Makauniyar Hanya

CHAPTER 2

by @hindatuauwal

Kanta ne yasara, zuciyarta tai wani irin tsalle kamar zata faso allon ƙirjinta tafito, jikinta yasoma ɓari numfashinta na maƙalewa aƙirjinta.

Jitayi wani abu yariƙeta, daƙyar taiya ɗago idanunta tasauke akan fuskar Inna A'i daye sharkaph da hawaye, cikin kukanda takeyi tace

"Allah yema Adda Aminat rasuwa....."

Kukan da takeyi ne yaci ƙarfinta. Jikinta tazame daga riƙonda Inna A'i tai mata, da nauyi mai girma taɗaga ƙafafunta ta-taka zuwa wurin mahaifiyarta.

Fuskarta dake arufe tabuɗe, kallonta take komai na cikin kanta na nitsewa, duk wani abu da takeji na tsayawa cak.

Batasan me zata kira abinda takeji ayanzuba, tanada tabbacin zafin fitan raine kaɗai zai shafe wannan ciwon datakeji.

Numfashi kawai take shaƙa tana fitarwa kaman mekoyon hakan, idanuwanta tsaye ƙyam akan Inna.

Ba addu'a take mataba. Ba fata take akan ta-tashiba, roƙo take akan wani yatadata daga mummunar mafarkin datakeyi, don ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka, she can't believe mahaifiyarta ta rasu, this is unbelievable.

A kodayaushe mahaifiyarta tana tareda ita, kuma zata cigabada kasancewa tareda ita, ayanzuma mafarki takeyi dazaran tafarka komai zai yi daidai.

Goggoce taɗago labule, tai tsaye abakin ƙofar tana mai kallon Diyana tace

"Ke Diyana! In kina iyawa kitaso ki sallama da Yayan ki Muhammad, mutuwa dai ɗayane don haka kyayi kya gama kafin ke anyi dubunki."

Tana kaiwa nan tasaki labulen tai wucewar ta abinta.

Talatu ne tasauke kan Inna daga cinyarta, se alokacin taga jinin daya ɓata hijjab ɗinda ke jikinta.

Hannunta Talatu takamo, batai gardamaba ta miƙe, tafiya kawai take yi batareda tasan inda take jefa ƙafafunta ba.

Atsakiyar ɗakin Baffa suka tsaya, akwance yake shima baya numfashi, zubewa tayi akan guiwoyinta, idanunta kafe akan gawan.

Mazane suka shigo da makara, tana kallo suka dauke shi suka sanya shi aciki.

Ɗaukanshi sukayi zasu fitar dashi Diyana tamiƙe, jikinta ko ina ɓari yake, numfashinta na sarƙewa, hannu takai tariƙe annashin tana girgiza kai ahankali.

Baki tabuɗe zatai magana amma muryanta yaƙi fitowa, hannunta Baffa yazame daga annashin, Talatu ta riƙeta da dukkan ƙarfinta.

So takeyi ta ƙwace daga riƙonda tai mata amma takasa, da dukkan wani abu daye mata saura arayuwa take ƙoƙarin yin wani abu,

"Ha....ha...Hamma.....!"

Tafaɗi daƙyar, numfashinta daya sarƙe na tsayawa, wani irin duhu yagil mamata ta cikin ƙwayannin idanunta;

Sama sama take jin sautin muryan Talatu na kiranta kamin komai yafita daga kanta, komai na duniyanta na tsayawa cak!

Hankali atashe Talatu tariƙota tafaɗa jikinta, sunanta take kira da ƙarfi tana girgiza ta, hakan yasa mutanen dake tsakar gida shigowa,

Ɗaukanta sukayi suka mai data ɗakin Inna, ruwa aka samo aka yayyafamata, cikin taimakon Allah segashi tabuɗe idanunta, ahankali take kallonsu da idanuwanta da suka sauya kala, duk abinda yafaru na tsaye ƙyam akanta ba abinda yaɓace mata balle yafice akanta.

