CHAPTER 4
Afusace yajuya yabar ɗakin, sauri yakeyi kaman zewuce ƙafafunshi, tsaban ɓacin rai jikinshi har tsuma yakeyi.
Allah sarki baiwar Allah Diyana batasanma anayiba haryanzu tananan a'inda take.
Ko kallon halinda take ciki Baffa baiyiba yasa hannu yajawota suka fito waje.
Inna da Goggo dama Ummah Iklima dataji hayaniya tafito suka rufa musu baya zuwa ƙofar gidan.
"Mutuniyar banza mutuniyar wophi kizauna anan idan Sojojin sunzo su ɗaukeki amma Ni banci naninba nanin bazata ciniba."
Baffa yai maganar ne asanda yai cille da ita atsakar kwaltan dake wajen hanayar wucewa.
Idanuwanta ta lumshe kalaman Baffa nazama a kowani sashi na jikinta, da ciwo mara misaltuwa taɗaga murfin idanunta tasauke ƙwayannin akan Baffa daya juya yashige gida ya maida ƙofa yarufe.
Batasan meya riƙetaba awannan lokacin amma jinta tai kamar ba itaba, ƙwa-ƙwalwarta tanatsa zuciyarta ta tsaya, emotions feelings and pain duk sun kauce sun barta ita kaɗai akaran kanta.
Daƙyar taja ƙafafuwanta da sukai sanyi ƙalau suna niman gaza ɗaukarta tazauna akan dakalin ƙofar gidan.
*_*
Aƙaramin zaure sukai kaciɓiss dasu Ummah Iklima.
Kamar zatai kuka tace"Alhaji don Allah kaji tausayin yarin yannan kadawo da ita gida, kowani hukunci zakai mata kai matashi acikin gida, kasan dai garinnan babu lafi....
"Iklima.....! Iklimaa.....!!"
Inna takirata da iya ƙarfinta tana cigaba da cewa
"Kewata iriyar ja'irar yarinyace,kinfimu tausayine ko me?...To wallahi barikiji idan kika ƙara magana akan waccan yarinyar to abakin aurenki."
Goggo tace"wannan shine dai dai Inna, Ni yarinyar nanma tsoro tabani tunda ta'iya ɗaga hannu tamari soja to wallahi Mu ko kashe mune setayi amma saboda gulma da iyayi anzo za'a hukunta yarinya kina wani bada haƙuri."
Ummah Iklima tai shiru tajuya cikin gida hawaye na saukar mata.
Su Goggo suka tsaya agun suna cigabada maimaita zancen seda sukaji iskan hadari sannan suka shige gida.
Ko motsawa batayiba sanda iskar ruwan yataso, taɗora kanta bisa guiwoyinta tanajin yanda zuciyarta ke curewa tanazama dutse amemakon gari.
Hadari baƙiƙƙirin yahaɗu asararin samaniya, iska mai ƙarfi yataso tareda walƙiya, akafara yayyafi kaɗan kaɗan, cikin hikimar ubangiji ruwan be sauko ba hakan yasa garin ye wani irin sanyi mai shiga jiki.
Ita kam Diyana taƙame, takasa motsi, takasa tinani, yayyafin da iskan ruwa nata kaɗata daga bisani sanyi yasauka.
Hijjab kawai tasa ta lulluɓe ƙafafunta, tadunƙule jikinta yanda taga rana haka taga dare.
Athuba tayi mutane suka soma fitowa suna tafiya masallaci, babu wanda ya lura da ita balle yemata magana.
Haka Baffa ya fito da shida matasan gidan suka tafi masallaci batareda yako kalletaba.
Misalin Ƙarfe 6:00am Baffa yadawo kallo ɗaya yai mata yace
"Taso muje"
Diyana tamiƙe tabi bayan shi. A dakin Inna suka yada zango a lokacin tana zaune tanajan carbi.
Ganinsu yasa tai addu'a ta shafa, rai aɓace takalli Baffa dake zaune kan carpet tasoma magana
"Alhaji ashe bakada mutunci, wato kai mai ƴa!shine gari na wayewa kaje kaɗau kota ko? Tunda nazama banza mara amfani meyasa zaka kawota wurina?".....
Cikeda ladabi da biyayya yace"Allah yahuci zuciyar ki Innata dama na dawo da itane saboda tai wanka takarya amaida ita makaranta."
Inna ta zuba mai idanu bata tsinkaba.
