CHAPTER 10
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA GOMA
“An samu rabo ba labari?”
Cak! kasaƙe, Sufyan ya tsaya ya kalli Farida, sannan ya kalli Inno.
Inno ta ci gaba da faɗin, “Sufuyanu, ai ko Farida kunya ta hana ta faɗa. Kai ya ci ka zo ka sanar mini a fara yi muku tanadi.”
Cikin yanayin rashin fahimta Sufyan ya ce, “Inno, wai wani rabo kuma? Da wa aka samu?”
Inno ta ɗaga hannu tana yi masa dakuwa ta ce, “Karɓi nan gidanku, Sufuyanu. Munafikan banza kawai! Kun yi abu kun zo kunata limi-limi da idanuwa irin na kadangaru. Kauce mini a hanya in shige.”
Ta ƙarasa maganar tana ficewa.
Farida na tsaye ta rasa abin cewa. Sufyan na yi mata kallon tuhuma, ya ɗaga yatsansa yana faɗin, “Wato ke, a naki barikancin har kin samu damar yin cikin da za ki danganta ni da shi?”
Ya yi wani guntun murmushin mugunta kafin ya ci gaba da faɗin, “Ashe dama can neman mafaka kike? Shiyasa kika aminta da auren ki samu damar jefa mini jakar tsabar da kika kwaso. Kin je can an yi miki ciki, kina so ki danganta ni da ɗan wani shege can a titi? To wallahi, a hir ɗinki, gwanda tun wuri ki san mafita, ki zubar da wannan cikin da ke jikinki. Don ba zan taɓa haɗa jiki da ke ba, bare ki yi tunanin haihuwa da ni. In kuma kika gagara yin hakan, ki shirya tonuwar asirinki.”
Ya ƙarasa maganar yana bangajeta ya wuce.
Cikin zafin rai Farida ta ce, “Kana sanin furucin da yake fitowa a bakinka fa, Ba ni da cikin kowa, kuma in sha Allah ba zan gani ba. Ni ba sa’arka ba ce, a girme dai ka san na girmeka.”
Har zai shiga ɗaki ya juyo yana dariya, “Oh, har yanzu kina tuna batun girman ne? Ai ya ci ki watsar gefe, tunda yanzu ƙarƙashina kike. Zancen ciki kuma, ni dai na faɗa miki, dabara ta rage ga mai shiga rijiya.”
Ya ƙarasa maganar yana juyawa ya shige ɗakin.
“Allah ya tsareni daga rayuwar zina irin taka,” Farida ta fada, ita ma tana shigewa nata dakin.
Sufyan na shiga ya dauko handout dinsa, domin a lokacin da zai je school ne ya tuna cewa ya manta da shi a gida. Lecturer din kuma ba zai bar shi ya zauna ba idan babu handout din. Hakan yasa ya dauko shi, sannan ya fita daga gidan.
Farida na shiga daki, ta dauko kayanta ta sanya, sannan ta zumbula hijabinta da nikaf kamar kullum. Ta fita, ta shiga motarta, ta dauki hanya. A zuciyarta kuwa, babu sake-sake, babu wani abu da take yi, domin goma da ashirin sun taru mata waje guda. Sufyan yana kallonta a matsayin mazinaciya, ga Inno kuma ta dauko mata jarfar ciki. Ta rasa inda za ta sa ranta.
Hakan yasa, tana cikin tukin, ta dakata ta yi parking a gefen titi. Azima ta kira, ta fara ba ta labarin duk abin da yake faruwa.
Azima ta numfasa, tana jinjina lamarin kafin ta ce, “Farida, na jima da fada miki ki daina damuwa da duk wasu batutuwa da kika san cewa ba gaskiya ba ne. Shi da ya zaba wa kansa wannan rayuwar, ai Allah yana gani, kuma shi zai biya miki hakkinki. Wai ni, tsaya ma! Kar ki ce mini duk tsawon zamanku tare, ba ku taba kasancewa tare ba?”
Farida ta ce, “Eh. To, ta yaya ma za a fara hakan? Allah ya sawake ni, ba zan ma iya ba.”
Azima ta ce, “Ba za ki iya ba kamar ya Farida? Ina ilimin naki? Idan shi ba zai cutu ba, tunda yana kawar da muradansa, ai ke za ki iya cutuwa.”
“Cutuwa a kan me? Azima, na rantse miki da Allah, da dai in ba Sufyan kaina, gwanda na mutu cikin bukata. Bare ma ni zan iya rayuwa haka, kuma babu abin da zai dameni,” Farida ta fada.
Murmushi Azima ta yi, sannan ta ce, “Ni fa na fada miki ki bar kallon Sufyan a matsayin kani. Yanzu ya zarce nan. Sannan ke fa mace ce. Dama dai babu auren akanki ne, shi zai iya zame miki katangar da ba za ki cutu ba, amma yanzu kam duk abin da za ki fada mini, sai dai in ji kawai.”
Farida ta gyara zamanta tana cewa, “Azima kenan, ki yarda da ni fa. Ganin Sufyan babu wani abin da zai same ni, har yanzu a matsayin yaro nake kallonsa, wanda na raina a bayana. Na ci fitsarinsa da kashinsa, to wane irin feeling zan ji a kansa? Abin mamaki ai babu wannan ranar.”
Azima ta yi dariya ta ce, “Allah, ni kallonki kawai nake. Duk zancenki sai wata rana mun ganki da makeken ciki, sai in ƙara tuna miki zancen yaro’.”
Dariya ita ma Farida ta yi, sannan ta ce, “Ai ko babu wannan ranar.” Ta karasa tana kallon agogo.
