.

Fauza ce zaune tana kallo, ganin Najlah ta shigo, ta miƙe fuskarta ɗauke da fara'a.

"Ammeen Basma an dawo lafiya?." Najlah ta faɗa ɗa murmushinta.

"Lafiya lau."

"Kawo jakkar na riƙe miki."

"Karki damu zauna ki ci gaba da kallon ki." Sai ta ɓata fuska.

"Dan Allah ki kawo....."

"Amsa." Ta bata jakkar, murmushi suka yi sannan suka shiga jera.

"Naga Basma ta shigo a ruɗe, Allah yasa lafiya?" Ta faɗa tana aje jakkar kan kujera, Najlah ta cire gyalen tana murmushi.

"Lafiya lau, kawai ta tsorata ne da wani abu."

"Ok, Uhmmm na ce wani abu?." Sai ta kalla Fauza jin sanyi a muryanta.

"Faɗa kanki tsaye Autar Abba." Fauza ta matsa kusa da ita, Najlah ta riƙe hannunta tare da zaunar da ita gefanta, cikin taushi murya ta ce.

"Uhum ina ji." Fauza ta sauke ajiyan zuciya ta ce.

"Ki yafe min duk abin da na miki, sharrin shaidan ne."

"Babu abinda kika min, in kin min ma na yafe miki wallahi." Cikin jin daɗi ta ce.

"Na gode sosai, zan iya rumgumarki." Najlah ta janyota jikinta tana cewa.

"Mun zama ɗaya ki ɗauke Ni kamar su Basma."

"Insha Allah........kina burgeni wallahi." Murmushi Najlah ta yi.

"Na gode Autar Abba."

"An shiga salla bara na je na yi." da haka Fauza ta fita cike da annashuwa.

Najlah wanka ta sake yi sannan ta yi sallah, ba ta sauka kan darduma ba sai da ta yi sallar isha'i, sannan ta miƙe ta cire Hijab, a Parlourn ta zauna tana jiran Abba, ta ji shigowarsa lokacin sallar isha'i, tasan masallaci ya wuce yanzu zai dawo.

Ba ta ɗau lokaci ba ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, da sauri ta miƙe ta nufesa da gudu, jikinta ta ɗane.

"Oyoyooooooo Mubeey." Murmushi ya yi.

"Baby a gajiye nake, karki ƙara sani." Sauka ta yi jikinsa.

"Oh sannu Baby." Ta amsa jakkarsa.

Da haka suka isa wajen kujera ya zauna, ita kuma ta sauna a ƙasa ta cire mai safa, sai ta cire mai hula, a jikinsa ta zauna.

"Baby wanka ko abinci?." ya lumshe ido sannan ya buɗe.

"Abinci, ina jin yunwa sosai." murmushi ta yi tana jan dogon hancinsa mai tsini.

"Muje muci to." tare suka tashi, main Parlour suka isa, babu kowa, sai suka zauna a Dining area, abinci ta zuba musu a plate ɗaya, ta sanya spoon ɗaya.

Tana bashi yana bata haka suka ɗau dogon lokaci suna ci Abba yana ta santin girkin Najlah.

"Baby a Ina kika kowa girki? Nasan ba wani zaman gida kike ba." Ta yi murmushi tana sake kai ma abinci bakinsa da hannunta dan shi baya son da cokali, cizonta kaɗan ya yi, ta yi saurin cire yatsar tana yarfe hannu.

"Auchh Abbaaaaa."

"Sorry Angel, duk santin abinci ne shi yasa."

"Hmmm a YouTube na kowa, ina yawon kallon girke-girke, hakan yasa na iya, kuma idan har naje gida ina taya masu aiki girki." Murmushi ya yi sannan ya goge bakinsa da tissue.

Parlour suka isa, suka zauna manne da juna, Najlah na wasa da gemun sa shi kuma yana kallon American film.

Suna zaune Marwa da Basma suka sauko, hakan besa Najlah barin abin da take ba, suka zauna daga ƙasa suna gaishe sa Abba, ya amsa cikin sakin fuska.

Basma jikinta har yanzu be dawo daidai ba, gaba ɗaya a ruɗe take, kawai ƙarfin hali ta yi wajen saukowa, shima saboda Abba ya ce za su yi magana ne.

Fauza ta sauko riƙe da littafi, calculator da biro wanda ta sa baki tana ɗan cizarsa.

"Ammeen Basma Please help me." Ta faɗa tana bata littafin hannunta.

"Abba Barka da dare."

"Yauwa autata."

"Kaina ya kulle gaba ɗaya, Basma ce ke taya Ni mathematics, sai dai bata yanayi mai ƙyau." Najlah ta duba Littafin tana cewa.

"Aunty Marwa fa?." lokaci guda Fauza da Marwa suka yi dariya.

"Ban iya maths ba, duk lissafin da ya wuce addition bana so." Abba ma murmushi ya yi.

Take Najlah ta fara fasa mata lissafin da kai, tana faɗa Fauza na rubutawa cike da jin daɗi, Duk kallonta suke yarda take zubo numbers Babu mistake tana kai ƙarshe Fauza ta tafa mata.

"Kaiiiiii you're Diamond."

"Thanks." Najlah ta faɗa tana mai da hankalinsa kan Abba da ya yi gyaran murya yana cewa.

"Marwa saura sati Uku biki, wani shiri kika fara akan haka, duk da Ammeen Basma ta yi order na kayan Kitchen, ki dai fara shiri, duk Ni bana son wasu bidi'a, and zan tura miki kudi na wasu hidindimu da za ki yi." cikin sanyi Marwa ta ce.

"To Abba Allah ya ƙara arziƙi."

"Ameen, ko da wata matsala ne? Na ga yaron ma baya zuwa." ɓoyayyen ajiyan zuciya ta sauke, ita har ga Allah auren ya fita a kanta, ko zumuɗi da farin ciki ba ta yi, hakan yasa ta gayyaci ƙawayenta kaɗai ta ce musu babu anko.

"Abba babu komai wallahi."

"To masha Allah.......ke kuma Basma, na bada aurenki, amma sun nema nan da ɗan lokaci kafin a ɗaura, ban faɗa miki ba saboda haka saurayin ya nema, kinsan na ɗauki Mukhtar kaman ɗan da mahaifa, Ni kaina zan yi alfahari idan har ya zama sirikina." Da haka ya yi shiru, Basma ta rasa meke mata daɗi, har ga Allah lokaci guda ta ji ta tsana Anas, ko ganinsa ma bata sonyi, haka ta yi blocking numbersa, tana kuma ta addu'a akan Allah yasa su sake haɗuwa.....

"Basma!." Da sauri ta kalla Abba.

