Makauniyar Hanya

CHAPTER 15

by @hindatuauwal

Duk yanda Musaddiq yaso shawo kansa yaki hakanan yahakura yakira likita aka sallame shi.

*DIYANA*

Bayan kwanakin da suka wuce na mutuwar Innarta wadannan awanni 48 ɗin da suka shuɗe na zuwan Adul Maleek ne sukafi ko wasu lokuta kuna arayuwarta.

Inda tanada raguwar zuciya a kirjinta da ta hakura ta daina dialing numbern Abdul Maleek.

Faiza da tagaji se data kwace wayar rai aɓace tahau fadin

"Kiran nashi ya'isa haka na tabbata yana gani sedai inya ɗauka me zaice miki?

Adda inaso kitina Arshad ƙanin A.Maleek ne uwarsu daya cigaba da soyayya dake cutuwa ce agareku aure ƙaddara ne kuwwa yana rayuwa ne da wanda ubangiji yabashi kuka beda wani amfani awurinki.

Ki roki Allah ye miki zabin alkhairi, me saukine awurin Allah ranar bikin afasa ayida wanda kikeso"

Inda tana cikin hayyacinta ne tai maganar da ta fahimta, ita batasan haka akeji idan anrabuda masoyiba da bazata taɓa bama Faiza hakuri sa'adda nata ƙaddarar tafaɗa mataba.

Tanayin numfashine kawai don yazamar mata dole amma ba wai don tana muradin cigaba da rayuwaba.

Acikin sallolin ta kaph rokon ubangiji takeyi akan idan har batada rabon auren Abdul Maleek awannan rayuwar to yakarɓi rayuwarta tamutu tabar duniya.

Ummah Sumayya, Faiza da Ummah Iklima sun yi iya kokarin su wajen bata baki amma abanza man kare.

Duk abin Inna sedata tasauko tadingi lallashin ta itama ta juya mata kai.

Tun hawaye na fita a idanunta har sun kafe, zuciyarta ne kaɗai ke wani irin ciwo mai zafi tayadda ko motsi tayi se taji azaba kamar tafama miki.

Ga wani irin zazzaɓi da yake damunta wanda bata damu da tasha mishi maganiba.

Kamar ko da yaushe a kwanaki biyunnan, kwance take akan tsakiyar gado idanuwanta alumshe tana jan numfashi ahankali kamar me koyon hakan.

Jin da tayi anbuɗe kofa besata ta motsaba balle tanuna alamar taji.

"Kitashi kisa hijjabi muje asibiti"

Muryar Goggo dake tsaye akanta tafadi.

Yunkurawa tayi tamiƙe duk da jirin dake barazanan kayar da ita.

Hannu kawai tasa ta jawo hijjabin da take sallahn batareda tadamu da asibitin ko wani wuri zata kaitaba tabi bayanta.

Ayanzu babu wani abu da bazata iya daukaba aduniya, duk wani abu da Goggo zatai mata zebiyo bayan cutarwar da tai matane na rabata da Abdul Maleek.

Aƙofar gida sukaga motar Baffa a packe yana jiransu, kofar baya tabuɗe ta shiga.

Tun ahanya taji Baffa ya kira family doctor ɗinsu yagaya mai suna hanyar zuwa.

*

A reception suka ganshi yana tsaye yana jiransu kai tsaye ye musu jagora zuwa offfice dinsa.

Bayan tambayoyi da yamata tabashi amsa, land line yadauka yakira nurse, tana zuwa yace da ita takaita lab adauki jininta.

Tana azaune wacce tadauki jininta ta fito tana murmushi tace"gaskiya ina ganin sena riga doctor yin miki albishir amma bari inyi shiru but congratulations"

Taƙarke maganan tana mika mata farin takaddar, daƙyar ta iya dago hannun ta dayake rawa takarɓa suka juya offfice din babban likita.

Goggo kawai ta taras Baffa yafita sakamakon kiranshi da akayi awaya.

Takaddan yabuɗe yadan kalli Goggo yaname cewa

"Budur wace ko matar aure?"

"Budur wace da matsala ne?"

Goggo tafaɗa cikin halin ko inkula.

Kallonsa ya mayar gun Diyana da tambayar

"Yaushe rabonki da jinin al'ada"

Gaban tane yasake fadi, wani irin yamutsawa cikinta yayi seda ya mai maita tambayar sannan ta iya lalubo muryarta daƙyar tabashi amsa.

"Se next month nake saran ganin s...

"Wai meke faruwa ne"

Goggo ta katse ta da tambayar likita.

Miƙewa yayi yana faɗin"pls wait me"

Be jimaba yadawo, wani dan siririn abu yabata yace

"Kishiga nan bayin kidan diga min fitsarinki anan"

Amsa tayi ta shiga bayin bata jimaba ta fito tami ƙamai.

"Yarabh!"

Yafadi da wata iriyar murya da kanaji kasan akawai matsala.

"Wai don Allah meke faruwa?"

Doctor yagyara zama yana soma bayani.

"I'm sorry to say tanada ciki two month"

"Wani irin ciki"

Goggo ta tambaya cikin matsanan cin tashin hankali.

"Bansan yazan ceba amma tanada juna biyu"

Kamar wanda paralise yakama ma ƙwaƙwal wa haka Diyana tazama, taƙame tanajin wani abu na kwance wa daga cikin kanta wanda take da cikakken yakinin baze taba komawa dai dai ba.

Jitayi an fizgeta idanunta da sukai nauyi taɗaga takalli Goggo, batai maganaba haka batai kokarin kwace kanta ba se binta datayi.

Isansu mota yedai dai da isowar Baffa hannunsa dauke da manyan ledoji masu dauke da tambarin rufaida.

