Makauniyar Hanya

CHAPTER 8

by @hindatuauwal

2:00am

Adai dai wannan lokaci ne wayan Goggo ye ringing.

Jikinta har yana rawa tazaro daga ƙasar pillow, ganin sunan Ƴar Shagali yasan yata ɗauka bako sallama tace

"Mutuniyar ya akayi"

Kallon Rauhan datake gabanshi tayi kafin tace

"Shegiyana ganinan awajen aikinki yanzu zan bashi se kigayamai yanda kikeso ayi miki dasu"

Dariyan jin daɗi tasaki tana tashi tazauna daga kwancen datake.

Tayi zaton zataji muryarsa wani iri dubada sunanshi amma setaji akasin hakan muryarsa normal yake magana.

"Acikin jironki(gida)akwai waɗanda bakyaso sudinga miki gardama duk abinda kikeso shi za'ayi, kinaso a mallaka miki mijinki atafin hannuki seyanda kikayi dashi, akawai ɗamarorin (aurarraki)da bakyaso aɗaurasu, akwai yarinya mai makarai (aljannu)kinaso ai maganin ta da jaririyanki (ƴarki)kinaso tai ɗamara(aure) hakane?!!"

"Eh...!Eh!!" Goggo ta'amsa tana gyaɗa kai kamar wata amaryan ƙadan garuwa.

Rauhan yacigaba daga inda yatsaya"kitashi yanzu kije tsakiyar ɗakinki zakiga wata fata aƙulle kada kiji tsoro kiɗauka kibuɗe zakiga wani rubutu kiɗauka kidafashi da ƙwayayen cikinsa inya dafu kije kihau kan masai inzaki bahaya kiɓare wannan ƙwan kinaci kina kashi,

Yanda wannan ƙwai yashige cikinki yazama kashi haka kuwwa na gidan zezama kashi awurin mijinki.

Akwai wani ɗanyen nama kada kiwanke kiɗauka kizuba acikin abinci kibama mutanen gidan duk wanda yasake yaci to seya biyu,

Zakiga wani farin tirare kiɗauka kibama ɗiyarki tashafe jikinta dashi takira duk sunan mijin da takeso aduniya ze amsa yasota.

Batun masuyin ɗamara da me makarai kizuba ido zakiga yanda zata kaya.

Amma akwai sharaɗi da Rauhanai suka bayar kada kitaɓa bari Diyana tai ɗammara idan kika bari haka yafaru duk wasu ayyuka naki zasu karye."

Batareda wani tinaniba ta amsa da"Nayarda na amince zanbi sharaɗinsu"

"Ha..ha..ha" yabushe da matsakaicin dariya yana cewa"shikenan tunda kin amince se anjima"

"mujima dayawa"Goggo tafaɗi cikin jin daɗi.

Tana sauke wayar tamiƙe tafito falo taɗauki baƙar fatan dake ajiye. da hanzari ta tashi Suhaima tai mata bayani tana ƙarewa da faɗin

"Kitabbata kyakkyawa ne ɗan gidan masu hannu da shuni mijin kece raini"

Suhaima ta amsa tai kamar yanda akace"Imran!...Imran!!...Imran!!!..."

Dagudu Goggo da tafita falo ajiye sauran kayan a fridge tashigo waɗɗakan amama kance tadubeta

"Ke wannan wani irin shashanci ne kirasa wanda zaki kira se Imran"

Suhaima ta yamutse fuska tana zuge zip ta amsata

"Eh shi nakeso amma besan inayiba bama don hakaba shiɗin saurayin Diyana ne nasan zataji zafi idan taganni atare dashi ko batai haukaba setayi ƙaninshi, tsakanin ciwon zuciya da hawan jini dole taɗauki ɗaya idan ita afuska tamareni to Ni azuciya zan mareta"

Taƙarke maganan sautin muryanta na fitowa da alwashi mai girma.

Dariyan jin daɗi Goggo tasaki itama Suhaima ta tayata suna mejin kakansu ta yanke saƙa akaro na farko nasara ta hararesu.

🔥ƘUNƘUN DIYANA🔥

Tsaye take atsakiyar gidansu, duhu da hayaƙi baƙiƙƙirin yalulluɓe gidan.

Daƙyar tasamu tahango Goggo azaune akan wata kujera ta hakimce mutanen gidan gabaɗaya suna tsaye agabanta kansu aƙasa alamar mubaya'a, da lalube tasamu taƙarisa inda suke.

"Mekefaruwa?"

Ta tambaya babu wanda yaɗago balle tasaran sunji har su bata amsa.

Dariya Goggo tasaki a izgilance ta dubeta tace

"Ai bazasu jikiba ayanzu sautin muryana kaɗai ke kai saƙo cikin ƙwaƙwalwansu.

Idan mutum yasoni, yemun biyayya da duk wani abu da nakeso to pha shima zasu sosa, su ƙaunaceshi sabanin haka to mutum zega abinda beyi tsammaniba.

Acikin biyu dole kizaɓi ɗaya kimun biyayya kisamu matsuguni acikin gidan ubanki, ki bijeremin kizama mujiya a wurinsu gabaɗaya....."

"Adda!....Adda Diyana!!.....Adda...!!!"

Afirgice tabuɗe idanunta zufa na keto mata. Takalli Faiza data tasheta daga suman zaunen da tayi bayan ta'ida sallahn athuba. takalli ɗakin seta yunƙura tazauna tana niman tsari daga sheɗan

"A'uzubillahi minash shaiɗanin rajim, allahuma ajirni feel musee batee waakliphni khairan minha."

