MATAR GIDA PAGE 24
MATAR GIDA 024
SHUUKRAN/022
P24
Karfe takwas na safiyar Alhamis Ɗalha ne tsaye kofar gidan su Unaisa yau zata yi walima hakan yasa mutane nata kaiwa da komowa a kofar gidan ƴan uwa da abokan arziƙi duk kowa ya na busy,Ɗalha na tsaye ya jingina jikinsa da motarsa yana ta gaisawa da mutane can ya fidda wayarsa ya yi kira layin Unaisa a karo na huɗu wayar ta yi ringing har ta ƙatse ba'a ɗaga ba yana shirin sake kiranta ya ganta ta fito daga gida,sanye cikin wata lapaya kalar madara an yi mata ado da koriyar fulawa kana ganinta kaga amarya har wani haske ta ƙara ta yi kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu,tana tafiya ilahirin jikinta na motsawa wanda bai santa ba zai yi tunanin da gangan take juya jiki alhali halittar ta ce hakan,ƙamshin humra haɗe da kabbasa ke tashi daga jikin Unaisa gaba ɗaya wajen ya dauki khamsinta,mutuwar tsaye Ɗalha ya yi ya kafeta da ido har ta ƙaraso inda yake tsaye ya ƙasa daina kallon ta,murmushi ta sakar masa bakinta dauke da sallama sai a sannan ne ya iya janye idonsa daga fuskarta,murya can ƙasa ya amsa mata sallama yadda ita kaɗai zata ji,buɗe mata kofar ya yi ya ce ''bismillah'' wani irin kallo ta yi masa kafin ta ce ''ina kuma za ka kai ni'' wani sassanyar murmushi ya yi kafin ya ce ''sace ki zan yi'' babu musu Unaisa ta shiga motar,Ɗalha ya zaga gefin driver ya shiga ya zauna amma bai rufa kofar ba,sai a sannan ne Unaisa ta gaishi shi amsa mata gaisuwar ya yi ya mayar da dubansa gareta ya ce ''kin yi kyau amarya'' Unaisa ta yi fari da ido ta ce ''ni ɗin mai kyau ce daman'' murmushi Ɗalha ya yi yana ƙara jinjina girman kai irin na Unaisa duk sanda ya ce mata ta yi kyau ko ya ce tana da kyau amsar da take basa kenan tana ji da kyawunta sosai,fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''to na ji mai kyau'' Unaisa na danna wayarta bata ce masa komai ba sai murmushi mai sauti da ta yi,ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke yana tunanin yadda zai faɗa mata cewar babu maganar tafiya honeymoon a ƙasar Poland bayan ya yiwa Ammi hirar tafiyar tasu ne ta ce saidai ya tafi da Dukansu har Amirah su bar yara a Nigeria saboda tunda ya aure Amirah ko Abuja bai kaita honeymoon ba Ɗalha ya yiwa Ammi bayanin cewar lokacin da ya aure Amirah bashi da karfin kaita honeymoon ko ina Ammi ta ce sam bata san zancen ba ko ya shirya a yi tafiya har Amirah ko a fasa tafiyar baki ɗaya,Ɗalha bashi da karfin tafiya da dukkan su biyu hakan yasa ya yanke hukunci fasa tafiyar gaba ɗaya
Gyara zama ya yi kafin ya fara magana inda ya ce ''daman na zo ne kan maganar tafiyarmu Poland'' har sannan idon Unaisa na kan waya ta ce ''uhmm ina jin ka'' Ɗalha ya ce ''tafiyar baza ta yiwu ba saboda matsalar rashin kuɗi a hannu na'' a sanyaye Unaisa ta ɗago ta zuba masa manyan idanuwanta kamar a mafarki take jin maganar ta sa me yake nufi da hakan ita da ta gama faɗawa ƙawaye zata tafi honeymoon ƙasar Poland har outfit ɗinda zata yi amfani da su a can ta siya ta gama shirya komai kawai jiran ranar tafiya take,tana son yin magana amma ta ƙasa furta ko da kalma ɗaya ce nan take ta ji wani zufa na kerto mata harda A C dake cikin motar zufa take,ganin yanayin da ta