Chapter 17
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 17
Sayyada barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
Bai taɓa jin ya aika abu kuma ya dame shi ba, irin abin da ya faru yanzu, yaji bai kyauta ba, me yasa bai saurareta ba ya tare ta da baƙaƙen maganganu, jiki a sanyaye ya shigo tare da rufe ƙofa ya zauna kan carpet ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa tana yi masa zafi da nadama. Ya kurawa wallet ɗin idanu yana jujjuya shi, kenan tana nufin ranar da ya yi treating ƙafarta a ranar ya yada shi, kenan a restaurant ya jefar!
Ya sauke ajiyar zuciya, ko da yake Oganniyar su ce ta shafa mata bakin fenti a idanunsa, da kuma ma'aikaciyar restaurant da ta kawo masa kanta. Ya buɗe wallet ɗin yaga kuɗaɗen sa suna nan a ciki ya fiddo su, ya kirki bata taɓa ko ƙwandala ba, ya jinjina kai, ya duba ID card nasa ya kurawa masa idanu, ya fahimci a inda ta san cikakken sunan sa, zai san yadda zai yi ya yi magana da ita....
Bilqees tana barin hotel ɗin cikin ɓacin rai ta iso restaurant, ta zagaya ta baya ta samu ƙarƙashin fonfo, ta kunnta ruwa yana sauƙowa ta saka ƙafafuwan ruwa yana zubowa kansu, a hankali hawaye yabi kuncinta, ta fuskanci matsaloli da dama waɗanda suka tsaya mata cikin zuciyarsa amma abin da ya faru yau ya fi komai taɓa zuciyar ta, me yasa zai jefeta da munanan kalamai? me ta yi masa? Ta yi wa kanta alkawarin ba za ta sake zuwa inda yake ba..
Ta jima a zaune, sannan ta tashi ta shigo ciki. Ƙarashe abubuwan da ta fara aikinsu kuma ta bari saboda abinci dare ta yi, tana ta zancen zuci ita kaɗai..
"Bilqees"
Majada ta kira sunanta, ta ɗago tare da cewa
"Majada"
"Ina ki ka tafi ne? Tun ɗazu nake duba ki"
"Me zan yi miki?"
"Babu kowai ina son sanin daga inda kike"
Ta zubawa Majada idanu, tana karantar yanayinta, ta tuna ta ganta a teburin wannan mutumin likita, tana yi masa magana, alamu ya nuna cikin ɓacin rai yake mai da mata, ko dai rashin kamun kai ta yi masa har yake ganin ita ma haka take...
"Kina kallona fah?"
"Na fita sayan abu ne?"
"Ok me kika sayo mana?"
"Majada what a lot of questions is that?!"
"Shi kenan nayi waje"
Bilqees ta sauke numfashi, jikinta ya bata tabbas akwai abin da Majada ke ɓoye mata....
*********************************
Wasa suke yi har da guje² duk sun ɓata jikinsu da kura, sai da suka gaji don kansu suka zauna suna haki, ɗago wa da su kayi idanunsu suka sauƙa kan BOBO da biscuit da uncle ya kawo, suka mik'e tsaya suna dariya. Ya zauna tare da cewa
"Good morning children"
"Morning uncle"
Suka haɗa baki wajen faɗin hakan, ya ce
"Yau na sayo muku BOBO, ku shiga layi na raba muku"
Da sauri suka shiga layi ya raba musu nan take suka buɗe suna sha. Ta iso tare da yi musu sallama suka amsa, Dr Waahab ya ɗago ya kalleta yaga ita ma shi take kallo, ya sauke numfashi tare da nuna mata wajen zama, ta zauna sai dai jikinta duk a sanyaye, ya miƙa mata BOBO da biscuit kamar ba zata karɓa kuma a amsa..
"Sannu da isowa"
Ya faɗa, ta amsa da
"Thanks"
"Ganin yau duk ta sauya yasa ya maida hankalinsa kan yaran, yana basu labari, idanunta har wannan lokacin yana kan sa, da ya ɗago suke haɗa idanu, shi yake janyewa ta rabawa yaran Alawa da biscuit kamar yadda take yi, ta mik'e tayi musu sai an jima, amma Dr Waahab ya tsaida ta ta hanyar kiran sunanta
"Angel"
Ta tsaya na tare da ta juyo ba, ya sallami yara ya ce su tafi, suka tafi, a hankali ya ce da ita
"Ki zauna"
Ta juyo tana kallon sa, sai da ya sake maimaita wa sannan ta zauna, shiru ya ratsa, ya ɗan sauke numfashi tare da cewa
"Me yake damunki yau kin yi sanyi da yawa?"