Baffa yaƙara sunkyarda kansa ƙasa cikin ladabi da niman sassauci yace
"Dama nai tinani akan maganan da muka taɓayi dake tun kafin rasuwar Aminat da kikace kinaso in auri ƙanwata Sumayya, idan kinyar jemin zanje insami su Baba ai magana"
Koda Hajiya taji wannan maganan taji daɗi aranta amma bata nunaba tace
"Kafin kai musu magana kabari kusoma fahimtar juna da ita, kasan yarinyar ƴar babban gidane kuma mijinta ne yarasu ƴaƴanta ukune kawai.
Nasan Arɗo zaiyi matuƙar jin daɗin wannan haɗin saboda amintakar dake tsakaninsa da mahaifinka."
"Hakane Inna"
Ya'amsa dasauri jin yanda tasaki lokaci guda.
Dubanta tamaida ga Diyana tace da ita ta tashi tashiga ciki.
Miƙewan tayi taje waje tasami buta tai alwallah Goggo nata mata habaici.
Itadai batabi takantaba tashiga ɗakin mahaifiyarta tai sallah.
Tun kafin ta idar Ummah Iklima tashigo tazauna.
"Ina kwana Ummah"
Ta gaidata asanda ta'ida sallahn.
Cikeda tausayi ta amsa gaisuwar tata tana miƙomata tea da bread.
Diyana takalli cup din takauda kai, tinanin sha ƙadai amai yake sanyata duk da kuwa rabonta da abinci tun shekaran jiya.
"Don Allah kidaure kisanya ma cikinki wani abu, horon yunwar da kikema kanki bazai sauya komaiba.
Yaya Aminat tarigada tarasu abu ɗaya take buƙata daga duk wani masoyinta shine addu'a"
Haka Ummah Iklima tadinga lallashinta tanai mata nasiha da jan hankali.
Ta daure taɗauki cup ɗin takai bakinta badon tana gane ɗan ɗanon shyayinba.
Bayan tagama sha tasake mata ruwan wanka tashirya Hamma Fu'ad yamaidata makaranta bisa umarnin Baffa.
Har cikin makaranta yakaita, duk wacce suka haɗu da ita sedai sugaisa tai mata gaisuwa.
Da shiganta ɗakinsu Umaima da Labiba dake zaune ko wacce da littafi ahannunta sukayo kanta.
Junansu suka rungume cikin kewa, nan sukai mata ta'aziyya sannan suka dinga janta da hira ahaka har tasaki damuwanta yaragu sosai.
Ahaka suka fara exam ɗinsu na WAEC kuma duka sunyi iya ƙoƙarinsu abin fata anan shine ubangiji yabasu sa'a.
Acan gida kuwa tun ranar da akai bakwai Kawu Shattima ƙanin Aminat da Baffa Halliru wan mahaifinsu da ƴaƴa yenta maza duka Dawood da Rafiq
Suka zo da babban alƙali yai musu rabon gado bisa dukiyarta dake hannun Kawu Shattima da Baffa.
Haƙƙin juya dukiya aka cire mai ɗaya bisa uku, aka cire mai gadonsa amatsayinsa na mijinta sannan aka rabama ƴaƴanta sauran.
Inda Diyana ta tashi da miliyan ashirin da biyar banda ƙaddarori.
Hannun Baffa aka bar komai nata sauran suka damƙa nasu a hannun Kawu Shattima yaci gabada kula musu dashi.
Daƙyar Goggo ta iya tashi daga wurin tashiga ɗakinta.
Tai zaman ƴan bori akan kujerar ta zuciyarta phall saƙe-saƙe,
Ayanzu duk rananda Alhaji yamutu atutar ma'ahu zasu tashi kenan komai zai zama mallakin Diyana nane,
Wannan abune dabazata taɓa bari yafaruba, yazame mata dole ayanzu tamiƙe tai abinda ya dace tun kafin lokaci yaƙure mata.
Anyi rabon gado da kwanaki 7 inda yazamana sati biyu kenan da rasuwar Aminat aka ɗaurama Baffa aure da amaryarsa Sumayya.
Goggo tai bakan tana kallonsu kafin lokacin data tanazar musu yacika.
*DIYANA*
Arananda sukai final exam sukai candy, akaraba musu kyaututtuka da yabo ga masu ƙoƙarin cikinsu tareda musu fatan alheri arayuwa.
Suna cikin ɗaukan hotuna wata yarinya tazo tace
"Aunty Maryam ana kiranki awancan motar"
Kallon motar da yarinyar tanuna Diyana tayi, itadai ko adangi bata taɓa ganin kalan wannan motarba kuma batajin akwai mai kalanshi.
Kamar zatace bazata jeba sekuma ta tsame tanufi wurin motar.