shiga ya sa Ɗalha daura da ''zan tura maki 1.5m daman na ajiye shi ne da niyyar muyi amfani da shi a can ƙasar amma yanzu da tafiyar bata yiwu ba sai ki yi amfaninki da su'' shiru Ɗalha ya yi yana nazartar yanayin ta jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya daura da ''tabbas na so tafiyar nan amma Allah bai nufa ba,dan girman Allah ki yi hakuri'' cikin yanayi na rashin jin dadi Unaisa ta ce ''bayan na riga na faɗama ƙawaye na zan tafi Poland yanzu sai kace babu tafiyar aiy sai suyi tunanin karya na yi masu'' Ɗalha ya gyara zama kafin ya ce ''ok duk wacce ta ce karya ki' ke ki haɗa ni da ita zan yi masu bayani'' lokaci guda Unaisa ta ɓata fuska ta ce ''ina ganin ka ƙara min 500k kan 1.5 in ya so sai na haɗa masu ƴar karama walima bayan auren mu'' Ɗalha ya ɗage kafaɗu tare da faɗin ''oky babu matsala duk yadda ki ke so haka za'a yi'' Ɗalha bai bar kofar gidansu Unaisa ba saida ya tura mata 2m kamar yadda ta buƙata
Bayan barin Ɗalha gidan su Unaisa bai tsaya ko ina ba sai ofishinsa yadda ya dauki hutun sati biyu saboda aurensa da za'a daura gobe,daga ofis gida ya wuce inda ya tarar da Amirah zaune cikin ɗakin su Sudais tana linkin kayansu da ta kwashi a injin wankin kaya,kallo ɗaya Amirah ta yi masa ta dauke kai tun dawowarta daga asibiti sai yanzu ta haɗu daga ita sai shi a waje ɗaya jiya bayan ya dawo gida tayi masa sannu da zuwa ta ajiye masa abinci a daining daga nan bai sake ganinta ba,bayan ya gama cin abinci ya shiga ɗakinta yaga tuni ta yi barci da Fauziyya a gefenta,bata yarda ta kalle fuskarsa ba ta tashi ta bar linkin kayan ta yi masa sannu da dawowa bayan ya amsa ne Amirah ta nufi hanyar fita daga ɗakin, fita take son yi daga ɗakin Ɗalha dake zaune kan kujera one siter ya yi saurin tashi tsaye tare da shiga gabanta ya kafeta da ido Amirah bata yarda ta haɗa ido da shi ba kawai ta raɓa ta gefensa da niyya fita daga ɗakin Ɗalha ya yi saurin riƙe mata hannu tare da janyu ta jikinsa wani irin runguma ya yi mata kamar za'a kwace masa ita Amirah ta shiga cakaniyar kwace kanta daga riƙon da ya yi mata Ɗalha ya kai bakinsa daidai kunnenta kamar mai raɗa ya ce ''pupsik'' cak Amirah ta tsaya ta daina kokarin kwato kanta da take yi pupsik yana nufin cutie a yaren Russai,Ɗalha ya rintsa ido yana jin wani irin nitsuwa yana sauko masa he just feel safe da kyar Amirah ta saita kanta ta tattara sauran karfin da ya rage mata ta ce ''na bar miya a wuta zan je na duba'' ba dan Ɗalha ya so ba ya raba ta da jikinsa a hankali ya ce ''ok ki dawo pls in kin duba'' murya can ƙasa Amirah ta ce ''ok'' daga haka ta fita daga ɗakin bata tsaya ko ina ba sai kitchen ɗinta dake bangarenta ɗinta,kamar yadda Rumaisa ta faɗa mata ta kwashi duk wani abun amfanin ta a babban kitchen ta maida su kitchen ɗin bangarenta,bayan ta duba miyar taga ya nuna miyar kuka ce,kashi gas ɗin ta yi tare da sakayi miyar daga haka ta bar kitchen zuwa ɗakinta bayan ta ji muryar Fauziyya tana kuka da alama bata daɗe da tashi daga barci ba, daukar Fauziyya ta yi ya kai ta bathroom ta yi fitsari tana shirin barin ɗakin Ɗalha ya shigo Fauziyya na ganinsa ta sake sabon kuka Ɗalha ya miƙawa Amirah hannu ya ce ta kawo Fauziyya,barin ɗakin Amirah ta