"Na.... Na'am Abba."

"Kinyi shiru." Kai ta ɗan dage tana cewa.

"Abba, kasan me na gani da idanuna yau?......kasan me Matarka ta yi a gabana?." Murmushi Najlah ta yi amma idanunta na kan tv.

"Basma nasan koma me kika gani Alkhairi ne"

"A'a Abba, ba shi bane?." Murmushi ya yi sannan ya ce.

"Me ya faru to?." Marwa ma ta kalleta, haka Fauza dake rubutu ta kalleta dan jin ta fara koro musu zance.

Abba ya yi ma Najlah wani irin yarda ne wanda shi kansa baya ce ga irin sa ba, ya karance ta da ƙyau, kowani abu da za ta yi yana da dalili mai ƙyau, ko da Basma ta furta sunje wajen Boka, ido ya zaro kamar yarda su Marwa suka yi, amma a ransa yana ta saƙe-saƙe akan Allah yasa ba wani abu ta mai ba, alai tana kai ƙarshe, Abba ya dafe ƙirji yana duban Najlah.

Basma ta kai ƙarshe tana hawaye.

"Ta harbesa har lahira, ko tsoron Aljanun da suke wajen ba ta yi ba, Abba wannan matar ta ka ba ita kaɗai ɓace, ka bincika lafiyarta." Ta share hawaye da suka zubo mata.

Marwa ta yi da ƙyar tukun numfashinta ya dawo daidai, amma ji ta yi ya dena fita ta hanyar da ya dace.

"Naga sai bina kuke da kallo, bayan wani abu na maiba, ki bari next fita idan zan yi kisan hulaƙanci da wuƙa za muje tare da ............" da sauri Basma tari numfashinta.

"Idan kin ganni a lahira kaini aka yi, babu inda zani." hayaniya suka fara yi kaman kaji, Abba, Marwa da Fauza kallonsu kawai suke yi, suna dariya.

"Ƴata ki fita a ido na rufe....."

"Sunana Basma, kuma Ni ba ƙyarki ɓace ki." Najlah ta miƙe tsaye tana masifa.

"Hmmmm yadda kasa ke ƙwai haka ƙwai ke kaza, na gaba ya yi gaba na baya sai labari, ko ki so ko ki ƙi matar Abba nake, Ammen Basma." da haka ta yi fari da ido.

Basma ganin hayaniyar zai koma faɗa, yasa ta shafa ma kanta lafiya ta yi shiru, dan tsoron Najlah take yi.

Abba cikin taushi ya kalla Najlah ya ce.

"Ammeen Basma ki dena hayaniya, yaranki ne fa, be dace ba sam, ya kamata komai da za ki yi a gabansu ya zama mai ƙyau saboda dake suka koyi." Najlah ta zauna tana sinne kai.

"Hakane Abba, na mata Ni uwace." Murmushi ya yi sai ya miƙe.

"Zan shiga ciki, sai kin shigo." Ta ɗaga mai kai, da haka ya wuce.

Najlah ta kallesu sannan ta fara magana kamar ita ta haifesu

"Marwa yaushe za ki gama exam?." Marwa ta amsa mata ba yabo ba fallasa.

"Jibi."

"Yauwaaaa, washegarin ranar Hajiyar ƙamshi za ta zo daga Maiduguri, za ta yi aikinta har zuwa biki."

"Wani aiki?." Cewan Fauza. Najlah ta kalleta ta ce.

"Gyaran jikin amarya, ina so a gyarata fes, jikinta ya yi fresh luwai-luwai."

"Naganeeee, Nima za'a min dilka ko?."

"Uhmmm Amarya kawai, ke ƴar kallo ce, sannan Marwa ki dage ko yayane ki iya girki kafin lokacin, Basma kuma kafin nata za ta goge sosai." Ƙaramin tsaki Basma ta ja.

"Bassey ki kama kanki, zan......" Da sauri Basma ta miƙe sannan ta bar musu parlour tana cewa.

"Ba za ki sauke min hauka ba, banda wannan lokacin ki." Najlah ta yi ƙwafa bayan ta haura, Marwa ta ɗan ƙara sakin jikinta, haka suka sha hira akan bikin, Najlah ta ji daɗi sosai ganin yarda suka ɗauke kaman ƴar uwa.

★★★★

Ƙwance tashi a sarar mai rai, rayuwa haka take tafiya, abubuwa suna faruwa masu daɗi da rashinsa, haka an samu sauye-sauye ta kowani ɓangaren.

*Gidan Abba*

Gida sai dai ace masha Allah, dan kuwa mutane ne ta ko ina ana ta shirye-shiryen bikin Marwa wanda washegari ne ɗaurin aure, ƴan uwa da mutanen arziƙi na nesa duk sun so, dan kuwa Najlah ce ta gayyaci kowa, wasu dai a ɗarare suka zo gidan kwana saboda su Basma, sai dai suna iske canji mai yawa, dama Fauza ƴar kowace, Amarya kanta ta sake ma kowa fiye da yarda ta saba, Basma ne dai ba yabo ba fallasa, gaisuwa ne ke haɗata da kowa daga haka shike nan.

Duk da gari ya yi duhu, amma haka hayaniya ke tashi a cikin babban Parlourn, mata kusan 9 da yaransu ne zazzaune suna ta hira ana shewa.

Fauza ce suka shigo ita da su yara kusan agemate ɗin ta su huɗu, sun sha make-up sai kaudi suke yi, ga Ankon Swess Less da suka yi marron colour, matan suka gaisar sannan suka nufa part ɗin Abba.

Suna shiga suka iske wasu manyan baki a nan suna kallo, gaishe su suka yi sannan suka nufa ɗakin Najlah, ƙawayen suka tsaya, Fauza ta yi knocking tana shiga.

Tana shiga ta iske Najlah gaban mirrow tana sa agogo a kan tsintsiyar hannunta, irin ankon dake jikinta, an mata ɗinkin buba, ya yi ƙyau sosai, Babban gyale ta yafa tana kallon Fauza ta ce.

"Muje, nasan an fara Event ɗin ma."

"Ammeen Basma kinyi ƙyau sosai." Murmushin kan fuskarta ta faɗa ɗa tana daukan key.

"Na gode kema kinyi ƙyau sosai." Da haka suka fita, lokaci ta kalla 8:46pm, kuma 8:30pm ake farawa.

"Ahhh ashe dai zan gane Mariya wannan ƙyau haka." Ta faɗa tana kallon yaran, dariya suka dukkansu sannan suka nufa babban Parlour.

Akwai ƴan tafiya ma a lokacin, haka suka hau mota biyu, suka nufa *Royal Palace Event Center* wanda a can za'ayi event ɗin.

