MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 23

by @maimunabala209

MATAR GIDA 023




SHUUKRAN/022





P23



Muhsin da Ɗalha basu dade da kaiwa asibitin ba aka fitar da Fauziyya har sannan hankalin Hafsah ya ƙasa kwanciya gani take duk laifin ta ne,bayan fitar da Fauziyya ne likita ya kira Ɗalha da Muhsin zuwa ofishinsa,bayan shigarsu ne likita ya mayar da dubansa gare su ya ce ''mun yi nasarar ceto rayuwarta ciwon bai yi tsanani sosai ba,munyi amfani da gastric lavage/endoscopy (na'ura mai dauke da kamera) mun duba daga bakinta, maƙoshinta zuwa ciki babu wani ƙonewa hypo bata yi mata illah ba,laɓen bakin ne ya ƙone dalilin goge leɓen da ta yi lokacin da ta sha hypo,ruwa da madara da aka bata a gida ya taimaka mata sosai wajen rashin ƙonewar baki da makoshi da kuma ciki,abu na gaba kuma duk wani abinci ko abin sha da za'a bata dan Allah ya zama marar zafi,sannan a yawaita bata madara,zamu cigaba da kula da jikin nata insha Allahu babu wata matsala,amma dan Allah a ƙara kula'' godiya Ɗalha da Muhsin suka yiwa likita kafin suka fita daga ɗakin,bayanin da likita ya yi masu ya sa Ɗalha ya ji hankalin ya ɗan kwanta wajen motarsa ya koma inda ya buɗe back sit ya zauna gorar ruwa faro ya dauka ba tsaya ɓata lokaci ba ya buɗe gorar ya kai ruwar baki,sai da ya sha kusan rabi kafin ya cire gorar daga bakinsa,yana mayar da numfashi,bayan fitar Muhsin daga ofishin likita idonsa ne ya sauka kan Hafsah dake zaune bisa ɗaya kujerun dake jere gefin word ɗin zama Muhsin ya yi bisa kujerar dake gefin Hafsah,ya mayar da dubansa gareta yaga har sannan kuka take murya can ƙasa ya ce ''ya isa haka kukan rayuwarta ta fita a haɗari''Muhsin ya yi shiru na wasu na mintina kafin ya ce ''ya aka yi hakan ya faru?me ya sa bata tafi makaranta ba alhali yau laraba?" shiru Hafsah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta yi magana cikin kuka ta ce ''Dadynsu bai kawo mata uniform ba jiya shi yasa na barta a gida''











Washe gari misalin ƙarfe takwas na safe Ɗalha ya kira Ammi ya faɗa mata abinda ya sami Fauziyya,Amirah ce zaune cikin motar Ammi daga gefinta Ammi ce ke ta kwantar mata da hankali cewar babu abinda zai sami Fauziyya insha Allahu zata samu sauki,tun ɗazu da Ɗalha ya kira Ammi ya faɗa mata abinda ya sami Fauziyya gaba ɗaya Ammi ta ruɗe ta fi Amirah burkicewa saida ta shiga bayi kusan uku,da kyar dai ta saita nitsuwarta,Amirah kowa tunda Ammi ta faɗa mata abinda ya faru da Fauziyya ta ƙasa ko da motsi karshe ƴar aikin Ammi ce ta haɗo mata kayanta cikin  jaka har hijab sai da aka dauko aka bata kafin ta sa hannu ta karɓa ta sa,a rikice Ammi ta shiga asibitin bata samu nitsuwa ba saida ta haɗu da likita ya yi mata bayanin jikin Fauziyya kamar yadda ya yiwa Ɗalha da Muhsin ɗakin da aka kwantar da Fauziyya Ammi ta shigo taga Amirah cikin ɗakin ta yi tagumi ta ƙorawa Fauziyya ido gani ta yi Fauziyya ta ɗan rami amma ba can ba kuma ta ɗan yi baƙi hasken ta ya ragu ba kamar da ba,duka yaran Amirah sun dauki hasken ta da dogon sunanta har mazan duk sun dauki haskenta,amma suma tsananin kama da mahaifinsu Ɗalha kakkayawan matashi ne yana da manyan idanuwa da hanci daidai misali,sai madaidaici bakinsa dogo ne sosai mai faffaɗan kirji amma bashi da hasken fata baƙi ne sitif,ita kuma Amirah fara ce ƙall amma Unaisa ta fita haske da diri Amirah irin matan nan ne masu matsaikaicin jiki tana da mazaunai daidai gwargwarɗo amma daga kirginta kamar yarinyar ƴar shekaru sha biyu da bata daɗe da fara al'ada ba,tana da tsawo amma ba can ba,Allah ya wadata ta da manyan idanuwa da babban leɓe,sai hancinta daidai fuskarta,tana da fata me laushi kamar na jarirai,masha Allah ba za'a kira Amirah mammuna ba kuma ba za'a kirata da kyakkyawa ba,ba kamar Unaisa ba da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da kyawun da Allah ya yi mata doguwar mace ce me kyawun fuska,Unaisa nada ƙaramin lips dogon hanci,da manyan idanuwa,Allah ya wadata da manyan mazaunai ga kirginta cike fam da dukiyar Fulani,ta fi Amirah haske nisa ba kusa ba gata da dogon suma baƙi kirin,kasancewar Unaisa jini biyu ce Fulani da shuwa mahaifinta bafulatanin Gombe ne mahaifiyarta kuma shuwa ƴar kasar niger












