Makauniyar Hanya

CHAPTER 10

by @hindatuauwal

Haka tadinga kafa sharudda masu tushe da marasa shi daga bisani ta sallami kuwwa yatafi tun kafinma sugama ficewa taima Baffa umarni yadauketa kamar baby suka shige toilet sui wanka.

♦️♦️♦️

"Yanzu Ummah Sumayya haka zamu zuba ido muna kallo ana mulkanmu"

Cikeda jimami da rashin sanin abinyi tace

"Baki gani bane baƙin asiri tayi shi kanshi Alhaji ba abakin komai yakeba balle mu amma mui ta addu'a shi ubangiji majirokon bayinsa ne"

"Hakane Ummah" faɗin Faiza.

Hakanan Diyana taja baki tai shiru, tanaji tana gani mafarkin da tayi yatabbata.

Itako Inna tana zuwa daki tafashe da kuka mai cin rai.

Arayuwarta gabaɗaya jin kalmar 'cin amana' kawai takeyi batareda tasan ma'anar taba, bata taɓama fahimtar me ake nufida kalmar ba se ayau dataji zuciyarta ta tarwatse asanda taɗora idanunta akan danta dake lumewa cikin kogin asiri.

Duniya batace da ita ta juya mata bayaba seda Goggo tasoma magana, abinda bata taɓa hasashen zefaru ko amafarki bane ke wanzuwa ayanzu, wacce tabama yarda da amana itace taima ɗanta bakin asiri ta maidashi bawanta, iyalanta da ma ita kanta suka zama mabiyanta.

"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un"

Tafadi cikin gunjin kuka wani irin tashin hankali na lulluɓe duniyarta kamar katon bargo.

Jin gina bayan ta tai da garun ɗakinta data shigo.

Kanta dake sarawa tadafe acikin tafukan hannayen ta jikinta na ɗaukan kyarma.

⚡⚡⚡

Da la'asar Diyana na zaune aɗaki ita kadai Suhaima tazo tana mata habaici akan Imran, tai shiru bata tankaba don intai magana ba za'a haifi ɗa mai ido ba, haka tayi tagama ta tafi abinta.

Washe gari iyayen wanda ze auri Faiza sukazo sukace yafasa, tai kuka kamar ba gobe zuciyarta kamar zata tsage.

Ba abinda yakai binne mutumin dayake da rai azuciyar masoyi, yanayine da baya misaltuwa ta kalmomi, zuciyar da ta taɓa dan danawa ne kawai zata fahimci ɗacin lamarin.

Diyana da Ummah Sumayya dama Ummah Iklima suka haɗu suka dingi bata haƙuri da kalamai har tahakura tasaki ranta bayan tamiƙa lamuranta ga ubangiji.

Bayan tsaida biki da kwanaki biyu Suhaima da Imran suka shirya suka tafi Kano hado kayan lefe saboda bikin sati hudu kawai aka sanya.

Kaya suka siyo na gani nafada, Imran yabuɗe bakin aljihu suka dinga shiga shaguna suna jidan kaya, dai dai da akwati set shida suka siya, kaya ko kamar sucii kansu, kai in ka gani se kadauka sabon kanti za'a bude.

Kasan cewar siyayyar tasu dayawa yasa dare tai musu adole sukaje hotel suka kama daki guda daya.

Be yarda sun ko zaunaba ya fita ya siyo musu abinda zasuci bai dawo ba seda yatabbatar ye sallahn magrib da isha'i.

Yashigo adai dai tafito wanka jikinta daure da towel, sam yakasa dauke idanunshi akanta.

Cikin salon i don't care takariso tamaida riganta, fuskarta ɗaukeda wani malalacin murmushi tadosana mazaunan ta adaya daga cikin karamin dining din dake ɗaukeda two chairs.

Imran da sakonta ya iske shi yai saurin cewa

"Ƙinyi sallah ko"

Dakai tai mai alamar "Eh"

Alalace sukaci gasash shiyar kaza da fresh milk, Suhaimace tafara kwanciya.

Yarage kayan jikinsa ya shiga banɗaki ye wanka, yafito yasanya kayan bacci yahau gadon bayan yasauya musu fitilla zuwa na bacci.

Jin mutum tayi abayanta, kansa yazuro ta wuyanta yana sakin mata hot kiss.

Suhaima shiru kawai tai mai tana amsar sakonninsa, tun tana yin mai kawaici har taga abinnashi yawuce misali yunƙurin kwacewa tafarayi amma takasa sabilida tamakara, hakura tayi da fizge fizge tabada kai bori yahau.

3:00am yadawo hayyacinsa, Suhaima dake manne akirjinshi kaman za'a kwace mai ita yakalla kamar ze fashe da kuka yasoma lallashinta yana bata baki

"Nasan na can canci dukkan wani hukunci da zefito daga gareki sedai inaso ki taimakeni kimin uzuri tsananin son da nake mikine yakaima nakasa rike kaina har seda muka zama daya.

Kin san dai ba halina bane kedin ma sone sanadi, duk duniya ke kadaice nake gani matsayin mace shiyasa duk wani feelings dina akanki yaƙare"

Haka yadinga lallabata har ta hakura sukaje sukai wanka, bayan sunyi sallah yaje yasiyo mata pain reliever tasha suka koma bacci.

Da suka tashi yai musu ordern abinci suka karya suka kamo hanyar gida.

Lokacin da tashigo ba kuwwa atsakar gidan se yaran da suka kwaso mata kaya.

Goggo na zaune ita da ƴar Shagali tashigo, a kujera me zaman mutum uku tazauna tana gaida Ƴar Shagali, ta amsa tana kwan zarta kayan da suka siyo.

"Gaskiya yarin yana na tayaki murna irin wadannan kaya haka se kace muna kasar waje, to amma lafiya naganki ahaka ko gajiyan ne"

Kai taɗaga alamar "Eh", tazame ta kwanta cikin dakikun da basu gaza gomaba bacci mai dadi ya kwasheta.

Goggo taɗora maganar da sukeyi asanda Suhaima tashigo.

"Ni dai ki koma aimata abinda na gayamiki shikadaine zaisa kuwwa yatsaneta kuma babu namijin da zeyima sha'awar aurenta koda kuwa akafa za'a dauramai ita to seya kwanceta ya gudu, kashin aladema se yafita daraja agunsu."

Dariyar mugun ta Ƴar Shagali tasaki"karkiji komai ƙawata me wuyan dai ki kawo kudi inda cikoma zan miki, kinsan wannan harkan iya kuɗin kine iya shagalinki"

Da jin abinda Ƴar Shagali tace se Goggo tamiƙe ta shiga uwar dakanta ₦100,000 taɗauko tabata taname ɗorawa da

"Ga wannan kije ki duk abinda ya dace nidai fatana naga aiki, ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba"

Dariyar mugun ta suka sheke dashi suna tafawa.

Masu karatu anzo wurin ga dai Goggo nan tariƙe wuta shin zatai nasara ko bazatayiba.

Suhaima an zama raguwa. Dama duk wanda yace tukunyar wani bazai tausaba nashi ko zafi bazai yiba.

Allah sarki Diyanar mu kinacan ana ƙoƙarin ruguza miki rayuwa amma ba komai Allah na tare dake.

Muhade a chapter 11 don jin yanda zata kaya.

Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