Driving take a hankali, tana yi tana murmushi, a yanzu abubuwa da yawa suna mata dai-dai, Allah-Allah take a gaba bikin nan, ta hau aiki gadan-gadan duk da kuwa a yanzu ma bincike take akan Black Dragon, Wanda a yanzu ta'addacinsa ya ƙara haɓaka, kisa, garkuwa da mutane, da kowani mugun aiki, sai addu'a kawai, ya addaba al'umma ta kowani bangare.

Parking ta yi a gefan inda aka jera motoci masu yawa, suka fita, a tare suka shiga ciki, suna taku a hankali.

Najlah sai ta fito kamar ɗawisu, ba ta yi make-up ba, faɗin haɗuwarta ɓata lokaci, dan kuwa daga sama da ƙasa ta yi match komai da tasa ya hau jikinta, ta fito ta yi fes, wani ƙiba da ta ƙara, kai kace babbar mace ce. (Babbace ai, tunda ta haifa su Basma 🤣)

************

Sanye yake da ɓaƙaƙen kaya, kamar kullum, yana zaune yana magana da Senator Tumɓa, wanda tun sati ɗaya bayan aka sallamesa, ya dawo gida, mutane sama da 100 suke zagaye da gidan dan bashi kariya, a kashi 75% na mutanen da suke ƙasar nan, suna ƙaunar sa da zuciya ɗaya, kuma akansa zasu iya rigima da kowa.

Senator Tumɓa, yana zaune daga gefan gado, murmushi ya sake saki yana kallon Black Dragon.

"A gaskiya bani da kalaman za dan iya gode maka, a yanzu mutanen da nake da goyon bayansu suna da mugun yawa, nan da wata uku zaɓe, tun yanzu ji nake na ci zaɓe ma, jama'a da kansu suke furta ko bazaɓe sai na ci, idan banci ba za su ƙona ƙasar nan." ya kai nan harda buga ƙafarsa akan lallausar carpet ɗin dake malale da ɗakin. Cikin wani irin murya mai amo Black Dragon ya ce.

"Karka damu, komai yana tafiya yarda ya dace, da so nake na kashe Mr. Muhammd Babangida Shamaki, amma zan bar shi da ciwon zuciya, haka zan sa mutane gaba ɗaya su juya mai baya, hmmmmm yanzu wasan zai soma." Murmushi Senator Tumɓa ya sake yi.

"Shike nan, ya maganar safarar yaran?."

"Nan da sati biyu zan tura su, kafin nan zan cika adadi, yanzu su 80 ne ƙasa kuma ana buƙatar 130, sun riga sun turo kuɗi, harƙalla ta faɗa." Kai Ya ɗaga sama.

"Nima akwai yaran da suke waje na, su 34 ne wanda ta gidauniyar taimakon yara zuwa ƙasar waje aiki, nan da ɗan lokaci matan za su fi haka ma."

"Shike nan, zuwa gobe a kaisu maɓuya na."

"Okay." da haka suka tattauna sosai akan mugayen harƙallolin su, sannan suka yi sallama.

Ta yarda ya shigo a ɓoye haka ya fice a gidan ba tare duk jama'ar gidan sun gansa ba, mota ya shiga sannan ya bar wajen...............

*THE PRESIDENT MUHAMMAD BABANGIDA SHAMAKI*

Besan lokacin da hawaye suka gangaro mai daga fararen idanunsa ba, komai da yake yi Allah ya sani ba da zuciya guda yake yi, amma mutane sun juya mai baya, idanunsu ya kulle basa ganin kowa sai Tumɓa, wanda yake da yaƙinin yana da hannu a cikin duk iftila'in da suke faruwa a ƙasar nan.

Abin da ya fi tsaya mai a rai shine, wasu ƴan jam'iyyarsa NUJP sun fita sun koma PRM, a cikinsu harda babban abokinsa Hon. Kabiru Jarma, da faruwar haka suka yi husuma sosai, har ta kai a babban gida gommati aka yi hargitsin, da ƙyar mutane suka raba, ashe tashin hankali na biye.

A washegari sai gawar Hon. Kabiru Jarma, an bishi har gida an mai yankan rago, kuma aka ake wani paper Mai ɗauke da gajeran saƙo.

"*WANNAN YA ZAMA KASHE DI GA MASU JIYAMIN BAYA.*"

A ranar sai dai Sir Muhammad Babangida Shamaki, ya faɗi har ruwa aka samai, bayan da ya farfaɗo, aka sanar da shi iyalen mamacin sun shigar da shi ƙara, maganar ta ƙara ɓata mai rai, hakan yasa ya yi amfani da ikon da yake da shi ya rufe maganar, sai an gudu ba'a tsira ba, mutane suka dinga surutu akansa, shi kuma ya kasa fitowa ya yi magana da kowa.

A hankali ya sauke ajiyan zuciya, sannan ya ɗauki mug ɗin gabansa ya kai baki yana raya abubuwa da yawa........

*Royal Palace Event Center*

Wajen ya kasance tamkar wata duniya ta alfarma da ake zuwa shagali dan kece raini. Tun daga bakin ƙofar shiga, manyan fitilu masu sheƙi suke haskakawa cikin launuka masu yawa, yayin da jami'an tsaro cikin baƙaƙen suit ke tsaye suna duba baƙi cikin tsari da nutsuwa.

Motoci na alfarma sun cika harabar wajen, wasu gadi ma sai buɗe musu ƙofa cikin girmamawa, kuma ajere cikin tsari.

Cikin hall ɗin kuwa, komai na wajen ya bayyana tsantsar ƙyau da tsari. Fararen labulaye masu laushi an kawata su da fitilun golden light masu ɗaukar ido, yayin da manyan chandeliers ke rataye daga sama suna baza haske mai sanyi da ƙayatarwa. Kujeru da tebura an shirya su cikin tsari irin na manyan taruka, kowanne tebur ɗauke da fresh flowers da ƙananan kyandirori masu ƙamshi.

A gefe guda kuma, masu abinci suna kai da komowa cikin uniform masu kyau, suna ɗauke da manyan trays na abinci iri-iri. Ƙamshin jollof rice, pepper soup, grilled chicken da sauran abinci masu tsada ya gauraye cikin hall ɗin, yana ƙara wa wajen armashi.

Akwai drinks station mai cike da juices, mocktails da kayan sha masu launuka iri-iri da ke ɗaukar idon baƙi.

Manyan mutane ne suka cika wajen-'yan siyasa, attajirai, sojoji, da fitattun mutane-kowanne cikin shiga ta alfarma.

Yawancin matan wajen sun yi wannan ankon. yayin da wasu mazan suke cikin suit masu tsada.