Awurin driver ta tsaya, se taga anbuɗe ƙofar baya wani ƙamashin tirare mai sanyi yadaki hancinta in batai ƙaryaba to zatace ta taɓa jin kalansa awani wuri.
"Shigo mana ai basaceki zanyiba"
Tattausar muryan mutumin dake cikin motar yafaɗi.
Kai tagirgiza alaman a'a.
Ganin bazata shigo ɗinba yasanyashi fitowa ya tsaya agabanta.
Diyana takalleshi da manyan idanunta, kyakkyawan matashine wanda baze wuce shekaru 28-29 ba.
Dogone, fari mai murɗaɗɗen jiki da alama yana zuwa gym,
Sanye yake cikin ƙananun kayan da suka amshi jikinshi, kansa ɗauke da askin zamani da yazauna tamkar an zanasa akan baƙin sumarsa daketa ɗaukan ido.
Irin wannan matashin da ke tsaye agaban tane ake kirada end of discussion wasu kuma suce one in million.
Duka wannan kallon Diyana tai maine aƙasada daƙiƙu uku kuma taɗauke kanta kamar bata ganshiba se shirun data katse tahanyar gaidasa.
Abdul-Malik ya'amsa gaisuwanta da murmushi yana kafeta da oily eyes ɗinshi masu kyan gaske.
Shirune yaratsa a tsakaninsu, Diyana taƙosa da tsayuwar har ta buɗe baki daniyyar magana taji yasoma magana
"Sunana Abdul-Malik niɗin likitane dake aiki a asibitin sojojin Saidi bawai commandern sojoji ba kamar yadda kika ɗauka awancar ranan."
Dasauri Diyana taɗago takallesa idanuwansu suka sarƙe cikin na juna hakan yasa zuciyarta wani irin dokawa tai saurin janye nata idanun jikinta na ɗaukan sanyin kunya da nadama alokaci guda.
"Kayahaƙuri...."
Tafurta kalmar daƙyar muryanta na fitowa da yanayin da take ciki.
Acikin kunnu wanta taji sautin murmushin sa, baicin tsayuwar idanu wansa datake ji aduk jikinta daba abinda ze hanata ɗagowa takalleshi.
"Bakomai kawai na gayamiki ne saboda banaso Ki cigabada jin haushina."
"Nagode"
Tafaɗi kanta aduƙe.
Abdul-Malik yagayara tsayuwar sa da faɗin
"Congratulations"
"Thanks"
"Zan iya ganin gift ɗin?"
Yace yana miƙo mata dogon hannunsa mai cikeda kwantac ciyar baƙar gargasa mai kyau da jan hankalin wanda yai tozali dashi.
Batareda taɗago takallesaba tamiƙamai, haka kawai taji tsayuwar duk ta gundureta, ga jikinta dake kyarma ahankali zuciyarta na wani irin dokawa dabata taɓajin kalansa akan kuwwaba.
"Wow yai kyau don Allah Ki taimaka Ki bani kyautar"
Kamar wacce aka shaƙema maƙoshi haka tabuɗe bakinta muryanta na fitowa asanyaye
"Nabaka"
"Gaskiya ina godiya Nima bari nabaki wani"
Baijira mai zataceba yabuɗe motar yaɗauko wata madai dai ciyar leda baƙa yamiƙa mata.
Kai tagirgiza da faɗin
"No kabarshi nagode"
"Please indai bakin raina bane Ki karɓa"
Yanda yai maganar cikeda roƙo yansayata yin shiru kamar mai tunani.
Irinsu Abdul Maleek ne mutanen da ba'a iya jaa in jaa dasu domin kwarjininsa da haibansa bazasu barka kaita mujadala dasuba.
"Don Allah"
Yafaɗi ataɓare yana wani karya kai kaman wani yaro ɗan shekara uku.
Batada yanda zatayi hakanan tamiƙa hannu takarɓa da kalmar
"Nagode"
Baki yabuɗe zai magana isowar wata yarinya da saƙon ana kiran Diyana yasanyashi yin shiru.
"Allah yabamu alkhairi"
Tai maganar da saurinta cikin zuciyarta tana godema kawayenta da sukai aiken akirata.
Ko kafin yace wani abu har tajuya ta tafi abinta.
Tattausar leɓensa na ƙasa yalasa yanabin bayanta da kallo seda ta ƙulema ganinsa sannan yashige mota driver yaja suka tafi.
Uh...Uhmmm....naceba wai mai wannan Abdul-Malik ɗin yake nufida Diyana?
Wannan kulawar? Da wannan bugun zuciyar nan.....da emotions ɗinnan duk na menene?
Domin samun waɗannan amsoshin kutara a chapter 5
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘
🌖 اءمى الطريق 🌒
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