Makauniyar Hanya

CHAPTER 9

by @hindatuauwal

Bayan mota Faiza tashiga, Abdul-Malik na tuƙi Diyana agefensa.

"Wai ina zamuje"

Taimai tambayan akaro na ba 'adadi tun jiya dayace mata zatai mai rakiya take tambayar yaƙi yabata amsa.

A.Maleek yai murmushi yana girgiza kai"idan mukaje zaki gani"

Batada yanda zatayi hakanan tai shiru suka cigabada tafiya.

Awani sabon restaurant me kyau na Asad Eatery Food Faster ye packing.

Saukowa sukayi daga motar suna kallon yanda wurin yatsaru kamar aƙasar waje, security ɗin dake tsaye a bakin ƙofar yashiga yagaidashi ya'amsa.

Atare suka sanya ƙafarsu acikin wurin, cikeda mamaki Diyana ke kallon yanda akai decorating ɗin wurin da ballons, da candrs, dasu flowers.

Ga wani babban bana dake ɗaukeda sunanta cikin design mekyau na birthday ɗinta ayau, baicin facebook da suka turo mata message ɗin happy birthday ita tama manta shaph.

Batareda tashiryaba taji ƙwalla sun ciko mata idanu sedai wannan bana baƙin ciki bane na farinciki ne, farincikin data samu saboda A.Maleek.

"Don Allah kar hawayen nan suzubo"

Kamar jira takeyi ye magana ta lumshe idanunta hawayen suka sauko saman fuskarta.

A.Maleek yarausaya yana ƙan ƙance mata idanunshi.

Dariya tayi mai cikeda tsari, tahaɗe hannayen ta duka wuri guda alamar ban haƙuri.

Murmushi yai yana cewa"muje"

Ba musu ta taka suka shiga tsakiyar wurin, agaban wani babban table suka tsaya, idanuwan Diyana suka sauka akan cake ɗin dake ɗaukeda sunanta.

Kusadashi tamatsa sosai tana kallon cake ɗin, wuƙa yamiƙo mata takarɓa, taduƙa tahure wutar, A.Maleek da Faiza suka soma tafi suna rera mata waƙar happy birthday.

Yankowa tayi, taɗauko tabashi abaki yakarɓa sannan shima yayanko yabata takarɓa akunyace tana sun kuyarda kanta.

Tabama Faiza itama tabata cikin nishaɗi.

Sosai sukai enjoying moment ɗin a tsakaninsu.

5:00pm suka fito daga nan suka hau mota sukaje mall sukai siyayya.

Sun fitowa daga wurin zasuje packing space yaji kamar ana kallonshi se yawaiga ta inda yakejin alamun hakan.

Atsaye yake ajikin motarsa, idanunsa sanye da baƙin glass daya cinye kusan rabin fuskarsa, kasancewar sa farinfata se yahaska glass ɗin ye kyau matuƙa.

Ƙananun kayane designers masu kyau da tsada ajikinsa, yanda yai tsaye yana amsa waya bazaka taɓa cewa yana kallon wani halitta awurinba,

Wani irin kallo mai cikeda abubbuwa da dama sukai ma juna, A.Maleek yakauda kansa zuciyarsa na dokawa ta fannin daya kasa fahimta.

Sam su Diyana basu kula dashiba har suka shiga mota suka bar wurin.

Abinda A.Maleek besaniba tun sanda suka soma tafiya Arshad shima yashiga motarsa yabi bayansu.

Suna shigowa anguwar yaja burki zuciyarsa na tabbatar mai da abinda yake zargi, ganin shima A.Maleek yai packing agaba dashi kadan su Diyana sun sauko yai wani killer smile zuciyarsa na ƙara tun zurashi akan ƙudirinsa.

*UMMAH SUMAYYA*

Bayan ta idarda sallahn isha'i tafito daga ɗakinta zuwa na Baffa tunda itace yau da girki.

Sallama tadingiyi be amsaba kuma tanajin tashin dariyarsa dana Goggo.

Bude kofar tayi azafafe tashiga sedai sunayin ido hudu da Goggo dake kwance akan cinyar Baffa yana bata yogurt abaki taji duk jikinta yasaki, duk wani kwarin guiwa da ta shigo dashi yabi iska, ta tsinci kanta da sunku yarda kanta zata juya.

"Ke bakiga mutane bane zaki tafi? Meya kawoki?!"

"Ki yahakuri dama nazone na bashi abinci sakamakon nice da girki"

Wani shu'umin murmushi tayi ta kalleta sama da ƙasa tasoma mata magana cikeda iko da ƙasaita.

"Daga yau ba wacce zata kara kwana dashi bayan Ni, shiɗin mallaki nane ayanzu, naku bauta ne da kula da yara da gida kinjini?"

"Eh" ta amsa jikinta na rawa ahankali.

"Wuce kibani wuri nanma da gobe zanzo in hada meeting in gayama kuwwa matsayinsa agidannan, sakar karu kawai"

Taƙarke tana hararar bayan Sumayya don tun sanda tagama bata umarni tajuya dasauri jikinta ko ina nabari.

Wayar Baffane tasoma ringing seda yafara nuna mata kowaye tabashi izinin dauka bayan yasa a speaker.

Alhaji Usman ne mijin Shatu kanwarsa, gaisawa sukayi.

Usman yace"Yaya dama danka Arshad ne yakirani yanzun nan wai yaga ƴar wajenka Diyana yanaso in ba'ai mata mijiba."

Baffa yai shiru yana kallon Goggo don jin umarninta agaresa.

Goggo tadanyi shiru alamar tinani idan yanzu ta dakile Arshad wani zai fito amma idan ta turketa dashi sannan tasamo hanyar da zatai destroying rayuwar ta gabadaya taraba ta da gidan shikenan karshen Diyana dukiyar ta kuma yazama mallakinta itada ƴaƴanta.

Tasa hannu tadanne speaker wayar yanda can ɓangaren baze jitaba tagayamai abinda zefaɗi.

"Kace mai kabashi ita, base sunzo sun kawo kayan al'ada dana saranaba ka tsaida biki nanda wata guda"

Yanda tace yafadi hakan yayi, Usman yai ta godiya cikeda farinciki sannan suka rabu.

Washe gari da safe kamar yanda ta kudurce haka tahaɗa meeting hatta Inna seda ta halarta.

Goggo na zaune akan kujera ƙafarta daya akan daya tasoma jawabi

"Yanzu komai na gidan nan yasauya, duk wani abu da mutum zeyi dole se ya sanar dani, matan gida nayi cancelled kwana da Alhaji seni kaɗai.

kema Inna ayanzu banason wannan ikon da mulkin da kikeyi adaa ko kai kara da yada sirrikan gidannan awaje, idannaji kinje wurin wani malami niman taimako to Ni dake ne agidan nan"

"Tom bazanyi ba"

Ta amsata kanta aduƙe.

"Yafi miki"

Haka tadinga kafa sharudda masu tushe da marasa shi daga bisani ta sallami kuwwa yatafi tun kafinma sugama ficewa taima Baffa umarni yadauketa kamar baby suka shige toilet sui wanka.

Kai yasa wani capacity se masu baƙin asiri... Jama'a kunga yanda gida yaɗau saiti kuwa?

Tom yazata kaya, wani irin rayuwa iyalan Baffa zasu fuskanta.

Ga Diyana kuma agefe abinpha dayawa mujame a chapter 10

Taku akullum akoda yaushe AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