A tsakiyar hall ɗin kuma, wata ƙungiyar mawaka tana rerawa a hankali, kiɗan violin da piano na ƙara wa wajen nutsuwa da martaba.

Wajen ya ƙawatu iya ƙawatuwa, ga mutane an cika sosai, haka suka raɓa har zuwa wajen da Basma ta tanadar musu.

Basma ita Angon ƙawaye ta yi, duk a ƙurarren lokaci aka fito da shi, amma mutane sunyi sosai.

Riga da skirt ta yi, ɗinkin ya zauna a jikinta sosai, ga lallen da ta sha sai ya ƙara mata ƙyau, ba ta yi make-up ba, Choculate skin dinta sai sheƙi yake, dan da su aka yi gyaran jiki, ko me Marwa ta shafa sai sun shafa suma.

"Ku zauna a nan, zan sa a kawo muku abinci." Ta faɗa a haɗe, haka take ma Najlah magana bata sake mata sam, wai kar ta rainata.

Da mamaki Najlah ta dafa Basma tana cewa.

"Ina Amarya da Ango?." Basma ta ɗan taɓe baki tana cewa.

"Sun zo har an fara, sai kuma suka fita waje wai zasu yi sirri, yauwa gasu nan ma." Ta kai tana murmushi.

Da sauri Najlah da mutane da yawa suka juya dan ganin shigowar amarya.

Najlah murmushi ta yi ganin farin cikin dake kan fuskar Marwa, wanda ta jima ba ta yi.

Kwatsam fitilun cikin Royal Palace Event Center suka ɗan dusashe, alamar akwai wani muhimmin shigowa da za a yi. Nan take hayaniyar mutane ta ragu, kowa ya maida hankalinsa zuwa babban ƙofar hall ɗin.

A hankali aka fara jiyo sautin kiɗan violin mai taushi yana tashi cikin nutsuwa, yayin da wasu fararen fitilu suka haskaka hanyar shiga. Ƙofar hall ɗin ta buɗe sannu a hankali, sai ga ango ya bayyana cikin wani lallausan suit baƙi mai matuƙar haɗuwa da farar riga a ciki, takalmansa masu sheƙi na ƙara masa ƙyau, Fuskar nan tasa cike take da murmushi da ƙasaita yayin da yake taku cikin nutsuwa.

Bayan shi ne amarya ta bayyana... Take numfashin mutane ya kusan ɗaukewa saboda tsantsar ƙyawunta. Tana sanye cikin doguwar riga mai launin silver da white, cike da duwatsu masu kyalli da ke walƙiya ƙarƙashin hasken hall ɗin. Dogon veil nata na jan ƙasa a bayanta cikin tsari kamar sarauniya, yayin da kayan adon wuyanta da hannunta ke ƙara fito da kyau da martabarta.

A hankali take taku tana riƙe da bouquet na fararen furanni, murmushinta mai sanyi na sa zukatan mutane narkewa. Yayin da take ƙarasowa kusa da ango, mutane suka fara tafa hannu cikin farin ciki da sowa.

"Wow!"

"Masha Allah!"

"Sun yi kyau sosai!"

Kalaman mutane suka cika hall ɗin, yayin da cameras ke walkiya ta ko'ina suna ɗaukar wannan lokaci mai cike da armashi. Angon ya miƙa hannunsa cikin salo, ita kuma cikin kunya da fara'a ta sanya hannunta cikin nasa, sannan suka fara takawa tare zuwa tsakiyar hall ɗin kamar wasu sarakai na gaske.

Lokaci guda M.C ya saki sautin da ya yi dai-dai da yanayin su.

Haka suka taka har zuwa wajen zamansu, suka zauna, suna ta sakin murmushi.

Duk wanda ya kallsesu yasan sun haɗu sun dace.

Marwa ta kalla Al-hussain tana mai raɗa, hakan yasa ya ɗan matsa kaɗan, jikinsu ya goga juna, wannan sanyi ya ƙara ratsa jikinsu gaba ɗaya, irin dai na ɗazu, a tare suka lumshe ido, sannan Marwa ta buɗe cikin taushi da natsuwa ta ce "Al-hassan ina cikin farin ciki fiye da misali, harga Allah rashin zuwan Al-hussain ya min daɗi sosaiiiii." ido ya ɗan zaro, ita kuma ta yi dariya tana gyara zamanta, da haka aka fara shagalin da ya tara kowa a wajen................✍️ END.

> Me....me.......bangane ba Jama'a, Al-hassan? Ta ya?????.

