MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 7

by @mrsisham12


MATUKAR INA RAYE
(As Long as i’m aLive)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)


Page 07

Washe gari Ummah na farkawa ta je ta tashe su su yi sallah. Da ƙyar-da-ƙyar aka samu Waheeda ta farka, nan ma sai da Ummah ta mata barazanar bulala kafin ta miƙe tana turo baki.

Bayan duk sun idar da sallah, kowa ya kama aikinsa. Waheeda tun kafin gari ya gama wayewa ta je ta yi wanke-wankenta, sannan ta yi wanka ta dawo ɗakin Ummah. Ko riga ba ta sa ba, daga ita sai skirt da underwear, ta faɗa gado sai barci. Su Ummah kuwa suna waje ana haɗa-haɗar yin koko da ƙosai da za a fita da su.

Karfe bakwai da rabi Baba Karami ya shigo gidan yana gaishe da su, sannan ya ce,

“Ku shirya, ni zan kai ku school. Ke kuma ina Waheeda?”

Ya tsare Rabi da ido.

“Tana ɗakin Ummah.”

Shiga ɗakin ya yi ya same ta ta baje tana barci har da minshari.

Siririn tsaki ya ja, sannan ya ɗaka mata mari a baya.

A gigice ta farka, za ta sa kuka. Da ta haɗa ido da shi, ta nemi kukanta ta rasa, sai ma cewa ta yi,

“Ina wuni Baba Karami.”

Bai kula ta ba, sai ma hararar da ya watsa mata.

Ummah ce ta shigo tana cewa,

“Babana, na ji ka ce kai za ka kai su makaranta yau. Fatan dai komai lafiya?”

“Ummah, kin san abin da yarinyar nan ta yi, makaranta ba za su bar ta haka nan ba. Yau da sassafen nan Principal ya kira ni, ya ce yana buƙatar in biyo Waheeda mu tafi tare.”

Jiki a sanyaye ta ce,

“To Allah Ya sa mu ji alheri. Ke kuma ki tashi ki shirya, ga can su Ikilima har sun gama sa kaya.”

Ko uffan ba ta ce ba. Ta fita ta kwashi kayan da ke kan igiya ta wuce ɗakinsu ta shirya.

Lokacin da ta fito, Ummah ta sa musu kunu da ƙosai. Suka ci, sannan suka bar gidan.


A ofishin Principal

Baba Karami da Waheeda ne zaune tare da Principal, wanda ke rubutu a kan wata farar takarda.

Bayan ya gama ne ya ɗago ya dubi Baba Karami.

“Na ji daɗin ganinka Malam Sadam.

Wato abin da yake faruwa shi ne, tun safiyar jiya na buƙaci ganinka bayan na fito daga ajin su S. Baffah.

Na fito daga ajin ne cikin matuƙar alfahari da ita. Har na ji tamkar in tura wa iyayenta katin gayyata zuwa ofishina nan take.

Na san ba ni kaɗai ba, har ku ma kuna yi mata kallon dagigiya wacce sam ba ta gane komai a fannin karatun boko. Amma ba haka abin yake ba.

S. Baffah ta kasance ɗaya daga cikin yaran da Allah Ya ba baiwa amma suke ɓoye ta. Sun fi son a dinga musu kallon raunana ta ɓangaren karatu, kuma hakan yana sa su farin ciki. Akwai yara da yawa masu irin wannan mentality ɗin.

Jiya na shiga ajinsu a lokacin da malaminsu ya matsa mata sai ta karanta abin da ya gama karantawa.

Amma ga mamakinmu, sai ga S. Baffah ta karanta duk wasu abubuwan da ya karantar da su a baya, har ma da waɗanda bai karantar da su ba.”

Ya ja numfashi ya dakata, yana duban fuskar Baba Karami, wanda mamaki ya kashe shi a zaune.

Principal ya saki murmushi domin ya hango zallar mamaki shimfiɗe a fuskar Baba Karami.

“Ka yi mamaki ko?”

“Kwarai kuwa na yi mamaki, Principal.”

Baba Karami ya faɗa yana duban Waheeda. Ita kuwa sai wurga ido take yi.

Principal ya ci gaba da cewa,

“Irin mamakin da ka yi, mu ma shi muka yi.

S. Baffah, ƙwaƙwalwarta ta zarce ta ɗalibar JSS 1. A maimakon haka, ta kai matakin SS 1.

Wannan dama shi ne dalilin da ya sa nake son ganinka jiya.

Dalilin son ganinka a yau kuma shi ne laifin da ta aikata jiya, inda hukumar makaranta ta yanke hukuncin dakatar da ita na tsawon sati biyu.

Ga suspension letter ɗinta.”

Ya miƙa masa wasiƙar da ke cikin envelope.