"Ba komai"
"Ban yarda ba Angel"
"Comment tu t'appelles?"
What's you name? Ta tambaye shi menene sunan shi, ya ɗan sauke numfashi tare da ɗan yin murmushi ya ce
"Je m'appelle Abdulwahab"
Sunana Abdulwahab, ya faɗa mata ta ɗan saki jikinta a hankali ta sake cewa
"Enchant'e!
Nice to meet you, nayi farin cikin haɗuwa da kai. Yaji daɗin karɓansa da ta yi, ko ba komai ya samu abokiya a Ghana, ta juya harshe zuwa harshen Hausa ta ce
"Zan tafi ina da abin yi"
"Ok ba damuwa, sai gobe kenan"
"Eh"
Ta faɗa ta mik'e tana tafiya a hankali ya taka mata baya suna tafiya ba tare da kowannensu ya yi magana ba, har suka iso bakin titi ya biya mashin ɗin ya hau suka tafi. Ya komo shi kaɗai, bai tsaya ba ya wuce hotel.
**********************************
Ya shirya cikin ƙananan kaya, wondo jeans baki da farar riga ya ɗaura jacket akanta kasancewar ana zabga sanyi. Duk da dare ne amma ana sanyi kamar irin na safiya, ya feshe jijinsa da turare yana ƙamshi ya fito ya tadda sauran yan'uwansa suna jiran fitowar sa su wuce cin abinci.
Ma'aikatan Alaja restaurant sun kammala arranging duk wani abin da ake buƙata, zuwan su kawai suke jira. Sun iso kamar kullum kowa ya nemi teburinsa ya zauna nan suka soma cin abincin, Bilqees gefen da Dr Waahab yake bata zo ba, ko kallon bangaren bai yi ba, ya fahimci hakan tun shigowar su, yaga ta kame jikinta daga inda yake, ya sauke numfashi yana cin abinci a hankali duk abin da yake buƙata shi aka ajiye masa, jikinsa ya basa ita ce ta shirya masa tebur.
Sai da ta ɗan zazzaga sannan ta bar wajen zuwa Server's room, ta haɗu da Alaja take tambayar ta ina zata je? Ta ce za taje ta zauna a ciki ne. Ta shigo Alaja ta wuce, tana shigowa ta cire rigar Server's dake saman uniform nata ta zauna kan kujera tare da miƙe ƙafafuwan ta.....
Nocking taji anayi, ta bada izinin shigowa ai ƙofar a buɗe take, sanin babu me shigowa sai waɗanda suke da Alaƙa da ɗakin yasa bata da komai cikin ranta ba...
"Sannu da hutawa"
Taji muryar namiji, lokaci guda ta buɗe idanunta suka sauƙa kan na Dr Waahab, mamaki ɗauke ƙarara kan fuskar ta, me ya shigo da shi?"
Ta tashi ta zauna yana tsaye idanunsa a kanta ya zuba dukkanin hannayensa biyu cikin aljihun jacket na rigar sa, ya zauna a kujerar da take facing nata, zai yi magana ta ce
"Ba a shigowa nan"
"Na sani"
Shine abin da ya ce a hankali, yana kallon ta, a hankali yake kare mata kallo ganin skirt na jikinta yayi har ƙasa saɓanin na saura da ya tsaya musu iya gwiwa, wasu ma mini suka ɗinka, a hankali ya sauke numfashi tare da cewa
"Sam ban kyauta ba da nayi miki mummunar fahimta"
Bata ce komai ba kuma bata ɗago ba, ya ci gaba da cewa
"Ashe wallet nawa kika kawo min nayi miki maganganun da suka ɓata miki rai"
Shiru ya yi yana kallonta ganin bata ɗago ba kuma bata da niyyar ɗagowa yasa a hankali cewa
"Ki yi hakuri, ki yafe min"
A hankali ta ɗago duk da kwarjininsa amma bai hanata kallon cikin ƙwayar idanunsa ba, ta ce
"Ka ce kada na sake zuwa inda kake, ai daliline yasa naje, haka kurum me zai kai ni"
Ya kurawa bakinta idanu na wani lokaci, yana mamakinta irin mutanen nayi masu tsayawa akan gaskiyar su ko da za a kashe su, ya sauke numfashi tare da cewa
"Na gane kure na, ayi hakuri"
Jikinta yayi sanyi ace mutum kamar likita yana bata hakuri, daman so ake duk wanda yayi ba daidai ba ya gane ya aikata to ya bada hakuri, kuma ya bata, ta ɗan gyara zamanta tare da cewa
"Shi kenan komai ya wuce"
"An daina fushi dani?"
