Makauniyar Hanya

CHAPTER 5

by @hindatuauwal

Tattausar leɓensa na ƙasa yalasa yanabin bayanta da kallo seda ta ƙulema ganinsa sannan yashige mota driver yaja suka tafi.

Wurinsu Umaima takoma, motar da suka sanya animo musune ta iso shiyasa suka sa aka kirata.

Already dama sun gama shirya kayayyakin su sekawai tahau suka soma tafiya zuciyarta cikeda sake sake.

Wace iriyar mata Baffa ya auro? Wani irin rayuwa zata fuskanta ayanzu da batada uwa da ɗan uwa, Shin zata sami farin ciki ko kuwa?

Wani ɓangaren zuciyarta kuma yafaɗa tinanin wancan mutumin da yakira kanshi da Abdul Maleek.

Haka tadingi karanta wasiƙar jaki har suka iso tasha yasaukesu suka hau ɗan sahu itada Umaima dayike Labiba ita ƴar gambuwa ce.

Itada kayanta aka saukesu, almajiran dake zaune aƙofar gidan suka tai maketa suka ɗaukar mata katifa da trolly ɗin kayanta.

Tun daga zaure takejin sautin muryar wata tana masifa itada Goggo.

Da sallama tashiga sedai babu wanda ya amsata domin hankulansu baya kanta.

Tsayawa kawai tayi tana kallon yanda matar ke sirfa bala'i tana jijjiga kamar zasu daku itada Goggo.

Inna dake tsaye tadaka musu tsawa akaro na ba 'adadi da faɗin

"Wallahi duk wacce taƙara magana abakin aurenta."

Kamar anyi ruwa anɗauke haka sukai shiru suna kallon Inna.

Goggo tai tsaki tashige kitchen, jiki asanyaye Diyana taduƙa akan guiwoyinta tagaida Inna.

"Lafiya kalau ya makarantar"

"Lafiya kalau"

Ta amsa.

"Kai shigarda kayan sashina"

Wucewa almajiran sukayi, Diyana tagaida Ummah Iklima daketa mata murmushi bayan ta amsa tagaida Sumayya.

"A'a Ni bazan amsa gaisuwar tsakar gidaba muje ciki"

Taƙarke maganan da murmushi taname juyawa tasoma tafiya.

Bayanta Diyana tabi itama tana murmushi, ɗakin Innarta adaa suka shiga.

Pure wata mai sanyi taɗauko mata a freage da zuɓo akan plastic flat mai kyau.

Tadauka tasha tana godiya, ahankali tasoma janta da hira har sun soma sakewa Goggo taleƙo tace

"Idan kingama surutun kitaso muje"

Ko rufe baki bata gamaba Diyana tamiƙe tabita. a kitchen suka tsaya Goggo tace

"Gayinan ki ƙarika girkin se ki ɗora miyar in kin gama ki kirani"

Da "Tom" ta masa tana gyaɗa kai.

Goggo na fita itama tafita taje tasauyo kaya zuwa wata material pink color, anyi mata ɗinkin riga da siket wanda yazauna dai dai jikinta, zata shiga kitchen kenan sukai kaciɓiss da Hamma Ummar tagaidashi.

"Lafiya kalau Diyana har kin dawo kenan"

"Eh Hamma"

"Yawwa dama ɗakina yanata kewanki yana kiran sunanki taimaka kije kimun kwalima kigyarashi tsaph yanda kika saba"

"Tom Hamma"

Makullin ɗakin yabata yafita, dayike dama tasaba gyara mai daki aduk sanda tadawo hutu.

Hakanan taraba kanta biyu tana girki tana kwalima, inkaga yanda take sarrafa jikinta da zafin nama seka rantse wata babbar macece ba yarinya ƴar shekaru 17 ba.

Ƙarfe biyar tagama girkin Allah yasa tarigada tayi sallahn la'asar asanda take aikin se kawai taje taƙarika kwalimar tasake ruwan wanka tayi tasauya kaya.

Tana cikin shafa mai Inna takirata. tamiƙe tafita falon.

Azaune taganta akan kujera sewani matashin saurayi. tagaidashi ya amsa yana binta da kallo.

"Wuce kije kitchen kisamo mai ruwa da lemu"

Ta'amsa ta wuce ta gabanshi tai na kitchen. Numfashi mai nauyi yasauke yakalli Inna yace

"Inna wallahi wannan itace yarinyar da zuwana naƙarke nace miki ina sonta amma kika kasa ganeta"

Murmushi Inna tasaki tana cewa

"To ai Kaine bakai min bayani dai dai ba amma ai ta kwana gidan sauƙi indai haryanzu kana sonta ba matsala"

Imran yace"gaskiya naji daɗi sosai ba abinda zance se godiya kin....

