Makauniyar Hanya

CHAPTER 12

by @hindatuauwal

Ta gwalalo idanuwanta tana kallon mutanen gidan dake ƙoƙarin ya kace Diyana ajikinta.

"Yau zamu barkine kawai saboda wani dalili namu, munai miki albishir zakiga karuwa ganin idonki "

Alokacin suka sami daman yakace ta daga jikin Goggo,

Goggo tariƙe wuyarta tana tarin wahala da azaba ga kunya jinta take duk ta muzanta a idanunsu sauƙin tama Suhaima batanan se ƙananun yaranta mata guda biyu mazan kuma yanzu bazama sukeba.

Dasauri ta wuce dakinta, Su Ummah Sumayya suka kama Diyana suka kaita dakin Inna.

Adduo'i aka dinga mata har aka samu tafar fado, a cikinsu babu wanda yagaya mata abinda ya faru duk da tambayan da ta dinga musu.

Sunyi zaton Goggo zatai wani abu idan Baffa yadawo amma se sukaji shiru har gari yawaye kuwwa ya cigabada harkokin sa.

*A.MALEEK*

Ƙarfe 4:00pm suka sauka a Zaria, mota daya suka hau da Musaddiq shiyasa suka fito atare suka jera wajen shiga falon gidan.

Zugan security ɗin Musaddiq suka tsaya daga waje.

Babban falone daya kawatu cikin wasu turkey furnitures red & sky blue, komai na falon irin wannan color din ne.

Sanyin ac da kamshin tirare yabada mood medadi da saukarka natsuwa ga ma'abocin ziyara.

Wata matashiyar budurwa dake zaune a dining room ta amsa sallamar tana tasowa cikin farin cikin ganin su.

Hannunta rikeda bowl din sanyay yiyar kayan fruits da madarar ruwa taƙarisa wajen su tana musu sanda zuwa.

"Oyo-oyo mutane na"

Sudukan su murmushi suka sakin mata.

Musaddiq yakai hannunshi bowl din dake hannunta, dasauri tajanye tana dariya.

A.Maleek yace"Kedai Mubaraka bazaki taɓa sauya halin kiba kullum mutum beda aiki se cii da rowa"

"Kai Yaya....."

"Aiba karya nayi mikiba abin takai cimma bakya kara auki kullum ga kinan kamar kazar mayu"

Fuska ta shagwaɓe zatai kuka Musaddiq yaja kumatunta yana dariya.

A.Maleek yagimtse nasa dariyar da faɗin

"Ke ina wadannan tsofaffin sukene"

"Suna babban falo Nima yanzun nan nafito"

Shi yafara gaba suka rufa mai baya, da sallama suka shiga falon Abbu da Ummu suka amsa da fara'a a fuskokinsu.

Abbu yamiƙa musu hannu sukai musa biha tukun suka durkusa har kasa suka gaida shi. Bayan ya amsa suka gaida Ummu ta amsa da farin cikin ganin jikokin ta.

Zama sukayi Mubaraka dake tsaye tace

"Bari naje nahada maka ruwa kai kuma Army inka gadama kazo kahada naka"

Taƙarke maganan tana wucewa cikin bedroom din su.

Cikin kasada awa guda sukai wanka suka shirya suka fito Mubaraka ta zuba musu abincin data hada musu.

"Assalamu alaikum"

Sukaji anfada ana zuge sliding door dinda yaraba ƙaramar falon da wannan.

Suduka suka amsa.

Arshad da Daddyn sane suka shigo fuskokinsu babu wal wala.

Arshad ye kyau cikin yellow t-shirt da black jeans wanda sukai matuƙar amsan jikinsa, mahaifinsa kuwa shaddace ash color anyi masa ɗinkin hannu.

Anatse suka karisa cikin falon, harkasa Daddy yagaida Abbu ya amsa da fara'a.

Arshad da yarigada yazauna a kujerar dake facing na Abbu yace dashi

"Inayini"

"Lafiya kalau"

Abbu ya amsa mai yaname takaicin kalan banzan tarbiyyar da suka bashi.

Wayarshi yahau sarrafa ta yana karkada ƙafansa daye crossing. Yanaji Daddy yagaida Ummu itama ta amsa afizge.

Abdul Maleek dake zaune yana ganin duk abinda ke faruwa afalon yagirgiza kanshi don besan lokacin da kan family ɗinsu ze haduba.

Daga shi har Musaddiq babu wanda ye kuskuren miƙewa da kasdin yagaidashi sakamakon sun san baya amsawa.

Daddy dake zaune kan carpet yatan kwashe ƙafafunsa ya sadda kansa kafa yaname cewa

"Dama mun zone mui wata muhimmiyar magana dakai inda hali kace da mutanen wurinan subamu wuri"

Ummu na jinsa tai mai banza tasan da ita yakeyi se su Abdul Maleek da ba lallaima suna jin abinda yake fadiba acewar ta bikin magaji baya hana na magajiya.

Abbu ye murmushin da iya karsa fatan baki

"Kada kaji komai kai maganar ka kai tsaye cikin su babu bako"

Daddy yasake sunnnarda kansa ƙasa sosai da ladabi yasoma magana

"Da farko dai zan fara da baka hakuri sakamakon na yanke hukunci batareda sanin kaba ata kaicen ta kaicewa dai yau sati biyu kenan dana nimama Arshad aure a gidan kawunsa na Saidi antsaida biki karshen wata"

Yanda yasau karda murya ye magana yasa ko Ummu bawani jinsa takeyiba seshi Abbu kaɗai da yake magana dashi.

"Yanzu kai da hankalin ka kaje kanimama wannan yaron aure agidan surikanka bayan kasan halinsa ka....

"Wani haline dani wanda baza'a bani aureba, kwata kwata baka kaunata nasan da za'a baka zabi tsakanin zuwana duniya da rashinsa zaka zabi rashin sa sedai A....."

Sauran kalaman da suke kan harshen shine suka suɓuce ye jimm wutan kansa na ɗaukewa wasu irin taurari suka gilmamai maganar da Abdul Maleek yasoma yi bayan yamaresa yasan yashi sakin murmushin da bayarda alaka da farin ciki.

"Mind your tongue Arshad nan ba gidan ku bane haka wanda kake ma magana ba sa'an kabane tazaran ka dashi kamar samane da kasa da be haifi mahaifin kaba da yanzu baka nan wurin balle har kai abinda kayi yanzu nonsense man kawai"

Shiru Daddy yayi don bayanda zeyida Abdul Maleek.

Arshad yakallesa cikin ido yace"bazan rama abinda kai min ba abinda zan maka seyafi komai ciwo arayuwarka, seka gwammaci na sami makami na kasheka da kalan kisan da naimaka with time zaka tabbatar da kalamai na"

Kamar ansa musu pause haka suka tsaya suna kallon Arshad har ya fice shida Daddy.

Acikin tarin shu'uman cin sa sun san zeyi komai kalamansa ayanzu sun haifar da wani irin tashin hankali a zukatan su suduka.

A.Maleek yashige dakinsa ranshi aɓace jikinsa na yin sanyi irinna taraddadi da jimami.

Duk wani farin ciki da suke ciki se yakau, shiru mara dadi ya mamaye gidan.

Uhmmm naceba wai me yake faruwa agidannan.

Naga dai kamar....tom kawai muhade a chapter 13

Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰🥰🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