"Uhmm"
Kawai ta ce, ya ce
"Shi kenan gobe ma a shirya min teburina kamar yadda aka shirya min yau, komai ya yi daidai"
Ta yi mamaki da ya gane ita ta shirya masa abincin dare, ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ba ni ce na shirya ba"
"Ƙarya ba ta yi miki kyau ba"
Ta sudda kai ƙasa, ya ce
"Na gode da kika kamin wallet nawa"
"Ba komai"
"Anan kika san sunana ko?"
Kunya ta kamata, zai ce tayi masa bincike, a hankali ta ce
"Eh saboda...
"Ah ba komai"
Ya miƙe ya ajiye mata kuɗi kan drower tayi sauri ta mik'e tare da cewa
"A'a bana buƙatar kuɗin nan in ma saboda na kai maka wallet naka ne, ai don Allah nayi"
"Ni ma don Allah na baki kuɗin"
Yana gama fadin haka ya fice. Ta kurawa kuɗaɗen idanu...
"My Bilqees who is that Man?"
A tsora ta kalli ALAJA ta ɗan yi baya..
"Kinga ki dakata ai ni nayi farin ciki da wannan al'amarin, cewa ya yi yana sonki"
"A'a Maa hakuri ya bani"
"Ah to ai watarana zai furta, daman haka maza suke, nawa ya baki?"
Ta ɗauka tana kirga wa, 20k ne kuma tayi mamaki sosai, ALAJA ta ɗauki 10k ta baiwa Bilqees 10k, tayi ficewarta cikin farin ciki, Bilqees bata so hakan ba, taso ta maida masa kuɗinsa gashi ALAJA ta taɓa, haka ta saka kuɗin cikin jakarta har lokacin tafiya gida ya yi suka taho gida.
Bayan ta yi shirin kwanciya, ta kalli mamarta tare da cewa
"Mama"
"Na'am Bilqees"
"Na baiwa mutumin wallet na shi"
"Ah to yayi kyau"
"Amma ya bani kuɗi, zan maida masa kuma Alaja ta taɓa"
"ALAJA kam ai kin san ba zata bari ba"
"Dubu ashirin ya bani, ta ɗauki goma ta bar min goma"
"Ashirin dai!"
"Eh Mama"
"Ikon Allah wannan bawan Allah da abin mamaki yake, ai abin sa ne don an kai masa ba sai ya bada komai ba"
"Eh to kinga ta taɓa kuɗin ai"
"Abin da za ki yi shine, ki mai da masa goman wajenki sai ki ce goma ma ta isa"
"To Mamata"
Suna hira har bacci ya ɗauke su....
***********************************
Dr Waahab sun fara fita workshop, basa zama, don haka abincin su ya koma na dare kawai suke ci, hakan ya sauƙaƙawa ma'aikatan Alaja restaurant, hidimar ta ragu, sai dai su kula da sauran customers nasu.
Yau ma haka, sun shigo suna cin abinci ta iso teburin sa, ta tsaya cikin girmamawa ta ce
"Barka da cin abinci"
Ya ɗago ya kalleta cikin sakin fuska ya ce
"Yawwa, sannu da ƙoƙari"
"Uhm Mamata ta ce na dawo da dubu goma daga cikin kuɗin da ka bani ya yi yawa"
Da mamaki ya dakatar da cin abincin da yake yi, ya kalleta ganin ta ajiye mishi envelope a gefen plate ɗin ta yadda ba za a kula ba, sun matuƙar burge shi, duk da ba wai ya bada don a dawo mishi da shi ba, amma rayuwarsu ya burge shi, a hankali ya sauke numfashi tare da cewa
"Mama ce ta ce ki dawo min da sauran kuɗin?"