Ayanzu data ga faɗin ɗakin tayarda Inna tarasu, tayarda tazama marainiya, tayarda tarasa komai arayuwa, komai yaƙare mata, zata iya rantsuwa akan tanajin hucin nata ajalin dake tunkaro ta.

Misalin Ƙarfe 12:pm

Inna, Goggo da Baffa ne suka shigo ɗakin, sabuwar gaisuwa suka sake yi.

Inna taci gaba da cewa"Dama mun zone mui magana daku na fahimta don Allah kar aimana mugun fassara.

Wato kuwwa anan yasan yanayin da ake ciki na faɗan aƙidanci da sabuwar cutar zamani corola(coronavirus)adun hakane muke so kowacce ta tattara ta koma gidanta.

Ita dai Aminatu tarigamu gidan gaskiya, haka shima Muhammad, ba abinda suke buƙata se addu'a, shi kuma addu'an nan ko daga ina akai musu zai riskesu har zuwa makwan cinsu, wannan shine."

Baffa ya amshe da faɗin

"Mufa ba don wani abu yasa mukace hakaba se karyaje garin niman gira arasa ido, nasan mutanen mu da son zuciya se kaga anje anai mana mugun fassara."

Goggo tamiƙe tana cewa

"Su Inna Allah yahuce gajiya, inkuma za'a tsaya cin tsabane to gayinan na ɗora."

Daga haka tasakai tafice. Baffa da Inna suka rufa mata baya.

Aunty Hafsat dake maƙure jikin bango tun ɗazu tana kuka tamiƙe daƙyar jirinda ke ɗibarta na niman kifadda ita atsakiyar ɗakin.

Tarufe idanunta zuciyarta na wani irin ciwo, ciwo mai ƙarfi kaman anyan kata da wuƙa mai kaifin gaske.

Ashe ba kukan dake fita da hawaye bane ke ciwo, kukan dake maƙale a cikine ke ƙona rai da ruhi.

Jan jiki tai daƙyar wata cousin Sister ɗinta tariƙeta suka fita.

Inna A'i tamatso kusa da ita ta fuskance ta sosai cikin tattausan harshe tace

"Diyana kiyahaƙuri haka wannan rayuwar tagada yau zuma gobe maɗaci, kuwwa kaganshi da nashi haƙuri yakeyi to kema abinda zakiyi kenan.

Duniya ba ataɓa cewa haƙurin mutum yaƙare sedai ace rashin haƙurinshi, muduka kinsan inda muke duk abinda kike buƙata zaki iya zuwa kimana magana."

Talatu tace"hakane A'i amma yakamata Diyana kisama zuciyar ki haƙuri da dangana, ubangiji ya shafi zuciyar ki da imani."

Hakanan tanaji tana gani sukai mata sallama suka tafi.

Umma Iklima tashigo tadinga bata haƙuri tana lallashinta.

Acikin magan ganun da take yi Diyana taji yanda akayi ƴan faɗan aƙida suka kashe su.

"Dukkan mai rai mamacine, yau gareka ne gobe ga ɗan uwanka.

Jiya uwar haka duk muna tare da ita agidan nan, wuraren magrib ciwon ciki yakamata taita asasa tana suma shine Muhammad yakira adai daita sahu suka tafi asibiti.

Mubamu saniba ashe anata hargitsi a gambuwa, Allah ne kaɗai masanin zahirin yanda abin yafaru mudai da safe ƴan Sanda sunzo sunyi sallama da Alhaji suka bashi gawar wakin......"

Kukan da takeyine yaci ƙarfinta.

Diyana tafashe da sabon kuka zuciyarta na karyewa aƙirjinta.

✨WAI WAYE✨

*SAIDI*

Ta magaji mai kamar ran sallah: Babu shakka wannan zance haka yake, Dalili kuwa shine duk wani baƙo idan ya shiga garin Saidi, se yarantse da Allah biki akeyi.