yi zuwa kitchen ta haɗawa Fauziyya madara da ruwan sanyi,cike da hikima Ɗalha ya rinƙa bata madarar a baki saboda har yanzu bakinta bai gama warƙewa ba lips ɗinta sun yi ja sosai a hankali Ɗalha ya rinƙa bata madarar a baki har ta shanye,bayan ta gama sha ne Ɗalha na riƙe da Fauziyya Amirah na zaune bakin gado Ɗalha ya mayar da dubansa gareta ya fara magana cikin kwantar da murya ya ce ''ki yi hakuri kan abinda ya faru ban san abinda ya shiga kaina har na rubuta maki saki ba dan Allah ki yi hakuri ki yafe min'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya cigaba da magana murya can ƙasa ya ce ''ina son na gode maki kan kula da yarana da gidana da ni kaina dan Allah ki manta komai mu cigaba da zaman mu kamar ɗa can na yi maki alƙawarin hakan bazai sake faruwa ba''ita dai Amirah ta yi shiru tana sauraronsa kawai take Ɗalha ya yi shiru na wasu ƴan mintina can ya ce ''in Allah ya kaimu gobe za'a daura aurena da Unaisa a nan Kaduna za'a daura auren daga wajen daurin aure zamu wuce can Kano,can amarya zata zauna na tsawon sati ɗaya daga nan zamu dawo nan Kaduna'' tunda Ɗalha ya fara magana kan aurensa da za'a daura gobe Amirah ta shiga wani irin yanayi ji ta yi jikinta ya yi mata wani irin sanyi tun daga ƙwakwalwarta har tafin kafa take jin sanyi ga wani irin bugu da zuciyarta ke yi cike da hikima ta yi ƙokarin saita nitsuwarta ta shiga karanto duk wata addu'a da tazo bakinta tana cikin wannan yanayi ta ji Ɗalha ya ce ''ina so zan canza furniture ɗin babban parlour da na bangaren ki gaba ɗaya,amma ina tunanin a maida tsofin can Kano tunda dai gaba ɗaya waɗannan basu fi shekara biyu ba,in yaso waɗan can na Kano sai ki kyautar ko ya ki ki ke gani'' cike da juriya da ɓoye damuwa Amirah ta ce ''hakan ya yi nagode Allah ya saka da alkairi ya ƙara buɗi'' Ɗalha ya ce ''Ameen..ba yanzu za'a canza furniture ɗin ba sai Sudais sun yi hutun makaranta tunda jarabawar tasu saura sati biyu bani son a ɓude bangarenki ba ki kusa ne shi yasa'' Ɗalha ya yi shiru yana nazartar yanayin da Amirah ke ciki tashin hankali ne kwance ƙarara a fuskarta amma tana ta ɓoyewa bata son ya gane wani irin tausayinta ya ji ya ziyarce sa lokaci guda,cikin kwantar da murya ya ce ''cikin bayanan da na yi maki in akwai wanda bai maki ba za ki iya faɗa sai in yi yadda kike so'' wani irin murmushi Amirah ta yi cikin zuciyarta ta ce ''abinda nake so ka fasa auren kawai amma na sani hakan ba mai yiwuwa bane a zahiri kuma ta ce ''babu komai Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar arziƙi ce'' sosai Ɗalha ya ji daɗin addu'ar da Amirah ta yi masa a hankali ya shimfiɗa Fauziyya da ta fara barci a hannusa ya shimfiɗa ta kan gado kafin ya koma ya zauna a inda ya tasahi wayarsa ya fidda daga aljihu ya yiwa Amirah transfer ɗin 2.5m bayan ya mayar da wayar cikin aljihu ya ce ''na tura maki saƙo ki yi amfani da su kafin na dawo ƙila zaku bukaci wani abu'' nan ma Amirah ta yi masa godiya shiru ya yi yana ƙare mata kallo kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ce ''ki kwantar da hankali ki bazan ci amanarki ba na kuma yi maki alkari zan yi adalci a tsakaninku'' kan Amirah ƙasa ta ce ''Allah ya baka iko'' Ɗalha ya ce ''Ameen''
SHUUKRAN