"Eh"
Ya ɗauka ya miƙa mata tare da cewa
"Ki ce ina gaida ta, kuma ba a maida hannun kyauta baya"
Shiru ta yi ba ta karɓa ba sai da ya sake yi mata magana sannan ta karɓa tare da cewa
"Na gode"
"Ki ce ina gaida ta"
"To"
Ta faɗa ta bar wajen. Dr Waahab ya jinjina kai daman akwai irin waɗannan mutanen a duniya? Har ya bar restaurant ɗin bai bar mamaki ba. Bilqees ta dawo side nasu ta zauna tana ji suka tafi.
Bayan kwanaki biyu
Tana zaune ta saka yaran a gaba tana binsu da ido, bayan ta raba musu Alawa da biscuit, suna sha suna hira a sakaninsu, bata soma musu baki ba tana sauraron su, Haneef ya ce
"Kyakkyawar Aunty"
Ta numfasa tare da cewa
"Na'am Haneef"
"Uncle kwana biyu bai zo ba"
Sauran yaran ma suka ce yaƙi su kwana biyu, ta sauke numfashi ita ma abin da ke cikin ranta kenan kwana biyu bai zo ba, Allah yasa lafiya, a hankali ta ce
"Uncle yana uzuri ne amma zai dawo"
"To yaushe?"
Ta rasa me za ta ce...
"Morning friend's"
Su ka ji muryarsa, a lokaci guda suka juyo don murna yaran suka tashi suka kewaye shi suna
"Oyoyo uncle"
Yana murmushi yana shafa kansu ya ce
"Ku yi hakuri uzuri ne ya riƙe ne, shi yasa kwana biyu ba ku ganina"
"Haka inji kyakkyawar Aunty ta faɗa mana"
Ya kalleta ganin kanta a ƙasa yasa ya zauna tare da cewa
"Angel"
Ta kalle shi tare da cewa
"Sannu da zuwa"
"Yawwa kun yi kewata ko?"
Idanunta cikin nasa, ta ɗan ware su sosai duk da suna cikin niqab amma ya fahimci maganar sa ce tasa tayi haka, ya rabawa yaran BOBO da biscuit suna ta murna, ya sallame su, ya juyo gare ta, ya yi magana kamar baya son kowa yaji, duk da su kaɗai ne a wajen
"Ba ki ne meni ba, ko na mutu ko ina raye"
"Ai kana raye ba ga shi ka zo ba"
Ya yi murmushi. Ya gyara zamansa
"Ai sai ki yi cigiya ta, kin ce da yaran ina uzuri, ya aka yi kika sani?"
"Saboda shi yake hana mutane zuwa inda suke son zuwa"
"Oh! Haka ne, sai mu yi exchanging number"
Ta yi shiru ita ba kowa take baiwa number ba..
"Ko ba za ki bani ba?"
"Na bar wayar a gida"
"Ok to ga wayata ki saka min number ki"
"Akan wane dalili?"
Yayi murmushi tare da cewa
"Saboda nayi abokiya a Ghana"
"Kana nufin ba anan kake ba?"
"Eh aiki ne ya kawo ni kuma zan koma"
Ta karɓo wayarsa tana juyawa, haɗaɗɗiya ce na gani na faɗa, tam wannan daga gani ta ci kuɗi da yawa, ta saka masa number sannan ta miƙa masa, ya karɓa ya yi saving da ANGEL, a hankali ya ce
"Zan kira da kin je gida sai ki yi saving"
Ya kira bugu biyu aka ɗauka
"Me wayar bata nan"
Suka ji aka ce, ya kalleta ita ma shi take kallo, mamaki yake yi, kamar yasan wannan muryar amma sanin a Ghana yake yasa ya sauke ajiyar zuciyar, tare da katse kiran, a ransa ya ce kama ne, Angel ta mik'e tare da cewa
"Na tafi"
"Ni ma zan wuce, kuma ba lalle ne na dinga zuwa wannan kullum ba, sai dai mu yi waya"
"Ok na fahimta bye"
Ta yi sauri ta iso bakin titi, ya maida wayar aljihu ya bar wajen cikin sauri....
Comments and share fisabilillahchap