"Adda lafiya "

"Bakomai mummunar mafarki nayi"

Kai tagyaɗa alamar tafahimta. Diyana tasauko daga gadon suka fito falo.

Inna suka gaida sannan suka wuce ɗakin Ummah Iklima sukai karin kumallo, dama inhar girkin Ummah Iklima da Ummah Sumayya ne a ɓagass ake cin abinci sedai sudan tayasu abinda ba za'a rasaba girkin Goggo ne zata zauna tabasu aikin gabaɗaya.

🔘🔘🔘

Da safe Inna na zaune tana kallon shirin gari yawaye a tv Imran yazo, gaisawa sukayi kamar yanda suka saba.

"Inna don Allah so nikeyi kisanya akiramin Suhaima"

"Uh...Uhm Suhaima ko Diyana?" Inna tai tambayar tana kallonsa.

"Suhaimar dai Inna tunda ita Diyana batasona toni banaso ai mata dole kawai zamu dai daita da Suhaima "

Baki Inna tabuɗe zatai magana sekuma tai shiru takuma buɗewa tace

"Shikenan Allah yasa haka shiyafi alkhairi"

Sanyawa tayi yarinya taje takira Suhaima dama yana shigowa Goggo tazo tagaya mata tasauya kaya tai kwalliya tamiƙe ta tafi ɗakin Inna.

Basui wani magana mai tsayiba suka dai daita, daze tafi yakarkace yaciro dubu ɗari yabata.

Dama ubanshi ba daganan ba wajen kuɗi, shima Imran ɗin atsaye yake da ƙafafunsa yana sana'arsa mai ƙarfi ta saida manyan riguna.

❇️ DIYANA ❇️

"Ummah zamu tafi"

Muryoyinsu suka fadi kalmar atare suna kallon Ummah Sumayya dake zaune.

"Tom se kun dawo amma don Allah karku kai yamma duk inda shida tayi kudawo kada Inna tai faɗa"

"Insha Allah "

Faiza ta amsa banda Diyana data maida hankalinta kan wayarta da kiran A.Maleek yashigo.

"Kada ku manta duk abinda akaci ko akashaa akawomin raguwa"

"Wannan yazama dole Ummah"

Suna dariya suka fita. kasan cewar Inna tasan aiken da Sumayya zatai musu zuwa gidan mahaifinta yasa bata tanka musuba har suka fice.

Acan bayan layin gidansu suka hango motarsa a packe yana tsaye ajikin motar.

Kallo ɗaya Diyana tai mai ta sun kuyar da kanta zuciyarta na dokawa baicin roƙon daya dingi mata tun jiya akan yanaso tai mai rakiya da ba abinda zehanata juyawa ayanzu.

Duk yanda zata misalta abinda takeji akansa babu mai fahimta.

Abdul Maleek dake tsaye yaɗora idanunsa akanta, tafiya takeyi kamar anyi mata dole tabishi, fuskarta acukule.

Yasauke numfashi ahankali yana kallon ƙerarren jikinta da akema laƙabida coca cola shape wasu suce figure eight.

Hakan yabama ɗinkinta na pitted gown damar zama daram ajikinta kamar anan aka ƙerashi.

Plate ɗin takalmine a ƙafarta onion color mai cizawa kamar yadda less ɗinta yake, dogayen yatsunta riƙeda ƙaramar jakarta mai kyau, ƙamshin tirarenta yacika kofofin hancinsa ayanzu da suka iso gabanshi.

Iska mai ƙarfi yakaɗa. Gyalen kanta yazame gabaɗaya ye kasa taɗago kanta dasauri zata kamosa ananne idanunsu suka haɗu.

Lokaci ya mutu, duniya ta tsaya cak se iskar cikinta kaɗai ke kaɗawa.

Yanayin dake cikin idanunta ya narke kamar ƙanƙara tafaɗa a wuta, karo na farko data ɗora idanuwanta acikin na wani takasa ɗaukewa, duk wani kunya nata da ƙyaliya sukai gefe suka barta da A.Maleek

Acikin ƙwayannin idanunsa akwai wani irin natsuwa, natsuwa ta mutumin da bata taɓa imagine ɗin zata iya ganin kalanshi aduniya ba, taga zallar kyawunsa da cikar haibansa sun cika mata idanu.

Shi kuma yaga yarinyar da kunya taima fuskarta kyau, yaga wani abu aƙasan idanuwanta ayanzu ba kunya bane ko fushi wani abune mai girma daya zarce kin tacensa.

Sai zuciyoyinsu suka soma dokawa da juna duk...duk...duk...🫀 ba bugun da kunne ke jiba.

Bugun da ƙirji keji. Bugun da ke cewa "na sameta" bugun da kecewa "na sameshi"

Basuyi maganaba, basu gaida junaba ko wasan da suka saba a tsakaninsu ba sai idanu.

Ido da ido. Maganar da bata bukatar kalma.

Ganin abin bana ƙarewa bane yasa Faiza yin gyaran murya mai sauti.

Sai suka farka.

Tajanye idanunta da sauri. tagyara zaman gyalenta a kafaɗarta. kunya tarufeta kamar ƙaton bargo.

Shi kuma yakauda kansa gefe yanayinta yasa murmushi bayyana a leɓensa.

Murmushi na farko cikin shekaru 29 na rayuwarsa da bai taɓayin kalan saba.

Soyayyan ayy😘

Jama'a antashi kaina yau bazan iya maganaba.

A chapter 9 zamu tattauna.

Taku akullum AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