CHAPTER 3
Da sunan niman taimako takoya mata zuwa wurin bokaye iri-iri, Inna tamallake Abubakar tsaph, duk wani abu datace ayi shi akeyi, idan tasanya mai kara baya iya tsallakewa.
Aminat dai baruwanta, duk abinda Inna tace ayi shi takeyi, tazamema Abubakar matar rufin asiri, matarda zakai kuka tare da ita kui dariya tare, matarda take kai mijinta aljanna tahanyar tayashi bin mahaifiyarshi.
Ko sanda karayar arziƙi yasameshi aɓangaren noma itace wacce taɗauki wani kaso na dukiyarta da taci gadon mijinta da na mahaifinta tabama Abubakar aro yayinda kaso mafi yawa yake hannun ƙaninta Shattima.
Kamar dama arzikin Abubakar akasuwanci yake sanine basuyiba, dukiya tasoma hau hawa, cikin ƙanƙanin lokaci yazama Alhaji aka soma sakashi acikin jerin masu kuɗin Saidi.
Har wannan lokacin Aminat batasami haihuwaba har seda malaminshi daye karatun addini a wurinsa yabashi ɗiyarshi Iklima salaka tazo gidan sannan suka sami ciki atare suka haifi ƴaƴa yensu maza.
Ɗan wurin Aminat yaci sunan Muhammad, ɗan wurin Iklima kuma Fu'ad.
Ganin haka yasa Kaltume huroma Inna wuta akan yakamata Abubakar ya'auri ɗiyarta Nazifa.
Dama a lokacin taɗauko lalacewa, bin maza takeyi, har kamata anyi aɗakin wani saurayi aka dinga bugawa a jarida.
Cikin farinciki Inna ta amshi zancen, aganinta ai taimakone duk wanda ya rufa ma wani asiri Allah zai rufa asirinsa, balle Nazifa ɗiyar tace na tashin aliƙiyama da wasu bare suita cin arziƙin Abubakargwara ita taci.
Rananda aka sanya musu rana Nazifa tazo gidan su Aminat suna ɗakunansu ta shiga turakar Abubakar tace dashi
"Ayanzu Ni nazama matarka, zaka iya yin duk abinda kaga dama dani."
Cikeda rashin fahimta yakalleta. Nazifa ta matse space ɗin da ke tsakaninsu tana shirin cire kaya yadaka mata tsawa
"Fitarmun aɗaki, banziya....mara kamun kai..."
Duk yanda Nazifa taso Abubakar yai amfani da ita yaƙi, wannan abu yai mugun ɓata mata rai wanda taje tagayama mahaifiyarta.
Masu abu da abunsu, nan Kaltume tamiƙe wurin malamai kala kala taje tasa aka asirce musu Abubakar dama Inna gabaɗaya yazamana basada abinso da ƙauna sai Nazifa.
Iyanzu ƴaƴan Nazifa takwas ne, ɗiyarta ta fari macece sunanta Suhaima se Faizan, Ma'aruf, Habiba, Mashida, Asiya, Lubna, Yasir se auta Najib.
Iklima nada ƴaya biyar Fu'ad, Nasir, Ibrahim, Faiza, Nasrim.
Aminat ƴaƴan ta biyu ne kacal Muhammad da Maryam.
Haka rayuwa tacigabada gan garawa, Aminat da Iklima suka zama ƴan kallo, duk yanda akayi dasu haka suke biyuwa, sunyi imani da Allah akawai ranarda komai zai zo ƙarshe, duk wannan mulkin da asirin zezama tarihi yayi kamar ba'ayiba domin babu inda makauniyar hanya ta-taɓa ɓullewa gamai binta.
______________________________________
*DIYANA*
Zaune take akan sallah yan data idarda sallahn isha'i, jinta take kamar wata butun butumi, kamar tana tsaye abayan duniya tana hango cikinsa daga nesa.
Allah ne kaɗai masanin abinda takeji, babu wata kalma da zata iya bayyana abinda takeji, zuciyarta wani irin ciwo take mata, arayuwama gabaɗaya tarasa dame zata haɗa wannan expression ɗin, imagination ɗinta betaɓa kaita wannan mood dinba, ita bata ɗauka akwai emotions masu tarin yawa da suke bada irin wannan yanayin ba.
She can't explain irin abinda takeji, mezata ce baƙin ciki, ɗaci ko damuwa acikima batasan a'ina zata sarƙafa yanayin da take cikiba,
Hayaniya taji alaman wasu mutane sun shigo gidan, muryan Goggo taji tana faɗin
"Yi ahankali ranka shidaɗe, shigo ahankali."
Ƙerarren mutum ne atsaye wanda jikinshi gabaɗaya a rufe yake ruph cikin shigan ƙananun kaya.
Ƙafansa sanye da takalmi mai rufi, fuskarsa sakaye abayan facemask, dai dai da hannunsa sanye yake da safa. Ƙamshin tirarensa yacika kofofin hancinsu.
Yazauna akan kujera escort nashi na tsats tsaye agefensa.