*★BUDURWAR ABBAN MU★* _by PRETTY SK CE 😍✍️_

*THE SHIDORIA WRITER'S 📚✍️*

*Zazzafan Littafin da suke ongoing na jaruman Shidoria*👇

```1. BUDURWAR ABBANMU Pretty Sk.``` ```2. WASAN KADDARA Asmeetah Writter.``` ```3. DAGA RUGA NAKE Mrs Awwal.``` ```4. KURUCIYA Fatima Bintu Hussain.``` ```5.MABANBANTAN ZUKATA Maryam Star.``` ```6. ƘADDARAR MASOYA Umulkhairy Hashim Abo.``` ```7. GARWASHI Hafiza Amanar Ameey Laylerh.``` ```8. YARINTA Amanar Ta Batulu.``` ```9. BOYAYYEN SIRRI Amanar Shidoria Writter.``` ```10. DAGA BAYA Sha'awanatu Farouk Diggi.```

LAST PAGE 4️⃣7⃣ ⏩5⃣0⃣.

> "Al-hassan ina cikin farin ciki fiye da misali, harga Allah rashin zuwan Al-hussain ya min daɗi sosaiiiii." ido ya ɗan zaro, ita kuma ta yi dariya tana gyara zamanta, da haka aka fara shagalin da ya tara kowa a wajen...............

Shagali ake fara yi babu tsayawa, mawaƙa suka rera waƙa, wanda aka haɗa sunan Amarya Marwa da mijinta Al-hussain, haka suka dinga rera waƙan cikin annuwa.

Al-hassan dake zaune ya lumshe ido, yaƙe kawai yake yi, amma cikin ransa a cunkuse yake, abubuwa da yawa suna mai yawo a cikin kai, balle abinda ya faru a ɗazu, da misalin 7:30pm na dare.

Al-hassan abin duniya duk ya ishe sa, tunda maganar aure ta ƙara shiga tsakani Marwa da Al-hussain, kishi yake ki mai yawa akan Marwa, gani yake ba zai iya rayuwa gida ɗaya da ita ba, yana ganinta a matsayin matar Al-hussain.

Da kanshi ya mata akwatuka, dama wanna niyarsa ce, kuma ya yi akwati na kerema sa'a, haka kuma kayan ɗaki shima ya yi mata masu ƙyau da tsaɗa.

Yana kwance yana nazarin al'amarin dake gab da riskansa a washe gari.

A daidai lokacin Al-hussain ya shigo cikin ɗakin da sauri, jin yarda ya buga ƙofar bayan shigowar, yasa Al-hassan buɗe lumsassun idanunsa ya zuba mai.

"Lafiya?." Ya tambaya jikinsa a sake, Al-hussain ya zauna kusa da shi yana cewa.

"A'a babu lafiya, tashi kaji." Sai ya tashi ya zauna yana kallon ƙanin nasa.

"Yanzu aka kira ni, yaron aiki na ya yi accident, number ne a farkon wayarsa vshi yasa suka kira Ni, yana asibiti cikin mawiyacin hali, zanje yanzu......."

"No.......kai da za ka event na bikinka yanzu, ga kayanka nan ka shirya kawai.......ka ban wayarka, in ya so zan je asibitin a matsayinka nasan babu mai ganewa." Al-hussain ya ɗan ciza leɓansa.

"A'a, ba zan iya zuwa wajen shagali a halin yanzu ba, ko naje ba zan iya walwalaba kasan yadda nake ji a yanzu......kai ya kamata kaje wajen event ɗin." ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Al-hassan ya zaro ido yana mai kallon baka da hankali, tashi ya yi jikinsa duk a sake, ya isa inda Al-hussain ke tsaye yana sauya kaya zuwa ɓakin riga.

"Bangane na je wajen event a matsayin ka ba........kasan abinda kake furtawa kuwa?." juyowa Al-hussain ya yi, suka kalla juna na wasu daƙiƙu.

"Eh Al-hussain kamin wannan alfarman, nasan za ka iya, ka yi duk abinda ya dace, ka je, ka saki ranka ka nuna Ni ne kai, babu wanda zai gane, Ni kuma zance ceton ran abokina..........." Da sauri Al-hassan ya tari numfashinsa.

"Ko me za ka yi ma abokinka nima zan iya......."

"Hmmmmm Ni dai na wuce, kasan an gayyaci mutane da yawa, da ɗin daɗawa Marwa ba zata ji daɗi ba idan banje ba, dan haka kai za ka je, na gama magana." ya kai nan yana kashe mai ido ɗaya, Al-hassan cikin sabon ɓacin rai ya koma inda ya tashi, zama ya yi yana kallon kayan daya siya ma Al-hussain dan wannan event ɗin.

Da sauri ya kalla Al-hussain ganin ya saɓa shegiyar jakkar nan, ya ɗau p-cap yana tafiya a natse, gefansa ya zo ya ɗau wayar Al-hassan, ya aje nasa sannan ya nufa ƙofa.

"Babu inda zani, sai dai a fasa event ɗin." ya faɗa yana fatan Al-hussain ya juyo, sai dai besan ya na yi ba.

"Da gaske nake, babu inda za ni." ya sake faɗa, sautin murmushin Al-hussain ya ji, be juyo ba amma a haka ya ce.

"Za ka je, na sani.......kuma ka yi yadda ya kama....."

"Idan Marwa ta gane ba kai bane ba?."

"Hmmm za ta gane ma, amma ka yi mata bayani, na wuce." Da haka ya fice.

Al-hussain ya rintse ido, kai ya dafe dan besan abinda ya dace ya yi ba, har ga Allah baya son zuwa, dan ganin Marwa ma zai ƙara sa ciwon soyayyar da yake yi ta ƙaru, gaba ɗaya Al-hussain ya ɗauresa da jijiyoyin jikinsa.

Ya zaune a haka har lokaci ya yi, wasu ƴan uwansu maza biyu suka shigo da abokin Al-hussain, sai suka iske yana kwance idanunsa a lumshe ga kayansa a gefe.

"Al-hussey, lokaci na tafiya, tun ɗazu Al-hassan ya ce ka fito wanka, me kake jira ne?." a hankali ya buɗe idanunsa yana zuba musu, lokaci guda ya yi murmushi yana cewa.

"Kuyaƙuri, Al-hassan ya ɓata min rai, wai ba zai samu zuwa wajen taron ba." Dariya Abdullahi ya yi wanda yaron ne ga ƙanin General.

"Hmmmm ai yana fita da sauri-sauri, Abbeey ya gansa, yanzu dai Abbeey ya ɗauke sa a motarsa sun fita."

"To bara na shirya." Da haka jiki a sanyaye ya sanya kayan dama be jima da yin wanka ba.

Bayan ya shirya suka nufa gidan su Marwa, yana zaune a backseat, ƙirjinsa sai bugawa yake, a haka Marwa ta shigo fuskarta a mugun haɗe, sam babu farin ciki.

Take ya lumshe ido ganin irin haɗuwar da ta yi, lokaci guda kuma ƙirjinsa ya dinga tsalle kamar zai fasa ƙirjinsa ya fito.

Ko kallonsa Marwa ba ta yi ba, haka aka ɗauki hanya, dan kuwa cike da take da Al-hussain, tunda biki ya matso ya fita a harkanta, idan ta kirasa ya ce yana busy zai kira, daga haka shike nan sai in ta sake Kira, wannan event ɗin ma dan ƙawaye sun dage ne, shi yasa ta shirya.