“Kin ga, bari in ƙarasa school, lokaci ya kusa.”
Da haka suka yi sallama, Farida ta ci gaba da driving.
A gefe guda kuma, Inno na fita daga gidansu Farida, ta dunga bi gida-gida tana shelar cewa, “Ai Faridatu da Sufuyanu sun samu juna biyu!”
Sai da ta bi gidajen dangin nan kaf, wasu ma a bakin layi take haduwa da su, ta tsaya ta sanar da su, sannan ta ci gaba da tafiyarta. A ƙarshe, a gidan Kawu Hamza ta yada zango, inda ta ɗauki Goggo ta raka ta kasuwa.
Suna cikin tafiya, Inno ta ce, “Hansai, kin san fa da sanyin safiya ake kama fara. Kamar gobe ne za ki ji wata tara ta yi, fa. Gwanda tun yanzu a gaggauta a yi abin da ya kamata.”
Goggo Hansai ta gyara gyalenta ta ce, “Ai kuwa, Inno. Kar a tsaya ana zaune ba shiri, hidima ta zo. Kuma da yake kin san halin Kulu, ba tsayawa za ta yi ta yi wa Faridatu abin da ya kamata ba.”
Inno ta taɓe baki tana tauna goro, ta ce, “Yoo, daga uwarta ne Jummai ta yo gadon shiririta. Ina gaya miki, hatta cikin nan ma fa da taimakona aka samu damar yinsa. Sai da nata faman zuwa gidan Faridatu ina koya mata rayuwar aure, wanka, ado da tarairayan namiji. Duk Kulu bata koya mata ba. Ganin sakacinta na ƙoƙarin tada mana da husuma, ai tuni na wanke zani na bazama, sai da na kwantar da ita komai ya yi dai-dai. Shi ya sa da zarar ta shiga watan haihuwa gidan zan koma.”
Goggo Hansai ta ce, “Aiko dai kin taimaka, kin yi jihadi, tunda gashi har da rabo.”
Inno ta ce, “Wallahi kuwa.”
Daidai lokacin da suka isa wajen kayan yaji, suka tsaya suka sayi komai wadatacce da zai ishe su yin yajin daddawa.
Goggo Hansai ta ce, “Kin ga sai in taimake ki aikin, mu yi dakan hannu. Kin san ya fi daɗi.”
Inno ta ce, “Kwarai kuwa, ai shi za mu yi. Yanzu mu je a siyo mata baho na yi wa jariri wanka ko?”
Goggo Hansai ta gyada kai tana cewa, “To, amma kar ki manta da sayen dawa. Kin san in an yi haihuwar nan, tuwon dawa na taimaka wa mai jego matuƙa.”
Da haka suka ci gaba da tafiya. Suka je wajen kayan robobi, suka sayi baho, sannan suka je aka siya dawa da kuka. Ci gaba da zaga kasuwar sukai suna siyayya hani’an, har kayan gwanjo na jarirai sai da suka je inda aka bude dila suka fara zaɓa.
Farida kuwa ta fito daga office kenan, za ta ɗauki wani abu cikin motarta. Tana buɗe ƙofar motar ta ji muryar wasu ɗalibai mata biyu a bayanta suna hira.
“Samira, ni dai in Allah ya ba ni jiki irin na Miss Farida ina budurwa, wallahi sai na haƙura da aure, in koma zaman gida kawai. Wai ina laifin ma ace a ga matar aure ce, amma jiɓeta zabbegiya! Wai kuma a hakan take budurwa?”
Samira ta kyalkyale da dariya ta ce, “To ke Hanifa, ta ina ma wani namiji zai yi sha’awar aurenta? Wannan ai sai ta kashe shi. Ai yanzu maza sun fi gane ’yan daidaitattun mata da kuma sirara, ba container guda ba.”
“Wallahi kuwa!” Hanifa ta amsa tana dariya.
Samira ta sake kallon Farida daga nesa, ta ce, “Kuma fa wannan ma ai sai a zaci ta haife mu. Kalli yadda ta tsufa, caɓ!”
Dukansu suka fashe da dariya.
Farida kuwa ta tsaya cak.
Maganganun nasu sun ratsa kunnenta kamar an zuba mata ruwan zafi. Ta lumshe ido na ƴan daƙiƙu, tana ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata zuciya. Ta san ba yau aka fara mata wannan kalaman ba, amma duk lokacin da aka faɗa, ciwon yana dawo mata sabo ne.
A hankali ta juya ta kalle su.
Nan take dariyar da su ta yanke.
Hanifa da Samira suka haɗa ido da ita. Jikinsu ya yi sanyi, domin a lokacin ne suka fahimci cewa duk abin da suka faɗa, Farida ta ji.
Farida ba ta ce musu komai ba. Sai dai ta ɗan girgiza kai, ta ɗauki abin da za ta ɗauka daga motar, sannan ta fito daga ciki ta rufe ƙofar.
cikin sauri tana tafiya wasu maza suka zo wucewa ta gefenta, kafin ta ankara ji ta yi an bigeta har jakar hannunta ta faɗi. Durƙusawa ta yi za ta ɗauka, shi ma wanda ya bigeta ya durƙusa, sai suka gware da goshin juna kafin ta ƙarasa dagowa sai jin hannunsa ta yi yana shafa mata ƙwanƙwaso. Suna haɗa ido ya ɗaga mata gira yana sakin murmushi ta gefe.
Cikin fushi da takaici, Farida ta ɗaga hannu ta kai masa kakkauran mari a kumatu….