Kawo tiren lemu da ruwa yasan yashi haɗiye sauran maganan.

Bata tsaya tambayarsa abinda yake soba tajuya daniyyar komawa ciki.

"Ke ina zaki?"

Inna tai mata tambayar tana tsareta da tsayayyun idanunta.

Shiru tayi haɗida sadda kai ƙasa.

Inna tace"tunda bakida wurin zuwa to dawo kizauna"

Batai gardamaba tadawo tazauna. seda takallesu suduka ɗaya bayan ɗaya tai magana

"Ke Diyana ga mijinan nayi miki ban damu da kina sonshi ko bakya sonshi ba abuɗaya dai nasani cewa aure tsakanin ku babu fashi insha Allah sedai inshine yace baya sonki."

Gaban Diyana ne yai mummunar bugawa asa'ilinda kunnuwanta suka kaima ƙwaƙwalwarta saƙon abinda tafaɗa.

Goggo dake tsaye abakin kofa tun sanda Inna tafara magana tai ƙwata tafurta

"Daga aurenki har na Faiza idan har ina raye baza'a yishiba"

Kamar wacce tahaɗiyi kunama haka zufa yashiga keto mata a kowani kafa najikinta.

Ta tashi daƙyar tashige daki ta kwanta hawaye na saukar mata.

Ko abinci kasaci tayi, da daddare ma sedai tadinga juye juye zuciyarta cikeda tarkacen tinani kala kala.

⚡⚡⚡⚡⚡

Tsaye take a kitchen tana kwashe alalen da Inna tasakata tai mata.

Suhaima ce tashigo tana wani harare harare don ita tun jiya da Goggo tagaya mata anzo niman auren Faiza daga gidan Sarkin Noma da na Diyana wanda Imran ƙanin Baffa ƴaƴa maza yake sonta taji duk haushinsu takeji.

Tayaya ita datake yayarsu batai aureba tana zaune kamar tasha hatimin jaki babu wanda yataɓa cewa yana sonta amma su ƙanninta databama shekaru uku zuwa hudu zasui aure,?.

Baicin kisa be halastaba da ba abinda zehanata daukar bingida duk takashesu ta huta da wannan baƙin cikin dake danƙare azuciyarta.

Ƙafa ta sanya tatake na Diyana dake tsaye tana aikinta.

Ƙara tasaki tana kallon Suhaima da faɗin

"Wayyo Adda Suhaima kin takani"

Meniman kukane aka jefeshi da kashin awaki se kawai Suhaima takai mata mari da faɗin

"Ke dan uwarki Ni zaki gayama na takaki banza to ko wacce tahaifeki agidannan tayimin kaɗan."

Diyana tasaki kuncinta data daphe tanuna Suhaima dayatsa

"Adda Suhaima ina matuƙar jin kunyar ki karki bari mu fara sa'insa tsakanin mu duk abinda zehaɗani dake karki ƙara kiran sunan uwata."

"Ahayye chass...."

Suhaima tasaki shewa tana ƙyalƙyalewa da dariya taɗorada

"Eh lallai bari inmiki wata ƴar waƙa Aminat.... Aminat....fanteka. Kafanta Kafanta fanteka....Yana mata mene azara.....Ya

"Tass!"

Shine sautin daye replacing da next word ɗinda Suhaima zata faɗa.

Cikin matsanan ciyar mamakin da Diyana tashayar da ita tace

"Diyana Ni kika mara?"

With her full confidence tabata amsa da"Suhaima na mareki kuma zanyi miki abinda yafi wannan matsawar kika sake kuskuren kiran sunan mahaifiyata idan kuma kinmusa pls try me."

Hannu Suhaima taɗaga daniyyar marin Diyana, aikam haƙanta becimma ruwaba Diyana tariƙe hannun takamo ɗayar taritsashi da hannunta ɗaya.

Tahaɗata da bango tareda sanya ƙafafunta ta take na Suhaima. hannunta na dama tasa tadingi kifa mata mari.

Duk yanda Suhaima taso taƙwaci kanta takasa se ihu datake kurmawa hakan yasa matan gidan shigowa hankali atashe.

Jama'a menake gani haka wai Diyana ce ke dukan Suhaima shalelen Goggo bayan dama ashaƙe Goggo take dasu awuya.

Ummm tom lamarin yafi ƙarfina koya zata kaya kawai muhaɗe a chapter 6.

Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