Yanzu da take gefansa sai ta ji haushinsa ya ƙara kamata ba, ido kawai ya zuba mata, ya kasa furta komai, ko haƙuri ya ƙi bata.

A haka suka isa *Royal Palace Event Center* Ango ya fara fita, sai abokai da ƙawaye suka ce ya buɗe na Amarya, sannan ya taimaka wajen fitowa.

Ba musu Al-hassan dake ta murmushin da be kai zuci ba, ya isa bakin ƙofar da Marwa take ciki, ya buɗe yana miƙa mata hannunsa.

Marwa ta sauke ajiyan zuciya, ita kanta tasan ya yi ƙyau sosai, ga idanunsa da suka mata kama dana Al-hassan, dan tana iya ganin wani ƙwantaccen farin ruwa ya kwana ciki.

A hankali ta fiddo hannunta na dama, wanda ya ɗau lalle kala biyu ja da ɓaki, ya ƙara haska farin fatarta, a kan na Al-hassan ta ɗaura.

Lokaci guda ta kallesa da sauri, jin wannan sanyi ya ratsa ta, da sauri ta janye hannunta, sai ya saki murmushi yana ƙama nata hannun.

Yarrr suka ji dukkansu, haka dai ta fito idanunta suna kan Al-hassan, wanda ta kasa ganewa, me Al-hassan ke yi a nan? Ina Al-hussain yake?.

Haka dai suka shiga ciki, har wajen zamansu, aka fara shagali amma idanun Marwa na kan Al-hassan, da duk wani motsinsa, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, hannunsa ta kama, shima ya miƙe sannan suka sanar zasu yi magana a keɓe, da haka Ango da Amarya suka fita.

A gefan babban ƙofar shiga suka samu waje suka tsaya inda babu wanda zai gansu, balle ai ta tambayar me suke yi a nan.

Marwa ta kalla Al-hassan.

"Ina yaje? Wai me yasa ɗan uwanka ya sauya ne? Me yasa yanzu baya sona? Jibi yarda na rame duk saboda tunaninsa da tunanin wani kalan rayuwa zanyi a gidansa, gaba ɗaya bana jin daɗin tarayya ta shi a...a... yanzu...." sai kuka ya ƙwace mata, Al-hassan jikinsa ya yi sanyi, amma haka ya taka zuwa gaban ta, hannu yasa ya matso da ita, sai ta rungumesa tana kuka mai sanyi.

Rarrashinta ya hau yi, yana goge mata fuska, kar make-up ɗin ta ya ɓaci, da ƙyar ta dena kuka, bayan ta gama sauraran abin da ya hana zuwan Al-hussain ɗin.

"Kin yarda da Ni?." ta ɗaga mai kai tana murmushi.

"Uhmm."

"To ki saki jikinki, ki dawo da murmushin ki wanda yake ƙara miki ƙyau, ki na da ƙyau sosai." Murmushi ta yi.

"Wallahi Al-hassan ina son...." bakinta ya rufe yana girgiza kai.

"Karki fama min raunin dake zuciyata dan Allah." Baki ta ɗan turo.

"Marwa, idan har ina raye ba zan bari murmushin dake kan fuskarki ya ƙare ba, ba zan bari Al-hussain ya sanyaki damuwa da ƙunci ba, ba zan bari abu mara dadi ya sake ki ba, zan tsaya miki a wani a ko wani irin yanayi........ke ɗin ta dabance a cikin raina." batasan ta sake rungumarsa ba sai da wannan sanyin ya ratsa ɓargon jikinta.

Jikinsu a haɗe, zuciyoyinsu sai zullo suke, da ƙyar suka raba jikinsu, wata ƙawar Marwa ta zo kiransu, hakan yasa suka bi bayanta, ta sanar da shigowar Amarya da Ango.

Shine suka shiga suna murmushi, murmushin dake haskawa da wasu taurari na musamman.

Abinda Marwa da Al-hassan ba su sani ba shine, abinda zai biyo bayan auren Al-hussain da Marwa, dan kuwa hargitsi mai citta, matsala, Chakwakiya yana nan tafe a gidan aurensu, matsala mai rai da lafiya tana nan tafe, hawaye da damuwa za'a yi har sai an gaji, zuciyoyi za su shiga tashin hankali, farin ciki zai ɗauke musu, walwala da annashuwa sunyi sallama da su na tsawon wani lokaci, salo ya sauya, labari ya buɗe sabon sashe a sabon bango cikin sabon littafin dake cikin sabuwar leda bugun farko.................

*Al-hussain*

Shuru ya yi sai saƙe-saƙe yake yi, lokaci guda kuma ya yi murmushi ganin inda yake son zuwa, unguwar suka nufa, a natse ya kalla Abbeey, wanda ya haɗe fuska alamun baya son magana, tun bayan tambaya ɗaya da ya yi ma a ɗazu bayan zai shiga motarsa.

"Al-hassan ina zuwa?." Abinda Abbeey ya faɗa kenan, dan yasa Al-hussain yana da event yau.

Al-hussain cikin murmushi ya ce.

"Fita zanyi Abbeey daga can zan biya wajen event ɗin." Abbeey sai ya tsaya turus, yasan dai Al-hassan baya sanya baƙaƙen kaya irin haka, kuma Al-hussain ne mai yawo da jakka.

Abbeey a ransa ya yi ƙwafa yana cewa. 'Hala guduwa zai yi, bara na ƙuresa.' sai ya ciro wayarsa ya kira number Al-hassan, da mamaki wayar dake ajiyun Al-hussain ya hau ringing, ya ciro yana kallon Abbeey.

"Abbeeyna nine fa." Sai Abbeey ya yi murmushi.

"Biyo Ni to." Ba musu ya rufe wannan motar ya bi bayansa.

Motar Abbeey ya shiga.

"Shigo muje?." Al-hussain ya so yaƙi shiga, amma kar Abbeey ga gane ba shine, dan Al-hassan baya mai musu, shiga ya yi.

"Abbeey ina zamu je?."

"Za ka gani ai." Da haka suna fita suka hau titi.

Al-hussain sai cije-cije yake yi, yana ta mazewa Abbeey kam be ma san yana yi ba, Draving yake hankalinsa kwance.

Al-hussain ya ga sun shiga unguwar da yake son zuwa, hakan yasa ya ji sanyi-sanyi a ransa, tafiya kaɗan suka ƙara Abbeey ya ya parking a bakin wani madaidaici masallaci, sai ya kalla Al-hussain ya ce.

"Al-hassan zan shiga Masallaci, akwai wanda zanyi magana da shi, uhmmmm dama ina ka nufa?." Al-hussain ya shafa fuskarsa sannan ya ce.

"Shago dama zani, akwai abinda nake so."

"Okay na baka 30mnt ka je ka dawo." Murmushi ya yi.

"Okay Abbeey thanks." da haka Abbeey ya fita, shi kuma ya zauna mazaunin Driver.

