CHAPTER 14
"Bazan taɓa yafe musuba idan har wani abu yasameta wallahi sena rabashi da rayuwar shi wannan alkawari nane because she's my life... My hayateey......"
Haka yadinga sumbatu basufi mintoci gomaba suka iso kofar gidan, ahanzar ce yafito kaman zeyi tuntuɓe haka yashiga gidan.
Musaddiq da sauran security dinshi suka rufa mai baya.
Kukan Diyana daya karade ko ina shiya alam tamai inda take, azaune yaga Goggo da Ƴar Shagali suna hira kasa kasa, Inna da Ummah Iklima na tsaye sun jingina da garu, Faiza na maƙale ajikin ƙofar tana rera kuka.
Kaman daga sama suka ganshi.
Faiza ta taso daga kofar hawaye jage jage afuskarta, magana takeso tayi amma takasa se nuna kofa da takeyi.
Cikin zafin nama yamurda handle din kofan yajishi arufe.
Diyana taƙara sakin ƙara lokacin da yemata rumfa yana ƙoƙarin kafa bakinshi anata.
Abdul Maleek yaja baya kaɗan da iya ƙarfinshi yasa kafa yatokari kofar yabuɗe.
Dan Tsito yaɗago ahassale don ganin kowaye yashigo.
Nan kishin ƴan maza yamotsa wani dishi dishi yake ganin kato akan Dee dinsa.
Lafiyayyen hannunshi yasa yafizgo Ɗan Tsito ya hadashi da garu punch yafara sakin mai kan kace takh! yahada mai jini da majina yana nishi dai dai kamar zeshide.
Ganin yana ƙoƙarin kisa yasa Musaddiq matsawa kusa dashi"pls bro control your self kada kaje kai kisan rai"
White sexy eyes nashi da suka sauya kala suka koma red yasauke akan Ɗan Tsito yace
"Ya akayi kashigo gidan...nan"
Da hannu yanuna mai Goggo da tagama tsurewa.
Ƴar Shagali na ganin haka ta sunnar da kanta kasa kazan da kwai yafashe mata aciki tafita kuzari, sum sum taja jikinta tasoma takawa.
"Gidan ubanwa zakije...kina ƙara taku daya daganan wurin sena cire miki kafa"
Cikin karaji A.Maleek yai maganan.
Faiza da tun shigowar su tahaye saman gado wurin Diyana tana jijjigata da kukanta.
"Sister kimike! Please kitashi!!"
Diyana dake kwance hannunta maƙale asaman kirjinta tasaki wani wahalallen kuka mara sauti, baki tabuɗe daniyyan magana numfashinta yaƙage, idanuwanta suka kafe hawaye na saukar mata.
Sosai Faiza ta hau girgiza ta tana faɗin"Sis....Sis can you hear me! Please wake up....say something..."
Wani irin gunjin kuka ne yataso mata takife kanta a wide chest ɗinta tana rushewa da kuka.
Daƙyar Musaddiq ya fincike Dan Tsito daga hannun Abdul Maleek ye cilli dashi gefe daya.
Abdul Maleek yakalli Goggo da Ƴar Shagali yanuna su da yatsa yace
"Wadannan cell za'a kai min su sesun fuskanci hukunci kuzo ku kamasu"
Bekaiga rufe bakiba security ɗin Musaddiq sukayo kansu.
Dagudu suka ruga suka rukun kume Inna ganin haka yasan yata tsawatar mishi.
"Bakada hankali ne? Akan me zakasa aka masu, idan hauka kayi to kadawo hankalin ka, waima duk akan me kake wannan hankoron"
White top nashi yatube ye cilli dashi one side kaman ze daki Inna haka yamatso da fuskanshi kusada nata har suna jin hucin juna, laɓɓansa har suna kyarma wajen fadin
"Hayateey! Kin san me ake nufida hayateey rayuwata! Diyana itace rayuwata"
Ye pointing Diyana dake kwance Faiza nakan wide chest ɗinta yacigaba.
"Itace zabin raina. Banada wata wacce nakeso se ita akanta zan iya yin komai bazan la...."
Marukan da Inna tasakin mai dama da hagu shiya katse maganar da yake yi.
