Makauniyar Hanya

CHAPTER 11

by @hindatuauwal

Kwanci tashi asarar mai begen duniya, sati biyu kenan da Goggo taɗauka tana juya gidan.

Ƴar Shagali se faman neman Rauhan take sedai bata same shiba yashiga halwar tsafi.

Daƙyar tasamu wani sabon boka me jini ajika bejima da fara aikiba hakan yasa aikinsa ke kyau fiyeda yadda kuke zato.

Imran da Suhaima kuwa kullum suna tare duk sanda yaga dama zezo yadauketa yakaita gidan da zasu zauna yai amfani da ita. Aure ne kawai ba'a daura musuba amma sungama cinye kansu.

Inna tayi baki tarame kullum sai tayi kuka tai tirr da ƙawan centa da Hajiya Kaltume. Tamaida lamuranta ga Allah, tarungumi ibada azumi, sallahn dare da nafilfili.

Arshad tunda yasa mahaifinsa yai magana da Baffa bai kara motsiba, gidan gabaɗaya babu wanda yasan maganar auren bayan Inna itama Shatu ce tagaya mata.

Diyana ta toshe duk wani hanya da ze sadata da Baffa, zuciyarta zafi take mata aduk sanda taganshi cikin wannan hali.

Ga soyayyar A.Maleek daya gama cika mata zuciya wanda takasa gayamasa kamar yadda shima baice da ita komaiba.

*DIYANA*

Dagawan hantsi tagama aikinta na gyaran dakin Inna kwance take atsakiyar gado suna wayada A.Maleek.

"Dee yakike"

"Lafiya kalau Hamma ya budur warka"

Jin abinda tafaɗa yasan yashi bata amsa da"tanan lafiyanta kalau tamace agaida ki"

Tanajin haka tai saurin bashi amsa"gaskiya bana amsawa"

"Dee meyasa bakya amsa gaisuwar uwar gijiyanki kar dai ace kinzama ƴar black stomach"

Ashagwaɓe tace"Ni ai bada ita nakeyi ba dakai nakeyi tunda baka taɓa bani labarin taba balle nasami arzikin ganin picks ɗinta, zan amsa gaisuwar tane kawai idanna san ko wacece ita"

Murmushi yasaki yana ƙara lafewa ajikin kujerar office"ki yahakuri Dee bawai don baki isaba sedon banyi tinanin gabatar da ita ba because yanzu take tasowa she's a young lady inaso se tayi diploma agidansu alabashi tayi degree acikin gidana. Gayamin ke waye saurayinki "

Shiru tayi taname sakin sanyayyiyar ajiyar zuciya daya ratsa dukkan wani gaba na jikinshi besan time ɗin da yamaida mata da martaniba.

Muryarsa mai daɗin saurara yaji akunnu wansa"baka tsoron ayi maka snatching shifa dinyar yaro yanuna ahannunsa, ita mace ƙirjin zakice komai ƙasaitar namiji zata iya daukar ragamansa banaso kai nauyin baki inhar baka sanar da ita ba kayi kokari tasan da zamanka"

"Idan mace ƙirjin zakice na miji zakinne gabadaya duk da ban gaya mataba amma na nuna mata alamun so kinsan bahaushe yace inkaga kare na sinsinar takalmi ɗauka zeyi."

Takara kwantar da murya"kace yarinyace tayu tai tinanin inkaga kare na sinsinar takalmi beyarda dashi bane"

Yasaki dariya cikeda nishaɗi betaba jin wannan hausanba se abakinta. shiru tayi tana sauraronsa daya gama dariyar yamai maita tamata tambayar daye mata.

"Baki gayamin ba waye saurayinki?"

"Uhmmm! Gaskiya bayan zuba kabini bashi."

"Shikenan kishirya anjima zanzo da la'asar "

"Tom muhadu a inda kake tsayawa"

"Ni gida zanzo"

"Shikenan gaka ga Inna nan"

Daganan sai hirar tasu takara daukan sabon maudu'i kiran sallahn azuhur da akayi yasan yasu ajiye waya badon sun soba.

_____***_____

La'asar din nayi ta shirya tafito, addu'a takeyi akan Allah yasa ba kuwa atsakar gidan tai ko sa'a Allah ya amshi addu'ar ta.

Tana zuwa tashige motarsa dama tunda ta taho yake kallonta yana karawa cikin zuciyarsa yake cewa

"I love her with all my heart but I never found the courage to tell her"

"Barka da wannan lokaci "

"Kinyima kayan nan kyau sosai ban saniba ko wani yagaya miki kafinni"

Kamar ba kuwa seta kalli kanta bakar abayace mara hargitsin kwalliya aƙasan farar hijjabin data sanya har kasa, fuskarta babu kwalliya gabadaya se lips tick ɗinda tasanya.

Farin takalmi ne mara tudu akafarta, ƙamshin tirarenta mai sanyi na tashi ajikinta.

"Nagode da yabawa kaima kayi kyau"

Dramatically yawaro mata idnunshi tai dariya har cikin zuciyarta take nufin yai kyau kamar ko yaushe.

Musamman ma yau da yasanya shadda brown color din kin tazarce, kansa babu hula hakan yabama colly gashin fulaninsa damar jan hankalin duk wanda yai tozali dashi.

Tiraren sa mai kamshin gaske yacika motar gabadaya har yadisashe nata.

Dayike akwai sabo sosai a tsakanin su shiyasa suka saki jiki da juna sukai hira sosai.

Ƙarfe biyar nayi tai mai sallama da fatan sauka lafiya saboda gobe zai tafi Zaria.

Hannunta rikeda ledar da A.Maleek yabata tashiga gida da sallamarta. Tozali tayi da kuwwa azaune atsakar gidan, tasunna kanta kasa sum sum tasoma tafiya jikinta asanyaye.

Maganan Goggo yadakatar da ita"Ina kikaje? Agidan ubanwa kika samo wannan kayan?!""

Batareda taɗago kantaba tai shiru tana rasa abin cewa, a tsakiyar zuciyarta takejin takun Goggo zuwa gareta.

"Ke! dago kanki sa idanunki anawa kigayamin wani dan iskan kikaje wurinsa ya baki wannan kayan"

"Ni banje wurin kuwwaba"

Tafadi daƙyar jikinta na rawa ahankali. Ganin haka yasa Goggo kara matsowa kusada ita, taja baya hawaye na saukar mata.

Goggo ta fizgota da magan ganun batanci agareta takai hannu hijjab din ta dakasdin dage rigar ta tadubata.

Inbanda kuka ba abinda Diyana keyi, kalaman Goggo na dukan zuciyarta, runtse idanunta tayi lokacin da taji Goggo na kokarin dage mata riga.

Kanta ne yemugun sarawa, kowani addu'a da tasani yi takeyi, batasan lokacin da hannunta yakai wuyar Goggo tai mata juyil kadri tamanna ta abangon wurin

"Gakinan babbar karuwa, wacce tazo gidan mijinta bayan tagama tambadewa a ti-ti yarinyar da ranar da aka sanya miki rana kika zo wurin shi kina cewa yau na zama matarka zaka iya yin komai dani na zama mallakin ka,

Nayi miki karya, ko bashi yakore kiba"

Ta gwalalo idanuwanta tana kallon mutanen gidan dake ƙoƙarin ya kace Diyana ajikinta.

Masu karatu yaupha ana yinta masu abune da abunsu ko ya zata kaya tsakanin Aljannun Diyana da Goggo?!!!

Kutara a kashi nagaba wato chapter 12.

Taku akullum akoda yaushe AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