Take ya figa mota, kuma cikin ƙasa da minti 40 ya dawo bakin masallacin, dama wani ƙaramin abu ne zai tattauna da Senator Tumɓa, Kuma har sun gama.

Yana parking sai ga Abbeey ya fito shi da wani babban mutum, suna magana suna ɗan raha.

Abbeey ya iso kusa da motar.

"Fito ka gaishe da shi, sannan duk abinda ka gani karka yi tambaya, ko ma menene shi kuwa." Ya ɗaga mai kai sannan ba musu Al-hussain ya fito, sannan ya tsugunna kamar yadda Al-hassan ya saba, ya gaida mutum cikin sakin fuska.

"Yauwa ɗan albarka, Al-hussain ne ko Al-hassan?."

"Al-hassan ne, kasan ɗayan yana wajen shagalin bikinsa." cewan Abbeey yana kuma murmushi.

"Kai masha Allah, Allah ya sanya alheri." Da haka Al-hussain ya miƙe yana ta ƙanƙan da kai.

Wata mata ce ta fito daga jikin gidan da ke gefan massalcin, ta iso tana faɗaɗa murmushi, gaishe da Abbeey ta yi, ya amsa, sannan Al-hussain ya gaishe da ita, ta amsa tana ƙare mai kallo.

"Al-hassan ka bi bayanta ina nan ina jiranka." Da mamaki Al-hussain ya kalla Abbeey, sai kuma ya tuna abinda ya ce, hakan yasa ya jinjina kai yana bin bayar matar da ta yi gaba.

Shiga gidan ya yi yana mai lankwasa wiyarsa hagu da dama.

Babban tsakar gida ne wanda ke wadace da mayan ɗakuna, ga mutane ta ko'ina kamar dai gidan da ake shagali.

Ganin mutane suna ta kallonsa yasa ya kalla ƙasa yana taɓe baki.

Wani madaidaicin ɗaki matar ta mai iso, ya shiga yana bin ko ina da kallo, ɗakin kujeru ne a ciki an jerasu ƙwanin ƙyau, da alamun Parlourn baƙi ne.

"Yauwa zauna a nan." Ta faɗa tana murmushi, shima murmushin ya mai da mata, sannan ta fita, ya zauna yana mamakin abinda ya kawo shi nan.

Yana zaune sai yaji motsi a bakin labulan ƙofa, ɗaya ɗaga kai ya kalla, sai mutane sun gudu suna dariya, wasu ta window suke leƙansa, suna yi suna shewa.

"Laaa na ganshi, Maryam zo ki ganshi kyakkyawa ne wallahi."

"Na ganshi."

"Nima haka."

"Ku matsa na ganshi nima." Kalaman da suke ta tashi cikin raɗa kenan, daga window haka ta wajen ƙofa inda ake daga labule daga ƙasa.

Baki ya saki yana ganin ikon Allah, can kuma sa ya ji ana ta faɗa.

"Ni zan kai."

"Ni dai." Duk yara mata ne suke wannan maganar.

Take yara uku mata suka shigo bakinsu ɗauke da sallama.

Ya amsa yana kallonsu da murmushi ganin duk yara ne.

Ɗaya riƙe take da try Babu komai a kai, ɗaya kuma plate wanda aka rufe ne a hannunta, sai ta tsakiyar riƙe da lemu fanta.

A gabansa, ɗaya ta ake tray, ɗayan ta ɗauka plate, sannan ta ƙarshe ta aje Fantar.

Fita suka yi, sai ga wasu maza biyu, ɗaya riƙe da cokali, ɗaya Kuma glass cup, suka je sannan suka fita da gudu suna cewa.

"Na ganshi, nima haka."

Al-hussain ya yi murmushi yana ɗaga kafaɗa, lokacin kuma ya joyo muryar babbar mace tana koran yaran, sai suka tafi da gudu suna shewa.

Matar ta yi sallama, Al-hussain ya amsa yana gyara zaman p-cap ɗinsa.

Idanunsa na kan ƙofa, aka buɗe aka shigo, babbar mace ce a farko, sai wacce ta riƙo ma hannu, be iya ganin wacece ba saboda hijab ɗin da ya rufe mata fuska.

A gefan Al-hussain ta zaunar da Yarinyar sanan ta fita tana murmushi.

Al-hussain ya riƙe baki cike da ganin ikon Allah, ya rasa me suke nufi da hakan.

A hankali yake kallon yarinyar dake takure a gefansa, gashi Abbeey ya ce kar ya yi tambaya, amma yana buƙatar ya tambaya abinda ke faruwa.

Sun ɗau lokaci a haka, kafin a hankali yarinyar ta fito da farare kuma siraran hannunta, ta ja Hijab ɗin baya kaɗan, amma har lokacin fuskarta be fito ba, a hankali muryarta cikin sanyi, yarinta da shaƙwaɓa ta ce.

"Kai Kaɗo ne?."

"Menene Kaɗo.?." ya tambaya.

"Hausa."

"Uhm." Ya faɗa badan shi Hausa bane shi.

Lokaci guda ta fito da fuskarta ta zuba mai ido, Al-hussain kuwa sai da ya ɗan ja baya kaɗan ganin fuskarta.

Murmushi ta yi tana kallonsa daga sama har ƙasa.

Kallonta yake da ido waje, yarinya ce wacce a ƙalla ba za ta wuce 15yrs ba, tana da haske dai dan daga gani Fulani ce, a yanzu dai zai iya cewa tana da ƙyau , sai dai ya ce ta yi kama da Aljanu, dan kuwa ta shafa wani farin hoda mai yawa, sannan ta sa jan jambaki 24h, ga baƙin Jagira da ta yi mai kaurin gaske, sai ƙwalli ta zizara a cikin fararen idanunta, sannan ta yi hawayen masoya, ba ta tsaya a ina nan ba, ta shafa eyes-shadow kala biyu baƙi da green.

"Me kake kallo haka?." Ta faɗa cikin hausarta wacce take haɗe da fullanci.

Dariya ya matse yana mai girgiza kai.

Baki yarinyar ta taɓa sannan ta miƙe tsaye, sai kuma ta zauna.

"Ƙaɗo miƙe tsaye ka yi tafiya ƙaɗan mana." Murmushi ya yi sannan ya miƙe ya taka step one....two.... three.

"Uhmmm ba laifi." ta faɗa tana turo ƙaramin bakinta.

Zama Al-hussain ya yi sannan ya yi tambayar dake cin ransa.

"Wacece ke?."

"Jallo ƴar mai gari, ko kace Sahura ƴar boko."

"Ke bafullata ce ko?."

"Uhm."

"Fulani......in which state.?." Dariya ya ga ta yi tana mai nunasa da hannu.

"Kaf rigar mu nice ƴar bokon da ake ji da ita, wested ɗina..........Adamwa sted." Ta faɗa cike da alfaharin iya boko, Al-hussain ya matse dariyarsa.

"Uhmm sannu ƴar boko."

"Yauwa." Sai kuma suka yi shuru, can ta kallesa ta ce.

"Da cewa na yi kona ganka ba zan amince ba, amma ka min, na amince da auren?."

"Au....me?." Ya faɗa cikin mamaki, baƙi ta sake turowa waje.

"Uhmm Aure mana, ai ka zo ne saboda na ganka idan na ji zan aureka na faɗa gobe a ɗaura mana aure." tai nan babu wasa a fuskarta.

"Bangane ba? Auren me kuwa wai ke ce za ki ganin ko na miki?." Ta ɗaga kai tana tashi daga zaunen.