Ganin yanda Diyana tai tsaye tana kallonsu kamar batasan da shigowar suba ya sanya ran Goggo ɓaci.
Muryanta aɗage kamar zata kai mata hannu tasoma magana
"Dan ubanki Diyana bakiga mutane sun shigo bane, to wannan yafi ubanki matsayi don commander ne na sojoji, duk garinnan aƙarƙashin kulawar shi muke bacci cikin salama."
Taƙarke maganan muryanta na fitowa ƙarara da ɓacin ranta bai cinma Diyanan ba akusa da ita takeba da ba abinda zehanata kai mata duka.
Abdul Malik yai shiru yanajin yanda Goggo ke ɗoramai matsayin da ba nashiba, baicin bayason tonan asiri daba abinda ze hanashi gaya mata gaskiya shiba commandern sojoji bane.
Waɗannan sojojinma adole yataho dasu saboda tsaro.
Tunda kalaman Goggo suka shiga kunnuwan ta tamiƙe daga zaunen datake tana takawa tamatse tazarar da ke tsakaninta da wannan mutumin dake gabanta.
Idan har batai kuskuren jiba to wannan mutumin ne yasaki linzaminsa, shine mutumin daya saki aikinsa har tai rashin mutum biyu arayuwarta, shine yai silan rushewar ginshikan rayuwarta suka tafi suka barta.
Tabbas wannan mutumin bai mata adalciba, kuma yake zaune agabanta har yake kallonta zai ce mata wai tayi haƙuri.
Batasan taɗaga hannunta tasaukeshi akan fuskar wannan mutumin ba seda taji sautin tass na amsakuwwa acikin kunnuwanta,
Ƙaranda Goggo tayi da salati gamida magan ganun da suka biyo baya sunzo ne abayan wannan marin datayi kuma bataji ko ɗarr arantaba, batajima cewa tayi badai daiba, idan tanada dama zata wankeshi da marukan da sukafi wannan domin taraba abinda takeji dashi.
Sojojin dake tare dashi suka yunƙuro zasu daketa ya dakatar dasu tahanyar ɗaga musu hannu.
Ta ɗanja da baya kaɗan tana sakin wani irin gunjin kuka, ta durƙeshe agurin jikinta na kyarma numfashinta na niman ɗaukewa na kukan da takeyi.
Kuka takeyi akan duk ciwukan dake ƙirjinta, kuka takeyi akan rashin da tayi, kuka take akan baƙin cikin rayuwar da zata fuskanta.
To dole tace rayuwar da zata fuskanta mana rayuwar gidansu bakaman kowace irin rayuwa bace, rayuwace tadaban, rayuwace da mutumin dake zaune a cikinsa kaɗai zai fahimta.
Ita kanta ayanzu tasan tabuɗe sabon babi takama wani hanya mai yiwuwa takirashi makauniyar hanya amma ba makauniyar hanya bace ƙila tasami dai dai to, ƙila tasami mafita sakamakon atare da ita akwai ubangiji daze bata mafita akan komai.
Yamiƙe ahankali cikin muryanshi mai sanyi yafurta
"Iname matukar baki haƙuri, ubangiji yajiƙanta"
Yana gama fadin haka yajuya ya fice daga ɗakin.
Diyana taƙara takure jikinta tana ƙara fashewa da kuka mai sauti.
Da gudu Goggo tafita tai naɗakin Inna dake zaune tana ƙirga kuɗaɗen da ya zuba mata.
Asaman kanta taji muryan Goggo na cewa
"Inna munshiga uku, yau kwanan mu yaƙare wato yarin yannan Diyana mari tazab gama wancan Sojan"
Nan take jikin Inna yaɗau rawa, akiɗime tace
"Allah yasa ban jiki dai daiba, mai-mai tamin mekika ce?!..."
"Kunnu wanki pha sunjini dakayu..... wallahi mari Diyana ta zab gama Sojan da yafita yan zunnan."
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un"
Baffa daya shigo yanzu yafadi jin abinda Goggo ke faɗama Inna.
Cikin hayani ya cigabada cewa"wallahi sedai ta baƙunci lahira ita kaɗai don nasan sunanan dawowa cikin daren nan"
Muryan Inna na makyar kyata tace"Alhaji katabbata yau yarin yannan bata kwana agidan nan ba inba hakaba wallahi Ni sena bar gidannan "
"Kwantar da hankalin ki Inna amma wallahi ƴannan bazata kwana agidan nan ba"
Afusace yajuya yabar ɗakin, sauri yakeyi kaman zewuce ƙafafunshi, tsaban ɓacin rai jikinshi har tsuma yakeyi.
Ummm masu karatu Diyana pha ta taro match......!!!
Koya zata ƙare tsakanin ta da Baffa, da Inna da Goggo da wanda aka wankama mari?
Toma wai zata kwana agidan ko bazata kwanaba?....
Tom domin samun waɗannan amsoshin kutara a chapter 4
Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘
🌖 اءمي الطريق 🌒
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