Zafafan hawaye suka sirnano ma Inna, murya na rawa ta nunasa da ɗan yatsa
"Bazata taɓa zama mallakin kaba har abada, nan da wasu ƴan kwanaki zata zama sirika agidanku mata awurin kaninka Arshad.
Idan itace rayuwar ka hakika rashin ta ze zama mutuwarka, wawa kawai sha sha sha"
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un "
Tafadi cikin matsanan ciyar tashin hankali, idanuwansa yarumtse biji biji yafara ganin mutanen dakin kansa yemasa nauyi wani irin duhu yagil mamai.
Hankali atashe Musaddiq da Fighter suka dauke shi sukai waje dashi.
Dan Tsito na ganin anɗauke Abdul Maleek ye ƴan sur kullenshi yaɓace batt kamar betaba wan zuwaba agun.
Inna ta maido da hankalin ta zuwa wajen su Diyana ganin halin da take ciki yasanya Inna samo ruwa ta yayyafa mata.
Nan nauyar ajiyar zuciya ta sauke, hawaye suka cigaba da saukar mata
"Inna ina yake...me kika gaya masa don Allah kice wasa kikeyi kice banji dai daiba"
"Kiya hakuri Diyana bansan yanda akayiba seda Shatu takira waya tagaya min ganin Goggo bata bani izinin yin miki magana ba shiyasa ban taɓa zancen da keba"
Tana gama fadin haka tajuya tafita. Jiki ba kwari Goggo da Ƴar Shagali suka fice.
Ummah Iklima tahayo kan gadon, Diyana taja numfashi daƙyar wasu hawaye masu zafi suka zubo mata zuciyarta na matsewa da wani irin ciwo mara misaltuwa.
*A.Maleek*
Bareak hospital suka kaishi nan da nan aka shigar dashi emergency.
Manyan likitoci suka shiga ciki. Musaddiq se faman kai kawo yake yi yana hango su ta sliding door.
Basu wani jimaba suka fito. Musaddiq yasha gabansu da tambaya.
Doctor yasaki murmushi yana bashi amsa"ka kwantar da hankalin ka insha Allah komai ze dai daita, stress ne yemai yawa and jininsa yahau but insha Allah ze dai daita"
"Thank you "
Kawai Musaddiq yace yashige ciki, azaune yagansa ya jingina bayansa da jikin gado.
Wuri yanima yazauna agefen katifar yana mishi sannu.
Abdul Maleek ye murmushin gefen baki, murya araunane yace
"Musaddiq inaso in rokeka wani abu ban saniba ko zan samu"
"Me kake so daga gareni idan har befi karfinaba nai maka alkawarin yin maka"
Faɗin Musaddiq araunane kamar ze fashe mai da kuka.
"Don Allah banaso kuwwa yasan maganan soyayyata da Diyana, nari gada nabar ma Arshad, zanyi iya kokarina wajen ganin na manta da ita.
Na tabbata rayuwar Arshad zata dawo abin burgewa aduk sanda ya mallaketa amatsayin mata.
Banida ilimin gaibu amma inada cikakken yakinin haka, ka kira likita yazo ya salla meni inada abubbuwa masu muhimmanci da yakamata nayisu"
Duk maganan da yikeyi idanuwan Musaddiq nakan shi batareda yaɗau ke suba yace
"Sadaukarwa a soyayya ba abune mai sauki ba, rasa wannan yarinyar agareka ba karamin barazana ze kawoma lafiyan kaba.
Arshad ba sonta yake yi ba, yayi amfani da itane wajen cimma burin shi na ƙunta tamaka kuma yasamu, be kamata yarinyar nan taci gaba da shan wahalaba"
"Banada wani wayau ko dabara nayi imani da matar mutum kabarinsa, ina ganin kawai mubar ƙaddara tai aikinta"
Duk yanda Musaddiq yaso shawo kansa yaki hakanan yahakura yakira likita aka sallame shi.
Jama'a kuji pha A.Maleek dai yace wai yahakura don pha dole nace wai tunda yanzu aka fara.
Tom aganin ku Diyana zata yarda adaura mata aure da Arshad kuwa.
Wani moving Goggo zatai wajen hana wannan auren.
Akwai pha talk mutanena kawai muhade a chapter 15.
Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