Murmushi Ammi ta yi ganin yadda Amirah ke kallon Fauziyya har Ammi ta zauna Amirah bata sani ba,murya can ƙasa Ammi ta ce ''kwantar da hankalin ki zata warƙe insha Allah na yi magana likita ya tabbatar min bata cikin haɗari'' numfasawa Amirah ta yi kafin ta ce ''Allah ya sa'' Ammi ta amsa da Ameen Amirah da Ammi na zaune cikin ɗakin Hafsah ta shigo ɗakin riƙe da basket ɗin abinci bakinta dauke da sallama ta shigo ɗakin duk suka amsa mata bayan ta ajiye basket ɗin hannuta ta tako har inda Ammi ke zaune ta gaishi Ammi ta amsa mata cikin sakin fuska,daga haka ta waigo inda Amirah ke zaune sun gaisa ɗakin ya yi shiru na wasu ƴan mintina suna nan zaune Ɗalha da Muhsin suka shigo ɗakin,bayan sun gaishi Ammi ne Amirah ta gaishi su duk suka amsa mata,Ɗalha dai sai bin Amirah yake da ido kamar maye,can dai ya mayar da dubansa ga Ammi ya ce ''Ammi in babu damuwa zan kai ku gida ku yi wanka ku ci abinci'' kamar Ammi baza ta yi magana ba sai kuma ta ce ''to'' Amirah da Ammi sun koma gida sun yi wanka sun ci abinci da Ɗalha ya siyu masu,lokacin karfe biyar ta wuce,Amirah ta yi mamakin ganin gidan tsaf tana son ganin yaranta amma ta ƙasa magana,bayan sun gama ne Ɗalha ya mayar da su asibiti daga nan ya wuce ya kwaso yaran daga makaranta,duk ya kaisu asibiti sosai yaran sun yi murna sosai ganin Mumy su,ita dai sai binsu kawai take da ido ta yi mamaki sosai ganin su tsaf har ta fara tunanin ko dai tun tafiyar ta yaran ke gidan Muhsin,a wannan rana Ɗalha ya kwashe yaran gaba ɗaya daga gidan Muhsin ya maida su gida inda Ammi zata cigaba da zama da su Amirah kuma zata zauna asibiti tare da Fauziyya,sosai yaran ke samun kulawa a wajen Ammi,Allah ya taimake Ammi suna mugun tsoronta wannan dalilin yasa da ta ce su yi kaza za su yi da ta ce su bari zasu bari kwanan Fauziyya biyar a asibiti aka sallame ta sosai ta samu lafiya,bikin Ɗalha da Unaisa saura kwanaki uku hakan yasa Ammi komawa Kano a ranar saboda shirye shiryen bikin harda ba wani program za'a ba iyaka buɗan kai kawai za'a yi,Ammi ta ce Amirah ta yi zamanta cikin yaranta ta kuma sake yiwa Amirah nasiha sosai kafin ta tafi,a ranar da aka sallame Fauziyya Rumaisa ta kawo masu ziyara tun bayan azahar take gidan,sosai ta taimakawa Amirah da gyaran gida da aikin abinci ita ce ta yi masu girki,ta zuba masu suna cikin cin abinci ne Rumaisa ta ce ''ya ƙi ka ji maganin na san kin fara amfani da shi'' taɓe bakin Amirah ta yi saboda gaba ɗaya ta manta batun wani magani ta lafiyar ƴarta take tsakanin ta da Ɗalha kowa daga gaisuwa sai in an rubuta masu magani ta dauki hoton sunan maganin ta tura masa ta whatsapp da ya gani zai siya masu,tun da ta dawo ta lura kamar tsoronta ma yake,ita dai ko da wasa bata yarda ta sakar masa fuska ba,saboda bata son surutun Rumaisa ta ce ''eh maganin na da kyau sosai'' Rumaisa ta ce ''aiy na faɗa maki,amma  fa wannan karon kuɗi za ki fitar ki siya da kanki dan ni dai bazan sake siya maki ba'' Amirah ta ce ''kar ki damu zan siya'' Amirah ta yi saurin kawar da zancen yadda ta ce ''wai ni kam an yiwa Yasmin baiko ne?" Rumaisa ta ajiye kofin lemo dake hannunta ta dauki cokali tana juya farar shinkafa da miya da ke gabansu miyar ta ji namar rago da kayan ciki ta ce ''wa wannan ita fa ko dariya bata cika yi ba bata ma da saurayi kullum za ki ganta kwance cikin ɗakin daga karatun boko sai kur'ani kullum haka take'' Amirah ta yi murmushi ta ce ''Allah ya kawo na gari'' Rumaisa ta amsa da ''Ameen'' Rumaisa ba ita ta bar gidan ba saida aka yi sallar la'asar








SHUUKRAN