Baba Karami ya karɓa yana cewa,

“Mun gode sosai Principal. Na san da a wata makaranta ce, da an kore ta saboda ta’asar da ta tayar jiya.”

Principal ya jinjina kai.

“Ba komai.

Idan hutunta ya ƙare, idan za ta dawo, a yi mata shirin fara rubuta jarabawa tare da ɗaliban JSS 3.”

Sai da ya miƙe tsaye ya sanya letter ɗin a aljihunsa sannan ya ce,

“In sha Allah.”

Gida suka koma shi da ita. Ya kira Ummah ɗaki ya sanar mata da duk yadda suka yi da Principal.

Girgiza kai kawai ta yi ta ce,

“Allah Ya sa haka shi ne mafi alheri.”

“Tunda haka ta zaɓa, sai ta haɗe da Salma su dinga talla har ta cinye wa’adin da aka ɗiba mata.”

Waheeda da ke zaune a bakin ƙofar waje tana saurarensu ce farin ciki ya lulluɓeta sa’ilin da ta ji za ta fara talla tare da Salma. Daɗi kamar zai hallaka ta. Finally, burinta ya cika.


Stanford University, California, USA 🇺🇸

Babban filin wasan ƙwallon ƙafa da ke tsakiyar jami’ar ya cika maƙil da ɗalibai zaune a kan manyan kujerun kallon wasa. Kowa ya maida hankalinsa kan wasan da ake bugawa tsakanin zakakuran ƙungiyoyi biyu, Campus Lions da Rising Stars.

A tsakiyar fili, ’yan wasan suna buga ƙwallo cikin kuzari da ƙwarewa. Kowane ɗan wasa burinsa shi ne ya zura ƙwallo a raga. Daga yadda suke taka leda kaɗai, mutum zai fahimci ƙwararrun ’yan wasa ne aka tara. Akwai fararen fata da baƙaƙen fata, kuma kowannensu sanye yake da jersey na ƙungiyarsa.

Ɗan wasan Campus Lions ya karɓi ƙwallon cikin nutsuwa, ya ɗaga kai ya yi nan ya hango Number 9, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi wani pass mai tsantsi. Ƙwallon ta ratsa tsakanin ‘yan wasan abokan hamayya tamkar an shimfiɗa mata hanya. Ba ta tsaya ko’ina ba sai a ƙafafun Number 9, ba tare da wata tangarɗa ba.

Lamba tara bai ɓata lokaci ba. Cike da ƙwarewa da azama ya karɓi ƙwallon da ƙafarsa, yana kauce wa mai tsaron baya. Sannan cikin salo da fasaharsa ya yi wani harbi mai ƙarfi. Ƙwallon ta tashi sama, ta ɗan karkata kaɗan, ta wuce hannun goalkeeper, sannan ta sauka cikin raga da wani irin armashi.

Nan take filin ya kaure da ihun murna. Sauran ɗaliban da ke zaune suka miƙe tsaye suna tafi da kururuwa, suna ta ambaton sunan lamba tara da ya zura ƙwallon.

“BK! BK! BK!”

Shi ne kaɗai abin da ake ta ihu ana faɗa, yayin da sauran ’yan wasan Campus Lions suka ruga gare shi suka rungume shi, suka ɗaga shi sama cikin murna.

A jikin scoreboard, inda sunayen ƙungiyoyin biyu da sakamakon wasan suke bayyana, an nuna cewa Campus Lions na doke Rising Stars da ci 5–0.

Bayan sun sauke shi ƙasa, ya juya yana mai gyara jersey ɗinsa. Amma hakan bai rage hayaniyar da ke tashi ba. Wani irin ihu da kururuwa suka ci gaba da yi suna kiran sunansa.

“BK! BK! BK!”

Kururuwar da suke yi ce ta sa ya juya ya kalle su.

Subhanallah… Allah Ya yi halitta.

Tsananin kyawunsa ne ya sa ‘yan matan jami’ar suke da crush a kansa. Ya haɗu ta kowace fuska fiye da yadda mutum zai yi zato. Duk da haka, fuskarsa babu alamar murmushi ko kaɗan.

Ya ɗauke kai daga gare su cikin halin ko-in-kula.

Ya karɓi bottle ɗin ruwa, ya balle murfinsa, sannan ya kai bakin kwalbar bakinsa ya fara sha a hankali.

Sai dai duk da hakan, ‘yan matan jami’ar ba su daina ba. Har zuwa ƙarshen wasan suna ci gaba da ambaton sunansa cikin tsananin ɗoki.

A wajen zaman ɗalibai, wata matashiya ’yar Najeriya ta dubi kawarta ta furta,

“Dinah, wannan balaraben da ake ta kiran sunansa, shi ɗin waye haka? Na ga kowa ya san shi. Kai na ya kulle. Duk wannan ihu saboda mutum ɗaya?”