"Harkun fito"

Baffa ya tambaya yana kurama Goggo data hada giran sama da nakasa ido.

Bata bashi amsaba se shigewa mota da tayi,

Seda ta tattara duk wani karfi da take dashi sannan ta iya bude motan tashiga.

Tanajin Baffa yana lallashin Goggo ta yahakuri besan zasu fito da wuri bane.

Gabadaya Diyana takasa tinanin komai "Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un" kawai take iya mai mai tawa.

Se yanzu tagane ashe kuka ma arziki ne, rahama ne babba saboda zaka samu ka fitarda abinda yake ranka kasami sauki saɓanin yanzu da zuciyarta tai mata tsaye da wani irin yanayi mai wuyar fadi, macenda ta tsinci kanta acikin wannan halinne kadai zata fahimta.

Batasan kowani gaɓa na jikinta na fitarda numfashi nasa nakan saba se yanzu da taɗaga hannunta zata bude murfin motan takasa.

"Kwana zaki yine aciki"

Goggo tafaɗa kamar zata kifa mata mari,

Idan ka tambayeta yanda akayi taja kafanta zuwa cikin gida bazata iya gaya maba.

Kai tsaye dakin Inna suka shiga, tana ƙoƙarin shigewa bedroom din ta taji Goggo ta daka mata tsawa da cewa

"Munafuka zonan"

Ko kallonta bata yiba tadawo tasamu can lungun kujera ta takure.

"Kadaga waya ka kira mun duk wani yaro da ya mallaki hankalin sa yazo yanzunnan inason ganin shi"

Ba musu yaɗaga waya yakira su, tasanya Faiza takira Ummah Sumayya, Ummah Iklima da Suhaima.

Cikin mintinan da basu gaza goma sha biyar ba kuwwa yazo, dakin ye shiru babu me cewa komai sai sautin numfashin su dayake tashi.

Baffane yakatse shirun da faɗin

"Gimbiyata kince ki nason ganin kuwwa to gashi sunzo kinƙi magana"

Numfashi tasauke, tawatsa hannun ta kafin tace"Diyana nada ciki"

"Ciki?"

Matasan gidan suka hada baki wajen furta kalmar banda Inna, Baffa, Ummah Sumayya da Ummah Iklima da sukai suman zaune.

"Karya ne wallahi karya ne"

Ummah Sumayya tafaɗa cikin kidima taname takawa zuwa wurin Diyana data dunkule awuri daya tana jin inama ubangiji ze dauki ranta ta huta da wannan rayuwar da babu komai acikinta sai rudani da tashin hankali.

Tana jin Ummah Sumayya na jijjigata tana roƙonta takar yata maganar da Goggo tafaɗa.

Kaman butun butumi haka tazama, kallonta kawai takeyi.

Ummah Sumayya taja wani dogon numfashi tayanke jiki tafadi asume.

Inna tadafe kirji cikin ma wuyacin hali, dasauri sukai kanta ko kafin su san abinyi numfashinta yadauke, jikinta yasaki gabadaya.

Nan da nan suka daukesu suka fice dasu zuwa asibiti.

Cikin Faiza ne yamurda bashiri tazari buta se bayi.

Baffa yamiƙe yatako zuwa inda take zaune, akan guiwoyinsa yazube yana maganar da ta sanya hawaye sauko mata.

"Ki kasheni"

Ya fadi cikin wata busash shiyar murya hawaye suka shiga rige rigen sauko mai. Yaja hanci yace

"Don Allah ki kasheni in huta da wannan baƙin cikin da kika kunsamin, bansan laifin da nai miki arayuwaba da nacan canci wannan hukuncin.

Kila haihuwar ki da nayi ne! ko ciyarwa, ilmantarwa da tufatarwa"

Jin kalamansa agareta yasanya zuciyarta matsewa a kirjinta, ba iya jikintaba hatta jinin jikinta se daye sanyi awannan gaɓan.

Hamma Fu'ad ne ya shigo, ganin shi a wurinta yasan yashi kama shi yamiƙe.

"Na tsaneki...ba haihuwar kiba auren mahaifiyarki da nayi shine babban kuskuren da na aikata arayuwana. Allah ya...."

Sauran kalaman suka maƙale a maƙo gwaronshi sakamakon wani irin tari daya ta somai. Sosai yake yinshi daƙyar yafada mai Hamma Fu'ad ya kamashi suka fita.

Kai tahai girgiza wa"bazan iya cigaba da zama acikin gidannan ba saboda bazan iya cigaba da haɗiye bakin cikin da ake cusamin ba"

Cikeda kwarin guiwa tamiƙe. Kayanta tahaɗa dama duk wani abu da yakasance natane me muhimmanci tafito har lokacin Faiza na bayi.

Cikin ikon Allah tana fita tasamu mashin "tasha" tace yakaita.

Suna isowa tacire kudin shi tabashi motoci ne birjikk! irin wadan da suke saukan dare, masu haƙurin cikin su subari se safe su dau passengers, marasa hakuri kuma musamman wanda ba yan garinba se sunima passengers su dauki hanya.

Ta lumshe idanunta kanta ye shiru sunayen da ake ambata na amsan acikin kanta.

Laifin dadi karewa.........

Nasan kawu nanku ayanzu cike suke da tarin tambayoyi kaɗan daga cikinsu akwai:

Ina Diyana zataje........

Shin ma wai cikin jikinta na gaskiya ne ko makircin Goggo ne?

Ya makomar Soyayyan Abdul Maleek da Diyana ze kare?......

Dasauransu da sauransu......

Zaku samu duk wadannan amsan tambayoyi idan kuka cigaba da bibiyar wannan littafin na Makauniyar Hanya.

Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