CHAPTER 7
Dariya tayi jin yanda yafaɗi sunan. Nan suka fara hira sosai tana janshi da wasa irinna abokan wasa.
Kusan awanni biyu suka shafe suna waya tukun sukai sallama badon sun gajiya da junaba.
"Yanzu Faiza yazamuyi da kayannan"
Diyana ta tambayi Faiza bayan ta'ida wayar.
Faiza taɗan nisa alaman tinani daga bisani tace
"Zaki ɓoye na ɓoyewa ne, na cii mucinye muzuba ledoji a shadda, wayar kuma kita amfani da ita aboye zuwa wani lokaci muga kamun ludayinsa"
Kai Diyana tajin jina alamar tagamsu da zantukanta, taɗauki tirare da sauran kayan tasaka a siff, suka buɗe chocolate suka soma sha suna hirar soyayya da rayuwa.
♦️BAYAN WASU KWANAKI♦️
Sanye take da wata jar atamfa wanda akaima ɗinkin doguwar riga mara hargitsin kwalliya, tayafa jessy shima red, tai wani simple dauri daya hau kan kyakkyawar fuskarta dake ta glowing duk da batai kwalliyaba se lips tick ɗinda tasanya.
Ƙamshin tiraren sense mai sanyi na tashi ajikinta.
Zaune take akan kujerar dake facing ɗin Imran,kanta aƙasa tana jin saukan kalamansa kamar ruwan dalma azuciyarta.
Akace so gamo na jini to ita tata jinin kwata kwata bai haɗu dana Imran ba shiyasa batajin komai akansa.
Yanzu kuma da yazo aka tinkireta take sauraronsa jitakeyi kamar tasaka hannu aka taita ihu watakil tasami sassauci akan abinda takeji azuciyarta.
Saɓanin haka seta zauna kamar babu ita awajen, shike kiɗansa yana rawansa.
"Batun yanzuba nake sonki Diyana, zuciyata tarigada ta'illatu da soyayyarki samun kine kaɗai ze zama waraka agareta.
Idan kika zama mallakina nai miki alƙawari akan zan baki duk wani farin cikin rayuwa, zan gatan taki ki.....
"Okay Allah yabamu alkhairi agaida gida"
Maganarta da miƙewarta alokaci guda yakatse nasa maganar.
Ganin tai wucewar ta seya miƙe yabi bayanta yana kiran sunanta.
Inna na zaune a veranda kan kujerar roba taga wucewan Diyana.
Imran da besan da zaman Inna awurinba ya fito yana cewa
"Don Allah karki tafi....kitsaya muƙarika"
"Kai ina zuwa? Dakata anan wurin!"
Inna tafaɗa taname shan gaban Imran, hannu yaɗora asaman goshinsa tareda lumshe jajayen idanunshi.
"Wuce muje ciki banaso kuwwa yaji"
Kaman yanda Inna tabuƙata haka Imran yakoma ciki.
Muryan Inna atausashe tace"kabari badai kana sonta ba to kaje abinka, hankalinka yakwanta bawani wanda ya'isa ya aureta bayan kai amma ban hanaka neman soyayyan taba."
Ahankali yanumfasa kanshi aƙasa yasoma mata godiya
"Nagode da wannan karamcin agareni, ina fatan ubangiji yakaimu ga nasara akan wannan al'amarin"
Da haka sukai sallama yatafi abinshi, Inna tabi bayansa da kallo imbanda Diyana wace macene zata sami namiji irin Imran taƙishi.
Na farko dai matashine, ɗan gayu da kuɗaɗen sa, ayanzu ma sanye yakeda wata boyel milk color, hularsa milk da sirkin coffee kaɗan saboda designer bottle din rigar coffee ne babu aiki ajikinta.
Takalminsa coffee da milk mara rufi, se kamshin tirare yake metsadan gaske ko ayanzu daya fita ɗakin bedaina ƙamshiba.
Tagirgiza kai tamkar da wani mutum agabanta
"Allah ka shirya Diyana"
*
Akan kujerar Ummah Sumayya tazauna tana sauke numfashi, rantse rantsuwa kai da baka awurin zakace wani shahararren gudu tasha mai nisan gaske a tsakiyar sahara.
"Wai har kin gudo?"