Murmushi wacce aka kira Dinah ta yi, ta sake kurawa BK da ke fili ido tana taunar cingam, ta ce,

“Hmmm… BK suna ne da ya samu sakamakon ƙwarewarsa ta musamman wajen jefa ƙwallo a raga tun yana ƙarami. BK na nufin Best Kicker. Shi ne tauraron ƙungiyar Campus Lions, domin shi ne yake sa su yin nasara a kusan kowane wasa. Yana 400 Level.”

“Wow! Gaskiya ya haɗu. Har na ji ya burge ni. Yau ne karo na farko da na gan shi a cikin makarantar nan.”

Dinah ta ce,

“Saboda ke sabuwar ɗaliba ce. Amma kusan duk wani ɗalibi a jami’ar nan ya san waye Muhammad BK, ɗan Najeriya da ba kasafai ake iya bambance shi da ’yan ƙasashen waje ba.”

Zaro ido ta yi.

“Wai kina nufin ki ce min wannan haɗaɗɗen gayen ɗan ƙasarmu ne?”

“Ba ki yi tsammanin haka ba ko?”

Sosai ta yi mamaki, domin har ga Allah ko kusa bai yi kama da wanda ya haɗa ko da dangantaka da Najeriya ba.

Ganin ya nufi hanyar fita daga filin wasa shi da wani daga cikin ’yan wasan ne ya sa Dinah ta ɗauki Stanley Cup ɗinta da hanzari ta rufa musu baya, ta bar kawarta cikin zurfin tunani.

Da ta yi nasarar isowa gabansu, ta tsaya tana gyara dogon gashin dokin  kanta, ta ja numfashi domin ta nutsu, sannan ta ɗan gyara murya.

“Hi, BK.”

Su biyun suka juyo.

Da ganin ita ne ya sake murtuƙe fuska. Ya haɗe gira ya watsa mata idanunsa masu firgitarwa, ba tare da ya amsa gaisuwarta ba.

Ganin duk su biyun sun yi mata banza, babu wanda ya ce mata komai, sai kallon da suka watsa mata ne ya sa ta sha jinin jikinta.

A daburce ta miƙa masa Stanley Cup ɗin tare da cewa,

“Wasanka na yau ya yi kyau kamar yadda aka saba. You’re the best player I’ve ever seen in my life.”

Har yanzu idanunsa na kanta. Bai ɗauke su ba.

Hakan ya ƙara rikita ta, domin ta kasa gane ma’anar kallon nasa.

Muhammad BK yana da irin fuskar da ba kasafai take bayyana abin da yake ji ba.

Idan kana kallonsa, za ka ga wata nutsuwa mai sanyi a cikin idanunsa, kamar mutumin da babu wani abu da zai iya girgiza shi.

Fuskarsa kullum tana ɗauke da wani irin cold expression,ba yawan murmushi yake yi ba, haka kuma ba kasafai ake ganin fushi a tare da shi ba. Kawai wani irin nonchalant look ne da ke sa mutane su kasa gano abin da yake tunani.

Idan ya kalli mutum, kallon nasa ba ya tare da hayaniya, amma yana da nauyi.
Lips ɗinsa kan kasance a ɗan matse, yayin da girarsa ke ɗan haɗuwa kaɗan, abin da ke ƙara masa mysterious aura.

A hankali ya motsa lips ɗinsa, sannan cikin sanyin murya ya furta…


“I know.”

Wani irin nauyin muryarsa ta ji ya sauka a kunnenta. Duk da a taushashe ya yi maganar, sai da ta ji tsikar jikinta ta tashi. Ta kame kanta tare da sakin murmushin basarwa. Za ta yi magana kenan sai ta ga ya juya ya ci gaba da tafiyarsa cikin nutsuwa.

Ta dubi wanda suke tare.

“Zannor, please me ya sa ɗan uwanka baya sona? Shin ba ni da kyau ne, ko kuma akwai abin da na rasa? Ina da duk abin da ake buƙata a tattare da mace. Bugu da ƙari, daga babban gida na fito. Why am I so invisible to him, Zannor?”

Sai da Zannor ya bi BK da kallo kafin ya dawo da idanunsa kanta.

“In ba ki shawarar da za ta amfani rayuwarki, yarinya? Stay away from BK. Ɗan uwana mutum ne mara son hayaniya kuma mai kyakkyawar zuciya ne, so you’d better not piss him off. Zai iya tsananki a banza. A yanzu shawara kawai nake ba ki. Kar ki bari a karo na biyu in sake yi miki warning, domin ba za ki so hakan ba.”

Yana gama faɗin haka ya zura hannunsa cikin aljihu ya bi bayan BK.