Wannan na iya kasancewa gaskiya saboda tsaftar dake ga jama'ar garin, haka kuma gasu farare soll kamar larabawa.

Bugu da ƙari ga garin da wadatar inuwa da noma, idan kaga mutumin Saidi akwance acikin inuwa yana hutawa kai kazaci wani baƙon balarabe ne.

Ga kyau ga fara'a ga fari, kamar ataɓa su jini yafito. Hakama a wajen addini, makarantu da masallatan zamani sekace Masar.

A gaskiya Saidi sun more gari.

⭐TORANKA⭐

Talaraba mai fulanin asali: Wannan wani kirari ne da ƴan birni kanyima garin torankawa.

Bawata tababa mutanen daa dana yanzu sun amince da wannan kirari.

Dalilin da suka bayar kuwa shine; Masu ƙididdigar garuruwan da Allah ya ajiye halittar sa masu kyau adoran ƙasa sun bayyana cewa:

Garin torankawa na cikin garuruwan da ake samun kyawawa. Har don hakane mutane keta garzaya wa torankawa domin samo matan aure.

Ga wani kirari da akema garin: Ta lallaba mai fulanin asali, ga fari ga kyau mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.

Ilalla, Sanyinna, da Gudun duk garuruwane da suke maƙo taka da juna kuma kowanne acikin su akwai baiwan da Allah yemusu.

Matsalan su ɗaya shine yawan samun matsala da sukeyi a tsakanin su na faɗan aƙidanci, wasu lokutan a tsakanin Fulani da Makiyaya.

Gidan katsina wan fulani babban gidane mai ɗimbin tarihi acikin Saidi.

Abubakar Tafida Ardo shine ɗana fari da iyayensa suka haifa, se ƙaramar ƙanwarshi Aishatu daganan Allah beƙara bama Inna haihuwa ba.

Malam Tafida kuma be ƙara aureba, suka rungumi ƴaƴayensu sukai musu tarbiyya suka auraddasu daga nan Allah yemai rasuwa yabar suda mahaifiyarsu.

Ita Aishatu acan Zaria tasamu miji tai aure, yayinda shi Abubakar ya auri matarsa tafari Rahinat.

Rahinat macece mai haƙuri da kawaici, ba ruwanta da kuwwa, tana bama Inna girma a matsayinta na uwa dai dai gwargwado.

Sedai Inna irin iyayen nan ne masu son zuciya, masu kishi da matayen ƴaƴansu, duk wani abu da Abubakar zeyima Rahinat setaji haushi tai ta faɗa tana masifa.

Abinnata yaƙara tsauri ne sakamakon aminiyarta matar wanta Hajiya Kaltume dake zigata akan kar tabari a mallake mata ɗaa, karta bari ɗanta yaƙare awahala yaɗige akan mace.

Ahaka Rahinat tai ta haƙuri harta haifi ƴaƴa yenta biyu, mace ɗaya namiji ɗaya, tazo haihuwar na uku Allah yemata rasuwa.

Wannan dalilin yasanyashi ƙara aure ya auri Aminat, bazawara ce tayi aure har sau biyu, mijinta na farko rasuwa yayi har ta haifi ƴarta guda ɗaya Hafsat, na biyu kuma ƴaƴayensu biyu dashi duka maza yasaketa batareda tayimai laifin komai ba.

Kasancewar Aminat bazawara yasanya Kaltume tadinga ziga Inna seta ƙara zage damtse akan ɗanta inba hakaba a mallakeshi sedai taganshi daga nesa.

Idan ya haifi ƴaƴa ze manta da ita ya komai nashi akansu zeƙare.

Da sunan niman taimako takoya mata zuwa wurin bokaye iri-iri, Inna tamallake Abubakar tsaph, duk wani abu datace ayi shi akeyi, idan tasanya mai kara baya iya tsallakewa.....

Ku tai makeni masu karatu kuce dani natsaya anan.

Mu haɗu a chapter 3.

Nice dai taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘

🌓اءمى الطريق🌗

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