Makauniyar Hanya

CHAPTER 6

by @hindatuauwal

Duk yanda Suhaima taso taƙwaci kanta takasa se ihu datake kurmawa hakan yasa matan gidan shigowa hankali atashe.

Duk yanda Goggo da Ummah Iklima suka so amsarta kasawa sukayi har seda Inna taƙarisa wajen cikin tsawa tace

"Diyana cikata.....Nace kisaketa"

Inkai da baka awurin kajita to Diyana ma tajita, Inna takalleta da kyau zuciyarta na ɗarsuwa da tsoron kada aljannun Diyana su tashi.

Dama tun tana ƙarama takedasu mahaifiyarta ke mata magani hakan yasa basa tashi amma yanzu dataga idanunta sunjuye sunyi jajir kamar garwashin wuta tana wani huci kamar kububuwar maciji seta tina.

Tai ƙarfi da zuciyarta ta zabga mata mari akuncinta nadama. Se alokacin Diyana tawaiwayo takalleta amma batace komaiba.

"Saketa kiwuce kibani wuri"

Inna taƙara faɗi cikin ƙarfin hali. sakinta tayi tajuya daniyyar tafiya Goggo tasha gabanta da cewa

"Sannu tabbatacciya mara kunya nufinki kindaki danza kenan ko me?"

Ashaye da toka takalleta, tawani raɓata ta wuce abinta.

Ummah Sumayya ta amshe da bama Goggo amsa akan bekamata tasanya bakiba.

Goggo tace dawa Allah yahaɗata bada Ummah Sumayya ba. nan dai fadan yajuye yazama nasu. seda Inna tashiga tsakanin fadar sannan aka sami sauƙi.

Imbanda kuka ba abinda Suhaima takeyi,ita gabaɗaya ma jitakeyi ta muzanta hakan yasa Goggo ɗaukar mayafinta batareda kuwwa yasaniba tanufi gidan Junun.

*

Zaune take agaban wani baƙin mutumi, bayada ƙiba kona misƙala zarratin, irin sune mutanen da ake tababan ko sunada tsoka ajikinsu bayan fatar data rufe kasusuwan su.

Jikinshi sanye yake da kayan saƙe jajjaye, tsohone ainun da yaman yanta yakai kimanin shekaru 80.

Duba yake akan ƙwaryar dake gabansa yana lelleƙawa tareda jijjiga kansa seda yashafe kusan mintoci biyar ahaka yaɗago yakalli Goggo fuskarsa babu fara'a.

"Aikinki babbane bazai kammala ba ayanzu har sai kin bani lokaci"

"A'a Junun kada mui haka dakai, indai kuɗine kasan ina dasu aikinnan amatse nake ayishi agama"

"Hhhh"

Yewata shu'umar dariya datai amsakuwwa acikin dajin, can yaɗaure fuska tamau yace

"Mutanen da ke jironki(gida) amallake suke dama sedai aƙara mallakesu amma waɗannan sababbin ayyukan dole kibani lokaci"

Duk yanda Goggo taso Junun yai mata aiki anan take ƙinyi yayi daga ƙarke se yace da ita

"Watan nan yarinyar Diyana itace babbar matsalar, jinnun dake kanta manyane dole se anyi aiki meƙarfi akansu don haka kibani lokaci"

Badon tasoba hakanan tabashi dubu hamsin ta taso zuciyarta na raya mata dole tasauya sheƙa tunda Junun yasoma gazawa.

Dama ita tun tasowar ta suke zuwa da mahaifiyarta, ƙarfin aikinsa da zafin namansa yasanyata riƙeshi amma ayanzu talura tsufa yakamashi shiyasa yake gaya mata waɗannan zantukan banzan.

Ranta duk ajagule tadawo gida.

*DIYANA*

Zaune take itada Faiza da tashigo tayata hira.

Kasan cewar akan faɗan ɗazu take ta magana yasanya Diyana yin shiru tana kallonta.

"Nifa wallahi bakiji yanda kika burgeniba yau ɗinnan tunda muka taso akema iyayenmu cin kashin da aka gadama har wayau, but insha Allah inaganin sanadin ki komai zai zo ƙarshe"

"Uhmmm"

Kawai tace agajiye tana dafe kanta daye mata nauyi.

Duban Faiza ne yakai ga ledan dake kan madubi.

Miƙewa tayi taɗauko tana faɗin"Adda Diyana wannan pha?"

Kallon ledan tayi zuciyarta na dokawa. Faiza tasoma zazzage kayan tana magana

"Kam bala'i wallahi antashi kaina Adda waya baki wannan gift ɗin?"

Tafadi tana tsamo wayar dake cikin tarin tarkacen kayayyaki masu tsada daya bata.

Diyana tai shiru tana rasa abincewa.

"Oh Allah iphone 17promax ce ahannuna yau..."

Kunna wayar tayi tana sumbatu, kamar anajiranta sega kira yashigo ɗaukeda sunan A.Malik

Seda tai picking sannan takara mata wayar akunni tana buɗe kwalin wani tsadadden perfumes da kwalbansa kaɗai abin kallone.

Gawani book mai bakin cover da pen ɗinsa ajikinsa anrubuta Congratulations Dee.

Anyi raping ɗin wasu chocolate masu tsada acikin mazubin daya kusa tsaida numfashin Faiza.

"Allah nagode maka da baiwar ka takunna wayarnan yanzu"

Sweat voice dinsa mai daɗin saurara yafurta kalaman acikin kunnuwan Diyana bayan ta amsa sallamar da yayi.

"Wanene kai?"

"Bawan Allah"

"Bayan wannan" tafaɗi cikin son jin ƙarin bayani daga garesa.

"Ni bazazzage ne ɗaga Aishat Tafida Ardo"

"Wai kai dama ɗan wurin Goggon Zaria ne amma shine wancan karon kazo ahaka? Meyasa?!"

"Inna mana"

Dariya tayi jin yanda yafaɗi sunan. Nan suka fara hira sosai tana janshi da wasa irinna abokan wasa.

Kai yasa jama'a.....😆 Akwai wutapha🔥 atafiyar nan kawai mujame a chapter 7

Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