"Eh mana, yanzu haka mutanen da suke cike da gidan nan amincewata kawai suke jira, ba laifi kana ƙyau kamar Saluluna, kuma kai ɗan boko ne, dan haka na amince." da haka ta yi hanyar fita sai kuma ta juyo tana cewa.

"Gangratulationssss da samun Beauty Jallo a matsayin mata, kana da sa'a sosai, dan haka na amince da kai." sai ta fice.

Al-hussain ya kasa motsi bare magana, dariya ko takaici ya rasa wannan zai yi.

"Yanzu wanna Abbeey ke shirin ɗaurawa Al-hassan aure.........a gobe kuma...... Why ƴar ƙauye?......" ya faɗa yana haɗiyan miyau mai kauri daga maƙoshinsa.

Fitarta da minti biyu, ta ji tsakar gidan ya hau guɗa na mata, ana yi ana shewa tare da cewa "Jallo ta amince, iyye amarya Jallo.............Amarya Hassan da yardan Allah"....................

***************

Shagali ake yi, ana ci ana sha cikin jin daɗi, amarya da kanta ta shiga fili ta yi rawa na hankali, kuma ta burge kowa, haka Al-hassan ya taso yana zuba mata liƙe, ita kuwa cikin soyayyarsa take kallonsa yana waƙa mai bayyana yanayin da zuciyarta ke ciki.

Abu ya kai abu, Amarya da Ango, suka riƙe hannu suna ɗan rawa akan stage, masu ɗauka suna ta video, ana ta musu liƙi.

Sai da mutane suka ragu sannan Najlah ta hau stage, tadinga zuba musu ruwan kuɗi, nan fa mawaƙa suka cafki sunanta suna koɗata.

Wajen zamanta ta koma ta zauna, idanu ta zuba ma wani saurayi dake can gefe, yana magana da Basma, sai wani zare mata ido yake, ita kuma tana magana cikin faɗa-faɗa, ga duk kan alamu dai rigima sukeyi, a natse ta miƙe ta zageye mutane ta isa wajen tana kallon yaron ya kai ma Basma mari, da sauri Basma ta tare tana kai mai lafiyayyen mari.

Murmushi Najlah ta yi, sai ta juya ganin Basma itama A ce ai, kafin ta zauna, wayarta ya hau ringing, tana kalla scren ɗin gabanta ya faɗi ganin sunan dake kai *BLACK SHADOW, OUR TEAM*, compress call ne, za ta iya cewa tunda ta fara aiki kiran daga team be taɓa zuwa wayarta ba.

Jikinta har rawa yake ta yi pecking tana fita daga hall ɗin.

Motarta ta shiga saboda har waje sautin ke tashi.

Zama ta gyara tana sauraren abinda wani ke cewa.

"Ta ɓangarena komai ya yi dai." Da haka wanda suke kira da shugaba ya ce.

"Nima ta ɓangarena komai ya zama daidai, aiki ya koma hannun ki Madam." Lumshe ido ta yi sannan cikin sanyi ta ce.

"Ni kaina ina bincike sosai, kuma ina fatan nan da kwana biyu Senator Tumɓa zai bukaci na fara zuwa aiki, na sha wiya sosai kafin na samu hankalinsa, tashi zanyi dubara zuwa ga Black Dragon.......shi kansa akwai abubuwa da na sani sosai akansa." Sai ta yi shuru.

"Shike nan aiki yana ƙyau, amma a matsayin wa zaki shiga Senator Tumɓa ɗin?." Sai da ta tauna harshenta sannan ta ce.

"Na yi dubaru kala-kala amma be yi tasiri akan sa ba hakan yasa na koma *Ƴar bariki* irin riƙarƙiyar ƴar tasha haka, da haka na samu shiga wajensa."

"Wow, aiki na ƙyau, zan sanar ma Sir Muhammad Babangida Shamaki, da ya kwantar da hankalinasa, komai ya kusa zuwa ƙarshe." da haka suka yi sallama da juna.

Najlah ta Lumshe ido, wannan shine aikinta na farko, gashi ya zo da mugun wuya, dan akwai hatsari babba, fatan Abba ya yi tafiyar da zai yi na wata biyu, da haka za ta sake ta yi aiki sosai, duk da ya bata ikon yin komai, kuma tana yi, saboda ita matar aurece amma yanayi da ƙaddara yasa tana sanya kayan da basu dace ba, duk saboda su kama Black Dragon, Babban shaɗain..............

*********

"Kamar mu dawwama a haka, ina jinka a kusa da ni...... Al-hassan, ba zan ɓoye maka ba, zuciyata ta karkata ne akanka, basan taya zanyi rayuwar aure a gida ɗaya da kai ba, wallahi banjin zan iya, gashi kai ka hanani na yi ma Al-hussain da Abba magana.....kai nake so." ta kai Nana ƙara matsa hannusa cikin tana.

"Nima ina sonki sosai, amma farin cikin Al-hussain ya fi min komai daɗi, idan muka yi haƙuri komai zai wuce, ke ki zauna da mijinki lafiya haka nima na aura wata na zauna lafiya da ita." Da sauri Marwa ta fizge hannunta, ta matsa daga kusa da shi, murmushi ya yi yana cewa.

"A yau bazance wani abu ba, amma daga gobe ana ƙulleki da ɗauri uku shike nan, tsakanina da ke sai gaisuwa." shi kansa maganar ba ta mai daɗi, amma haka ya ɗaure ga faɗa. Marwa ta ja hanci tana jin ba za ta iya zaman aure da Al-hussain ba, ba za ta Al-hassan ta kasa mai magana ba, haka ba za ta iya juran ganin sa da wata mace ba..........

Abinda ba su sani ba shine yanzu za'a fara, yanzu wasan zai soma, yanzu zuciyoyi za su fara kuka da shiga tashin hankali.

✍️ END.

*ANNOUNCEMENT* Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Daga wanna page ɗin Salo ze sauya dan haka sunan book ma dole ya sauya, Book 1,2&3 ya kai ƙarshe cikin ikon Allah.

Da na ce Free book ne, to book 4, kansa sabon labari ne mai cike da ruɗanin da ta fi wannan, hakan yasa littafin zai koma Paid Book, ga duk buƙatar a ci gaba da yin Update da shi, na sabon tafiya mai dogon zango, whatsApp Group ne wanda shiga 300 ne cakal idan an kammala kuma 500.

Irin hargitsi da zafin da ke tafe a Book 4, hatta sabon suna zai samu daban 😳🔥 Ga duk mai son shiga cikin farko-farkon masu karantawa, registration ɗin ₦300 ne kacal. 💳 Account Number: 8126151523 🏦 Bank: Opay 👤 Name: Sakina Abdullahi 📌 Posting: Monday za mu fara insha a Privet group

Complete documents is 500 only PRETTY SK CE 8126151523📲