Ta kasa motsawa daga inda take. Ji take kamar ta zube a ƙasa ta sanya ihu, amma ta haɗiye hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata, gudun kada wani ya ganta a wannan hali.

Da sauri Zannor ya cim masa.

“Shi ne za ka tafi ka bar ni ko?”

BK ya watsa masa kallo ɗaya kawai, bai ce komai ba. Haka suka ci gaba da tafiya har suka shiga library suka zauna. Ya fitar da wayarsa ya fara dannawa, yayin da Zannor yake karatu.

Bayan ɗan lokaci Zannor ya ajiye littafinsa ya dubesa.

“BK, za mu shiga exam nan da thirty minutes, amma sam ban ga alamar kana da niyyar karatu ba.”

Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce,

“That doesn’t concern you.”

Tun farko Zannor ya san amsar ba za ta wuce haka ba. Ya girgiza kai sannan ya sake cewa,

“Amma ka san yadda wannan semester yake da muhimmanci…”

“Zannor.”

BK ya katse shi ta hanyar kiran sunansa.

“Can you please let me be?”

Kai Zannor ya gyada masa, ya ɗauki littafinsa ya ci gaba da karatu.

Kira ne ya shigo wayarsa. Picking ya yi ya kara a kunne.

Yana waya, amma duk hankalinsa na kan BK da ke ci gaba da danna wayarsa. Siririyar iska ya furzar sannan ya ce,

“Yes, Mamie. Muna tare. In sha Allah zan sanar da shi.”

Bayan ya gama wayar ne ya dubi BK.

“Mamie ta ce mu yi booking flight da zarar mun kammala exams ɗin yau.”

Tun da suka zauna sai yanzu BK ya dakatar da danna wayar da yake yi. Ya ɗago ya kalle shi da cold expression ɗinsa kafin ya furta,

“Ta yaya ta san yau za mu gama exam?”

Zannor ya ɗan sosa kai.

“Ni ma na yi mamakin hakan. Ta yaya aka yi ta sani?”

BK ya kafe shi da ido yana karantar yanayinsa, domin ya san Zannor fite da yanda ya san kansa.

Da wannan calm voice ɗinsa ya ce,

“Don’t you dare lie to me, Zannor.”

Sosa kai Zannor ya yi, ganin ya gano shi. Babu abin da zai iya ɓoye masa.

“I’m sorry, bro. Laifi na ne. Zanaya na sanar wa. Ban san maganar za ta kai kunnen Mamie ba.”

BK ya lumshe idanunsa yana jin nauyin da ke cikin zuciyarsa ya sake ninkuwa fiye da yadda yake ji a baya. Ya ɗauki wayarsa ya fita daga library.

Zannor ya dafe goshinsa, yana dana sanin sanar wa Zanaya batun gama jarabawarsu a yau. Ga shi ya ɓata ran BK. Wani irin tausayinsa ne ya lullube shi, tare da jin haushin kansa.


Da suka fito daga exam, babu inda Zannor bai duba ba ko zai ga BK, amma babu shi. Hakan ya sa ya hau motarsa ya nufi apartment ɗinsu.

A bedroom ɗinsa ya same shi ya gama shirya duk wasu abubuwan da yake buƙata. Yana jingine a gaban window, ya zuba wa harabar apartment idanu, hannayensa zube cikin aljihunsa.

Jiki a sanyaye Zannor ya dafa kafaɗarsa.

“Ka yafe min, ɗan uwa. Ban sanar da niyyar cutar da kai ba. Na san ba ka son komawa, zan nema mana wata hanyar da za mu ƙara lokaci a nan.”

Ba tare da ya juyo ba BK ya ce,

“Na yi booking flight. Karfe takwas da rabi jirginmu zai tashi. Sannan bana son ka sa damuwar komai a ranka.”

Zannor kallonsa kawai yake yi ba tare da ko kyaftawa ba. Ya rasa yaushe BK zai sauya, ya daina binne damuwarsa a ransa, ya dinga fitar da abin da yake ji kamar kowa.

BK mutum ne da ko za ka yi shekara ɗari tare da shi, ba za ka taɓa gano a wane yanayi yake ba. Ba za ka iya karanta expressions ɗinsa ba. Ba za ka gane farin cikinsa ba, haka kuma ba za ka gane bakin cikinsa ba. Bugu da ƙari, ba za ka taɓa gano abin da yake tsoro ba. Haka yake tun yana yaro, kuma wannan ne ya sa mutane da yawa ba sa iya fahimtar inda ya dosa a rayuwa.

Sanin cewa ko zai shekara yana magana a kan dakatar da komawarsu Nigeria, BK ba zai sauya shawara ba, ya sa Zannor ya haƙura. Shi ma ya shiga ɗakinsa ya soma haɗa kayansa.