"Haba namayi kokari saura kadan kunnuwana su soma zuban jini"
Atare Ummah Sumayya da Faiza suka kwashe da dariya, cikin dariyar Faiza tace
"Gaskiya Sis bakida mutunci"
"Ni ban gama aibun Imran ɗinba, ga kyau, ga ilimi, ga....
"Zanyi amai idan kika cigabada magana ahaka"
Pillown kujera taɗauka tajefa mata. Faiza taƙara kwashewa da dariya tace
"Barta Ummah dole tai haka tanada A.Maleek ahannu"
"Wayeshi" Ummah Sumayya ta tambaya.
Diyana tawaro mata manyan idanuwanta cikeda gargaɗi.
"Kinji karki kalleta gayamin"
Ummah Sumayya ta sake faɗi.
Labarin kuwa tasoma bata tana kuranta kyawu da class irinna Abdul Maleek, Ummah Sumayya na biye mata suna tsokanarta, falon yacika da dararrakunsu.
Dama kuwwa yasani aƴan kwanakin nan tazama kamar ƙawarsu, tasauke shekarunta da girmanta tazama kamarsu shiyasa suka saki jiki da ita sosai.
♠️♠️♠️
"Assalamu alaikum......wai matar ɗakin batananne"
"Muryan wani keji kamar Ƴar Shagali tawa!"
Jin an amsata yasanyata zare takalmanta tashiga ɗakin.
Goggo dake zaune tamiƙe cikin mamakin ganinta tace
"Ahh ƙawata yau kece agari"
"Ai ke dai bari kawai ƙawata"
Fridge taje taɗauko ruwa da lemu masu sanyi tahaɗo matada ƴan snacks ɗinda takanyi saboda bakin kunya irin haka.
Bayan sun gama hirar yaushe gamo Ƴar Shagali takalli Goggo cikin idanu tace da ita:
"Wai ke mutuniyar haryanzu waɗan nan ababen halittun nanan acikin gidannan tare dake?!"
Adamu wance Goggo tace"Kedai bari nayi iyayina amma wallahi haryanzu sunan atareda Ni kullum cikin fafutuka nake amma yanda kika san anaƙara manna Ni dasu,
To gwara dai ɗaya tarasu duk da anmaida madadinta, babban abin haushinma yanzu idan Alhaji yafaɗi yamutu ahuhun ma'ahu zamu ƙare"
"Bangane ahuhun ma'ahu zaku tashiba?!"
Labari tabata akan aron kuɗinda Aminat tabashi, rabon gadon da akayi da dukiyar Diyana dake hannunsa ayanzu.
Mtsss.... Ƴar Shagali taja wani dogon tsaki da faɗin"kayan takaici kinsan in labari akaban bazan yardaba wallahi danasan haryanzu kinan tare dasu dana daɗe da kawo miki ziyara.
Kinsan tunda mai gidana yawula nacala Saudiyya sai last week nasauka almost five years ina can but akwai mafita sha yanzu magani yanzu se yanda kika so da waɗannan banzayen.
Kinsan Allah har uwar mijinnan naki karki barta don tacika zaƙewa ayanda daa nasani komai zakiyi se kin sanar daita."
Baki Goggo ta taɓe tace"hmm!Kedai bari yanda kika santa daa haka take yanzu abin takaicin yanzu lalacewana yakai Inna tana gani ana cin mun mutunci bazata tankaba.
Ita kuma ƴarki Suhaima ba mijin aure yanda kika san ansanya mata hannu ataurarinta na aure gashi har ƙanninta zasui aure anma kusan tsaida rana.
Ƙawata tarin matsaloli ne dani dayawa, na rantse da sarkin dayake busamin numfashi jin zuciyata nakeyi kamar zata buga tsabar masifa."
"Kece duk kin sauya ƙawata yanda kika san ba keba koda inkaji ana ƙigudu sagudu baizo bane.
Ni Ƴar Shagali nai miki alƙawari nan da 48 hours komai zeyi clear bi ma'ana zedawo normal wannan shine babban tsara banki awurina ƙananan kuma nanan zuwa."
"Ahayye chass " suka faɗi atare suname kashewa.
"Gaskiya nagode in kikai min haka kingama mun komai arayuwa ba abinda zance sai godiya"
Goggo tai magananne taname nuna tsan tsar farin cikinta agareta.
Wasa farin girki masu karatu a sauya zama ashiryama littafin nan da kyau shimfida kawai akayi tafiya yanzu aka fara.